Page 39/40
A hankali ya kashe motar yana zare keys din hadi da bude kofar ya fita. Bangaren da nake ya zo ya bude yana kallona, ya mika min hannunshi wai in kama; yi na yi tamkar ban gan shi ba na fito ina karewa kayataccen wajen kallo.
"Yanzu a nan zan yi aikin kenan?" Na tambayi kaina ina bin bayanshi a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Babban gida ne da ya kayatu da ni'imomin duniya, ko dan ban saba ganin ire-iren gidajen bane? Ban ji motsin kowa ba a palon kasan, na dai ga kafar bene dake nuna akwai sama kenan, amma ta karkashin benen ya bi yana kuma nuna min hanzari da hannunshi. Bin shi kawai nake a zatona zai sadani da bangaren matar gidanne, shiyasa na zage nake binshi a baya.
Cikin wani kayataccen palo marar tarkace muka bayyana. Idanuna suka sauka a kan jerin tabka-tabkan hotunanshi kala-kala dake palon, ga kuma shelf mai cike da awards awards da ya samu a wasanni mabambanta da ya halarta. "Dan kwallo ne kenan," na fada a raina.
Daya daga kujerun palon ya nuna min. Hada idanu mukayi na yi saurin kawar da nawa idanun, zuciyata na bugawa da gaske; idonshi suna bani tsoro, kamar mage nake gani har da walkiyar cikinsu. Da sauri na kai zaune, shi kuma ya tabe baki ya wuce daya daga cikin kofofin da ke manne da palon.
Ya jima sosai a ciki har na fara sarewa, dan ma TVn dake kunne yana ta babatun da ban mai da hankali ba kasancewar tashar ball ake nunawa. Na ji an murda handle din ya fito. Wani irin zabura na yi na mike ina dafe kirjina da na ji ya yi wani irin rawa kamar zai tsinke. Rumtse idanu na yi, labbana masu kauri suna karkarwa na ce, "Allahumma ajjirni fi musibati, wa akhlifni khairan minha."
Tunda nake a tsawon rayuwata ban taba ganin abun da nake gani yanzu a gabana ba. Jikina na ci gaba da rawa, hakan ya baiwa halittata damar girgiza kamar da gangan nake yi; yanayin da ya kara yamutsa jinin jikin Jack kenan, ya ji kawai komai ta fanjama-fanjam.
Coffee da ya fito dashi sai tururi yake, ya ajiye a kan center table ya fara nufo ni. Idanuna a rufe, kusan suman tsaye na yi a wajen kamar an dasa ni; kafafuna sun yi nauyi na kasa motsasu. Duk takun da yake yi har cikin kwakwalwata nake ji. A hankali na fara jin saukar numfashinsa dai-dai fuskata, hakan yasa na yi hanzarin bude idanun, amma abun da na kara yin arba dashi ya sani kwala wani uban ihun da ya sanya Jack daura hannayenshi duka biyu saman kunnenshi domin basu kariya daga barazanar balle masasu da ihun ke yi.
Baya-baya na fara yi, ya fara biyoni dan bai san meke faruwa ba. Ya saba mu'amala da matan turawa masu kawo mishi kansu ma ba sai ya nema ba, shiyasa abun da take yi din ya ba shi mamaki. A hankali nake baya yana biyoni, still idanuna a rufe. I assured idan na kara ganin wannan girmansu, babu abun da zai hanani makancewa.
"Hey girl, open your eyes," ya fada da saukakakken turanci, hakan ya sa na ji abun da ya fada. Kara tamke idanuna na yi gam, jikina na ci gaba da rawa kamar mazari, sai karanta duk addu'at da ta zo bakina nake yi. Maimaita abun da ya fada ya kuma yi dan ya fara kaiwa makura, kawai controlling kanshi yake.
Na hada hannu biyu, hawaye na bin kuncina na ce cikin turancina irin na 'yan koyo, "Dan girman Allah ka suturta jikinka, na rokeka ka suturta jikinka, wayyo Allah ka kawo min dauki."
Sakato Jack ya yi cike da mamaki dan sarai ya fahimci abun da ta fada da yadda take rufe ido, hakan ya sa shi yin murmushin gefen baki; dama Mummy ta fada mishi sabuwace, so dole ya bi a hankali. Murmushin ya kuma yi tuna wani abu. Hannunshi ya miko ya dago habata dasu. Wani irin zafi na ji tamkar an zuba min ruwan zafi a jikina, yayinda Jack kuma ya ji wani irin shocking ya ziyarceshi. Da sauri ya janye hannun.
Ihu na yi yunkurin kurmawa a karo na biyu, ya yi nasarar danne bakin da tafin hannunshi; bai bani wani dama ba ya dagani cidak kamar 'yar baby, ya wuce dakin da ya fito!
Ihu nake iya karfina, idanuna suna gwalalowa waje amma bakin a rufe. Wani irin zafi nake ji a cikin jikina ina rokonshi ya taimaka ya sakeni, amma ina, ya yi nisa! Har dai ya samu nasarar jefa ni bisa shirgegen gadon da ke dakin. Ji na yi duk jikina ya dauki kaikayi, tunawa da na yi wannan gadon kazantace, gashi ina kwance bisa kuma ana kokarin keta min haddi. Zafi nake ji a kirjina tamkar zan hadiyi zuciya in mutu.
Duk da haka ban daina yunkurin kwatar kaina ba, amma kasancewar karfinmu ba daya ba, tuni ya ci karfina. Bayan ya hada hannayena duka biyu ya lankwasasu ta baya, ina jin sanda suka yi wani kara katt. Radadin azaba ya ziyarceni, daga lokacin na fara ganin dishi-dishi, na kasa yunkurin kwatar kaina, na kasa motsawa, yayinda na fara hangoshi yana tunkaroni girmanshi yana rinjayarshi. "Tabbas Uwa zata ga sakayya tun a duniya," wani bangare na zuciyata ta ambata.
Da hanzari na kauda tunanin na fara karanto addu'ar neman tsari daga shaidanun cikin mutane da malaman islamiyyarmu suka koya mana, kana Maahh ta jajirce sai da na haddace. A dai-dai lokacin da Jack ya fara nisa yana kokarin rabani da mutunci da kima ta ta diya mace, wasu hawaye masu dan banzan zafi ne suka ci gaba da kwaranya daga idanuna. "Ya Rabbal'alameen, ka samar min mafita irin mafitar da kake bawa salihan bayinka, ka kareni ka karemin maraicina." Na fada a dai-dai lokacin da Jack ya kwada wani uban karar da ya gigitani, ya fara amsa kuwwa a illahirin gidan.
Mom nashi da ke zaune da Elisha kwance saman kafarta tana combing mata gashinta—idan kaga yarinyar sam ba zaka ce budurwace ba tsabar kankantar jikinta yadda rashin lafiya ya maida ita—duk sun ji ihun. A rikice Mom ta mike tana fadin, "Son!" Sai kuma ta ciccibi Lisha hadi da daurata saman kekenta dan bata iya tafiya, ta fara gurgura keken zuwa bangaren Jack.
Bubbuga kofar take kamar zata ballashi tana ambaton, "Jack, Son, Jack!"
A lokacin shi kuma yana rike da girmanshi da ta koma ta yi lakwam tamkar lagwani. Ba karamin tashi hankalinshi ya yi ba; bai taba ganin abu makamancin haka ba duk yawan neme-nemen matan da yayi a rayuwarshi, hakan ba karamin tsoro ya ba shi ba har ya buga ihu bai sani ba. Jin kofar tana barazanar ballewa ga muryar Mom da ke kiranshi da kuma kukan Elisha da yake ji har cikin kanshi ya sa shi nufar kofar. Har zai bude ya tuna babu kaya jikinshi, dan haka ya juyo. Bathrobe nashi ya gani a kasa, shigarshi dazu ya yi wanka ya fito dashi, ko da ya cire nan kan gado ya ijiye ya fita palo a haka.
Bathrobe din ya daura kana ya fito duk ya wani yi laushi kamar ba shi ba. Da sauri Mom ta karaso tana kamashi da tattaba jikinsa. "Son, me yake faruwa? Mene ne a dakin? Me ya sameka?" Jerin gwanon tambayoyin da take jefa mashi kenan.
Dan sunkiyowa yayi saboda ya fita tsaho sosai, ya daura kanshi saman kafadarta. Da kyar ya motsa pink labbansa, "Nothing Mom, faduwa na yi a toilet." Karon farko kenan a rayuwa da Jack ya yi wa Uwar tashi karya; baya boye mata komai, ta kai ta kawo a gabanta ma yana iya duk abun da ya ga dama da mace, sai idan ita ta bar musu wajen. Rikicewa ta yi sosai tana tattara gashin da ke kime a kanshi duk ya watse saboda yakin duniya na uku da ya tunkara. "Son, baka ji ciwo ba? Bari in kira likita, ina ke maka ciwo yanzu?"
Sakinta ya yi yana durkusawa jikin Elisha ya bata peck a goshi, "Stop crying little love, kawai faduwa na yi kuma kinga na tashi ko?"
Gyada kai ta yi ta ce, "Bro love, ka dinga kulawa." Yana share mata hawaye ya ce, "To."
A hargitse Jack ya mike ya kamo Mom tashi dake kokarin shiga dakinshi. Haka kawai yau ya samu kanshi da rashin son taga yarinyar da ke dakin. "Zan kira Dr da wayarka ya zo ya duba ka ko?"
"No Mom, zuwa safe zan je da kaina." Da kyar yayi convincing Mom ta tafi, ya koma dakin yana murza key.
Ina kwance har lokacin bana iya ko motsa jikina, sai harshena da zuciyata da ke yi wa Ubangijina kirari dan nuna godiyata a gareshi. Ya dade tsaye yana kallona kafin ya kada kai ya wuce bayi. Sosai ya yi wanka da ruwan dumi ya fito. Firij dake dakin ya bude ya dauko energy drink ya balle hancin ya kafa a bakinshi; bai sauke ba sai da ya shanye shi tas, ya jefa can din cikin wastebin da ke bakin kofa. Jijjiga ya yi mai kyau take ya kara daukar harami, ya koma gadan-gadan ga Fannah yana ayyana sai ya ga abun da ya ture wa buzu nadi. Still lakwam ya kuma zama. Wannan karon gigicewarshi ya fi na farko, dan ba karamar rudani ya shiga ba. A wannan dare dai Jack ya je ga Fannah sai hudu amma abun ya ci tura. Daga karshe palo ya koma bayan ya rufe kofar ta waje, ya zare makulli yana tunanin da sassafe gobe zai je wajen Mummy ta fada mashi dalilinta na hadashi da ghost, dan bai yarda cewa Fannah mutumce ba la'akari da komai nata daban ne da na mutane.
Washegari karfe sha daya da rabi na safiya muka dira gidan Mummy, ina bin shi a baya da kyar nake iya daga kafata. Idanuna sun yi luhu-luhu kamar puff puff, jikina ya yi tsami tun sallar. Jack bai fita da wuri bane har sai da Mom ta fita wajen aikinta, Elisha kuwa na tare da mai kula da ita, sannan ya damko Fannah suka fito.
Da fara'a Mummy ta tareshi, amma ganin yadda ya murtuke fuska ya sa ta shan jinin jikinta. Ni dai ina tsaye daga gefe sai rarraba idanu nake yi kamar kace kyat in arce. Ba na jin me yake fada dan da irin pure turancinsa suke magana; ko ma dai mene ne na san fada yake yi, ita pula sai aikin lallabashi take yi. Kusan minti goma sannan ya bar gidan.
Wani irin harara ta jefo min sannan ta ce, "Kin yi wa kanki ai sakarya kawai. Sai mu ga waye ne zai zuba makudan kudi irin haka a kanki bayan shi din. Wuce ciki ki jirani, ina nan tafe."
Kamar jira nake fiitt na wuce inda masaukinmu yake. Sauran 'yan matan duk ba sa nan, hakan na nufin suma sun wuce gidajen aikinsu kenan. Nawwara na tuna, "(poor girl)" na fada a zahiri. Samun kaina na yi da addu'ar Allah ya sa ba irin abun da na tarar zasu tarar ba, Allah ya sa ni dince kawai ban yi sa'a ba. Wanka na shiga na dinga dirzar jikina tamkar zan cire fatar ne; duk na tuna abun da ya faru jiya sai in ji jikina ya dauki kaikayi. Sosai na yi wanka hadi da dauro alwala, ko mai ban shafa ba na sanya hijabi na fara ramakon sallar asubahi. Na dinga istigfari ina neman yafiyar Ubangiji; a can din kasa yin sallar na yi gaba daya gidan kyama ya bani, to in yi sallah in ce na yi me?
Ina nan zaune Mummy ta shigo. Hararar da take watsa min ya sani sunne kai da wuri. "Idan kin ga dama ki tashi ki yi breakfast, sannan ki zauna da shirin cewa anjuma da dare zaki kuma fita, kuma duk wanda ya zo damka ka zanyi a hannunsa tunda bakisan arziki ba. And let me make it clear for you, abun da ya faru jiya dake shi ne ainahin dalilin shigowarki turai, shi ne neman kudin da iyayenki suka turoki so ki zama cikin shiri."
Daga haka ta fita ta bar min dakin. Ina nan zaune abun duniya sun hade min har na rasa kalar tunanin da zan yi. Kwanon da ta shigo da shi na janyo na fara cin abincin a hankali, ina jin daci a makoshi na amma haka nake daurewa ina ci dan dai kar in mutu. Bayan na gama na fitar da kwanon na dawo. Rasa abun da zan yi ya sa ni fara tattara dakin na karkade duk da ba wai datti ya yi ba, na koma ina zama jugum na fara tilawar Qur'ani a raina tunda dai gidan ban ga alamar akwai Qur'an din ba duk da kasancewar mamallakiyar gidan musulma.
Kamar an jefota ta fado dakin. Wani irin gunjin kuka take yi kamar ranta zai fita, idanuna sun yi luhu-luhu da alamar fitar hayyaci tattare da ita. Da kyar take daga kafarta ta fada saman gado tana ci gaba da kuka. "Nawwara!" Na fada a hankali dai-dai sanda Mummy ta fado dakin ita ma, hannunta rike da wani container bayi ta wuce. Bayan minti biyar ta fito tana kama Nawwara wacce ke tafiya da kyar tana kuka suka shige.
"Idan kika yi gardama tsaff zaki rube shegiya babu ruwana, dan haka nitsu ki taimaki kanki ya fi maki. Shima mutu min, in ban da shegantaka irin ta yaya maza ta ya kana ganin yarinya karama zaka zo mata da karfi har ka ji mata irin wannan ciwo haka." Na jiyo muryarta a bayin tana ta bambamin masifa, ga kukan Nawwara kuma a gefe.
"Shikenan ta faru ta kare, sun kassara mata rayuwarta," na fada hawaye na bin kuncina.
Bayan sun fito magani ta ballar mata ta sha ta kwanta hadi da rufuwa da bargo; tun tana kuka ina ganinta har bacci ya rinjayeta. Da dare, kamar yadda ta fada, bayan sallar isha ta sani yin wanka. Ni kadai ne, su Halima dai ban gansu ba kuma ban nemesu ba. Nawwara kuwa sai da likita ya zo ya ganta ya tabbatar wa Mummy sai an mata dinki, tun lokacin bata farka ba. Kayan da ta bani da sunan in sanya sun linka na jiya rashin mutunci sau biyar, sannan ta tusa keyata zuwa palo gun wani Alhaji da ganinshi dan uwa ne dan Nigeria. Dama Mummy haushina take ji, a cewarta na za mata asara jiya dan haka take min komai da wuta-wuta.
Kamar yadda ya faru da Jack, haka nan ya faru da wannan Alhajin; duk yadda ya so biyan bukatarshi sai girmanta koma ta yi lakwam. Babu shiri ya dawar dani kuma ya yi wa Mummy cin mutunci ya karbe kudinshi gaba daya. Tsabar takaici rufeni ta yi a daki ta dinga jibgata tamkar ta samu baiwa; tun ina iya kuka har ya zama sai sheshsheka da ajiyar zuciya nake saukewa.
Wasa-wasa duk wanda ya daukeni da dare, da sassafe yake dawar dani; wasu su bar mata kudin da suka biya, wasu ko su mata cin mutunci kuma su kwace kudinsu. Abun ya fara damun Mummy ga shi dai duk kwastoman da zai zo ni yake fara cewa yana so. Su Halima da Rabi'ah tuni suka zama 'yan gari, suka saki jiki suna cin duniyarsu da tsinke. Al'amarina ya ishi Mummy ya kai ta har wuya. Da tayi magana da Titi da Hajiya Babba kuwa, cewa suka yi ta yi yadda take so dani kawai. Dan haka ranar da na cika sati uku, ranar Mummy ta yanke hukuncin abun da zata yi dani.
**ABUJA**
Biki Bidiri Burede. Tuni shagulgulan bikin auren Al'ameen da Badar ya mika, an gabatar da kayatattun event wanda naira ta yi kuka. Amarya da kawayenya gogaggun 'yan duniya sun cakare sun sashe. Sosai bikin ya dauki hankalin social media, musamman Sword crossing da aka gabatar. Badar ta yi shiri cikin kakin soja haka shima gogan, duk suna rike da bindiga sojoji suka dinga gabatar da wasanni masu daukar hankali. Duk inda ka zaga a media hotunan bikin ne, musamman da ya kasance mijin ya fi matar kyau; 'yan tsegumi sun samu abun fada da yadawa. Idan ka gansu a kan high table kamar auduga da gawayi aka ajiye, lollz. Sai shishshigewa Badar take shi kuma yana biye mata. Sai kusan karfe dayan dare aka tashi taron, dama shi ne event na karshe cikin jerin guda shiga da suka gabatar.
Washegari da ya kasance asabar za a daura aure. Gidan ya cika ya batse da jama'a, yawanci dangin Ummah, sai kawayenta da gayyara kawayen Saudat da ita Amaryar zuga guda; kowacce ka gani ta sha ruwa ba laifi. Babu 'yan uwan Ummie da Abeey ko guda, sai wasu tsirarun larabawa maza da suka zo daurin auren daga Masar abokan Abeey ne, ciki har da babban amininshi Hosni. Ummie kuwa sai rufeta akayi ta waje dan ihu ta dinga yi jin gidan ya dauki hayaniyar.
Yana tsaye gaban mirror din dake dakinshi yana gyara zaman hular da ke kanshi fari kal kalar fara sol din yadin da ke jikinshi an mishi dinkin babbar riga. Sai baza kamshi yake, yau burinshi zai cika Aminullahinshi zai auri Badariya. Gyara zama Hosni ya yi a bakin gadon ya ci gaba da fadin, "Fadlallah, kana nufin har yanzu kana ganinshi kenan?"
"Ai ya wuce gani Hosni, maganar da nake maka saura kadan Alburhan ya haukatani Hosni. Idan lamarin bikin yaron nan ya kare dole mu koma tushe, dole mu koma inda zancen ya dauko asali."
Kafin Hosni ya ce wana abu, aka kece da wani irin mahaukacin dariya cikin murya mai amon sauti, suka fara jin ana cewa, "Akhi Fadlallah, ina tayaka murnar auren danka! Ina tayaka murnar auren danka! Ina tayaka murnar auren danka!" Shi ne kawai abun da ke amsa kuwwa a dakin cike da karfin amo.
Wani irin rawa jikin Hosni ya dauka, da gudu ya tunkaro Abeey zai rungumeshi amma cak ya ji an dagashi sama; kafarshi tana sama kanshi yana kasa sai lilo yake, baya sama kuma baya kasa. Baya-baya Abeey ya fara, zufa na keto mishi. Dariyara aka kuma kecewa da shi kafin Alburhan ya bayyana a tsakiyar dakin cikin shirinshi na farar shadda sol shima sai walkiya take, kuma a siffar mutane. "Ina tayaka murnar auren danka Akhii, nima na zo daurin aure duk da ba a gayyace ni ba."