MARYAMA

Page 44

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

   44.

Wani wawan zabura Sadeeq ya yi zai maida kofar ya rufe. Amma ya makaro dan tuni Mommy ta hankado kofar ta wangale hadi da shigowa tana masifa, "Wannan ma ai walakanci ne MAN, taya kana jinmu muna ta faman knocking kofa amma ka s......." Sauran maganar ne ta makale a bakin Mommy sakamakon arba da tayi da Maryama wacce ta fito itama da niyyar bude kofar, a tare su duka hudu kirjinsu ya bada wani irin sauti.

Kallon kallo kawai ake a tsakaninsu amma ba bu wanda ya samu damar furta ko da kalma guda daya,.

Sadeeq ne ya yi karfin halin fadin, "Mommy barka da zuwa, baku sanar dani zaku zo ba ai da naje airport na dauko ku." kansa a kasa yayi maganar ba tare da ya yadda sun hada ido da kowa ba.

Jiki na rawa da kyar Mommy ta iya daga hannunta tana nuna Maryama da yatsarta manuniya cikin rawan baki ta ce, "Ma....M...Ma.n....Man wannan ne abin da kake aikatawa a patakot dama, dama akan wannan mai kama da sadaka yallar ce ka ki yar uwarka, jininka, zabin mahaifiyarka?


Sadeeq wannan shine tarbiyar da muka baka? Wannan ce rayuwar da ka daukarwa kank...?" kasa karasawa tayi sakamakon kukan da ya taho mata. Khadija dama tun hada ido da suka yi da Maryama taji wani irin kuka ya taso mata, dole Sadeeq ya kita, dole ya ganta tamkar ba mutum ba tunda yana tare da wannan da ko mace yar uwarta sai ta yaba kyawun da Allah ya mata balle kuma Namiji lafiyayye. Kuka take yi tsakaninta da Allah har ta kai duke kasa.

"Sadeeq kaci amanar tarbiyar da muka baka, karuwa zaka kawo ka ajiye har cikin gidanka kuna aikata masha'a da ita? Idan bakaji kunyar mu bazaka ji kunyar ubangijinka ba?" Mommy ta fada tana dafe kujerar dake gefenta dan saura kadan ta fadi kasa.

A mugun razane Sadeeq ya dago kanshi yana kallonta yace, "Wllh Allah mommy ba abin da kike zargi bane, sam ba haka bane, ita ba abin da kika ambaceta dashi bane. Hasalima yarinyace mai mutunci bata hada hanya da irin mutanen da kike tunani ba, dan Allah ki bani dama in maki bayani,".

Hannu ta daga mishi gami da fadin, "Dakata, babu abin da zaka fadamin har in aminta dashi MAN, Bayan wanda na gani da idona, karuwa a gidanka ka ajiyeta a madadin mata, shiyasa da muka ce ka auri yar uwarka kayi biriss da lamarin ka nuna mana bamu isa dakai ba ka sa kai ka tafi ka barta da ciwo, ashe wannan karuwa mai kama da sadaka yallar ce ta shanye min kai, to bata isa ba wallahi tayi tsororo,"

A fusace Mommy ta taso kan Maryama gadan gadan, Maryama da ta kasa koda motsa kafarta a wajen ji tayi tamkar bata raye, kalaman da wannan mata take jifanta dasu sun mata tsauri tunda take babu wanda ya taba ci mata mufunci irin wanda take mata a yanzu. (DAMA HAKA MASU KUDIN SUKE?) Tayiwa kanta tambayar da babu mai bata amsar shi....Daidai isowar Mommy wajen tana karewa Maryama kallo daga sama har kasa tace, "Ina iyayenki suke suka barki kina bin maza da yarintar ki,?"

Shiru maryama batace komai ba sai tsananta rawa da jikinta ke yi.

Da wani irin tsawa Mommy ta ce, "Ke dan ubanki ba magana nake maki bane kin ba banza ajiyata, nace ina uwarki da ubanki suke suka barki kina yawon karuwanci da kananan shekarunki?." Wannan karon kasa jurewa Maryama tayi tana fashewa da kuka ta kai duqe kasa bisa guiwanta, bakinta yana rawa idanunta na zubda hawaye ta ce, "Wallahi Allah kenan ni ba karuwa bace mama, iyayena kuma sun....."

Wani wawan fincikar da Mommy ta mata ne ya sa maganar tata tsayawa, gigitaccen mari ta sakar mata a fuskarta gefen dama wanda ya sanya maryama ganin wasu taurari.

Tun batayi recovery ba ta kuma dauketa da wani marin wanda yafi na farko a gefen hagu, wannan karon jin Maryama ne ya dauke cakkk sai wani dummmmm da ta ke ji a kunnuwanta, wani marin ta dago zata kai mata wanda tabbas idan ya sauka a fuskar ta maryama zata gama kurumcewa ne gaba daya, amma sai taji an rike hannunta ta baya, a fusace ta juyo Sadeeq ne ke rike da hannun ya marairaice murya, kafun ta ce wani abu ya sake hannun gami da fadin.

"PLSSS Mommy wallahi ba laifinta bane, laifi nan...." shima bai karasa ba mommy ta sauke mashi marin da tayi niyyar kaiwa Maryama shi, tsabar masifa har idanunta suna yi kamar zasuyi tartsatsin wuta, cable na chager dake makale jikin socket kusa da inda suke ta zare hadi da nufar Maryama da har lokacin jikinta ke mazari tamkar ana kada mata gangi, dan kaza kazanki yau sai kin fada min abin da ya kawoki gidan dana, zaki san ke karama ce a bariki zaki san Sadeeq...." 

Da wani irin gudu Maryama ta nufi bayan Sadeeq ta rungumeshi gam da hannayenta bibbiyu ganin da gaske fa mommy dukanta zata kuma yi da cable din nan, sadeeq da duk da halin da ya ke a ciki rungumar shi da Maryama tayi bai hanashi jin wani irin shock ba, amma baida zabi face na karbarta

Dan haka rumtse idanu ya yi gami da budewa a take suka kada suka yi jajur dasu ya ce, "Plsss Mom wannan ba girmanki bane, ki bari in maki bayanin abin da ke faruwa".

"Sakar ta, Sakar ta na ce maka yanzun nan,". Babu yadda ya iya haka ya bambare hannun Maryama dake makale kirjinshi yana juyota, duk ta rikice sai rawa jikinta keyi ga hawaye masu zafi dake ta turereniya wajen fita daga gurbin idanunta.

Tabbas Maryama bata taba ganin tashin hankali irin wannan ba a rayuwarta, "mai yasa zan fara fuskantar kalubale alhali ga kudi ga komai ina gani kamar yadda nake bukata, mafarkina ya kusa tabbata amma lokaci daya wani al'amari yana neman rusa min komai."Maryama ta fada cikin ranta, niko na ce (AI SHI ALHAKI KWUIKUYO NE MARYAMA).

Da idanunta mai dauke da tsananin bacin rai Mommy ta juyo tana kallon Sadeeq har cikin idanu ta ce, "Man idan ni na dau cikinka wata tara, na yi nakudarka na haifeka, na shayar da kai lallai lallai wannan karuwar ta bar gidan nan yanzu yanzun nan karta kara ko da minti ashirun ne, idan kuwa ba haka ba wallahil azeem sai na tsine maka albarka....

A tare Maryama da Khadija da har lokacin ke durkushe tana kuka suka sanya kara mai karfin gaske, Sadeeq kuwa wani irin duka kirjinsa ya yi da saida ya rike saitin wajen yana zaro ido hade da dafe kirji cikin raunin da ya gama bayyana saman fuskarshi ya ce, "Mommmy I love her, ina sonta da dukkan rayuwata, i will be useless idan babu ita a rayuwata Mom, wllh ina kaunarta daga ranar da na fara ganinta har zuwa yanzu ki taimaka ki barni in auret......"  

Kasa karasa maganar yayi ganin Mommy ta damki hannun khadija dake ta rusar kuka suna kokarin ficewa daga palon, har sun kai bakin kofa sai kuma Mommy ta juyo ta ce, "Idan har nidin ce mahaifiyarka kamar yadda na fada ina son ganinka kafun nan da sati daya a gida, idan kuma ita ka zaba then ka zauna..."daga haka ta fice daga gidan janye da khadija da ta zama abin tausayi. 

Hawayen dake malala saman kuncinta ne kawai zai tabbatar maka tana da sauran numfashi..

Kallon Maryama da tayi suman tsaye Sadeeq ya yi, a hankali ya ce, "Sorry pretty. She don't meant to hurt you, haka take tana da zafi sosai amma tana da saukin kai idan ta sauko ita da kanta zaki ga ta ce muyi hakuri. Yanzu ki tattara kayanki tunda dama gobe zaki koma school kawai ki wuce yau kafin in rarrasheta. Hurry up plsss kar time din da ta bani ya cika," 

Daga haka ya juya da sassarfa yabi bayan Mommy, sai dai babu su a tsakar gidan, watchman ya tambaya ko sun fita, ya tabbatar masa da lallai sun fita. Da sauri har yana hadawa da gudu ya fita waje, amma isowarshi ya yi daidai da shigewar Mommy cikin taxi suka bar anguwar.

Dafe goshi ya yi yace, "Damn it!"

Sai bayan kusan mintuna uku Maryama ta dawo daga shock din da ta shiga, yayin da maganganun Mommy ke ta amsa kuwwa cikin kunnenta, Karuwa,... ina uwarki da ubanki kika fito karuwanci da kananan shekarunki?... lallai karuwar nan ta bar gidan nan cikin mintuna ishirin, inba haka ba sai na tsine maka albarka MAN...Da sauri ta rumtse idanunta da karfi. 

So yanzu ta zama prostitude kenan? Kowa kallon da zai ringa yi min kenan,? Jikinta ta bi da kallo daga sama zuwa kasa sai kuma ta nufi hanyar dakinsu wani bangare na zuciyarta na tuna mata da maganar Sadeeq na yanzu, wai yana sonta, ba zai iya rayuwa idan babu ita ba, how comes?".

Tsalle Siyama ta yi ta koma gefe sakamakon bude kofar da Maryama ta yi. Tun shigowar su Mommy ta farka jin hayaniya yayi yawa yasata tashi ta makale a bakin kofar tana jin duk abin da ke faruwa fuskarta fal fara'ar irin cin mutuncin da ake yiwa Maryama,...


Hannun Siyama ta kama da sauri tana girgiza kai sai kuma ta rungumeta tana fashewa da kuka. Cikin kukan mai dan sauti ta ce, "I am not a prostitude Siyama, ni ba karuwa bace,Allah ni ba karuwa baceeeee!". Ta kare cikin wani yanayi mai bada tausayi.

Siyama da ta aro tausayi ta manna saman fuskarta ta ce, "Yi shiru abinki, ke ba karuwa bace, can zata ga karuwai cikin zuriyarta kuma sai Allah ya saka miki yanzu tattara duk abin da kike bukata kawai mu wuce in kai ki makarantar nima ina dawowa zan wuce gobe".

"Ni ba karuwa bace Siyamaaa!" Maryama ta kuma fada cikin radadin zuciya da alama wannan kalma ta karuwa ta yi mata zafi sosai.

"Ehh duk mun sani ke ba haka din bace, kuma Allah zai saka miki, " cewar Siyama tana sakin Maryama hadi da fara janyo sabbin akwatu guda uku da Sadeeq ya sai mata shake da kayan amfani na mata, sauran tarkacenta siyama ta hau shirya mata tana jin ranta fari sol, yau burinta zai cika Insha Allah.

Akwatin daya ta janyo kiiiii zuwa palo ta ajiye ta koma ta janyo sauran ta ajiye su waje daya sannan ta janyo Maryama da har lokacin ke tsaye tana ta faman sharban kuka. Fitowar su ya yi daidai da shigowar Sadeeq palon gaba daya a hargitse yake. Da kallo ya bi su sai kuma ya matso kusa da Maryama, hannunta da take ta juyawa ya kama duka biyu ya rike yan yatsun, a tare suka dago suka kalli juna kafun ta maida nata idon kasa.

"Plsss Maryama ki saki ranki, idan kinje kiyi abin da ya kawo ki kada ki bani kunya dan Allah. Karatu kawai zakiyi ki saka min abin da na miki, be a good girl irin wanda ni da iyayenki zamuyi alfahari dake. Kar ki biyewa abokan banza plsss.

Nasiha ya dinga mata mai ratsa jiki, yayinda take ta kuka tamkar an aiko mata da sakon mutuwa, ji yake tamkar ya rungumeta ya lallashe ta, amma idan ya aikata haka tabbas maganar Mommy ya zama gaskiya kenan, da sauri ya sake ta jin shaidan na kara kawata masa abun.

Wani karrarrawa ya danna a palon, ba jimawa mai gadi ya shigo, jakunkunan dake zaune palon ya nuna masa da ya kai bayan mota ya zo dan paper ya zare cikin jotter din dake gaban laptop nashi yana aiki dazu ya dau pen ya dan yi zanen Emoji heart mai kyau sannan ya rubutu pin nashi a cikin zanen ya zaro Atm nashi guda daya ya nannade a ciki ya taso gami da kama hannun Maryama ya damka mata ya ce, "Take care of your self, zamu dinga yin waya ohk?" Zaro ido Siyama ta yi tana karewa Atm din kallo hadi da dan girgiza kai.

Dawowar mai gadi ne yasa shi dagowa ya ce, "Samuel ka kaisu Portsu yanzu nan ni zanje airport ne," Ya fada yana mika mashi car keys dake hannunshi, yess sir,wanda aka kira da samuel ya fada, siyama ce tayi gaba Maryama na binta a baya tana jin wani irin zafi da ba tasan dalilinshi ba a kasan ranta gashi dai yau zata fara zuwa jami'a, abin da ta dade tana mafarki da burin tabbatuwarsa amma kuma ya zo sai dai babu wani excitement a tare da ita, sai ma wani tarin kunci da takaici da take a ciki.


Har ta kai kofa sai kuma ta tsaya ta juyo, kafeshi tayi da idanunta da suka sauya kala a kasan makoshi ta furta, "Nagode sosai da taimakon ka, insha Allah zanyi karatu sosai bazan taba baka kunya ba".

Kai kawai Sadeeq ya gyada mata dan samun kanshi yayi da kasa yin magana. Da haka suka fice bayan motar suka shiga gaba dayansu samuel ya ja suka bar harabar gidan,saida ya tabbatar sun fita sannan ya koma sama ya canza kaya da sauri sauri ya dau wani car keys din ya sauko, airport zaije ya duba su mommy dan yasan baza'a samu jirgin da zaije gombe yanzu ba shiyasa ya bari sai da yaga fitar Maryama tukunna.

Har cikin harabar hostel namu samuel ya kaimu, da taimakonshi muka shigar da kayan zuwa dakinmu, kamar yadda na sanar muku dama na gama komai a school din ciki harda accomodation. Dan haka akwai keys na dakinmu a hannuna. Dakin mu hudu ne a ciki, saidai da alama babu wacce ta zo har yanzu, da taimakon Siyama na kimtsa kayana gaba daya a corner dina muka share dakin hadi dayin mopping tas kasancewar dakin babu abin da ya rasa dan bayi ma ciki yake bayin na bude na leka babu laifi ya tsaru amma akwai dan datti, hakan ya sa duk da raina babu dadi na cire abayar da na daura kan kayan dake jikina na ajiye gami da daure dogon gashina da gyalen abayar na fara wanke toilet din, da wannan damar Siyama ta yi amfani ta aiwatar da kudurinta dake ranta tun dazu, Atm da pin din da Sadeeq ya bani ta dauka tana cusashi cikin jakarta, hannunta yana rawa ta fitar da wani atm din na daban ta ajiye gami da rubuta pin nashi jikin wani paper ta nannade ta mayar inda ta dauki na farkon. Juya fuska tayi tamkar bata aikata komai ba a ranta tana jin wani irin dadi, tasan ba kananan kudi za:a samu a wannan account din ba.

Wanki mai kyau na yiwa bayin sannan na fito ina gyara hannun rigata.

"Sannu yar boko," cewar Siyama tana dan dariyar tsokana ko uffan ban ce mata ba sai biscuit da minerals da na janyo mana cikin shopping din da Sadeeq ya min dan na tabbata ba zamu iya yin girki yanzu ba. 

Muna kan ci aka bude kofar dakin, wata da bazata haura shekaru ashirin da biyar ba ta shigo janye da akwatuna guda biyu, tana sanye da wani wando pencil da ya matukar kamata tamkar zai fashe kalar blue, sai wata yar yololon riga milk colour da bai gama rufe mata cibiyarta ba, kanta yasha kitson wig manya manya wanda ya sauko har kan duwawunta, faratanta ko zako zako sunsha jan farce kala mai daukan hankali kana kafarta sanye cikin sandal baki, tana da kirar hallita mai kyau duk da kasancewarta ba musulma ba, farace sol tafi kama da igbos.

Kallon kallo aka fara a tsakaninsu kafun wacce ta shigo din ta mikawa Maryama dake kusa da ita hannu tace, "Hey ladies i am Chioma, nice to meet you," ta fada fuskarta dauke da murmushi, hannu Maryama ta mika mata itama tana tabbatar da addu'arta na samun room mate musulma bai karbu ba, cikin muryarta mai dadi ta ce " I am Maryama, nice meeting you too".hannu ta mikawa Siyama ma cike da murmushi, siyama ta karba suka gabatar da juna amma kasan ranta tana jin so tayi Maryama ta samu room mate masu tribalism sosai ba irin wannan da da alama zatayi kirki ba, niko nace hmmmm.

Koda suka gama cin biscuit din Siyama ta yi haraman tafiya, a cewarta zataje ta shirya dan gobe zata koma, amma a kasan ranta sam ba haka abin yake ba, tana sauri ne taje ta aiwatar da shirin da tazo dashi na musamman akan Sadeeq.

Kuka Maryama ta fashe da shi, yayinda Chioma ta fara mata dariya da tambayar dama ba dukkansu bane zasu zauna? Siyama tace ita kadaice zata zauna ita ta rakota ne kawai...

Har wajen makaranta Maryama ta kai Siyama da samuel ya koma tun da jimawa, duk ranta babu dadi abubuwa sun mata yawa a kwanyarta ga wani irin bad feeling da take ji,.

"Ki koma haka Maryama dan kar ki bata kinga ba wai kin gama sanin kan wajen bane, plss kiyi karatu mai kyau, kinga dai nan ba arewa bace, zaki hadu da mutane daban daban masu kabilu daban daban.

Gyada kai tayi tana kara tamke hannun Siyama ta ce Insha Allah.

Allah Allah Siyama take Maryama ta wuce dan ta hango wani banki can tsallaken kwalta so tanason taje ta ga nawane a cikin wannan account da ta dauka, wajen akwai zirga zirga ababen hawa sosai kasancewar express way ne. Da kyar suka rabu Maryama ta juya tana share hawaye yayin da Siyama ta nufi kwalta tana juyowa hadi da yiwa Keyar maryama gwalo da Murmushin mugunta,..

Wani irin mummunan karan da Maryama ta ji ne yasa ta juyowa a tamanin duk hayaniyar da wajen ke dashi take ya tsaya cakkk tamkar babu sauran wani bil adama dake numfashi a wajen, a hankali kuma hayanaiyar ta fara jama'a suka fara nufar wajen da abin ya faru kamar wacce aka hankada Maryama ta ganta a wajen ba tare da tasan yadda akai ta je ba, cikin wani irin yanayi ta fara jin tamkar ana kankare mata tsokar jikinta ana zubarwa a kasa a hankali duhu ya fara maye gurbin jama'ar datake kallo suna ta hayaniya a wajen, abu na karshe da ta gani shine pieces na jikin Siyama da tirela ta markade, daga haka bata kara sanin inda kanta yake ba.......

Hoooooooo, wazai min calculating wannan maths din, masifa+bala'i 

Maryama ita duniya a nutse ake binta😭