KARFE DÜKKA KARFE NE

The end

by @maidambu41

KARFE DUKKA KARFE NE...!!!

{Zanen ƙaddarar Falilah}

BABI NA SHA TARA DA ASHIRIN.


🌸 Assalamu Alaikum Yan'uwa Mata.


Kowace mace tana son ta ga kitchen ɗinta cikin tsari da kyau, tare da kayan zamani masu inganci. Amma abin da kan hana mutane shi ne tara kuɗin saye lokaci guda.


Shin tara kuɗin saye ne ke miki wahala?

Ko kuma idan kin tara sai wasu buƙatu su sa ki kashe su?


Ki kwantar da hankalinki, domin MA KITCHEN ta zo da mafita.


Mun buɗe Adashen Kayan Kitchen domin ki mallaki kayan da kike buri cikin sauƙi, ba tare da wahalar tara kuɗi lokaci guda ba.


Abubuwan da za ki samu:

Kayan kitchen na zamani masu inganci.

Farashi mai sauƙi.

Adashe mai sauƙi da kwanciyar hankali.

Ana kai kaya zuwa duk inda kike.

Biyan kuɗi a hankali cikin sauƙi.


Za a fara nan ba da jimawa ba, In shaa Allah.


📞 WhatsApp/Call: ***


📲 Shiga WhatsApp Group ɗinmu domin samun cikakken bayani da fara rajista:

***


🌹 Arha ta fi bashi, adashe kuma ta fi bashi kwanciyar hankali. Ki yi rajista tun da wuri, ki mallaki kitchen ɗin mafarkinki cikin sauƙi.


MA KITCHEN – Muna tare da ke har ki cika kitchen ɗinki da kayan da kike buri. 💚



Zubawa Latifa idanu yayı kafin ya ce mata. “Ki yi hakuri!” Ya furta tare da mai da hankalinsa kan abinda yake, “kana nufin.” “Tifa ina aiki ne?” Ya fada yana cigaba da abinda yake, ta so ta ji haushi amma sai ta hakura ta ajiye mishi glass cup din tare da barın mishi study room din, wayarshi ya janyo tare da kiran wata layi,


     Ana dauka ya ce mishi.

“Asad ban ce ka fita harkan Tifa da Mutanenta ba? Asad Ina wasa da kai ne? Ban maka iyaka da Reinah ba? Zanci Ubanka sai na maka rashin mutunci ka guji haduwa da ni.”

   Yana gama wayar ya cilla can, yana ganin yadda  ake ta kiranshi yasan Mahaifiyar Asad dince tunda ita bata da kunya, kamar ba zai dauka ba sai ya dauka ba tare da ya saka a kunnensa ba ya ce mata. “Ina jinki Shema’u.” Yadda ya kira sunan babu sakayewa dağa can ta ce mishi. “Khalid me kake nufi da Asad?” 

“Ban gane ba?” Ya tambaye ta yana sosa kai, ganin zai bata mata rai ta ce mishi. “Ok ina gidan Hajiya” katse kiran yayı ya dafe kanshi, ba shi ya haifi Asad ba, amma bala’i da fitinar da Yaron yake ja mishi yasa shi Jin like ya cire hannunsa.


         

      

        Kiranshi Hajiya tayı ya dauka ta ce mishi, “ina son ganinka Auta!” Shafa kanshi yayı kafin ya ce mata. “To Hajiya” ya kashe kiran , mikewa yayı a kujeran da yake ya dauki wayarshi ya saka a cikin aljuhu, sannan ya fito, a parloun ya sami Latifah, “zaka fita ne?” “Gidan hajiya zan je!” “Allah ya tsare hanya.”

“Amin Ya Allah.”  Ya furta tare da barın parloun bai dauki direbansa ba, da kanshi ya tuka motar har gidan Hajiya da basu da nisa sosai,  a dakin Hajiya na kasa ya same su, Daada tana ganinsa ta ce mishi. Saifullahi maasum, zo nan khaliduna “ ta nuna mishi wuri ya zauna, kallonshi tayı ta ce mishi a karo na biyu, “Bayan sallah azhar nayi mafarkin abin arziki zai same ka in sha Allah.”  Murmushi yayi ya ce mata. “Na gode!” Ya kalli Hajiya mahaifiyarshi ya gaida ta, sannan ya kalli matar wanshi ya gaishe ta, kana ya juya yana kallon Asad din da ya lalace kamar bashi ba. “Hajiya gani nan!” 

“Akan me zaka tsangwami Yaron nan?” Murmushi yayi ya ce mata, “Hajiya ban tsangwame shi ba, shine bashi da hali. Hajiya haka Aswad yake? Me yasa ban tsangwame Aswad ba?” Budar bakin mahaifiyar Asad Shama’u ta ce mishi. “Ina Aswad zai yi laifi bayan kafi sonshi da sauran yaran tunda uwarshi ta asirce ka.” 

Murmushi yayi me sauti domin idan da sabo ya saba da wannan kalaman na Matar wanshi,.



    Su uku hajiya ta Haifa, Alhaji Sa’id, sai Alhaji Saddam mahaifin Aswad , sai shi lauya a karkashin unicef, dukkansu yan jahar Yobe ne, kuma Allah ya musu rufin asiri, 



   Khalid mutum ne mai zafin kai, a lokacin da aka dawo da Asad najeriya shi ya dauke shi zuwa Yobe ya karasa karatu a can, bai taba zatan Kai shi makarantar zai kara fanɗarewa ba sai da yaji labarin abin da ya faru a makarantar, ya zare hannunsa a kanshi domin wani irin so da gara ake nuna mishi wanda yasa Yaron ya lalace. Amma Aswad kan yana da hankali wnada yanzu haka yana da mata da yarsu daya. Amma Asad  yaki aure sai shaye-shaye kamar salansa.



     Bude baki Hajiya tayı zata magana wayarshi yayi kara, a hankali ya dauka ya ga number Ya Man ne, çıkın girmamawa ya amsa. “Alhamdulillahi, in sha Allah zan rike ta da Amana, zan turo Yan uwan Abbanmu su zo jibi in sha Allah! Na göde Allah ya kara lafiya da nisan kwana na gode In sha Allah zaka same ni da rokon Amana.” Sannan ya sauke wayar ya cewa Daada. “Alhamdulillahi tsohuwa ki shirya zuwa umara, an bani takwararki. Ayshatou Falilah zan tura baffa Hamidu da Baffa Nuhu, Alhamdulillahi sadakın da kome zan tura musu gobe Yobe in sha Allah!”


    “Falilah? Asad ya furta da karfi yana me mikewa, “Uncle Khalid Falilah Mustapha Liman?” Mantawa yayı da yana jin haushin Yaron ya ce mishi. “Eh ita wani abu ne?” “Wata baka doguwa Babanta Malami ne?” “Ka Santa ne?” Wani irin ihu ya Fasa ya ce mishi, “Aa wallahi, Falilah tawa ce, wallahi ba zan barka ka aure ta ba, ita din muradına ce.”

     Haushi ya çıka Khalid kamar ya rufe shi da duka, Girgiza kai yayi ya kalli Hajiya mahaifiyarshi, tana tsananin kaunar Asad,, amma ba zata iya hana autanta abinda ya jima yana so ba, “Yaushe ka hadu da Falilah?” Ta tambayi Asad, “A makaranta da aka kai ni Yobe hajiya ki saka baki ya bar min ita domin ta haramta gare shi?” “Kamar?” Dük suka zuba mishi idanu, shiru yayı ya ce musu. “Ni na fara lalat…” wani irin naushi Khalid ya kai mishi, “Kai he ka lalata mata rayuwa da iyayenta suka zare hannu akan ta na tsawon shekaru kusan goma sha?” Ya rufe shi da duka Mahaifiyarshi tana ihu tana rokon hajiya. “Kyale shi Saifullah aure a tsakaninka da Aisha babu fashi idan Shema’u bata rike kanta da danta ba zan saka Said ya sake ta na gaji da halin da Asad yake jefa min ahalina, Yarinyar nan tun tana tsuma Khalid yake bin rayuwarta amma saboda shaidancinka sai da ka ruguza mata rayuwa hankalinka ya kwanta, ka

Je Allah ya shirya ka. Ku fita a gabana.”


     Sannan ta juya ga Khalid ya ce mishi. “Daughter ta san da Falilah?” “Ta santa!” Gyada kai tayi ta ce mishi. “Gobe ka kawo min ita mu yi magana.” “Allah ya kai mu.” Ya furta a hankali.


***

Falilah

Tında ya Man ya gayawa Hajja Mama cewa ya bada aurena, na cire dama wani soyayya ko wani Abu,  abinda na sani shine Ahmadi ya tafi har abada babu namijin da zai so ni kamar shi, na kuma karawa kaina hakuri da juriya domin a karon farko Ya Man ya kara zaba min MIJIN da yake Muradin na aura, ya bawa Hamma Jamal hakuri tare da nuna mishi zumunci nan tında jini ya tsaga, haka dai nayi hakuri na shanye Ya Nafi’u ne ma yafi bani mamaki, wai Ashe sona yake, all these years, amma na kasa yarda na amince domin matarshi a uwa na dauke ta.



Ban san ya aka yi ba a wurin aiki aka turo min sakon hutu, don haka Hajja Mama ta saka ni gaba muka wuce Yobe, ranar laraba, muna isa bayan isha na gaji Hajja Warisa ta shiga kawo min Kayan gyaran jiki, tun ina ci a dadin rai har na koshi, washe gari alhamis, manyan mitimin da  zaa aura mun suka zo da sadakinsu, da kome sannan Ya Man ya gaya musu bayan sallah jumaaa gobe zaa daura auren bazawara ce ni ina da kome bana bukatar kome, haka suka tafi. Ya shigo gidan ya fada ni dai da to nake binsu, ina rike da Ahmadina Hajja Mama ta ce min, “Mahaifiyar Ubansu ta ce zasu zo su amshi Yaran, amma Malam ta gaya musu. Su yi hakuri yaran su kara wayo zuwa uku sai su amshe su yayi miki?” D’ago kai nayi ina kallon Yaran don naki Baffansu shine zaa raba ni da su, murmushi nayi Saura yara biyu ai suma iyayensu suke da matsala amma da sun karbe su tuni.


   “Allah ya rufa asiri!” Nasiha sosai Hajja take min wnada bata yi min a baya ba, amma naji kuma na nutsu da auren nan, ko ba kome akwai albarkan iyaye,  wani abin mamaki kafin wayewar jumaa yan uwa da abokan arziki sun cika gidanmu, an cika kafin karfe biyu na rana daidai lokacin da zaa daura auren sai ga sako dağa gidan ango kayan kwalliya da na fitar amarya, haka na shiga wanka na fito, na shirya tsaf sannan aka min kwalliya.



                Karfe uku daidai aka shaida aurena na Takwas da Khalid Abdullahi Hammayo, ikon Allah rayuwata dai Fulani suka shiga dağa sama

Har kasa,  an daura aure çıkın aminci da dattako, sannan ango ya shigo çıkın gidan aka gaisa da iyaye , ban da iskanci har da hoto. Ni ce dai naki, karfe biyar na yamma aka wuce Abuja da ni, wurin karfe bakwai muka isa, gidan mahaifinsa da yake maitama, lokacin da aka shigar da mu parlorn Mahaifiyarshi ita da kanta da matarshi suka tare ni, aka ajiye ni a kujeran da yake parlorn Ana guda, kusa da kakarshi. “barka da zuwa Aishatu Falilah.” Inji Mamanshi, “Sannu takwarata barka da zuwa gidan.” Na kasa amsawa kaina çıkın farın laffaya. “Barka da zuwa Kanwata.” Sai na rasa gane wacce duniyar nake raye a cikinsa, Anya ni ce kuwa? 



    Kafin wani lokaci an kuma riko hannuna zuwa dakin da aka tanadar mana, sallah muka yi tare da cin abinci, sannan aka ce nayi wanka zaa kai ni gidanshi. Gobe zasu yi walima!


         Haka nayi wanka na shirya a Kayan da aka kawo min daga mamanshi, aka shirya ni tsaf muka wuce gidana, tare da Mamanshi da kishiyata,  lokacin da muka isa mun same shi a gidan, yana ma falour,  haka ta hada mu tayı mana nasiha da ta saka kowa ya shiga jikinsa, sannan tayı mana Addua, ta bar gidan matarshi ta raka ni dakina tana zolayata. “Ki taimaka min ki kula da Daddyn Reina please ya sha wuya akanki kada ki bashi wahala.” Ni dai ban ce mata uffan ba.


        Bayan tafiyarta na ya shigo, “Sannu Ayshatou” ban amsa mishi ba har ya gama surutunsa, kafin ya umarce ni nayi alwala, koda na shiga ban dakin kome tsaf sannan na fito na same shi Akan abin sallah,  sai da ya gabatar da Addua kafin muka yi sallah, duk abinda yake Ahmadina nake tunawa, har muka gama ya fito ya kawo abinci ban iya ci ba sai ruwa na sha na kwnata, sannan na ya biyo ni, Allah ya gani na rasa yadda zan yi na kyale shi, yayi budirinsa yadda ya mishi, kafin wani lokaci naji a jikina. Domin ya gigita ni ainun da taimakonsa nayi wanka na dawo na kwanta, koda asuba tayı a a daddafe na farka na gasa jikina, nayi wanka nazo nayi sallah ina azkar ya shigo kamar na nutse a kasa don kunya. Haka ya zo inda nake kwance ya d’ago ni, yadda nake sunkuyar da kai ya saka shi ja na zuwa bakin gadon, kallon Gaban rigana yayi da ya jike, ya ce min. “Suna Ahmad naso abincin su.” Ni dai ban ce kome ba, fita yayi zuwa an jima can har na fara barcı naji muryan Batul. Tana ta kuka, bude idanuna mayi ya shigo da su, a daidai ina kallon kofar. Suna ganina suna fara zilo. Ajiye min su yayi, ya koma gefe na ciro nonon bakidaya na saka musu a baki, suka kama. Murmushi ya sake ya ce min. “Allah yasa last night na ajiye kamarsu.


  

 Sunkuyar da kai nayi ban kula shi ba, fita yayi a dakin can sai gashi da akwatinsu. Ya samu Ahmad yayı barcı Saura Batul kafin na raba gefensu na kwnata yazo bayana ya kwanta.



      Sai karfe daya muka karya, sanman aka fara shirin walima. Biyar ba yamma gidan ya çıka aka yi walima wanda aka yi nasiha akan rayuwar aure da mutuwar dake a wannan halin, sai tarbiyyar da aka yi magana akai.



   Bayan an gama hidima yan uwana suka min fatan alkhairi suka wuce Yobe washe gari, na fuskanci rayuwar aurena da gidan mijina. Mutum ne da yake da kırkı da son jamaa, yana da hakuri da kawaici, sannan mutum ne da yake da abin ban darıya koda yake Maman Reina ta ce saboda yana sona ne ya zama haka, ina haduwa da kishiyoyi wannan karon na hadu da wacce ta goge min hadda, ba ruwanta ba tashin hankali, satina biyu na koma aikina, Yarana kuwa Akwai me renonsu da take hidima da su.



   Bayan wata uku ban kawo da gaske rabo ne ya kawo ni gidan ba, sai da na fara rashin lafiya tun kafin mu je asibiti na gane ciki ne da ni, haka muka isa aka gama gwada ni aka tabbatar da ciki, ya Kira Ya Man ya gaya mishi, ba sai laulayi ba, Latifah take tsaye a kaina har Auntu Zuhra tazo ta kwashe Yaran ta mai da su Yöbe kamar yadda Hajja Mama ta umarta ni kuma ba cigaba da kula da kaina.


   Ban samu lafiyar kaina ba sai da cikin ya cika wata hudu, sannan na koma aiki a lokacin muka hadu da Asad Allah ya gani ma razana, amma ganin wanda yake kaina da gefena na share.  Haka rayuwa tayı ta tafiya dangin mijina da Mahaifiyarshi tare da Matarshi suna tsaye akan

Lamarina.


      Wata na goma cib na sauka lafiya inda na samu baby boy dina, Alhamdulillahi. Tun kafin mu dawo gida duniya tasan anyiwa Khalid haihuwa domin babu inda sakın haihuwa bai shiga ba.


       Kusan satı aka dauka aka hidima kafin aka go taron suna Yaro ya ci sunan Babansu, Ana kiranshi da Adnan, haka muka sha suna.


       Ban taba tsammanin a cikin shekaru uku rayuwa zata sauya min ba, Amma Alhamdulillahi na samu MIJIN da yake sona yake kaunata yake kuma kula da lamarina, Hamida tana gidan Ya Nafi’u haka karamı shima yana gidan Aunty Zuhra.  Yan biyu suna wurin Iyayena, Alhamdulillahi yarana suna inda ya dace, Asad da mahaifiyarshi da Mahaifinsa sun zo sun roke ni domin hakkina bai barshi ba, wasu abubuwan ma sai a hankali haka Alhaji Salisu shima na ji labarin rayuwar Maman Ayuba, na ce na yafe. Akwai abubuwan da babu amfanin rike su, rayuwata ta samu majingina, bayan haihuwar Abdullah na gani yadda nake azabar son Khalid na kuma fahimci shine Mr Aljani, Alhamdulillahi, 

 Kuma na fahimci bayan Ahmadi Akwai wani zinarin da Allah zai bani shine Khalid muna zaune lafiya bakidayanmu wannan Karon Uwar mijina kamar ta hadiye ni, ga kuma yadda na ke zaune lafiya da Latifa ita kanta kishiya ji da ni take kamar ta Goya ni.


 Anan na kawo karshen labarin karfe dukka  karfe ne, zanen kaddaran Falilah na gode sosai. Allah ya hada mu da ku a wani labarin amma na gaji……