BARA A KUFAI

Page 3

by @zeeykumurya

*BARA A KUFAI*

*Zeey Kumurya*


3.


BRIGHT PENS 2026

YOTA ID 003


Bismillahir rahmanir rahim.




Fuskarsa a cunkushe yake takawa zuwa inda motarsa take, rauni da damuwar ciwon Daddy da ya fito da su suka dishashe saboda tuno saƙon da ya yi karin kumullo da shi a ɗazu, ba ƙaramin daure zuciyarsa ya yi ba na yaƙar halin da ya shiga ganin yadda Ramlah ta tayar da hankalinta, don ba ya son sanar da ita abin da yake faruwa sai ya gama tabbatar da abin da yake son sani, hatta yanayin takunsa sai da ya sauya ya koma na asalin JURAIJ ɗinsa. Tun kafin ya ƙarasa ɗaya daga cikin yaransa ya yi hanzarin buɗe masa mota bayan ya gaishe shi, da kai kawai ya amsa masa sannan ya shiga motar ya mayar ya rufe. 
Wani irin gudu yake yi da motar tamkar zai tashi sama, hakan ya sa cikin mintuna ƙalilan ya ƙarasa wani madaidaicin gida da ya ƙawatu da ginin zamani, daga waje ya yi parking ya tsaya yana kallon gidan da idanunsa da suka kaɗa suka yi jajur. A hankali ya furta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Tare da tattaro ragowar juriyar da ta rage masa ya buɗe motar ya fita ya shiga cikin gidan. 

Tun daga harabar gidan yake jiyo sautin kukan da ke ƙara dagargaje zuciyarsa, jikinsa ya fara tsuma, da sassarfa ya ƙarasa parkourn ya shiga kamar an cilla shi. Idanunsa suka sauka akan hoton Sheikh Adnan Bukhari da ke manne a bangon ɗakin yana fuskantar ƙofa, saurin kawar da kansa ya yi saboda bugawar da zuciyarsa ta yi, ya tsayar da idonsa akan matashiyar matar da ke ta kukan da ya cika gidan. 

"Sun kashe shi! Sun kashe mana miji! Sun mayar mana da 'ya'ya marayu, sun raba ni da farincikina!" 

Kalaman da ta furta masa kenan a ɗimauce cikin tsantsar tashin hankali. 

Ɗauke idonsa ya yi daga kanta ya mayar kan uwargidanta da ke zaune ta ƙura wa waje ɗaya ido tamkar mutun-mutumi, idonta babu alamun hawaye, sai wata irin rawa da jikinta yake tamkar an jona mata shocking, ga yaran gidan gabaɗaya sun baibaye ta suna kuka mai taɓa zuciya.

A sanyaye ya tsugunna a gabansu tare da zare glasses ɗin idonsa, kamar wanda aka yiwa farraƙu da furta harafi haka ya rasa me zai ce musu, yana jin kamar duk kalmomin da zai yi amfani da su sun yi kaɗan wajen rarrashi da sanyaya musu zuciya. Ƙaramar yarinyar gidan ya yi jarumtar ɗauka ganin tana ta rarrafe da kuka amma babu wanda ya bi ta kanta, ya rungume ta a jikinsa cikin tsantsar tausayin ta na rayuwar maraicin da ta same ta tun kafin ta san me duniyar take ciki.

"Ina gawar take?" Ya tsinci kansa da furta haka. 

"Tana sama, yanzu su Yaya Lawal suka wuce da ita, duk suna can, Ummu ma tana can." 
Amaryar ta ba shi amsa cikin kuka, kai kawai ya gyaɗa mata. Ta ci gaba da magana cikin wani irin rauni da kukan da ta kasa tsayar da shi.

"Sun hana mu zuwa wai sai an gama yi wa gawar gwaje-gwaje, Yaya Lawal kuma ya ce ko iyayenmu kar mu kuskura mu sanarwa a yanzu saboda wani babban dalili wai sai an gama bincike, na rasa ya zan yi, na ruɗe na rikice shi ya sa na yi maka text, don jikina ya ba ni ba mutuwar Allah ba ce, akwai wani abu a ƙasa, akwai abin da ake ɓoyewa, na san kuma duk duniya kai kaɗai ne za ka iya ganowa, kai kaɗai ne za ka tsaya ka ƙwato mana haƙƙinmu, kai ne kawai hope ɗinmu a yanzu, Ummu mace ce ba za ta iya komai ba, ga tsufa, duk yadda suka tsara mata yarda za ta yi, shi ya sa bayan sun hau sama na je na buɗa ƙofa don kar ka zo ka yi knocking su ji su san da zuwanka, wallahi kashe shi aka yi, amma suna so su binne komai, ka taimaka mana kar ka bari haƙansu ya cimma ruwa, ka taimake mu a gano ko su waye a bi mana haƙƙin mijinmu." Ta ƙarashe maganar tare da ɓarkewa da wani irin kuka. 

A zafafe ya sauke yarinyar jikinsa ya miƙe ya nufi sama jikinsa na wani irin tsuma, kukan Ummu ne ya sanar da shi dakin da suke, a sukwane ya tura ƙofar ya shiga. 
A tare duk suka ɗaga kai suna kallon shi, Ummu ta yunƙura za ta tashi a hanzarce amma ta kasa, ta koma sharaf ta zauna, hannunta na rawa ta nuna gawar ɗanta ɗaya tilo a duniya tana faɗin. "Juraij mutuwa ta ɗauke mini Adnan, ta raba ni da shi, ka gan shi, kalle shi, abokinka ne amma ya zama gawa! Ya mutu! Ya...." Ta kasa ƙarasa abin da take son furtawa saboda wani irin gigitaccen kuka da ya ƙwace mata, da sauri ya ƙarasa ya riƙe ta amma ya gaza furta ko da harafi ɗaya ne, bayanta kawai yake bubbugawa alamar rarrashi, idonsa na kan gawar Sheikh Adnan da ko jiya da yamma sun haɗu, Likitan da ke tsaye a kusa da Yaya Lawal yana rubuce-rubuce ya ce. "Sai haƙuri Hajiya, lokacin Sheikh Adnan da Allah ya rubuta zai rayu a doron duniya ya riga ya ƙare, sai dai fatan Ubangiji ya ji ƙan shi da gafara." Hawayen da ya sauko a kuncin Yaya Lawal ya goge ya ce. "Rayuwa kenan, mutuwa ba ta da iyaka, ga ni ga Ummu da sauran ƴan'uwanmu amma sai ƙaramin cikinmu ta ɗauka, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Idan na tuna jiya har dare muna tare da shi sai na ji tamkar mafarki nake, kamar za a tashe ni na farka na ga Adnan tsaye akan duga-dugansa mu ci gaba da rayuwa....." Wani kallo Juraij ya wurga masa ba tare da ya gama jin ƙarshen zancen nasa ba, shi ma kallon shi yake hakan ya sa idanunsu suka sarƙe da na juna, tsawon wasu sakanni suna haka kafin Juraij ya janye nasa ya mayar kan gawar abokin nasa. Sai da ya jingina Ummu da jikin gado sannan ya ƙarasa ya yaye zanin da aka rufe Sheikh Adnan da shi, fuskarsa da ba ta motsin komai ta bayyana, idanunsa a rufe amma kamar za a yi masa magana ya amsa, yana ƙoƙarin janyo zanin ya mayar ya rufe fuskar idanunsa suka sauka akan wani abu da ya saka zuciyarsa doka wani uban tsalle, jikinsa ya kama tsumar da ta zarce ta baya, ya tsaya cak yana kallon abun cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa.

***** ****** ******

SAUDAT

A kullum da kodayaushe idan ta kaɗaice babu abin da take yi sai tunanin masu matsalolin rayuwa da take ganin sun fi nata, musamman idan ta hasaso waɗanda iftila'in rayuwa na hatsari ko na gobara ya faɗa musu, a dalilin haka duka gidan su mutu su bar mutum ɗaya tak da ciwon kewa, ko kuma wanda ba za su mutun ba amma za su sha wahala ko su nakasa, ko kuma masu gudun hijira da ƙaddara ta tarwatsa garinsu da ahalinsu, ko waɗanda suka tashi a gidan marayu ba tare da sun san kowa nasu ba, da waɗanda linzamin ƙaddara ya ja su ga ƙare rayuwa a gidan kaso, wani ma bai aikata abin da ake tuhumar shi ba amma tunda ubangiji ya jarrabce shi babu yadda zai yi. Duk da hakan ba ya rage mata komai na raɗaɗin da take ciki amma tana cewa "Alhamdulillah!" Tana samun ƙwarin gwiwar jurar duk wani ƙaluben rayuwa domin ta tuna akwai waɗanda suka fi ta shiga tasku. Tana jin kamar watarana komai zai wuce kamar labarin wahalar rayuwar wasu da take ji, amma yaushe? Me zai faru ta daina rayuwar BARA A KUFAN da ta ginu tana yi? Shi ne tambayar da take yiwa kanta a kullum da kodayaushe ba tare da ta san amsar ta ba. Bugun ƙofar banɗakin da take ciki da aka yi ne ya sa ta miƙe ta goge hawayen fuskarta, wanda ba su damar zuba ne ya shigo da ita toilet ɗin. Da nauyin da zuciyarta ta yi mata da ya bi dukkan jikinta ya sagar mata ta janyo butar gabanta da ƙyar ta ɗauraye fuskarta. Sai da ta yi iya yin ta na ganin ta ɓoye halin da take ciki sannan ta buɗe ƙofar banɗakin kanta a ƙasa ta fice ba tare da ta bari sun haɗa ido da wadda take jiran nata ba. 

"Ni da dinkum-dinkum." 

Ta ji an faɗa cikin izgili, ba ta tsaya ba bare ta san waye ta ci gaba da tafiya kanta a ƙasa, cikin fatan kar mutanen da suke hada-hada a tsakar gidan su gane ta. 

Wasu mata guda uku da suke zaune suna kallon ta suka kwashe da dariya, ta tsakiyar wadda ita ta taɓo su ta nuna musu ita ta ce. "Allah ya raba mu da duhun kai ya ƙara ba mu wayewa, wannan dunkumewa haka har ina? Ji fa yadda take tafiya kai a ƙasa saboda kawai kar ta yi wa kowa magana." 

"Shi ya sa ai ga shi nan ƙannenta suna ta aure suna barin ta." 

"To wa zai ɗauki macen da ba ta da wayewa? Kullum tana fama da hijabi kamar matar liman." 

Ƙara kwashewa suka yi da dariya sannan wadda ta fara maganar ta ce. "To ita liman ɗin ma ya gagara samuwa ai."

Duk maganganun da suka yi a kunnenta amma hakan bai sa ta ɗago kanta ba bare ta kalle su, ta ci gaba da ratsawa ta cikin taron mutanen bikin da suka cika gidan nasu.

Ta zo daidai ƙofar ɗakin Mama ta ji ana ƙwala kiran sunanta, kamar ta share sai kuma ta tsaya ta juyo tana duban mai kiran nata, ganin Shamsiyya ce ya sa ta ɗan ɓata fuska don kamar mai kiran ƴar cikinta haka ta cika gurin da hayagaga. Tana ƙarasowa kusa da ita ta miƙa mata ɗan hannunta tare da faɗin. "Affan za ki goya mini don Allah, ina son na yi wanka na yi shirin  zuwa bridal shower ɗin nan amma yana ta kuka ya ƙi zama shi sai goyo kawai yake so." Fuska a sake Saudat ta ce. "Bari na je na ji kiran da Mama take yi mini tukunna, idan ba aiki za ta saka ni ba sai na karɓe shi." Ba ta jira cewar Shamsiyyan ba ta shige ɗakin Mama, da kallon takaici Shamsiyya ta bi ta baki a sake, a kufule ta tallafe ɗanta da ya callara kuka ta bi bayan Saudat.

Saudat na shiga ɗakin Mama ta rufe ta da faɗa ba tare da ta damu da mutanen da ke ɗakin ba.

"Wai don iskanci na aika a kira ki tun ɗazu amma sai yanzu za ki zo? Kin san kuma akwai abubuwa da yawa a gidan nan da suke jiran ki." 

"Ki yi haƙuri Mama banɗaki na shiga..." Ba ta ƙarasa ba muryar Shamsiyya da ta banko ɗakin ta katse ta a harzuƙe.
"Mama wai na ba wa Yaya Saudat riƙon Affan don na samu na shirya da wuri na tafi gurin bikin nan amma ta ƙi karɓar shi?" 

"A saboda me kuma? Karɓe shi dalla ki riƙe mata shi, ke da komai ba kya yin abin da ƙuda zai bi." 

A raunane Saudat ta ce. "Ni ma shiryawar nake son na yi ne saboda na ga yamma na yi, amma ba cewa na yi ba zan karɓe shi ba, na faɗa mata..."

"Ki shirya ki je ina?" Mama ta katse ta a tsawace sannan ta ci gaba da faɗin. "Kunyar da kika saba ba ni ita kike so ki ƙara ba ni a gurin bikin ko me Saudat? Ina zaman zamana ina tarona cikin mutunci da girma ba za ki janyo mini ƙaranta a wajen surukai har biyu ba, musamman ma iyayen matar Zubair da suke masu arziƙi da wayewa da ta amsa sunanta wayewa, to ba zai yiwu ba, babu inda za ki je kina yawo da hijabi zugwi-zugwi bare ki janyo mini abin faɗe." Sai da ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi sannan ta iya furta. "Ba hijabi zan saka ba, fabric ɗin da kowa zai saka ni ma shi zan saka." Kallon sama da ƙasa Shamsiyya ta yi mata ta tuntsire da dariya, cikin izgili ta ce. "To ai gara ma ki je da hijabin, don wallahi ɓata mana sha'ani kawai za ki yi, kin san jikinki ba ɗaukar kaya yake ba, wanka ba ya kama ki don haka gara ki haƙura kawai ki zauna ki taya masu su girki aiki shi ya fi dacewa da ke." 

"Daina ma ɓata bakinki Shamsiyya babu inda za ta je wallahi, ana sabgar arziƙi ba za ta ɓatan rai ba, Salma ma idan ta gan ta ba za ta ji daɗi ba, don ko cikin ƙawayenta ba kowa ta gayyata ba gudun kar su ɓata mata taro, bare kuma ita da gara su ma suna ɗan gayun nan ko yaya ne." 

Wata Ƙanwar Mama da ke zaune a ɗakin tana shiryawa ta ce. "To ai Maman Rasheeda da kin bari ta je, saboda idan tana shiga cikin mutane ne za a samu ta waye har ta samu mashinshini ko za a samu ta shiga daga ciki." Taɓe baki Mama ta yi cike da takaici ta ce. "Wallahi babu wani abu da za a yi wa Saudat da zai saka ta waye, don babu haƙilo da ƙoƙarin da ban yi ba amma kullum jiya i yau, shi ya sa na tattara ta na watsar ta je ta ƙarata, indai duhun kai ne babu inda zai kai ta sai turbar da na sani."

"Gaskiya dai yadda kike da gayu da son kwalliya da sabgar girma ban taɓa tunanin za a samu irin Saudat a ƴaƴanki ba." 

"Hmm." Kawai Mama ta ce ta ci gaba da laluben magi za ta bayar a zuba a miya ana jiran ta. 

Inda sabo Saudat ta saba da irin waɗannan abubuwan da wariyar launin fata daga mahaifiyarta da ƴan'uwanta da kyarar da suke nuna mata, ba ma kamar Yaya Rasheeda, da ta tabbatar da tana nan sai ta saka ta kuka saboda maganganun da za ta caccaɓa mata kamar ba ciki ɗaya suka fito ba. Jiki a sanyaye ta karɓi Affan ta goya ta shiga jijjiga shi, tana tsaye har Shamsiyya ta yo wanka ta zo ta shirya a gurguje cikin wani yadi da ya haska farar fatarta, rigar ta kama ta sosai ta bayyana komai na jikinta, amma maimakon Mama ta yi mata faɗa sai ma koɗa kyan da ta yi take yi ita da ƙannenta. 

Baki a washe Mama ta ce. "Don ma ba ki yi make up ba da sai kin fi haka fitowa." Tana zira takalmi mai tsini a ƙafarta ta ce. "Lokaci ya riga ya ƙure ne, amma gobe dinner ai dole na yi, kuma yau ɗin ma na ji har su Yaya Rasheeda suna cewa ba za su yi ba." 

Saudat ta ɗauka za ta karɓi ɗanta ne, amma sai ta ji tana ba ta sallahun inda za ta ga diaper ta canza masa idan ya yi kashi da kuma madarar da za ta haɗa masa idan ya tashi. Da mamaki Yayar Abbansu da ta shigo ɗaki a lokacin ta ce. "Lallai Shamsiyya, sai ka ce ba yayarki ba kike ba ta wannan umarnin ba ladabi ba komai?" Da sauri Ƙanwar Mama ta ce. "To ai ta zama yayar yanzu tunda ta yi aure har ta ɗanɗani zafin haihuwa." 

Da kallo Saudat ta raka Shamsiyya idanunta cike da ƙwalla, saboda kawai ta zaɓi saka hijabi ta suturta jikinta akan wannan shigar ta bayyana jiki ya sa kowa ya tsane ta? Ko kuma tana da wani aibu ne bayan rashin iya gayu da duk inda ta je sai an kushe ta? Tun tasowarta tun tana ƙarama ba ta da farinjini ko kaɗan, kyara da tsangwama su take samu a gurin mutane a kodayaushe, duk da nasu ba ya yi mata ciwo sosai kamar na mahaifiyar da ta tsugunna ta haife ta. Ganin hawaye na ƙoƙarin zubo mata ya sa ta yi yunƙurin barin ɗakin, amma Mama ta hana ta a tsawace da faɗin. "Ina za ki je kuma? Jira fa nake Affan ɗin ya yi bacci ki kwantar da shi ki je ki ɗebo mana ruwa, tun ɗazu aka ce na tankin ya ƙare ga shi babu nepa ga almajirai ba su taso ba sai shida." Tsabar mamaki ba ta san lokacin da ta ƙame a inda take ba, ɗiban ruwa a shekarunta, ƙanwarta ta biyu fa ake aurarwa, ta tabbata ko cikin yaran da suka zo bikin ba za a rasa masu iya ɗebo ruwan ba. 

"Ba za ki je ba ne kika tsaya mini a ka?" Mama ta faɗa cikin hargowar da take yi mata magana a kodayaushe. 
Kai ta girgiza ta dawo bakin gado ta sauke Affan a hankali gudun kar ya farka sannan ta fice daga ɗakin zuciyarta a ƙuntace. Kanta a ƙansa ta ƙara ratsawa ta cikin mutanen da suka cika tsakar gidan ta je ta ɗauki bokiti ta ɓoye a cikin zunbulelen hijabinta, tun kafin ta ɗauko ruwan har wata irin kunya ta rufe ta, addu'a kawai take Allah ya sa babu wadatar mutane a wajen.

Ta je ta bugo ruwan ta ɗauko ta dawo ta tarar ƙofar gidan a cike da abokan Ya Zubair suna ɗaukar hotuna tare da tsokanar shi irin wadda ake yi wa kowanne ango, shi kuma sai sakin fara'a yake da take ƙara tabbatar da farincikin da yake ciki, amma yana hango ta ya tamke fuska tamkar bai taɓa dariya ba, musamman da ya san wasu abokan nasa sun san ƙanwarsa ce. 
Ɗaya daga cikin abokan nasa ne ya zungure shi yana nuna Saudat da hannu ya ce. "Wannan ba ƙanwar nan taka ba ce?" Kamar an yi masa dole ya ce. "Ita ce mana." 

"Kamar ba ƴar gidanku ba amma, duk kun fita kyau da fari da wayewa, ita kullum cikin burma hijabi kamar wadda ta zo daga ƙauye ba tashin birni ba." 

Aminin Zubair ɗin ne ya amshe zancen da faɗin. "Ga shi an haɗa ta da ɗiban ruwa, ana bikin yayanta da ƙanwarta gaskiya ba a duba mata ba." Ya ƙarashe maganar yana sakin dariyar shaƙiyanci. Daidai lokacin Saudat ta zo gilmawa ta kusa da su a hanzarce don kauce wa idanuwansu da suke bin ta da shi kamar za su cinye ta, Zubair da ke bin ta da kallon raini ya ja tsaki ya ce. "Shegiya ai ɗiban ruwan ne ya dace da ita, kowa yana abin da ƙuda zai bi a duniya amma ban da yarinyar nan, wallahi har Mama wani lokacin cewa take ko dai an canza mata ita ne a asibiti? Saboda mu duk ba haka muke ba, ƙauyanci da gidadancin nata ya yi yawa." Duk yadda ta so daurewa sai da ta ɗaga kai ta kalle shi don kalmar shegiyar da ya kira ta ba ƙaramin dukan zuciyarta ta yi ba.

***** *****

Zuciyar Juraij na wani irin bugu ya yi parking a harabar ƙaton gidan da ya shiga, sai da ya jingina kansa a jikin kujera yana mayar da numfashi na wasu mintuna a ƙoƙarinsa na daidaita nutsuwarsa sannan ya fice daga cikin motar ya nufi cikin gidan. 

Bayan ya yi knocking an buɗe masa ya shiga parkourn bakinsa ɗauke da sallama, matar da ke tsaye suna shirya dinning ita da yaranta ƴanmata guda biyu suka amsa masa cikin mamakin ganin shi da safe haka.

"Ina kwana Hajiya." 
Ya faɗa cikin girmamawa.

"Lafiya ƙalau Juraij." Ta amsa ba yabo ba fallasa tare da ci gaba da magana. "Malam ɗin yana part ɗinsa ka shiga." Kai ya jinjina mata ya nufi ƙofar da za ta sada shi da ɓangaren Maigidan, ganin haka ƴanmatan suka haɗa baki gurin gaishe shi da sauri, hannu kawai ya ɗaga musu ya shige. Hajiya ta taɓe baki tare da faɗin. "Faɗin ran yaron nan yana ƙona mini rai wallahi, shikenan kullum a cukule kamar wanda ya shiga gasar rashin fara'a." Murmushi Muhibba ta yi ta ce. "Ni kuma ba ƙaramin burge ni yake ba.."

"Mtsss." Hajiya ta katse ta da jan tsaki sannan ta ce. "Haka kuka iya, ba ku da aiki sai yabon shi ku da Malam, kun manta abin da ya yi mana a gidan nan kamar bai taɓa sanin mu ba." Ta ƙarashe zancen tana jan ƙwafa.

"Hajiya wannan daban, amma Yaya Juraij ba ruwansa, yana da kirki da..."

"Na ji! Zancen ya ishe ni haka, je ki ci gaba da kwaso sauran kayan a kitchen, na haɗa na Malam ku kai masa, don tunda wannan mutumin ya zo kuma fitowar Malam ba yanzu ba."


Sallamar Juraij haɗe da buɗe ƙofar part ɗin Malam ya saka shi ɗago kai daga duba wani littafin addini da yake, tattausan murmushi ya saki tare da amsa masa sallamar. 

"Lale maharbin da MURUCINA."

Kai kawai Juraij ya jinjina masa yana jin sassauci na tafarfasar da zuciyarsa take yi masa, hakan ya tabbatarwa Malam da akwai wani abu.
Tun kafin ya ƙarasa Malam ya miƙe bayan ya ajiye littafin hannunsa ya miƙa wa Juraij hannu suka yi musabaha.

"Bismillah." Ya faɗa har lokacin da murmushi akan fuskarsa mai cike da haiba yana nuna wa Juraij kusa da shi. 
Ƙasa kawai ya yi da kansa yana sauke numfashi da sauri da sauri, ya lumshe idonsa da suka sauya kala yana sauraren bugun da zuciyarsa take yi masa kamar za ta faso ƙirjinsa ta fito. Cike da kulawa Malam ya kama hannun Juraij ya zaunar da shi ya fara bubbuga kafaɗarsa a hankali alamar rarrashi tare da furta. "SUBHANALLAH! LAHAULA-WALA-ƘUWWATA ILLA BILLAH!" Maimaitawa Juraij ya shiga yi a hankali don ya fahimci me yake nufi, sun ɗauki mintuna a haka sannan malam ya sake shi ganin ya fara dawowa cikin nutsuwarsa ya koma kusa da shi ya zauna ya dube shi a tsanake ya ce. "Yanzu Lokacin kasancewarka a gurin aiki ne, a yadda na san ka kuma ba ƙaramin abu mai muhimmanci ba ne zai saka ka bar office ka zo nan, duk da yanayinka kaɗai ya alamta mini ba lafiya ba don ruwa ba ya tsami banza, ina fata dai ba jikin mahaifin naka ne ya....." Kwankwasa ƙofar parlon da aka yi ya katse Malam, umarnin shigowa ya bayar, Suhaila ta turo ƙofar bakinta ɗauke da sallama, bayan sun amsa ta ƙarasa ta ajiye tiren hannunta a kan Centre table sannan ta juya ta fice.

Malam ya ƙara duban Juraij a karo na biyu ya ce. "Ina sauraren ka, me ya faru?"

"Sun kashe Sheikh Adnan!"

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Sheik Adnan din? Yaushe? Su waye? Ya Hayyu ya Ƙayyum, Hasbunallahu wa'ni'imal wakil!"

"A daren jiya! Su suka kashe shi! Azzaluman da suka saba ɗaiɗaita mana rayuwar al'umma." 
Ya ba shi amsa a rarrabe ƙirjinsa na ɗagawa da komawa.

Salati da sallallami Malam kawai yake yi cikin tsananin razani da gigita, a rikice ya ce. "Saboda lecture ɗin da ya yi a huɗuba ranar Juma'a ne ko? Tun a lokacin na kira shi na ce kar ya sake, mutanen nan ba imani ne da su ba, barin su da Ubangijin da ya halicce su shi ne abin da ya dace mu yi tunda babu yadda muka iya da su."

"Har wanne lokaci za mu kai a ƙasar nan muna ƙin hoɓɓasawa mu ƙwaci kanmu? Mutane ne fa su kamar mu, yadda suke yin duk abubuwan da suka ga dama haka mu ma za mu dinga ɗaukar mataki a kansu!" 

Cike da damuwa malam ya ce. "Tabbas haka ne mutane ne su ma kamar mu, sai dai muna da banbanci da su ta kowacce fuska, su sun zaɓi duniya ne akan lahirarsu, sun zaɓi tsafi da shirka da zubar da jinin muminai don samun duniya, shi ya sa Ubangiji yake yi musu talala ya ba su sa'a akan dukkan abubuwan da suke yi, wanda yake saka su ganin kamar  wayonsu da dabararsu da isarsu ne suka ba su, shi ya sa da zarar mutum ya yi yunƙurin yaƙar su ko fallasa wani sirri nasu suke kawar da shi nan take..."

"Haka za mu zauna a yi ta tafiya kenan Malam? Suna mayar mana da mata zaurawa, su mayar da ƙananun yara marayu? Dole mu ma sai mun dage mun ƙwaci kanmu, idan ba haka ba watarana sai dai mu wayi gari mun zama bayinsu, numfashi ma sai sun so za mu yi, babban abin da yake ƙara baƙanta mini raina yadda duk wata ɓarna da suka yi sai sun bar alamar da za a gane su suka yi, suna yi mana izgili da nuna ba mu isa mun yi komai a kansu ba, tunda da suna yi a ɓoye, amma daga lokacin da hankali ya kai kansu aka farga da su suka fara bayyanawa, wanda hakan yake nuna sun yi ɗin mu yi duk abin da za mu yi, to za su gani! Za mu yi abin da ba su taɓa zato ba da yardar Allah! 

Numfashi Malam ya sauke tare haɗe hannunsa guri guda ya tallafe haɓar fuskarsa, a raunane ya fara faɗin. "Kar ka manta Juraij ina daga cikin waɗanda suka fara farga da wannan ƙungiyar gami da yunƙurin yaƙar su, amma babbar illa da suka yi mini a matsayin barazana ya sa na janye ƙudirina ba don abin ya daina damu na ba, na koma gefe na zuba musu ido kawai ina kai ƙarar su gurin mai duka akan ya yi mana maganin su, tunda idan sun fi ƙarfinmu ba su fi ƙarfinsa ba shi." 

Miƙewa Juraij ya yi ya zura hannayensa a cikin aljihun wandonsa, sai da ya shaƙi iska ya fesar sannan ya fara magana cikin ɗacin rai. 

"Ba zan iya ci gaba da jurar yadda suke lahanta rayuwar al'umma da rushe musu farinciki a duk lokacin da suka so ba, rantsuwar da na yi kafin fara aikina ba za ta tashi a banza ba, da izinin Allah yadda na kafa ƙudirina a kansu ba ja da baya sai na ga abin da ya ture wa buzu naɗi." Ya yi taku biyu tare da ƙara murtuke fuskarsa kamar yana gabansu, a kaushashe ya ce. "Yanzu aka fara wasan da ni da su, domin tun lokacin da na yi arba da gawar Sheikh Adnan na yi wa kaina alƙawarin shi ne ɓarna ta ƙarshe da za su yi matuƙar ina numfashi in sha Allah!"  Jinjina kai Malam ya yi ya ce. "Na san taurin ranka da nacinka akan duk abin da ka saka a gaba tun kana yaro, amma ka sani ba komai ba ne ake son ganin baya kuma ake gani ba, wani abun gobara ne daga kogi da maganinsa sai dai Allah kawai, ba mu da sanin inda mutanen nan suke, ba ma sanin lokacin da suke aikata ɓarnarsu, ba mu da ƙarfin iko kamar su, manyan ƙasa ne da masu mulki da masu madafan iko da masu dukiyar da ba mai iya ja da su, kana kallon dai yadda duk malamin da ya fito ya yi magana ko yaya take a kansu suke sai sun yi masa kisan gilla, kai ma na san labarinka da ƙudurinka ya daɗe da zuwa gare su, don ciwon da mahaifinka yake yi na daɗe ina hasashen daga gare su ne." 

"Duk da haka ba zan karaya ba Malam, kai kaɗai ne hope ne, ka ba ni ƙwarin gwiwa kawai tare da ci gaba da yi mini addu'a don Allah."

Takawa Malam ya yi ya dafa kafaɗarsa tare da sakin murmushi, cike da ƙarfin zuciya ya ce. "In sha Allahu ina tare da kai a kodayaushe Juraij! Ina ji a jikina wannan jajircewar taka za ta taka muhimmiyar rawa a cikin al'umma wajen inganta musu rayuwa, fatan nasara da sa'a MURUCINA, Ubangiji yana tare da kai gaskiya, in sha Allah zai ba ka kariya da sa'a akan waɗannan azzaluman." Sai a lokacin fuskarsa ta ɗan saki, ya saki ajiyar zuciya a hankali ya ce. "Na gode." Daga haka ya yi masa sallama ya tafi bayan Malam ya yi masa tayin tsayawa ya karya ya ce masa sauri yake ana jiran shi a office. 

Tagumi Malam ya rafka yana saƙa abubuwa da dama a cikin ransa na tsoron kar allura ta tono garma.