Chapter 19
Suna haɗu ido, ta balla masa harara kamar idanunta za su fado, tare da ɗauke kai tana taɓe baki, tamkar wacce ta ga kashi. Da sauri ya buɗe baki da nufin sake yi mata magana, sai dai ganin yadda ta kawar da kanta daga gare shi ya sa shi yin shiru, kamar wanda aka tsawatarwa.
Kaɗan ya fito da harshensa ya lashe, kamar yadda kare ke yi, yana sakin wannan makirin murmushin nasa, wanda shi da kansa ya san wannan murmushin ne makaminsa a kan duk wata ƴa mace.
Sai dai shi da kansa yana mamakinta, tare da tunanin wani dalili ne ya sa ita hakan baya tasiri a kanta.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa a lokacin da na ji kina gari, na yi maza na zo, saboda naga my lovely daughter-in-law.”
Ummi, wadda har yanzu take kallonta da murmushi a fuskarta, ta faɗa.
Da sauri Mammy ta ɗaga manyan idanunta ta sauke su a kanta, yayin da a hankali yanayin fuskarta ya fara sauyawa, daga kyakkyawan murmushin da ke samun leɓenta tun ɗazu zuwa ɓacin rai saboda kalmar ƙarshe da ta fito daga bakin Ummi yanzu.
A hankali ta daga kanta da nufin ta saci kallon Ummin,
Amma ganin yadda take kallonta ya sa ta saki ɗan ƙaramin murmushi, sannan ta janye idanunta daga kanta, ta sauke kai ƙasa a hankali, kamar wacce ta yi wa sarki sharri.
Haidar, dake zaune, ya kasa hana kansa kallonta ko da na daƙiƙa ɗaya, kamar wanda aka manne masa idanuwansa a kanta. Yana jin kamar idan ya ɗauke kansa daga gare ta a yanzu, ba zai sake samun damar more ganin nata ba.
Yayin da a cikin zuciyarsa yake jin wani irin zazzafar soyayyarta da shauƙin kasancewa tare da ita na ƙara taso masa fiye da ko yaushe. Saboda ganinta da yake yi a yanzu, ji yake kamar ya je ya rungume ta, ko hakan zai ɗan rage masa wutar abin da yake ji a game da ita.
Sai dai ina shi da kansa ya san bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne, domin ya kwana da sanin duk iskancinsa kuma ko da giyar wake yake sha, bai isa ya riƙe ko hannunta ba. Balle har ya kai kansa ga rungumar ta, ita da ba ta buƙatar ko ganin fuskarsa ma.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da kwatar da kansa a jikin kujera ya fitar da harshensa yana kashe leɓe, kamar yadda hakan ya zame masa ɗabi'a a duk lokacin da yake bukatar wani abu.
Wace ce Ummi a taƙaice?
Aunty Sakina kenan, babbar aminiya, kawa kuma abokiyar shawarar Hajiya Zainab (Ammi). Wannan shakuwar da ke tsakaninsu ya sa ake musu kallon tamkar waɗanda suka fito ciki ɗaya, saboda tsananin ƙauna da tausayin juna. Aminantakarsu ta samo asali ne tun da lokacin ƙuruciyarsu. Duk da kuwa yadda mahaifiyar Zainab ba ta ƙaunar wannan alakar tamkar mutuwarta.
Sai dai ina duk yadda ta kaɗa ta raya hakan ya cutura saboda Sakina sai ita ce babbar kawar Zainab kuma aminiyar dogaronta wajen shawarwari. Tun lokacin da suke yara, Zainab ba ta iya aikata wani abu, walau na alheri ko sharri, sai da shawarar aminiyar tata,
Dukansu asalin Fulani ne daga Jihar Adamawa, sai dai aure ya raba su. Sakina ta yi aure a Abuja, inda take zaune a Asokoro, yayin da Zainab ta yi aure a Kano. A lokacin nan, mahaifiyar Zainab ta yi murna sosai, tare da tunanin sun rabu kenan, kasancewar ba gari ɗaya suka yi aure ba.
Sai dai ina, duk da wannan banbancin wajen zama da nisan garuruwa, bai taɓa komai daga cikin aminantakarsu ba.
Saboda da duk lokacin da aka yi hutun makaranta
Sakina kan tattara yaranta su je kano su yi hutun su acan.
Yayin da
Mazajen su basa cewa komai
Saboda wannan ƙaƙƙarfan aminci da ke tsakaninsu su ma ya shafi don sun zama manyan abokai, duk da cewa ba sa zama a gari ɗaya, kuma harkokinsu ma ba ɗaya ba ne.
Amma aminantakar matayensu ce ta sa su ma suka zama abokan shawara, suna taimakon juna a kowace irin matsala, musamman Daddy, saboda ya fi mijin Sakina harka.
Saboda wannan kusanci da shakuwar da ke tsakaninsu, ya sa ƴaƴan nasu suke ɗaukar su tamkar uwa ta biyu. Musamman Mammy, tana matuƙar ƙaunar aminiyar mahaifiyarta, kasancewar ita ma Ummi tana nuna mata ƙauna sosai, don a wasu lokutan har Mammyn take ganin kamar Ummi ta fi Ammi sonta. Yaran Sakina ma duk suna ƙaunar Ammi a matsayin uwa. Wannan yasa yanzu duk suka zama ɗaya ta hanyar hadu zuri'arsu aure.
Sakina tana da ƴaƴana uku. Aliyu Haidar, kyakkyawan saurayi mai shekaru ashirin da takwas, shi ne ɗanta na fari, sa’ar Fahad, kasancewar ba ta haihu da wuri ba.
Bayan Haidar sai A’isha, matar Umar. Daga ita kuma sai autarta Fadila, wadda tun ba yau ba aka sa aka musu rasa da Fahad, jira kawai ake ta kammala karatunta a sha biki.
Kuma a duk lokacin da ko wannensu ya gaji da zama a Abuja, zai tattara ya zo Kano. Hakanan ƴan Kanon ma, a duk lokacin da suka ji sun gaji da zama a garinsu, za su tattara su je Abuja su zauna.
Musamman Haidar, wanda a da, kafin Daddy ya mayar da Mommy England wajen kaninsa da zama, kusan rayuwarsa gaba ɗaya ya fi yawa a Kano. Saboda tun tana yarinya ƙarama, Haidar yake matuƙar ƙaunarta, kuma babu wanda bai san da hakan ba. Musamman Ammi da Ummi, da suka fi kowa farin ciki da hakan.
Sai dai an samu matsala a gefe biyy. Mammyn, ita da Daddynta, ba ta ƙaunar Haidar ko kaɗan. Wannan kuwa ya samo asali ne saboda tsauraran ra’ayinta na ɗaukar maza da soyayya a matsayin ɓata lokaci da shirme tun tana yarinya ƙarama har yanzu da ta girma.
Duk da kasancewar Haidar saurayi ne kyakkyawa, mai ji da ƙuruciya da kuɗi, son kowace budurwa, kuma ƙin wacce tarasa. hakan bai sa ta so shi ba. Shi kuma yana nan kamar maye don duk yadda za ta nuna masa cewa ba ta sonsa, baya ganewa, saboda shi irin mutanen nan ne masu nacin tsiya da saka ran samun duk abin da suke so. Gani yake dukka abin da zata yi sai dai tayi amma ya lashi tokobin aurenta ko bata so.
Tun tana ƙoƙarin kauce masa, har ta fara fito masa a zahiri. Tana faɗa masa ba ta sonsa, kuma ba ta jin kunyar faɗa masa hakan a gaban kowa, ko da kuwa Ummi ce.
Aunty Aisha ta sha faɗa mata cewa:
“Mammyn, ko don saboda yadda Ummi ke sonki, bai kamata ki dinga faɗin ba ki son Haidar a gabanta ba.”
A duk lokacin da Aisha ta yi mata wannan magana, sai ta ɗauki hakan a matsayin ƙinda A’isha din ke yi mata ne ya sa take faɗin haka. Saboda ita a ganinta, hakan ba komai ba ne, don kawai kana bayyana gaskiyar abin da ke cikin zuciyarka.
Sannan duk wanda ya yi mata maganar Haidar ma, kai tsaye take cewa ba ta sonsa. Hatta Ammi, ba komai ne ya sake bata wannan ƙarfin gwiwar ba kuma sai ganin Daddy yana bayanta.
Shi kuma Daddy, Yana da nasa dalilin kin amincewa da Haidar din. Amma sai ake ganin kamar saboda abar kaunar tasa ba ta son Haidar din ne ya sa yake goyon bayanta, shi kuma ya kwale a hakan.
Wannan shi ne alaƙar da ke tsakanin iyalan biyu, da kuma dalilin da ya sa sunan “my daughter-in-law” da ya fito daga bakin Ummi ya sa Mammy ta sauya yanayinta a take.
10:56pm
THE UNKNOWN MAN
Cikin tsananin saurin da ya fi kama da gudu, yake taka ciyawar da ke gefen titin fita daga cikin garin, yayin da yake juyawa lokaci zuwa lokaci yana kallon bayansa, tamkar wanda ya san bai kulla gaskiya ba.
Sai da ya yi tafiya mai ɗan nisa kafin ya tsaya a gefen hanya, dai-dai bakin wasu shaguna da ke a rufe.
Duk da kasancewar wajen cike yake da ciyayi, ga kuma duhun da ya mamaye wurin saboda dare, hakan bai hana shi sake kutsawansa ciki yana ɓuya ba, ba tare da tunanin ko akwai maciji ko wata dabba da zai iya cutar da shi ba.
Jikinsa sanye yake da baƙaƙen kaya, daga sama har ƙasansa, ta yadda ba za ka iya gane ko wane ne ba.
A hankali, sautin tafiyar baƙar motar da ke tunkarar wajen ya fara yin ƙasa, alamar mai motar na ƙoƙarin tsayawa.
Jin ƙarar motar ne ya sa mutumin da ke labe cikin ciyayin yunƙurin lekowa a hankali, ta yadda ba za'a iya gani shi ba, cike da sanin makamar aikinsa.
Sai dai kafin ya isa wajen, hasken motar ya haskesa nan take, fuskarsa da ke sanye da face mask ta bayyana.
Da sauri ya ɗaga hannayensa duka biyu ya kai su kan fuskarsa, yana ƙoƙarin kare idanunsa daga tsananin hasken motar da ya dallesa.
Cikin wani irin salon isar da saƙo, aka kashe hasken motar, tare da sake kunna shi a lokaci ɗaya.
Ganin hakan ya sa mutumin sauke wani ajiyar zuciya mai ƙarfi, tare da sauke hannayensa, saboda samun tabbacin ya tsira daga waɗanda suka haɗu a hanya kafin zuwansa wajen da suka yi za su haɗu da ogan nasa.
Cikin sauri ya isa gaban motar ya tsaya, tare da ƙwanƙwasa gilashin a hankali, kamar yadda ya saba a duk lokacin da suka haɗu.
Duk da na cikin motar ya ji sa, amma sai ya yi banza bai motsa ba kusan mintuna uku, kafin mutumin ya ɗan zuge tinted glass ɗin kaɗan, ta yadda za a iya jin maganarsa ba tare da an ga fuskarsa ba.
Cikin tsananin zumudi da rawar jiki, kamar marokin da ke gaban sarki, mutumin ya ƙara matsawa gaban motar, kamar zai zube gwaiwarsa a ƙasa, ya ce:
“Ranka ya daɗe, Allah taimake ka. Na ji kira na amsa, kuma ni mai amsa kiranka ne a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Ba zan gaza ba har sai lokacin da ƙudiri da burin tsawon shekaru suka cika.”
Ya ƙara maganar tare da zame baƙar hular kansa. Nan take kansa ɗaya da ya sha askin malu-tal ya bayyana. Duk da kasancewar duhu ne a wajen, hakan bai hana ƙaton kansa da ke nan kashi-kashi bayyana ba.
Shiru wajen ya yi kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya buɗe baki, cikin wata irin murya mai kaushi da tsauri, ya ce.
“Abun hari na yawo a gari. Ku kasance cikin shiri a kowane lokaci. Aikinku zai iya farawa.
Sannan ku sani, bana son shirme. Ba na son a samu wata matsala. Idan har haka ta faru, ban san ku ba.”
Ya kai ƙarshen maganar tare da fito da wani baƙin baƙo daga cikin motar, ya miƙa wa mutumin.
“Wannan shi ne kayan aikinku. Akwai komai da komai da za ku iya buƙata a ciki. Idan ka bari aka gani, ka nemi wanda ya ba ka.”
Ya ƙarashe maganar tare da cilla masa bundle ɗin dubu-dubu har guda biyar.
Cikin rawar jiki, mutumin ya sa hannu yana tattara kuɗin, saboda guda biyu ya samu damar cafewa, sauran sun kai ƙasa.
Da sauƙi ya ɗago tattaro kudin. Duk da face mask ɗin da ke fuskarsa, hakan bai hana a ji sautin murmushinsa ba.
Cikin tsananin jin daɗi da zumudi, ya kankame kuɗaɗen a kirjinsa, kamar mai shirin yi wa motar sujjada.
Cikin muryarsa da ke kama da ta riƙaƙƙun ƴan daba, ya ce:
“Sai oga. Allah ya taimaki oga, da yardar Mai Sama aiki zai gudana fiye da yadda kake tunani. Tabbas za ka yi mamakin hakan. To amma yaushe kake so a ƙaddamar?”
“Ku shirya hakan.”
Yana kai wa nan ya maida glass ɗin motarsa ya rufe, tare da ja ta a guje, kamar zai tashi sama.
Cikin tsananin farin ciki, mutumin ya bi motar da kallo har sai da ya tabbatar ya yi nisa sosai. Sannan ya sa hannunsa saman face mask ɗin da ke rufe fuskarsa, a hankali ya zare.
Nan take fuskarsa ta riƙaƙƙun ƴan daba, mai ɗauke da tsofaffin raunukan da suka daɗe da warkewa, ya bayyana. Duk da cewa a cikin farin ciki yake, amma kallon ɗaya za ka masa ya tsorata ka, saboda tsantsen rashin imanin da ke bayyana a kan fuskarsa.
Cikin farin ciki ya shiga buɗe baƙon da ke gabansa. Ganin abin da ke ciki ya sa ya ɗaga kansa sama, tare da buɗe hannayensa duka biyu, tamkar wanda ke shirin rungumar abu.
Da ƙarfi, kamar ba dare ba, ya bushe da wata iriyar mahaukaciyar dariyar rashin imani, tamkar wani zararre. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya dakata.
Nan take fuskarsa ta sauya daga farin ciki zuwa tsananin baƙin ciki lokaci ɗaya, kamar an yi ruwa an ɗauke, kamar ba shi ne mutumin da ke ɓaɓɓaka dariya na ƴan daƙiƙun da suka wuce ba.
Cikin wata kakkausar murya mai ɗauke da fushi da alkawarin da aka daɗe da ɗauka, ya ce
"Dama na faɗa ai, IDAN HAR KERE NA YAWO, ZABO NA YAWO, WATA RANA DOLE NE A HAƊU.
Yallaboi, wannan ɗin ba aikin ka ba ne kai kaɗai. Wannan wani tsohon buri ne... buri da muradun da suka kasa cika tsawon shekaru.
Wannan ɗin alkawari ne da ɗan gida ya daɗe da ɗaukar wa uban gidansa. Wahahahahahahahah...”
Ya sake bushewa da wani irin dariyar muguntar da ta fi ta farko ƙarfi.