Hs 26
by @legendspen
_Page 26_
"Ni gaskiyya bansan nawa za ayi ba, kai nawa kake so?."
"Ina da abinda nake so ne bayan wanda kike si Fulani."
"Zan iya shawara ko?." Dariya ya yi sanan ya ce. "Ki yu shawarar ki, zuwa Anjima zamu zo ni da su Anas gaba dayanmu, sai ki kara su Amrah."
"Tom Annur, Allah ya kawo ku lafiya."
"Amin Fulaninah."
"Shegiya soyayya, Allah ka aurar damu." Jannah ta faɗa, dariya suka yi baki daya sanan Amrah ta ce. "Fulanin Annur, ya aka yi?."
"Ya ce Events din Mom guda uku ne, kuma ƙawayena sha biyar ake so, duk ashobe da kayan da zansa za a akwo su yau zuwa gobe." Wata uwar guɗa Jannah ta saki sanan ta ce. "Kaji masu yi dan Allah."
"Ke banza ki bari muƙarasa ji." Amarah ra faɗa, sanan ta ce. "Naki fa."
"Ya ce wai guda nawa muke so, muyi shawara."
"To yanzu dai Bhatool ai inaga baki da ƙawaye sama da sha biyar ko?." Jannah ta faɗa. "To ai ko sunfi sha biyar ɗin cire su za ayi." Amrah ta faɗa. "Kunga dangin Abba za a dauki Furee da Habi, dangin Mama akwai guda uku, sai kuma Na'ima da wata Rukayya yan nan unguwar."
"Bakwai." In ji Jannah. "Wai shikenan?." Amrah ta faɗa. "Gaskiyya su nake tunanin xan iya sawa a harkar bikina, sai dai ko wata fauziya dake kusa da gidan Yaya Karima."
"A'a ƙyale ta, ni su Furee din ma da an ciresu."
"Ke Amrah gaskiyya abarsu, ni wallahi Bhatool kin burgeni da kika sunansu, yanzu ragowar takwas din sai a haɗa, idan ansami extra sai asa Fauziya ɗin ko?."
"Ta ina za a sami extra?." Amrah ta sake faɗa. "Ke jarabar duniya, yanzu ya zamu yi da bakwai."
"Nima ai kallonta kawai nake." Bhatool ta faɗa. "Dalla malamai, ko a makaranta biyar sun fita, sabida ina so mu bayar a cikin team din su Hafsa alƙali, kinsan idan muka bayar muka ce Free Ashobe wallahi zasu je kuma kinga su biyar ne, muka bawa biyu ai sai mun haɗasu faɗa."
"Mene ribar mu dan mun haɗa su faɗa, mu bar su suje da muguwar aniyarsu ko banza yanzu cikinmu biyu sun yi aure, kuma sauran biyun ma in Allah yayarda muna hanya." Jannah ta faɗa. "Idan ma za a bayar a cikinsu Fadila za a bawa ita kaɗai muke mutuncin da ita, har a waya ta kirani jiya, amma wallahi sauran babu shegiyar da zan bawa dan ubansu." Bhatool ta faɗa. "To yanzu dai kinga Amrah ke, Sai ni, sai kuma Suhaima, sai Fadila, to asa Fauziya ɗin, biyar kenan."
"Kun manta da su Lawisa?." Amrah fa faɗa, dariya sukayi sanam Jannah ta ce. "Aikuwa da muncika butulu, bikin Labiba mukaje har aka ce munfi kyau a akan su namu kuma mu manta da su." Dariya suka sake yi sanan suka yanke shawara. "Yanzu bara naje na ji yadda zamuyi da Mama akan nata event ɗin sai mu tsayar da namu ko?." Bhatool ta faɗa tana mikewa.
"Ke Bhatool fita idona, babu wani event da zan yi."
"Haba Mama,gaskiyya a'a ko daya ne ki yi."
"Zaki mun dole ne?." Waya Bhatool ta dauka ta kira Abdul. "Kai na ina?."
"Ina inda kika aike ni Uwata."
"Dalla maganar serious nake maka."
"Munfita ni da Yaya Karima, muna nan muna bauta miki kina mana iskancin, kayan gado Set uku muka siya miki wajen 7million duk jarin shago na ya ƙare." Dariya ta yi sanan ta ce. "Ai daman danni kake fita neman dan albarka, yanzu wai Mama ce ba zata yi event ba."
"A'a wasa take miki zata yi."
"Zaka mun dole ne." Mama ta faɗa daga inda take. "Ni na isa Hajiya Mama, amma dai zakiyi inji babbar Yaya."
"Zai zo ne anjima zamuyi magana yadda za a tsara komai, su za su yi guda uku shine ya tambayeni Mama fa."
"Kece za ta yi guda ɗaya, yanzu ma zamu biya mune mi Hall."
"Shikenan dan albarka." Daga haka ta kashe wayarta ta ta shi zuwa ɗaki. Bayan ta yi zauna ne ta ce. "Mama daya, yanzu shi zamu fitarwa da Ashobe, sai ladies night namu ko?."
"Eyh Bhatool, amma ba za ayi cocktail ba harda abokan Ango." Amrah ta faɗa. "Eyh gaskiyya dai zai yi kyau, amma bara muji dame suka zo."
~~~~~Red bricks.
Senate ne da team din abokansa baki daya, wansa ya haɗa da Anas, Juraij, Salman, sai kuma Faruq. Senate ne ya ce. "Duk wasu events na Mama already ta gama da komai, sanan yanzu Anas ya ce zai haɗa night party da ƙawayenta, i think komai ya isa haka kar bidi'a ya yi yawa." Faruq ne ya ce. "Yanzu ka ta shi muje wajen nasu, a tsayar da komai ba mu da enough time fa." Mikewa suka yi zuwa inda Mom take, itama duk ta yi busy baƙi ta ko ina, bayan sun gaisa ne ya ce. "Mom zanje gidansu Bhatool, zamu tattauna yadda events ɗin zasu kasance."
"Okay, ita kayan da zata sa an kawo su ɗazu gaba daya, na ƙawayen na ta ne ba a kawo ba har yanzu." Amma ga cards nam kowanne events ga 50cards nan, banda ƙawayenta masu Ashobe."
"Okay Mom, kawo cards ɗin kayan nata idan an kawo wancan a haɗa gaba daya."
"Okay." Ta faɗa tare da ta shi, kallon jama'ar dake gidan ya yi, yau saura kwana goma cif Bhatool ta tare a gidansa. "Gaskiyya ina cikin alheri." Ya faɗa yana murmushi. "Ungo sanan ka ce mata, kar su wahalal da kansu akan cards din mu na na su event ɗin, idan bai da yawa."
"Tom Mom." Ya faɗa tare da amsa ya fice, a waje ya sami abokan nasa kowa cikin motarsa. "Ina zamu da motoci haka kuma?."
"Zamu raka ango ne."
"Dan Allah kar su yi yawa, daya ma ta ishemu duka?."
"Allah Senate A'a, kai ka shiga ta Anas amma mu duka daga nan gidajen mu zamu huce." Juraij ya faɗa, sauran kam duk suka shige nasu motocin, ba dan ya so ba ya shiga suka tafi. A hanya ya yi mata text gasu nan sun tawo. "Kun ji gasunan sun tawo, sai mu ta shi mu gyara." Ba musu suka ta shi suka hau shiri.
Ba daɗewa suka kara so, gaba dayansu suka zauna a barandar gidan kan kafet, bayan an cika gabansu da kayan ciye-ciye ciki har da Furee da Habi, su Amrah dai sai ƙara kame jiki ake. "Amare namu." Anas ya faɗa yana murmushi. "Angwaye namu." Amrah ma ta faɗa, nan suka kwashe da dariya gaba dayansu, daga nan suka shiga tattauna yadda komai zai kaya musu, har da sanye cocktail din da zasu yi da abokan ango da ƙawayen amarya, sanan suma suka ware Backlorate party da za suyi abokan Angon ranar da zasu yi ladies night, sanan Faruq ya dauki nauyin duka rogowar Ashoben ƙawayen Amarya, suka yanke matsayar gobe zasu shiga kasuwa da Jannah da Amrah su zaɓo komai, bayan sun gama ne aka bar Senate da Bhatool ya bata cards da kuma mukkin gidan sabida masu zuwa Kafi (jere), sanan ya ce zai a aiko da kayan da zata sa da na ƙawayenta zuwa gobe har da Mint (kuɗaɗen liƙi).
Sai yamma su Abdul suka dawo, lokacin duk ƙawayen Bhatool sun tafi sai su Furee da hari, komai da aka siyo ya yi kyau sosai sanan aka yanke shwarar gobe zasu a afara zuwa ayi jerin jibi kuma a ci gaba, cikin daren aka aiko da kayan nata da Ashoben ƙawayen, kuwa ya ji daɗin lissafi da ta yi mussaman da tasa Furee da Habi.
~~~~~~Washe gari
Masu kafi sun sha matukar mamakin ganin girman gidan, domin kuwa a iya part daya Bedroom uku ne, falo ya kai biyar ga maka-makan kitcehn guda biyu, hala ma daya part ɗin, Yaya karima ce ta ce. "Chaɓ, ai wallahi mu zuba abinda muke da shi."
"Daman ai abinda za ayi kenan, kar ma asanar da wancan fitinanniyar yarinya, bare ta tayar mana da hankaki." Anty Sailuba ƙanwar Mama sa ta zo daga Jigawa ta faɗa, suna cikin jerin ne wata motar kayan ta shigo, itama dauke da kayan gado seat biyu, kujeru seat uku, waya Yaya Karima ta dauka ta kira Abdul ta tambaye shi ko shi ya kawo, amma ya ce A'a, nan ta kira Umma ita ma ta ce A'a, Bhatool ta kira itama ta ce A'ah. "To kira mijinki ko shine?."
"Banajin shine Yaya, ko ɗazu mun yi waya kuma bai faɗan ba."
"Kirashi dai."
"Tom." Ta faɗa tare da kiransa, bayan ya ɗaga ne ta ce. "Wai kai ne ka tura da kaya gida?."
"Eyh nine Bhatool, kinsan gidan yana da girma so wanam kawai na yi sune ba tare da kowa ya sani ba, kuma banaso kowa ya sani, sanan ki faɗa musu daya part ɗin banda shi, Anty Shuwa ta dauki nauyin cika komai na shi."
"Tom bara na faɗa musu, kayi magana da masu zuwa kasuwa?."
"Eyh, sun ce suma hanya."
"Okay." Ta faɗa tare da kashe wayar ta mai da kiran na ta ga Yaya Karima. "Ai daman na yi tunanin shine." Yaya Karima ta faɗa bayan Bhatool fa faɗa mata shine, daga haka suka ci gaba da jerensu.
Legendspen
***