MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 5

by @maimunabala209

MATAR GIDA 005



SHUUKRAN



P5




Zama Ɗalha ya yi kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn,bayan sun gama gaisawa,shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakkani cike da girmama Ɗalha ya fara magana ya ce ''Mama daman Fauziyya ce bata jin daɗi tun ɗazu nake ta fama da ita taƙi shan magani,shine na kawo maki magungunan ko zata kaɓar a hannuki'' Mama Uwani ta ce ''Allah sarki,Ubangiji ya bata lafiya,to ita Amirah fa?me yasa ba ta bata ba? ko kadan Fauziyya bata son shan magani haka Amirh ke fama da ita duk sanda bata da lafiya'' Ɗalha ya ce ''ta yi tafiya ne,kiran gaggawa aka yi mata daga gida'' cikin yanayi na ɗan damuwa Mama Uwani ta ce ''Allah dai yasa lafiya irin wannan tafiya haka ko sallama babu'' Ɗalha ya ce rasuwa aka yi masu'' Mama ta ce ''Allahu akbar Allah ya jikan musulmai Allah Sarki in Allah ya yarda zan kira da safe na yi mata ta'aziyya'' shiru Ɗalha ya yi bai ce komai ba Mama ta ce ''ina magungunan?" tashi ya yi daga inda yake zaune ya ajiye wa Mama ledar magani Mama Uwani ta sa hannu ta ƙarɓa,cikin hikima Mama ta bawa Fauziyya magani daga haka ta goyata,da kyar dai ta samu ta koma barci,mayar da duban ta yi ga Ɗalha ta ce ''in ka koma gida ka samu towel ƙasa cikin ruwan sanyi ka goga mata jiki da shi ka yi ta mata haka bayan duk awannin biyu in har safe ba'a samu canji ba ka kai ta asibiti rashin nono ne'' Ɗalha ya amsa da to,Ɗalha na shirin barin parlour Mama Uwani ta ce ya jirata bayan wasu ƴan mintina ta fito daga kitchen riƙe da wani babban food wormer ta dire shi gaban Ɗalha ta ce ''ka kaiwa ƴan jikoki na wannan shinkafa ce dafa duka,in Allah ya kaimu gobe zan yi tafiya Alhaji ya kirani baya jin daɗi,in Allah ya kaimu gobe zan je can Legas,can suka maido shi,karfe huɗu zan bar gida da anyi sallar asuba zamu kama hanya''godiya Ɗalha ya yiwa Mama Uwani, ya fito daga gidan jiki babu kwari shi da yake tunanin kawo su Sudais wajenta,kafin a yi bikinsa da Unaisa saboda har ga Allah  baya tunanin zai iya dawo da Amirah,Mama Uwani babbar mace ce da akalla zata kai shekaru sittin a duniya Allah ya azurtata da ƴaƴa biyu mata wanda tuni sun yi aure yanzu haka ita kadai ke zaune cikin gidan mijinta Alhaji Abubakar babban soja ne bai cika zama ba hakan yasa ya sama mata ƴan aiki biyu zaurawa,kullum suna zuwa su yi mata ayyukan gida,kafin sallar magrib suke tafiya gidajensu,wannan dalilin ne yasa Ɗalha tunanin kawo mata yaran,jin ta ce zata yi tafiya gobe yasa hankalin sa tashi amma bai nuna a fili ba kawai ya yi mata godiyar abinci da ta basu,daman yana shirin zuwa siyawa yaran abinci bayan ya koma gida.











Bayan komawarsa gida bai tsaya ko ina ba sai kitchen inda ya tarar da kwanuka jibge cikin sink,food wormer dake hannunsa ya ajiye kan carbin daga nan ya wuce ɗaki ya shimfida Fauziyya kan bed ɗinsa,bai bar ɗakin ba saida ya yi sallar isha'i,parlour ya koma inda ya tarar da yara duka zaune cikin parlour Sudais da Afef na buga game inda Sumayya da Ummu Abiha ke wasa da dull baby shi kuwa Rayyan na can yana aikin tiƙar rawa ba kiɗi,Suhail na kwance ƙasan tiles yana surutai shi kaɗai,gayrar murya Ɗalha ya yi amma dukkansu babu wanda ya kalle inda ya ke hakan yasa ya yi magana cikin ɗaga murya ya ce ''ku ba kwa ji ni?,ta shi ku je ku yi sallah'' ya kare magana yana zare masu ido duk suka tashi sun yi hanyar ɗakunansu banda Rayyan da har sannan yana aikin rawa,kiran sunansa Ɗalha ya yi cikin ɗaga murya ya ce ''Rayyan what are you still doing there?" da sauri Rayyan ya waigo ya kwaɓe fuska alamar yana son yin kuka ya ce ''you scared  me Dady,why are you shouting'' baki buɗe Ɗalha ke kallon Rayyan dake share hawaye,fuska babu walwala Ɗalha ya ce ''wuce ka je ka yi alwala ka yi sallah kafin na zane ka'' kallon Ɗalha Rayyan ya yi murya can ƙasa hawaye na zuba daga idonsa ba ya ce ''Dady yunwa nake ji l want to eat'' wani mugun kallo Ɗalha ya masa hakan yasa Rayyan wuce ɗakinsu ɗan yi alwala,shi kuma Ɗalha ya wuce kitchen plate ɗinda suka ci abinci da rana ya fara wankewa har ya gama wanke plate ya yi morping kitchen basu fito ba hakan yasa ya zuba masu abincin da Mama Uwani ta basa ɗazu,da kansa ya kai abincin daining yadda ya haɗawa Sudais da Afef da kuma Rayyan da Suhail a waje ɗaya Sumayya kuma da Umu Abiha a plate ɗaya kamar yadda yaga Amirah ke yi,zama ya yi bisa ɗaya daga cikin kujerun parlourn da niyya cin nasa abinci ya ji muryar Afef ya kurma ihu hakan yasa ya tashi ya nufi hanyar ɗakinsu bayan shigarsa ɗakin yaga Afef kwance ƙasar ɗakin yana kuka Rayyan na tsaye gefen sa hannusa riƙe da buta yana hararan Afef cike da mamaki Ɗalha ya ce ''me ke faruwa wa ya dake sa?" Sudais dake cire takardu daga jakarsa ta makaranta ya ce ''Rayyan ne ya dake sa'' Ɗalha ya ce ''what!! Rayyan lafiyarka ƙlau?Afef sa'an ka ne da zaka dake sa?" shiru Rayyan ya yi bai ce komai ba sai kuma ya ce ''tun ɗazu ya shiga tiolet ya ƙi fita har na  gaji da jiransa shi yasa'' Ɗalha ya ce ''shi yasa me? shi yasa ka dake sa,saboda ba ka da kunya Afef bai girme ka ba?" Rayyan ya ce ''da watanni sha ɗaya ya girman in ji Mumy'' Ɗalha ya dake bakinsa ya ce ''rufe min baki marar kunya wuce ka ji ka yi alwala'' babu musu Rayyan ya wuce bathroom ɗinsu yana matsar kwalla Ɗalha ya mayar da duban sa ga Afef ya ce ''kai kuma tashi sakare kawai,oya wuce ka je ka yi sallah'' Afef ya tashi daga kwanciyar da ya yi ya nufi praying mata dake cikin ɗakin nasu ya tada sallah,shi kuwa Sudais tun ɗazu da ya faɗawa babansu abinda ya faru bai sake kallon inda suke ba,Ɗalha ya mayar da duban sa ga Sudais ya ce ''ka yi sallar ne?" Sudais da har sannan idon a kan littattafan dake gabansa ya ce ''eh'' kallon takardun dake gaban Sudais Ɗalha ya yi kafin ya ce ''me ka ke yi da littattafan?" Sudais ya ce ''ina son yin homework ne amma ban gane ba'' shiru ya yi yana kallon Ɗalha kamar yadda shima yake kallonsa ya ce ''dan Allah  Dady ka taimake ni mu yi tare,kullum Mumy ce ke yi mana'' numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''na ji zan taimaka maka amma sai kun gama cin abinci sai muyi'' Ɗalha ya daura da ''ka dauki homework ɗin ka kawo min parlour da mun gama cin abinci sai muyi'' cike da farin cike Sudais ya ce ''to Dady'' daga haka Ɗalha ya fito daga ɗakin bai tsaya ko ina ba sai ɗakin su Ummu Abiha da ƴar uwarta Sumayya ganin su ya yi tsaye gaban madubi suna shafa hoda,fuskar Sumayya bajau da hoda ta baza jam baki har gefen bakinta kusa da  kunne ganin Ɗalha yasa ta saki murmushi ta ce ''Dady kalle na yi kyau ko'' ta faɗa tare langwaɓar da kai ita kuma Ummu Abiha sai cewa ta yi ''Dady ni na mata yanzu zan yi nawa'' ta kare magana fuskarta dauke da murmushi









Zuwa wannan lokaci Ɗalha ya ji ina ma akwai inda zai kai yaran ko na kwana ɗaya ne ya huta,wannan wacce irin rayuwa ce a gaskiya bazai iya ba,wata iska ya fesar daga bakinsa kafin ya ce ''kun yi salla?" Sumayya ta ce '' munyi amma ni ban yi alwala ba Ummu ce kadai ta yi itama muna sallah ta shiga bathroom ta yi popo,kuma bata yi flushing ba kuma bata yi sabon alwala ba'' shi dai Ɗalha binsu kawai yake da ido Ummu Abiha dake tsaye gaban madubi hannunta riƙe da gazal ta ce ''zan yi flushing gobe da safe'' dafe kai Ɗalha ya yi gaba ɗaya ya gaji da lamarin yaran,hakan yasa ya mayar da duban sa ga Ummu Abiha ya ce ''drop that thing ki wuce ki je ki yi flushing kafin na zane ki'' ya ƙare magana yana zare mata ido babu musu Ummu Abiha ta ajiye gazal ɗin gaban madubi ta wuce bathroom kamar wata munafuka,bayan Ɗalha ya haɗa kan yaran duka zama suka yi nan kasar parlour domin cin abinci kowa na cin abinci amma banda Sumayya sai binsu take da ido Ɗalha ya lura bata cin abinci hakan yasa ya tambayeta ''me ya faru kin sa abinci gaba ki na kallo?" langwaɓar da kai ta yi tare da maƙe kafaɗa ta ki magana Ɗalha ya ji kamar ya duke ta tsabar haushi wai me ki damun yaran nan ne? so suke ya yi hauka ko me? tunanin yake cikin zuciyarsa cike da jin haushi ya ce ''ba magana na ke ma ki ba why are you not eating?" Ummu Abiha ta kalleta sai kuma ta mayar da dubanta ga mahaifinsu ta ce ''duk dare bata cin abinci da kanta Mumy ke sa mata a baki'' a takaice Ɗalha ya ce ''to yau ba Mumy ki ci da kanki'' Sumayya ta kallesa ta ce ''a'a Dady ka bani da kanka'' banza Ɗalha ya yi mata ya cigaba da cin abinsa,saida ya gama cin nasa kafin ya fara bawa Sumayya,bayan sun gama cin abinci ya haɗo masu ruwan wanka,nan ma dai ya sha magana,ya yi magana ya fi a kirga ya kuma raba faɗa sau bakwai,karfe goma daidai ya samu dai sun yi wanka kuma duk sunyi barci,bayan ya tabbatar da sun yi barci ne ya shiga gyaran gidan,ya dauke awa guda wajen gyaran gidan kafin ya samu ya yi wanka,karfe sha biyu daidai Fauziyya ta farka Ɗalha dake zaune kan darduma yana azkar ɗin yamma da bai samu ya yi ba, tashi yayi ya nufi bed ɗinsa Fauziyya ta tashi zaune tana goge ido lokaci guda tana kiran Mumy daukan ta Ɗalha ya yi ya daurata  cinyarsa yana kai hannu kuncinta ya ji zafin jikin da sauki ba kamar ɗazu ba,kwanciya ta yi jikinsa lamo cikin hausarta da bai fita da kyau ta ce ''Dady in je Mumy ba ni momo'' tana nufi zata je wajen Mumy,Mumy ta bata nono Ɗalha na shirin magana ya ji damshi a cinyarsa da sauri ya ɗagota yana kallon wandon dake jikinta yaga wandon ya jiƙe kaɗan ya kai hannu ya taɓa wando akwai pampers me hakan ke nufi ɗazu a gidan su Unaisa bayan Aisha ta wanke mata jiki a ka fito da ita da pampers a jikinta kenan har pampers ɗin ya cika nan ya shiga tunanin yadda zai yi da ita,daukan ta ya yi zuwa bathroom ya cire mata pampers ya gyara mata jiki shima ya gyara  jikinsa,ɗakin Amirah ya wuce ya buɗe drower kayan Fauziyya ya ciro pampers da wasu kayan,bayan ya sa mata riga ne ya riƙe pampers a hannu ya shiga jujjya yana tuanin yadda zai sa mata kawai wata tunani ya faɗo masa,daukar Fauziyya ya yi zuwa ɗakinsa bayan shigarsa ɗakin wayarsa dake kan bed site drower ya dauko nan yaga tarin misscalls ɗaga Unaisa kusan guda goma,data ya buɗe ya shiga You tube ya yi typing yadda ake sawa yara pampers nan suka fitar masa da vidoes kala kala,sai da ya kalla vidoes huɗu kafin ya gane yadda ake sa pampers,doguwar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya sawa Fauziyya pampers ita ko ta shiga dariya tana faɗin ''clap for Dady'' Ɗalha ya laƙaci hancin ta ya ce ''good girl'' 









Kwaɓe fuska Fauziyya ta yi alamar tana son yi kuka kafin ta ce ''Dady in ca momo'' Ɗalha ya yi kamar bai ji ta ba ya ce ''za ki sha tea?" da sauri Fauziyya ta ce ''eh'' saboda ba ƙaramin yunwa take ji ba nan Ɗalha ya haɗa mata tea bata wani sha sosai ba ta ce ya ishe ta,Ɗalha ya karɓi kofin ya ajiye kan bed site drower ya rungume Fauziyya yana buga mata baya a hankali yana faɗin ''sleep my princess'' ya dauki kusan mintina talatin a haka kafin ya samu ta yi barci ba ƙaramin gajiya Ɗalha ya yi ba ga wani mugun barci da ya cika masa ido bayan ya tabbatar Fauziyya ta yi barci ya rufe idonsa ba tare da ɓata lokaci ba barci mai nauyi ya dauke shi,misalin ƙarfe biyu cikin barci Ɗalha ya ji kukan Fauziyya kamar a mafarkin jin kukan ya cigaba da kusanto sa yasa ya buɗe ido Fauziyya ya gani zaune,da kyar ya samu ya buɗe ido saboda nauyin da idonsa suka yi masa sakamakon barci da ke cike cikin idonsa cikin muryar barci ya ce ''my princess me nene?" cikin kuka  Fauziyya ta ce ''injin yunwa in ci tuwo'' ta kare magana tare da  sakin wani  sabon kuka,tsabar mamaki Ɗalha bai san sanda ya tashi zaune ba ya ce ''me ki ka ce'' Fauziyya ta ce ''tuwo Dady'' Ɗalha ya dafe kai murya can ƙasa yana furta kalmar ''innalillahi wa inna'ilahi raji'un''







SHUUKRAN