MATAR GIDA PAGE 6
MATAR GIDA 006
SHUUKRAN
P6
Ɗalha ya dauki a ƙalla mintina biyar zaune kan bed,sautin kuka Fauziyya na ƙara chaza masa kai,bayan wasu ƴan sakkani ya mayar da dubansa ga Fauziyya ya ce ''my princess za ki sha tea'' Fauziyya ta maƙe kafaɗa ta ce ''a'a inci tuwo Dady'' ta kare magana cikin kuka,bai sake cewa komai ba kawai ya tashi daga bed tare da daukan Fauziyya ya nufi hanyar kitchen,bayan shigarsa kitchen hannu ya kai jikin switch ɗin kitchen ya kunna,nan take hasken ya gauraye kitchen ɗin,wata ƴar karamar kujerar roba dake kitchen ɗin Ɗalha ya zaunar da Fauziyya a kai,har sannan kuka take amma ba da karfi ba,bayan ya zaunar da ita ne ta shiga goge idanunta, shuru Ɗalha ya yi yana tunanin yadda zai yi tuwo cikin wannan daren can dai wata dabara ta faɗo masa,tunawa ya yi Fauziyya na son cin indomie sosai,hakan ya sa ya mayar da duban sa gare ta ya ce ''my princess za ki ci indomie?" da sauri Fauziyya ta amsa da ''eh'' ba tare da ɓata lokaci ba Ɗalha ya nufi pantry ya dauki indomie ɗaya da kwai,kamar yadda take so haka ya dafa mata,sau da yawa yana lura da yadda Amirah ke dafa mata indomie wani lokacin ma sai yay ta cewa Amirah ta dena dafawa Fauziyya indomie haka saboda a ganinsa kazanta ce,bayan an daura indomie ɗin a wuta an sa masa ɗandano dake zuwa cikin ledar, yana daf da dahuwa sai a fasa kwai da albasa a zuba cikin indomie,kamar yadda Amirah ke yi mata,bayan ya gama dafa mata indomie daukanta ya yi da hannu ɗaya hannu ɗaya yana riƙe da plate ɗin indomie,nan cikin parlour ya zaunar da ita ya ajiye mata plate ɗin indomie a gaba shima waje ya samu ya zauna kafin ya mayar da dubansa gareta ya ce ''oya eat'' kallonsa Fauziyya ta yi ta ce ''papi'' ma'ana da zafi tashi ya yi zuwa daining ya dauke mafici dake daure kan daining table ya shiga aikin fita mata bayan ya tabbar zafin ya rago ne ya ce mata ''yanzu babu zafi ki ci'' maƙe masa kafaɗa ta yi ta ce 'a'a Dady ka ba ni'' babu yadda ya iya haka ya shiga bata a baki, bata wani ci sosai ba ta ce ta koshi, ya ce ''tashi muje ki wanke baki'' babu musu ta tashi ta nufi hanyar kitchen Ɗalha na biye da ita hannunsa riƙe da plate ɗin indomie,muryar Suhail ya jiyo daga parlour inda ya ce ''Dady ina jin yunwa''Ɗalha ya ji kamar ya fasa ihu tsabar haushi,Allah Allah yake ya gama ba Fauziyya indomie ya je ya kwanta ba ƙaramin gajiya ya yi ba,ba tare da ya juya ya kalle Suhail ba ya ce ''oky za ka ci indomie?" ya faɗa yana karasa shiga kitchen,cikin muryar barci Suhail ya ce ''eh'' ya faɗa yana goge idonsa, Ɗalha ya ce ''to zo ka dauka'' ya faɗa tare da daura plate ɗin kan carbin ɗin kitchen,daukar Fauziyya ya yi ya zaunar da ita kusa da sink dake kitchen ya fara wanke mata hannu daidai lokacin Suhail ya shigo kitchen tare da daukan plate ɗin indomie,wani irin ihu Fauziyya ta sake ganin Suhail riƙe da plate ɗin indomie ta fara kuka tare da nuna wa Ɗalha Suhail tana kiran ''Dady Dady'' Ɗalha ya gane abinda take nufi amma bai kulata ba ya cigaba da wanke mata hannu,bayan ya gama wanke mata hannu ya share mata baki ya saukar da ita nan ta shiga tsalle tana ihu dole ita Suhail ya aji mata indomie,kwanciya ta yi ƙasan kitchen tana kurma ihu shi kuwa Suhail cin indomie yake hankali kwance ganin kukan nata ba mai karewa bane yasa Ɗalha komawa cikin pantry ya dauki ɗaya daga cikin ƙananun juice da ya siya masu ɗazu ya ba Fauziyya da fari ƙin amsa ta yi saida Ɗalha ya nuna mata zai zane ta kafin ta yi shiru ta ƙarɓi juice ɗin ta fara sha,Ɗalha bai bar kitchen ɗin ba saida Suhail ya gama cin indomie sannan ya raka sa zuwa ɗakinsu,bayan shigar Suhail ɗaki Ɗalha na tsaye daga bakin kofa yana kallon Sudais da Afef yadda suke barci,yana shirin rufa masu kofa idonsa ya sauka kan Afef inda ya riƙe wando yana juye juye kan bed da alama fitsari yake son yi,da sauri Ɗalha ya sauke Fauziyya daga hannusa ya shiga cikin ɗakin,yana kiran suna Afef da ɗan karfi,sai da ya kira sunan Afef kusan sau uku amma Afef bai farka ba hakan yasa a hankali Ɗalha ya fara buga Afef a ƙafa tare da kiran sunan sa,firgici Afef ya buɗe ido Ɗalha ya ce ''fitsari za ka yi?" Afef ya ce ''eh'' daga haka Ɗalha ya riƙe hannun Afef zuwa bathroom,bayan fitarsa daga bathroom ɗin ya tashi Sudais da Suhail ya ce duk suje su yi fitsari Suhail ya ce ''Dady ni na yi nawa kafin na fita na ci abinci'' Ɗalha ya ce ''oky'' Ɗalha bai bar ɗakin ba saida ya tabbatar Sudais ya yi fitsari,kafin ya wuce ɗakin yaran mata yana riƙe da Fauziyya da ta manne masa kamar chewing gum,switch ɗin dakin ya kunna idonsa ya sauka kan Ummu Abiha dake kwance ƙasan ɗaki ta dunkule waje guda saboda sanyin AC,shiga ɗakin ya yi ya fara tashinta kasancewar bata da nauyin barci yasa ta farka da wuri,kallon ta Ɗalha ya yi kafin ya ce ''me yasa ki ka kwanta a ƙasa'' cikin yanayi barci ta ce ''Sumayya ce ta jiƙa min jiki da fitsari'' gaba ɗaya Ɗalha ya manta duk dare sau biyu Amirah ke tada yaran ta kaisu fitsari,hakan yasa bai ga laifin Sumayya ba,tashinta ya yi ya kaita bathroom ya gyara mata jiki haka ma Ummu Abiha duk Sumayya ta ɓata mata jiki da fitsari,shirya su ya yi cikin wasu kayan kafin ya cire zanin gado ya ajiye cikin bathroom,ruwa a zuba wa katifan ya goge shi duk a daren,bai bar ɗakin ba saida ya kunna fanka ya kuma buɗe tagogen ɗakin kafin ya haɗa kan yaran zuwa ɗakinsa,bayan shigarsu ya ce duk su kwanta,waje ya samu edge ɗin bed ya kwanta wayarsa dake daure kan bed site drower ya dauko ya duba time yaga karfe uku da rabi na dare,iska ya fesar daga bakinsa kafin ya rufe ido yana addu'a cikin zuciyarsa Allah yasa kada wani daga cikin yaran ya kuma tashin sa,tsabar rashin wadatatcen barci ya ji kansa ya yi masa nauyi sosai,yana jin yadda Fauziyya ke matse kwalin juice dake hannunta amma ya ƙi cewa komai,he is so exhauted barci kawai yake buƙata,rufe idonsa ya yi a hankali ba tare da ɓata lokaci ba barci mai nauyi ya dauke sa
A firgice Ɗalha ya farka daga nannauyar barci da ya dauke shi,dalilin muryar Fauziyya da ya ji tana faɗin ''Dady tashi zan popo'' babu shiri Ɗalha ya tashi tare da daukan Fauziyya bai tsaya ko ina ba sai bathroom ɗin Amirah inda ya dauki pur ya daura ta a kai yana nan tsaye kofar bathroom har Fauziyya ta gama ya mata tsarki ya sa mata sabulu,cike da kyankyami ya dauki pur ɗin ya yi desposing popo cikin sit ya yi flushing ya dauki a ƙalla mintina uku yana wanke hannu kafin daga bisani ya dauke Fauziyya zuwa ɗakinsa ya kwantar da ita,shi ma kwanciyar ya yi idonsa ya sauka kan wayarsa dake daure kan site drower,daukar wayar ya yi ya duba time yaga karfi karfe huɗu daidai,tsaki ya yi kafin ya ajiye wayar ya rufe ido nan take barci ya daukeshi,a can wajen Amirah kuwa wani irin zugin da nonowanta ke mata ne ya farkar da ita daga barci a hankali ta tashi zaune tare da rintse idanunta jin yadda n*n* ke mata zafi gashi ya ciko sosai ruwan n*n* ya jiƙe nigth wear dake jikin ta,cike da karfin hali ta tashi zuwa bathroom,cire kayan jikinta ta yi ta sakar wa kanta ruwan sanyi,ta dauki a ƙalla mintina goma tsaye tana jin yadda ruwan ke shiga jikinta,daga karshe ta kashi shawa tare da daukan towel ta daura a ƙirji,cike da hikima,bata bar bathroom ɗin ba saida ta dauro alwala,bayan fitar ta daga bathroom hand bag ɗinta ta dauko inda ta ciro auduga da farar gam da ta siyo ɗazu,zama ta yi bakin bed yadda ta ɗiba audugar kaɗan ta daura a bakin n*n* daga haka ta sa hakori ya yanke gam ɗin kaɗan ta manna shi a bakin n*n* haka ta yi ma ɗayar,doguwar riga materail ta zura,Allah ya taimake ta taga darduma a ɗakin,saida ta karkaɗe darduma sosai kafin ta shimfiɗa ta tada sallah,nafila raka'a huɗu ta yi kafin ta daura da shaf'i da wutri,bayan ta idar zama ta yi kan darduma hannunta riƙe da charɓi tana ja istigfari ta yi sosai kafin ta daura da salatin Annabi (S A W),ta dauki lokaci me tsawo tana jero addu'a'o'i wa ƴaƴanta daga bisani ta shafa,tilawar Alkur'ani take son yi sai dai babu ƙur'ani a ɗakin hakan yasa ta dauki wayarta ta kunna tun da azahar da ta kashe wayar bata sake bi takan wayar ba sai yanzu,bayan ta kunna wayar tasa a flight mode gudun shigar kira,application ɗin kur'ani ta shiga nan ta fara karatu,kiraye kirayen sallar asuba ne ya sa ta dakatar da karatun,bayan idar da sallah ta yi addu'a tare da aji wayar ta cigaba da istigfari har lokacin sallah,bayan ta idar da sallah ta yi azkar ɗin safe tana nan zaune kan darduma ta ji barci ya fara daukanta,nan kan darduma ta yi kwanciyar ta babu ɓata lokaci barci ya dauke ta
Karfe shidda da mintina goma na safiyar Litinin,a firgice Ɗalha ya farka daga nannauyar barcin da ya dauke shi,ganin gari ya fara haske yasa Ɗalha sauka daga bed da wani irin sauri tare da faɗin ''subhanallahi mun makara ke Ummu tashi ku je yi alwala ku yi sallah maza'' Ummu Abiha dake kwance tana barci har sannan,ta gyara kwanciya ta cigaba da barcinta,ganin bata da niyyar tashi ya sa Ɗalha shiga bathroom inda ya dauro alwala ba tare da ya ƙara kallon inda yaran ke kwance ba bayan fitarsa daga bathroom nan cikin ɗaki ya yi sallah kan praying mata,bayan ya idar da sallah ya tashi da sauri ba tare da ya yi addu'a ba,tunawa ya yi yau yana da metting me muhimmaci a office,ya kamata ya bar gida da wuri,saboda metting ɗin karfe takwas da rabi ne,sosai hankalin sa ya tashi tunani ya fara ta inda zai fara tashin yaran zai yi su yi sallah ko shirin zuwa makaranta zai yi masu?sanin kansa ne in ya tashi su sallah za su sashi magana ga rabon faɗa hakan yasa ya kyale su ya wuce kitchen bayan shigar sa kitchen pantry ya wuce inda ya fara tunanin abinda zai dafa masu na breakfast da wanda za su da shi makaranta,karfe biyar suke tashi hakan yasa kullum da abinci kala biyu suke zuwa makaranta,tunawa ya yi duk sati Amirah na yin miya kala kala tasa cikin freezer dan samun sauƙin ayyuka,hakan yasa Ɗalha ya buɗe freezer da niyyar daukar miya in ya so ko farar shinkafa ce sai ya dafa masu da indomie,lokaci ɗaya jikinsa ya yi sanyi ganin duk abubuwan da ya siyo na cefane cikin freezer wasu ba'a ko cire su daga ledar kasuwa ba,danyar tumatir,danyen ƙubewa,danyar nama,danyen kifi,da dai sauran su,numfasawa ya yi murya can ƙasa ya ce ''l can do it'' yayin da yake riƙe da murfin freezer ba tare da rufe freezer ba ya shiga tunanin abinda zai dafawa yaran,bayan dogon nazari karshe dai ya dauki doya da indomie da kwai,ba tare da ɓata lokaci ba ya fara feren doya bayan ya gama ya wanke ta tass kafin ya daura mai kan wuta,wani pot ya dauko ya zuba ruwa ciki kafin ya daura kan gas,freezer ya buɗe ya fidda carrot green beans,ya dauki a ƙalla mintina arba'in kafin ya gama dafa masu breakfast saboda yana tsaka da aiki Rayyan da Suhail da Ummu Abiha suka tashi daga barci bayan tashin su Rayyan ya kama Ummu Abiha da faɗa Suhail kowa na kitchen wajen Ɗalha wai zai taya Ɗalha aiki,da fari Ɗalha ya dauka da gaske aikin Suhail zai taya shi,saboda kullum in Amirah na kitchen za ka ga Suhail da Fauziyya manne da ita,in few minute Ɗalha ya fahimci abinda ya shigar da Suhail kitchen,Suhail yana da yawan cin abinci kome yawan abincin da Amirah zata bashi zai ce mata bai ƙoshi ba koda kuwa ya ƙoshi haka Allah ya halicce sa,surutu yake yiwa Ɗalha babu kakkautawa yana yi yana daukan slice ɗin doya ga tambaya kamar ɗan jarida,daga karshe Ɗalha ya kora shi parlour,nan ya shiga rabon faɗa Rayyan da Ummu Abiha,ji ya zai yi,sai faman ihu ya ke kamar mahaukaci tun da suka tashi kalmomi biyu zuwa uku yake ta faɗa ''kai bari,kai tashi a wajen,ka ajeyi kaza,kai bar kaza haka ya rinƙa yi'' shiru ya yi lokacin da ya tuna duk safiyar duniya Amirah sai ta yi ta ihu da yara,shi kuma ya yi ta jin haushinta wani rana ya yi shiru bazai ce mata komai ba,wani rana kowa yay ta mata faɗa ya ce bata da hakuri da yara,tana damun mutanen unguwa da ihu kamar ita kaɗai ce me yara,karfe 7:20 na safe ya gama dafa masu abinci,ya yi sarving ɗinsu doya a gida sauran ya zuba masu cikin flask wanda za su je makaranta da shi,ɗaya flask ɗin kuma ya sa masu indomie shi za su ci da rana,da wani irin sauri ya shiga parlour lokacin da ya ji sautin kukan Fauziyya Sumayya ce ta dake ta kan ta dauka mata littafi,daukan Fauziyya ya yi ya shiga rarrashinta da kyar dai ya samu ta yi shiru,kafin ya ce duk su tashi suje su yi wanka,Sudais ya ce ''Dady bamu yi sallah ba'' Ɗalha da gaba ɗaya kansa ya gama zafi ya ce ''na sani in kun je makaranta sai ku yi'' duk suka yi shiru suna kallonsa wani tsawa ya yi masu tare da faɗin ''baku ji abinda na ce ba,ku tashi ku je ku yi wanka'' yanayin yadda Ɗalha ya yi magana yasa duka sun firgita sun tashi tsaye Sudais da Afef tuni sun shiga ɗaki,Rayyan dake zaune har sannan shi bai taɓa jin tsoron Dadyn su ba,ko yanzu ma da ya yi masu tsawa bai ji komai ba,hankali kwance yake wasan sa da mot, idonsa kan motar wasa ya ce ''Mumy ce ki yi mana wanka kullum kafin mu je school da dare kuma mu yi kanmu amma fuska da hannu kawai muke wanke da kanmu sauran wanka duk Mumy ce ke yi mana'' cike da mamaki Ɗalha ya ce ''dukan ku bakwai?" Rayyan ya bashi da amsa bayan ya hau kan motar da yake wasa da ita ya ce ''a'a ni da Ummu Abiha da Suhail,sai Sumayya da Fauziyya kawai Mumy ke yi mana wanka yayah Sudais da Afef da kan su suke yi'' har Ɗalha ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya tuna da shekarun yaran,tabbas basu kai su yiwa kansu wanka ba Sudais shekaru 8,Afef 7, Rayyan 6,Suhail da Ummu Abiha 5 ƴan biyu,Sumayya 3,Fauziyya 1/5, haka Ɗalha ya tara ruwa ya yi masu wanka wajen wanka saida ya buge Rayyan saboda cewa ya yi da ruwan sanyi zai yi wanka,haushi yasa Ɗalha ya dake sa,karfe takwas da mintina goma Ɗalha ya gama masu wanka har Fauziyya duk ya shafa masu mai tare suka fita parlour,bayan fitar su parlour ne Ɗalha ya tambaye Sudais inda uniform ɗinsu yake,shiru Sudais ya yi yana karewa mahaifinsa kallo,Ɗalha ya ce ''ba ka ji abinda na ce ba ina uniform ɗin ku kun yi late fa'' Sudais ya yi narai narai da ido kamar zai yi kuka ya ce ''na manta su cikin washing machine'' yana gama faɗin haka ya yi hanyar kitchen da gudu,ƴan uwansa sun shiga yi masa dariya suna faɗin ''mantau ya manta, mantau ya manta'' haka suka rinƙa faɗa suna yi suna tafa hannu kamar waƙa
SHUUKRAN