ZAFIN WUTA

Book one Chapter 1

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000096798 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000096790

 

Chapter 1-5 

 

بسم الله الرحمن الرحيم. 

 

LEGOS NIGERIA 

 

UNGUWAR AGEGE 

 

Wani ƙwararaɓaɓɓen gida ne ginin ƙasa wanda ko arzikin shahen siminti bai samu ba, gida ne ƙarami sosai kuma marar tsayo dan dama waje za'a iya hango kaiwa da komowar mutanen gidan. 

 

Da gudu na fito daga cikin kurkukun gidanmu wa ni dattijo biye da ni hannunshi riƙe da zabgegiya bulala irinta dukan dawakai, gudu ni ke iyakar ƙarfina tare da ihun neman agaji dan saura ƙiris Dattijon ya kama ni damma ina zillewa. 

Shawo kwana yai hannu shi riƙe da jakar bakko, lokacin da ni ke ƙoƙarin bige shi insha kwanar nima, caraf na ji anriƙe hannuna da mugun ƙarfi, wa ta iriyar ƙara na saki tare da gantsarewa jin saukar duka a jikina, kafin in aje numfashi na sake jin saukar wa ta bulalar a bayana aiko na sake gantsarewa tare da kai gwuiwoyina ƙasa saboda yanda zafin bulalar ya ratsani, rufe ni yai da duka babu ƙaƙƙautawa yayinda har lokacin ba'asakarmin hannuna ba, birgima  ni ke a ƙasa ina bayarda haƙuri tare da neman agajin jama'a amma babu wanda ya kula ta kaina. 

 

Sai da wannan dattijon yai min lis yanda ko hannuna ba na iya ɗagawa saboda tsabar yanda na daku sannan ya rabu da ni, wannan matashin kuma wanda ya riƙe hannuna bai sake ni ba har aka gama dukana, bayan dattijon ya juya ya na sababi kamar ze haɗe harshenshi saboda  masifa ya koma ya shige  cikin gida ba tare da ya kula da ko hijabi babu a jikina ba, daga ni sai doguwar riga irinta shan iska wacce duk ta jeme ta ji jiki, kaina ko atziƙin ɗan kwali babu sai baƙin sisilkan gashina da ya sauka har tsakiyar bayana, sanadiyar burkiɗa da nai duk ƙasa ta cika min gashi da jiki. 

Cike da raɗaɗin zuciya na tashi ina karkaɗe jikina har lokacin ban daina kuka ba kuma hannuna na riƙe da na wannan matashin. 

 

Baice da ni komi ba ya ja hannuna ina turjewa amma bai tsaya ba sai da ya sada ni da cikin gidanmu, a gaban wannan dattijon wanda ya yi min duka ya sake ni tare da komawa gefe inda wa ta farar matashiyar ma ta ke zaune ta yi tagumi hannu biyu. 

 

"Mama barka da wuni, munsame ku lafiya." 

 

Matashin ya katse ta daga tunanin da ta ke. 

 

"Lafiya lau Hashim fatan ka dawo lafiya ya hanya ?". 

 

"lafiya lau Alhamdulillah, ga wannan." 

 

Yai maganar ya na miƙo ma ta bakkon hannunshi. 

Cikin sassauta fuska ta amshi ledar  tare binshi da addu'a. 

 

Amsawa yai tare da tashi ya koma wajen wannan dattijon shima ya gaida shi tare da zaro kuɗaɗe daga cikin aljihunshi ya ba shi tare da faɗin. 

 

"Abba ga wannan babu yawa anyi cefane, kuma idan andawo daga sallah idan baku komi ina son muɗan tattauna." 

 

"Ah bakomi Hashimu yaron albarka, ina gaya maka kaf gidannan babu me hankalinka ubangiji Allah ya biyaka da gidan aljanna." 

 

 

Ya faɗa tare da zuran kuɗin a aljihun rigarshi. 

 

Kallo Hashim yai tare da faɗin. 

 

"Mubeenah ki tashi ki yi alwala lokacin sallah ya gabato." 

 

Cikeda masifa Abba yai caram ya ce. 

 

"Yauwa Hashimu gara da Allah ya kawoka a daidai wannan lokacin, wallahi na gaji da halin wannan yarinyar, na gaji da nunamin ita yanzu ta kangare ta balage, kullum cikin janyomin hasifa da tashin hankali ta ke, ace yarinya rai ɗaya amma ta addabi rayuwata ta hana ni sakat, banda damar gindaya doka a gidana sai wannan masifatattar ta nuna ban isa da ita ba, to na gaji wallahi ta kaini ƙarshe na ƙure da bango, kodai ta nemi aiki inda za ta dinga ciyar da kanta ko kuma ta fito da mijin aure in aurar da ita in huta, Allah yana gani na gaji da riƙon wannan yarinyar." 

 

Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Hashim ya sauke, a cikin zuciyarshi ya na karanto A'uziyya jin irin kalaman da Abba ya ke jifar ƴar cikinashi kamar ba shi ya tsugunna ya kawo ta duniyar ba. 

 

Fice wa sukai daga gidan zuwa masallacin da ke cikin kayi don gabatar da Sallar La'asar. 

 

Mama ce ta tashi daga inda ta ke zaune ta nufi Mubeenah ta ɗago ta tare da kama hannunta suka shiga cikin wani ɗaki me ƴar ƙaramar ƙofa, akan wa ta jemammiyar katifa ta zaunar da ita, itama ta zauna tare da kama hannun Mubeena cikin na ta, cikin nuna damuwa ta ce. 

 

"Mubeenah! tabbas Abbanku baya kyauta, sam abubuwanda ya ke miki ba su dace ba, musamman zafafan kalaman da ya ke yawan jifanki da su masu kama da ZAFIN WUTA saboda muninsu, bazan ja da baya ba wajen sake jadadda ma ki cewa ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi a yanzu, komi zai wuce kamar ba'aiba wuya ko ƙunci basa taɓa dawwama, bayan wuya sai daɗi, kicigaba da haƙuri da ƙaddararki, jarabawace Allah ya ke jarabtar ki da ita, idan kika jure nan gaba zakiyi alfahari da hakan, tabbas Ubangiji ya na son ki tunda har ya  jarabce ki da rayuwa me cike da tarin ƙalubale gami da tukitattun al'amurra, ki ci gaba da yin addu'a akan Allah ya zaɓa ma ki abin da ya ke alkairi a gare ki, da yardar Allah kina tare da nasara." 

 

Zafaffan hawaye ne suke ambaliya akan fuskata, yayinda nike tunanin shi har tsawon wane lokaci zan ɗauka ina fuskantar ƙalubalen rayuwa, har zuwa yaushe Allah zai dube ni ya sauƙaƙamin lamurrana kamar sauran mutane, ina so inyi farin ciki kamar kowa, ina so inzama kamar sauran mata sa'annina waɗanɗa ke rayuwa cike da farin ciki. 

 

Shafa bayana Mama ta ke alamar rarrashi, a zuciyarta ta na matuƙar tausayamin da irin rayuwar da na tsinci kaina. 

 

Mun ɗauki lokaci a hakan gani da Mama tai lokacin  Sallah na ƙurewa ya saka ta lallaɓa ni muka fice a tare dan gabatar da Sallah akan lokaci,  da kanta ta zubamin ruwa a ƙaramar butar da ita kaɗai ta rage mana a gidan, kamar talauci a kanmu ya ƙare, kullum ina Allah wadai da irin hallayar Abba ta mamaƙo da bin diddigi, Abba ya kasance cikin irin mutanenan masu hannun ƴan dambe, ga son banza muddin zai ƙyalla ido ya hangi mutum da ɗan maiƙo ba shakka sai yasan yanda yai wajen haɗa alaƙa da shi ta yanda zai yagi rabonsa. 

 

Shiga banɗakinmu wanda ya kasance ɗan ƙuƙut, sam baya da faɗi sai tsawo shima ba canba, raɓewa naj gefe na malala ruwa a ƙasa sannan na biya buƙatata na fito, alwala na gabatar cikin nutsuwa tare da godewa Allah da ya yo ni cikin hasken musulunci, yanda ruwan alwata ke bin muguji ya na gudana haka damuwar da ta cunkushemin zuciya ke kwaranyewa saboda ƙarfafa iymani na da nai a lokacin da nike alwala dan ganawa da mahaliccina.