Chapter 2
Chapter 5-10
Bayan na kammala alwalar na yi addu'a kamar yanda manzo ya koyar, sannan na tashi na zubawa Mama ruwa na kai ma ta butar bakin ƙofar bayan gida na juya na wuce ɗan tsukakken ɗakina me kama da gidan Tantabaru, yamusashe abin Sallah na shimfiɗa sannan na janyo daguwar linkakkiyar hijabina wacce ta ke a tsarkake fes sai zuba ƙamshin turare ɗan ɗure ta ke, zura hijabin nai tare da kabbara Sallah na fuskanci Mahaliccina cike da ƙanƙan da kai, wani irin rauni ne ya ziyarce ni lokacinda gaɓoɓin jikina suka taimaka mani wajen yin Sujjada ina ganawa da Ubangijina, addu'a nike jerowa cike da fata da yaƙinin Allah zai kalle ni ya amsamin roƙona.
Bayan na sallame Sallar nai tazbihi gami da azkar wanda Manzonmu ya koyar, na jingina da bangon ɗakin ina tunanon irin ƙalubalen da ke baibaye da rayuwata tun tasowata har zuwa yanzu, ko a labaran hausa da nike bibiya ban taɓa cin karo da makamanci labari wanda yai shige da nawu ba, kullum cikin fuskantar sabon babin ƙalubale da littafin ƙaddarata ke buɗe min nike, sam bansan farin ciki ba a rayuwata, abu ɗaya na sa ni shine, tarin ƙalubale da wahalhalun rayuwa.
Ina a zaune ina tunanin yanda rayuwa ke gara ni kamar kwallon ƙafa na jiyo maganar Abba tun daga waje, Abba irin mutanen nan ne masu hayaniya waɗanda ba'a sirri da su, idan ya na magana muryarshi na fitowa da ƙarfi sosai, tumbama ace faɗa ya ke wayyo Allah wallahi inada tabbacin har masu wucewa a bakin hanya su na jiyo amon sautinshi, kafin in ankare na ji Sallamarsu a cikin gida shi da Hashim, runtse idanuwana na yi da ƙarfi jikina yahau tsuma kamar yanda nike tsintar kaina aduk lokacinda Abba zai shigo gida, ina jingina shigowarshi da tashin hankalina saboda da zarar ya sako ƙafarshi ya ke fara ƙirƙirar abin da zai saka ya kira ni ya yi min faɗa wa ta ranama harda duka.
Zagi, gori, cin mutunci sune abubuwanda ke maimaita kansu a bakin Abba akaina, nakan cintsi kaina a cikin wasiwasi lokuta dadama idan nai Abba ya jefe ni da mummunar kalma, zuciyata na raya ma ni cewa ba shine wanda yai silar zuwana duniya ba, musamman idan na natsu ina tunani akan yanda ya ke ina nakasa ina naka aje da Sumayya da Habiba, Sumayya da Habiba yayena amma ba uwarmu ɗaya ba, Sumayya Mamace wacce ta haifeta ita kuma Habiba ɗiyar Umma ce abokiyar zaman Mama wacce ayanzu ta tafi da Habiba da Sumayya ganin gida acan Katsina.
"Mubeena! Mubeenah!! ke Mubeena wannan wane irin iskanci da raini ne ace kina ji na sai faman kwaɗa kira nike amma kiyimin banza saboda ke ba yarinyar arziƙi ba ce, idan kika bari daƙiƙa biyu ta shuɗe ba tare da kin fito ba Wallahil'azim na iske ki a ɗakinan sai jikinki ya gaya ma ki."
Tsulum na fito kamar wacce aka hankaɗo na isa gabanshi tare da duƙawa na ce "Dan Allah ka yi haƙuri Abba wallahi Sallah na idasa, kafin in kwashe abin Sallar ne ka kira ni."
"Mtswwwww aikin banza da wofi, da anyi magana ki kama sunne kai ke ala dole ta Allah, ki buɗe kunenki da kyau ki ji abin da zan gaya ma ki, Allah ya so ki yayanku ya ceceki daga hukuncin da na zartar a kanki, ya tsaya tsayin daka ya nemo ma ki aiki a gidan wasu manyan mutane shahararrun attajirai waɗanda kowa ya san da zamansu a Legos ke harma da sauran ƙasashe da garuruwa, idan kika natsu kika yi aiki me kyau to ba shakka mun warke daga wannan addababen talaucin, idan kuma bakiyi abin da ya dace ba har suka gaji suka koroki kamar yanda akai ma ki a gidan Alhaji Ɗan Gaske to babu makawa zaɓi biyu ne ya rage ma ki, kodai ki auri Samual abokina ko kuma ki fita salin alin kibarmin gidana dan bazan iya ci gaba da riƙe ki ba tunda na lura ke me farar ƙafa ce, daga lokacinda Allah ya haɗa ni da ke na fara fuskantar matsaloli a cikin rayuwata."
Ɗif na ji jina ya ɗauke na tsawon lokaci, kwanyata ta shiga maimaita min maganganun Abba da ya ce ni me farar ƙafa ce, daga lokacinda Allah ya haɗa shi da ni ya ke fuskantar matsaloli.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, Hasbunallahu wa ni'imalwalkil, Allahumma ajirni fi musubati, Abba maimaita min maganarka dan Allah ko zan daina kokonto akan abin da zuciyata ke raya min, Abba da gaske ne abin da kake faɗi Allah haɗaka da ni yai, kenan ba kaine ka haifeni ba ko, dan girman zatin Allah ka amsa min."
Tsit Abba yai ya na jin babu daɗi akan yanda na fassara maganarsa, harga Allah ba haka ya ke nufi ba, bai zata hankalina zai kai ga waɗannan kalaman da suka suɓuce ma shi ba, kafin yasan abin yi muka jiyo muryar Umma da ta shigo yanzu ita da su Habiba ta na faɗin.
"Yo Allah na tuba Mubeena miye banbancinki da tsintacciya, ai wallahi baki da maraba da waɗanda ake kaiwa gidan marayu waɗanda ake yasarwa a kan kwalta, akaɗa a raya Abban dai shine ubanki wanda za ki yi taƙama da alfahari da shi, domin kuwa ya yi ma ki sutura tunda ya kasance uba agare ki."
Saurin katse zancen Mama ta yi gudun abin da kan iya zuwa ya dawo idan aka tsawaita zancen.
"A,ah Umman yarah kece tafe da la'asar sakaliya, lalle marhaban da isowa, Biba Sumayya ku shigo daga ciki manah kun toge a bakin ƙofa kamar wasu baƙi."
Taɓe wawakeken bakinta Umma tai tare da jifar Mama da wani banzan kallo sannan ta cire yalolon mayafin cikinta ta sagaleshi a igiyar shanya sannan ta turo ɗan kwalinta gaba ta na faɗin.
"Wallahi ko Zainabu kinganni nan yanzu nai ra'ayin isowa, kuma babu wanda ya isa ya mayar da ni, ya muka same ku?."
Cikin rashin jin daɗin yanda Umma ke gwasaleta idan tai ma ta magana ta ce.
"Muna lafiya lau Alhamdulillahi."
"A,ah kaga uwar gida me Capacity, Hajiya Halima ikon Allah, anbuga da ke ambarki maƙiyanki fadawanki, ke ce ɗaya rak amintaciyya a zuciyar Ibrahima, yo in banda ƙaddara da jaraba irin tawa mi na gano a wajen sauran mata da na nace akansu harda fa ƙaro ma ki kishiya, oh ni Iroro jikan Me ƙosai, In sha Allah daga Zainabu na kulle bazan sake yo maki kishiyaba da yardar Allah."
Abba yai maganar ya na zuro kanshi ya na leƙa cikin jakar Umma wacce ya ke hango walƙiyar ƴan dubu-dubu sababbi dal, kamar wuyanshi zai ɓalle saboda leƙe.
Ita kuwa Umma sai wani fari ta ke da idanuwa tare da ƙara buɗe bakin jakar dan Abba ya samu damar ganin kuɗin da kyau.
Cikin rashin jin daɗin abin da Umma ta yi wa Mama ta tashi tare da jan hannun Mubeena da ke duƙe cikin mawuyacin hali ta nufi ɗakinta da ita.
Habiba da Sumayya ne suka shigo su na yatsine fuska a fizge suka gaisarda Abba, cike da fara'a ya amsa ya na musu sannu da hanya.
"Mama bazan iya ci gaba da jurar waɗanan munanan kalaman daga bakin Abba ba, Mama ki tausayawa halinda nike ciki ki faɗamin wacece ni? shin dagaske Abba shine wanda ya haifeni, ko kuma ni ɗin ba ƴarsa ba ce, miyyasa ya ke banbanta ni da Yaya Babiba da Yaya Sumayya?."
Nai maganar ina me tsareta da rinannun idanuwa waɗanda launonsu ya koma jah saboda kuka, ji nike gaba ɗaya rayuwar ta ficemin, duniyar tai min zafi, banajin daɗin komi, ga zafin zuciya ga zafin dukanda Abba ya yi min.