Chapter 3
Chapter 10-15
Gudu ya ke shararawa a cikin dajin da babu komi sai kukan tsuntsaye da halittu masu firgitarwa, bai tsaya a ko ina ba sai nesa kaɗan da wajen wani kogon dutse, kashe motar yai tare da fito a firgice ya tsaya daidai wani waje inda aka aje wasu tsofaffin ƙorai, cikin rawar jiki ya cire kayan jikinshi tas yai tsirara haihuwar uwarshi sannan ya jefarda kayan a saman ƙoran ya rufe idanuwanshi tare da juyawa ya na karanto wasu damatsilan tsafi ya isa gaban kogon, a zahiri kogon baida wa ta ƙofa sai wa ta ƴar huda ƴar ƙarama wacce wani bakin hayaƙi ke fitowa, ci gaba da karanto damatsalan yai har wannan baƙin hayaƙin ya baibaiye inda ya ke tsaye, ɓat ya bace daga wajen bai samu kanshi ba sai a gaban wani shirgegen baƙin mutum me tsananin muni wanda ya ke tsirara haihuwar uwarshi babu ko ƙyalle a jikinshi sai wani jan abu da ya naɗe al'aurarshi da ita, a hankali matashin ya fara ruɗe idanuwanshi bayan jin saukar wani ruwa me yauƙi akan jikinsa, buɗe idonshi yai tare da yunƙurawa cikin zafin nama yai Sujjada tare da kirari ga wannan ƙaton zindiƙin bokan.
Wa ta arniyar dariyace ta cika kogon wanda ke zagaye da abubuwan ban tsoro iri daban-daban, bayan ɗaukewar sautin dariyar matashin ya ɗago tare da sharce guminda ke tsatstsafo ma shi sannan ya maida hankalinshi akan bokan.
"Kamar dai yanda aka saba sadaukarwar wannan karonma tayi kyau, Zuka ya ji daɗin jininda aka bashi yanzu a shirye ya ke dan ganin ya biya maka dukkanin buƙatunka."
Boka yai maganar bakinshi na amayarda tururin baƙin hayaki harda tartsatsin wuta a lokacinda ya ke magana.
"Ina godiya Boka uban bokaye, hatsabibi uban hatsabibai, Mutum uban Aljannu, zaka dawwama kana juya duniya da mutanen da ke cikinta ta ƙarfin ikon ka."
Wani mumunan murmushi Bokan ya saki wanda ya sake bayyana munin halittar fuskarshi wacce sam babu kyan gani.
"Kana tare da sa'a da nasara saboda biyayyarka agaremu, tabbas akwai shahara a tare da kai burukanka da yawa zasu cika saboda ƙarfin iymanin da ka yi da mu."
Nan matashi ya zube tare da kwararo godiya sannan ya shiga lissafo abubuwanda ya kawoshi, bayan ya gama jawabinshi Bokan ya ɗaga hannunshi sama tare da karanto wasu kalmomi, nan take hanun ya shiga buɗewa har wani dunƙulallen abu ya bayyana, ɗayan hanun nashi me kama da icce ya ɗaga tare da shafa abinda ya bayyana, nan take ya shiga warwarewa yana buɗewa gamida bada tsawo da faɗi, wani madubine ya bayyana.
Mutum ne a kwance kamar gawa, babu abin da ke motsi a jikinshi, babu ko tufafin kirki a jikinshi sai wani farin gyalle da aka lulluɓe iya al'aurarshi, jikinshi kamar babu tsoka saboda tsabar yanda ƙasusuwa suka firfito miraran, fatar jikinshima duk ta taƙune ta yamushe kamar tsoho, wani abin mamaki kuma gashin kanshi na nan kwance luf kamar baƙi ƙirin kamar na larabawa ko indiyawa, wani tururin hayaƙi ne ke fitowa daga ƙofofin gargasar da ke jikinshi.
Wata iriyar dariyace matashin ya kece da ita tare da faɗin.
"Fauzan Shareef Abdallah kaga abin da taurin kai da binciken ƙwaƙwaf ya janyo maka ko, ka ga abin da nike mama gargaɗi akashi ko, indai ZAFIN WUTAR tsafi ne yanzu aka fara, sai na ƙone gangar jiki da ruhinka da ZAFIN WUTA wannan itace makomar da ka zaɓawa kanka, duk wannan iko da dukiyar da kake taƙama da ita sai na yi sanadiyyar ƙarewarsu, sai rayuwarka ta ɗaiɗaice ta wulaƙanta, sai na maidaka abin tausayi a cikin mutane, dole ne in nuna maka nafika tantiranci da hatsabibanci."
Cike da mugunta ya kalli Bokan bayan ya gama magana a fusace ya ce.
"Ya shugabana Boka uban Bokaye ina so ayiwa Aljani Zuka albishirin jinin jinjirin da ƙanwata zata haifa, ina so ya sake ninka azabar da yakewa wannan kafaffen Fauzan ɗin azaba me tsanani ta yanda hatta makusantanshi zasu ji tsoron kusantarshi, so nike asa wuta ta dinga ƙona gangar jiki da ruhinshi, ina so hannu ya gagara taɓa jikinshi, ina nufin a ƙone duk wanda zai taɓa shi, sannan ina so a hana gangar jikinshi saurin ƙonewa saboda banso ya mutu da wuri, ina so ya ɗanɗani uƙuba da azaba me raɗaɗi."
Dariya Boka ya kece da ita tare da dunƙule madubin sannan ya shafa, nan take ya ɓace hannunshi ya dawo daidai, har zuwa lokacin be daina mumunar dariyarba wacce ke kama da saukar aradu saboda tsananin munin muryarsa.