ZAFIN WUTA

Chapter 4

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000080638 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000080630

 

       CHAPTER 15-20 

 

 

 

Wata jaka ce ta faɗo daga sama ji kake timmm, ɗaukarta boka yai tare da faɗin. 

"Angaishe da hatsabibi uban hatsabiban aljannu, aikinka ya na kyau." 

 

Jakarce ta shiga buɗe kanta, wani farin abu ya bayyana acikin wata ƴar farar roba, fito da abin Boka yai tare da miƙawa matashin haɗi da yi ma shi bayani akan yanda  zai yi amfani da maganin. 

 

Bayan ya amsa yai godiya gamida kirari sannan ya rumtse idonshi, nan take ya ɓace ɓat bai ɓulla ko ina ba sai gaban wannan dutsen da ƙorai ke ajiye, kayanshi ya mayar tare da hanzartawa ya nufi wajen da ya aje motarshi ya shiga ya jata da mugun gudu dan duhun dare ya fara. 

 

 

BANANA ISLAND 

 

Tamfatsetsen gida ne wanda ya lashe million kuɗaɗe wajen ginashi, tun daga nesa zaka tabbatar da lallai ko waye ya mallaki wannan gjdan tabbas ba ƙaramin me dukiya ba ne. 

 

 

Wa ta hamshaƙiyar mata ce me tsananin wayewa da gayu ta fito daga wani ɗaki fuskarta da alamar damuwa, yayinda wa ta matashiyar budurwa ke biye da ita a baya ta na zubda hawaye. 

 

Wani haɗaɗɗen ɗaki suka shiga basu tsaya ko ina ba sai gaban gadon da wani marar lafiya ke kwance yana amai, wa ta iriyar ƙara wannan matar ta saki tare da yin baya tai taga-taga kamar za ta faɗi tsabar firgicewa, cike da tashin hankali ta ke faɗin. 

 

"Sulaima kina ganin abin da ni ke gani kuwa, wuta! wuta ce nike gani na fitowa daga bakin Fauzan, please ki ce min ba gaskiya bane mafarki ne, tayaya hakan zai faru, ki gaya min tayaya mutum zai dinga amayo wuta daga cikin jikinshi."  

 

A firgice ta ke maganar hankalinta idan ya yi dubu y tashi, yayinda hawaye ke zaryar saukowa daga idanuwanta su na zuba akan kyakkyawar fuskarta. 

 

"Mommy! wallahi dagaske ne, dagaske Yah Fauzan ne kike gani a cikin mawuyacin hali, shikenan nasan zamu rasa Yah Fauzan, nasan ba lallai ya tashi ba, wayyo Allah ka kawo manah ɗauki, ya Allah ya tashi kafaɗar wannan bawan naka me tsananin biyayya ga umurninka, Ya Allah ka bawa wannan bawan naka lafiya domin ya tashi yaci gaba da bauta maka kamar yanda ya ke yi lokacinda ya ke da lafita, Ya Allah ka yanke ma shi wannan wahalar hakanan." Kukane ya ci ƙarfinta har jikinta na jijjiga saboda tsabar yanda ta ke kuka. 

 

Cike da juriya, tausayi gami da zazzafar soyayya irinta uwa da ɗa matarda aka kira da Mommy ta taka zuwa inda wannan mutumin ke kwance ya na maida lumfashi, yayinda tururin wuta ke fita daga bakinshi da hanci, zama tai a ƙasan gadon glass ɗin da yake a kwance bai ko iya motsi ta na zubarda hawaye, yayinda ta ɗaga hannunta zata ɗaura akanshi wani irin ZAFIN WUTA ya bugo ma ta, da mugun sauri ta janye hannunta tare da sulalewa a ƙasan wajen ta na sakin kuka me ƙarfi , irin wanda ya ke fitowa daga can ƙasan rai, kuka ta ke ta na surutai wanda babu me iya jin abin da ta ke faɗi. 

 

A hankali marar lafiyar ya shiga buɗe idanuwanshi tare da ƙoƙarin juyasu zuwa inda matar ke nuƙe tana kuka, wani irin ja da baya Sulaima ta yi tare da fasa ƙara me tsananin ƙarfi ta na nuna marar lafiyar, ɗagowa Mommy tai daga duƙen da ta ke, aiko ta ci karo da abin da ya kusa tsaida bugun lumfashinta. 

 

"Yah Fauzan dan Allah ka rufe idanuwanka banason gani, please bana son gani tsoro ka ke bani." 

 

Sulaima ta yi maganar ta na saka hannayenta ta dafe idanuwanta da ƙarfi. 

 

A hankali wanda ta kira da Fauzan ya fara karkata kanshi zuwa ɗayan sashen, abin mamaki duk sanda wuyanshi ya motsa da niyyar juyawa sai wajen ya saluɓe ya ƙone, a maimakon jini ko ruwa ya fito sai hayaƙi ya dinga fitowa daganan kuma sai wuta ta kama kamar wacce aka zubawa fetur ko kalanzir. 

 

Mommy da ke kallon abi  da ke faruwa ɗif kukanta ya ɗauke wani irin tsoro, fargaba da tashin hankali ne suka bayyana a fuskarta, yawun bakinta ya ƙafe laɓɓanta suka bushe sai ƙoƙarin buɗe baki ta ke dan tai magana amma ta kasa, ko motsi kasawa tai sai idanuwanta da ke sake firfitowa waje. 

 

 

Duk irin azabar da ya ke ji baj daina motsa jikinshi ba sai da ya juyar  da kanshi saitin glashin da aka kewaye ɗakin da shi, ƙur ya ƙurawa ƙwarangwal ɗin fuskarshi ido ya na jinjina girman ikon Allah, yayinda tsoro ya kamashi ganin yanda idanuwanshi da ya sa ni a farare suka juye zuwa launin jah, ga wani tururi da ke fitowa daga cikinsu, duk da ya na jin azaba a duk lokacin da yai ƙoƙarin yin magana amma haka ya daure cikin ƙarfi hali ya ke faɗi a fili. 

"Inalillahi wa'inna'ilaihi raju'un ya Allah ka ɗauki rayuwata dan sauƙaƙawa mahaifiyata wahalar da ta ke da ni, yah Allah ka yankewa jajirtacciyar uwa hawalar jinyar yaron da ka jarabceshi da cuta, Allah ka ga zuciya ban butulce maka ba akan jarabawar da ta same ni ba, na roƙeƙa ne dan tsananin tausayin mahaifiya me rauni akan ɗanta." 

 

Maganace ta gagareshi domin kuwa tuni bakin na shi ya dare tare da saluɓewa, yayinda Sulaima da ke kaklonshi ta cikin glass ke faɗin. 

 

"A,ah Yaya a,a please kadaina kana jiwa kanka ciwo, dan Allah ka daina magana yah Fauzan." 

 

Ta faɗi ta na kai gwuiwoyinta a ƙasa dan ƙafafuwanta sun gaza bata haɗin kan tsayuwa. 

 

Ganin halin da Mommy ke ciki na suman zaune ne ya sakata sake fashewa da wani matsanancin kukan tare da dafe saitin ƙirjinta jin lumfashinta na barazanar ɗaukewa.