Chapter 6
CHAPTER 25-30.
بسم الله الرحمن الرحيم.
Cike da tsoro Umma ta matso cikin sanɗa ta jijjiga Mama gami da kiran sunanta, amma Mama ba ta amsa ba kuma ba ta motsaba, shiko Abban tafe bango ya yi tare da silalewa ƙasa ya zauna ya na maida lumfashi gami da sharce gumi, Yaya Habiba ce ta nufi inda ya ke ta na ma shi sannu ganin yanda ya diririce duk ya tsure kamar wanda yai jinya.
Da ƙyar Abba yai nasarar ƙwato kalmar "Ruwa." daga bakinshi, aiko da sauri Yaya Habiba ta ɗebo ma shi wanda ke cikin randa, tun da ya kafa kofin bai sauke ba sai da ya tabbatar da yanshe tas sannan ya aje tare da lumshe ido ya na sauraren yanda zuciyarshi ke bugawa da sauri-sauri.
Umma ta tsorata ainun da abin da ya faru hakan ya saka ta haɗa kawunan su Yaya Sumayya tai ɗaki da su, acewarta wai karasu kwashi jangwam.
Shima Abba lallaɓawa yai tare da rarrafawa ya shige ɗakin Umma harda kullo ƙofa, ni da Mama kuma aka barmu anan kamar kayan banza.
A hankali na fara buɗe idanuwana da sukaimin nauyi, kaina ne ya sara da tsananin ƙarfi wanda hakan ya tilasta ni saurin rufe idanuwan nawa, ƙoƙarin tashi na fara yi zaune amma sai naji jikina kamar anyimin tsinannen duka, ko ina ciwo ya ke min, daurewa nai na tashi ina cije baki cike da dauriya dan sosai kaina ke barazanar tarwatsewa, a hankali na buɗe idanuwa da sukai min tsananin nauyi na sauke su akan Mama da ke kwance,mamaki ne ya kama ni ganinta a kwance ta n barci gashi magrib ta kawo kai, cike da jarumta na matsa kusa da ita na shiga tashinta ganin irin kwanciyar da tai, buɗe idanuwanta tai tare da ƙoƙarin tashi, na lura itama jikinta sam babu ƙarfi, bayan ta tashi zaune ne na shiga jera ma ta sannu.
"Halan baki jin daɗi, naga kinyi barcin marice, sannu bari imfadawa Abba ya siyo ma ki magani." Nai maganar ina kallon yanda Mama ta dafe kanta.
Cikin sanyi murya ta furta.
"A,ah Mubeenah! lafiya lau kawai naɗanyi barci ne shine jikina yai sanyi, zan warware da zarar nai sallah."
Sannu na sake yi mata gami da lallaɓawa na tashi tsaye na nufi wajen ruwa na ɗauki ƴar gudaliyar butar gidanmu na cikata da ruwa na nufi kewaye dan in watsa ruwa saboda rashin daɗin da jikina ke min, raɓewa na yi ta samu na watsa ruwan sannan na fito na fara gabatarda alwala cikin nutsuwa, ina alfahari da yanda ni ke nutsuwa idan zan gana da mahaliccina, ni mutumce me tsananin son ibada da tsoron Allah, bana wasa wajen kiyaye haƙoƙin ubangijina, nakan yi iya bakin ƙoƙarina wajen kaucewa saɓo, da wannan nike kira ga ƴan uwana musulmai da muji tsoron Allah mu kyautata makomarmu, mu dinga kiyaye haƙoƙin Allah dan samun sakamako me kyau a lahirarmh, Allah ya datar da mu Ameen.
Bayan na kammala alwalar nai tasbihi kamar yanda mazonmu ya koyar, sannan na zubawa Mama ruwa a buta na shigar ma ta da ita sannan na dawo na shiga ɗakina wanda ko arziƙin fitila babu, gashi babu ko taga se wasu ƴan bulillika da aka jera a can sama, da lalube na ɗauki hijabi da abin Sallah ta, da yake na haddace inda komi ya ke a cikin ɗaki a haka nike gudanar da rayuwata ba tare da na takura ba.
A zaune na gabatar da Sallar saboda yanda kaina ke sarawa, bayan na gama ne na shiga yin azkar ɗin marice da bansamu damar yi ba, da yake na riga da na hardace shi tas a kaina, bayan na gama ne na jingina da jikin bango ina sauraren yanda bugun zuciyata ya sauya lokcinda na farka naga na yi barci wanda bansan lokacinda ya kwasheni ba, ina jin sauyi sosai a jikina wanda kafin in kwanta sam banji hakan ba, hakanan kawai na ji a jikina akwai abin da ya faru wanda ban sa ni ba, a gefe ɗaya kuma ina tunani akan abin da ya hana Umma da Abba fitowa yin alwala, ina jiyo tashin muryarsu a ɗakin Umma, hakanan kawai na ji ina so inje in taso su dan suyi sallah ƙila basusan an kira ba tun da ba wani ji ake sosaiba daga masallaci idan aka kira, ni da Mama mune masu ƙoƙarin yin sallah akan lokacinta.
Cikin amincewa da shawarar zuciyata na tashi ina dafe bango na nufi ɗakin Umma, ina tura ƙofar naci burki ganin Abba zaune akan taƙunanniyar dadumar Umma ya na sallah, gefe ɗaya kuma babbar robar Umma ce da buta a jiye sai wasu ruwa a cikin robar masu datti da alama awala akai ciki.
Cikin shanye mamakina na yi sallama cikin sanyi murya, abin da ya ɗaure min kai be wuce yanda naga firgici da razana ba kwance akan fuskar Yaya Habiba da Yaya Sumayya waɗanɗa suka salame Sallah.
"Innalilahi wa'inna ilaihi raju'un!!! Mubeena lafiya kika zo kikai min tsaye a bakin ƙofa." Umma ta faɗi da yanayin tsoro.
Kallon tsaf nai ma ta, ina ganin yanda ta ke ƙoƙarin haɗiyar yawun da ya maƙale ma ta a maƙoshi, idanuwanta da alamun tsoro ƙarara.
Bangama ƙare ma ta kalloba na tsinayo muryar Abba shima a sanyaye ya na faɗin.
"Mubeenah lafiya dai ko? ko wani abu kike buƙata." yai maganar shina maƙogwaromshi na kai komo.
"Dama naga baku fito yin sallah ba shine na ce bari inzo in sanar muku." nai maganar ina kokonto akan yanda naga su na wani ɗari-ɗari da ni.
"A'ah ai da kin barshi ba sai kinzo ba, yau a tasha da zan dawo na siyo sabuwar gora, shine nace ba sai mun dinga yin alwala a waje ba mayi a ɗaki kawai tunda tsakar gidan caɓewa ya ke harmu gaza samun wajen kwanciya ga kuma saurayen da ke yo gayya idan wajen ya caɓe." Umma tai tsulum ta bani amsa.
Haka kawai naji ban yarda da wannan maganar ta ta ba, hakanan ma Umma idan ta bushi iska sai ta tsiro wanki da marice dan kawai ta jiƙe inda muke kwanciya ni da Mama, musamman idan ranar ita ke da girki.
Bance komi ba na juya na nufi ɗakin Mama na isketa akan dadduma ta gama sallah, gaishe ta nai cike da girmamawa, amsawa tai cike da kulawa tare da tambayata lafiyata, bayan na bata amsa mukai zaman shiru na tsawon lokaci, ganin shirun yai yawa ne yau ko ƴar fira bamuyiba ya saka nace.
"Wai Mama yau babu aikin girkin dare ne, naga har yanzu baki ce inhura rushi ba."
"Da yake kinga Ummanku ta dawo to shine Abbanku ya ce imbar ma ta girkin tunda nata ne dama, ban musaba na bata abinta."
Mama ta bani amsa ta na ƙoƙarin kunna ragwargwaɓaɓɓiyar redionta wacce taci uban ɗauri da robali, shiru mukai muna sauraren labaranda ake a gidan redion.
Bamu daɗe da fara sauraren labaranba Abba ya aiko Yaya Habiba akan Mama ta fito tai shimfiɗa zamuci abinci.
Firgigit na dawo daga tunanin da na tafi.
"Mubeena ki ci abincin mana kar ya yi sanyi, wai kodai baki jin daɗi ne tun ɗazu nike lura da ke sam baki da walwala." Mama tai maganar ta na jiran amsata.
"Dan Allah Mama za ki iya gayamin abin da ya faru ɗazu, haka kawai nike ji a jikina akwai abin da ya faru, kinga su Yaya Habiba basa kula ni kamarma tsorona suke bayan ba gaka muke ba, Abbama bai yi min faɗa ba yanzu, shiyasa nike son insan abin da ya faru.
"Ke ko wannan yarinya kin shiga uku, haka kika koma kuma bayan sa ido yanzu harda bin ƙwaƙwaf kike yi, to ni gaskiya bazan iya ɗaukar wannan rainin hankalin naki ba, tabbas wani abu ya faru kuma ba komi bane face aljannun da kika tada kika nemi hallakamu da ruwa, kuma mun riga mun yanke hukunci akanki ni da Abbanku, ba za ki sake ƙara kwana a gidannan ba daga gobe, dan tsaf za ki hallakamu alhalin da sauran lokacinmu, mun shirya tsaf dan mu kai ki aikatau can bariki."
Sak kowa na wajen yai jin abin da Umma ta ce, Abba kuwa cike da ƙulewa ya banka ma ta uwar harara ya na takaicin hali irinnata na rashin siri, inde tonon sililine to fa Umma ta yi dgree akanshi, sam ba ta da sirri ko kaɗan, sai Abba yajata gefe suyi magana ba tare sanin Mama ba amma mudin za'azauna da Umma sai ta faɗi wannan maganar, ga shi Allah ya ɗaurawa Abba son yin shawara ko sirri da Umma.
Kallon yanda nike kokowa da hawayen da suka dage akan dole sai sun zubo, ni kuma naƙi basu damar hakan Mama ta yi, cikin sanyi jiki ta janyo ni ta kwantar akan kafaɗarta ta na jin babu daɗi da maganar da Umma ta faɗa min alhalin ba ita na tambaya ba.
Gyaran murya Abba yai tare da janyo hankullanmu akan zai yi magana kowa ya nutsu, ɗago kaina nai ina son jin abin da Abban zai faɗa.
"Ke Mubeenah ki natsu domin maganar ta ki ce, bayan zuwan Yayanku Hashimu ya yi min wani abishir akan ya samo ma ki aikatau a can cikin bariki, na yi murna sosai da hakan dan idan ba ki manta ba nace ma ki, ko dai ki fidda miji in aurar da ke, ko kuma inbawa abokina aurenki ko ki fita ki barmin gida dan na gaji da ciyar da ke hakanan babu wa ta riba, ga matsalolinki da sukafi ƙarfin kanki bare kuma ni Iroro wanda ban aje ba kuma ban bama wani ajiya ba, na rigada na yanke shawara akan gobe da yardar Allah zan ɗaukeki da kaina in kaiki can gidan aikin, mutanen a matse suke da son samun wacce za tai aikin,yanzu abin da nike so da ke shine, ki tattaro dukannin abubuwan da kikasan ki na buƙata ki shirya gobe tun da sassafe zamu kama hanyar tafiya dan kuwa ana so muje kafin wani me magani ya iso, kuma ban amince kiyi magana da Mamanki ba akan wannan aikin, umarni ne na zartar a kanki ban amince kiyi magana da kowa ba akan wannan aikin face ni kaɗai ko Ummanku idan kika yi magana da wani Allah ya isa ban yafe muku ba wallahi, dan ba shawararki na nema ba na riga na zartar da hukunci."
Zuciyata ta shiga dokawa da tsananin ƙarfi, ya yinda na gama jin kalaman Abba, hakanan na ji na amince da hukuncin da ya zartar a kaina, hakanan nike ji na gaji da rayuwa a ƙarƙashin innuwar kulawar Abba, na daɗe da gane cewa Abba baya so na, ban san daliliba sai tsintar kaina na yi a cikin farin ciki, ban san wane zaren ƙaddara ba ne ya ke jana akan amimcewa da aikin, ni dai kawai ina jin daɗin zan nisanta da Abba na tsawon lokaci, zan yi nisanda zan samu nutsuwar gangar jiki da zuciya, ina buƙatar samun inda zan zauna inyi tunani akan rayuwata tun daga farko har izuwa yanzu da tarin ƙaddarori suka samu muhallin zama a rayuwata.
Bancewa kowa komi ba sai tashi da nai babu alamun damuwa atare da ni na wuce ɗaƙina, Mama ce ta bawa Yaya Habiba ƴar ƙaramar fitilarta ta kawo min, aiko na ji daɗin hakan dan so nike in sadu da ma'ajiyar ƙur'ani na dan amma duhu ya hana hakan.
Jakar iskamiyya ta na ɗauko na fito da ƙur'ani na izufi sittin, na buɗe shi tare da fatan samun salama da dangana akan ƙaddarar da ke tunkaro ni, a lokacinda na fara karanta alƙur'ani me girma da tsarki, wani irin raunine ya baibaye ni har ban san sanda na fara hawayeba, ban daina karatunba kuma ban daina kukanba, hakanan nike ji a jikina wannan hawayen da nike na samun salama da sauƙin zuciya ne.
Ban daina karatun ba sai da na tabbatar da na samu gamsashiyar nutsuwa, sannan na rufe alƙur'ani nai addu'ata tare da tashi na gabatar da Sallar Isha'i.
Bayan na gama ne na ta gyara wajen kwanciyata sannan na ɗauki fitilar Mama na mufi ɗakin ta, turus na yi ganinta durƙushe a ƙasa ga Abba tsaye a kant sai huci ya ke, ban ce komi ba na nufi inda ta ke ajiye fitilar na ajiye tare da juyawa na fice zuwa ɗakina, azkar ɗin kwanciya narci na gabatar sannan na haye yamusashiyar katifata nai lamo ina jin yanda har yanzu zuciyata bata bar dokawa da ƙarfiba, ban bawa kaina damar tunani akan komi ba haka na kwanta har barci me nauyi yai nasarar tafiya da ni.
Kyakkyawan matashi ne zaune a wa ta kujerar alfarma ya na aiki, sai wa ta mummunar halitta marar kyan gado ta zo ta bayanshi ta buɗe mumunan bakinta ta shiga yo aman wuta, juyawa yai ya na salatin jin ZAFIN WUTA amma sai wannan hallitar tai amfani da wannan damar ta sake amayo wa ta wutar me yawa akanshi, sai da halittar ta cike inda matashin ya ke da wuta sannan ta fice da jikin gini, wa ta mata ce ta zo kusa da wamda aka sakawa wutar ta na kuka tare da tattaɓa jikinshi, amma duk inda ta taɓa sai ya kwalje ita kuma sai hanunta ya ƙone, a haka ta zauna ta na ta kuka babu me rarrashi, yayinda muka zo wucewa ta wajen ni da Abba sai muka ga wannan matar shine Abba ya ja hannuna ya bata ya na faɗin nice kaɗai zan nemo maganin da zai warkar da wannan matashin wanda wuta ke ƙonawa, hannu biyu matar ta amshe ni tare da yiwa Abba alkairi me yawa ya juya ya barni da ita, da na tunkari inda wannan matashin ya ke, sai ruwa me ƙarfi ya zo ya maido da ni, haka na dage sai na isa gareshi har nai nasarar kama hanunshi, abin mamaki ina kama hanunshi sai wannan wutar ta ɓace ɓat sai de baƙin hayaƙi da ya karaɗe daƙin wanda wa ta murya marar daɗin amo ke faɗin, "kin yi nasarar rabani da shi amma tabbas zan dawo, zan dawo domin ɗaukar fansa."
A firgice na farka cikin matsanancin tsoro.