Hs 27
by @legendspen
_Page 27_
Sai yamma su Jannah suka shigo niƙi-niƙe da kaya, wai Amrah ta huce gida ana kiranta, bayan sun yi sallah suka shiga ware na kowa da niyar washe gari za abawa mai delivery ya kai wa kowa, sai bayan takwas Faruq ya zo ya ɗauke Jannah, ita dai Bhatool har wani murmushi take dan ta fahimci kamar Faruq ya faɗa son Jannah ne, haka kawai sai kuma tausayin Amrah ya faɗo mata, kawar da tunanim ta yi baki ɗaya ta shigi hidimar dake gabanta.
Washe gari.
Da ci gaban bidirin da hada-hada kowa ya tashi, Gida gaba daya ya kacame, daga gidansu Bhatool har gidansu Senate, Yaya karima ma ta kwaso kayanta ta tawo biki, ganin rana ta yi Amrah ba ta zo ba yasa Bhatool ta kirata, sai ta sanar da ita sunje Kaduna amma suma hanye ne, baban Anty ne ya mutu kishiyar mamanta, hakan yasa Faruq da Jannah suka wakilci komai harda zuwa kai Ashobe, anan wata shaƙuwar ta ƙara shiga tsakaninsu, wani abin arziƙi da Faruq ya dinga yi duk wacce aka kaiwa Ashobe sai anɗora mata da 20k na ɗinki akai.
Amarh bata sami zuwa ba sai washe gari, wanda ana gobe za a fara gudanar da Kamun Mom, mai ƙunshi guda aka ɗakko zuwa gidan ta ke yiwa mutane, banda Bhatool da ƙawayenta da aka dakko musu wata ƙwararriya daban tana musu. Abunka da kuɗi a ranar da za afara events kowacce ta amso dinkunanta, an saki kuɗi anyi musu ɗinki masu kyau sosai da sosai.
A babban Hall na Dehall Event Centre za a gudanar da kamun yau, babban waje biki da ya amsa sunansa kaf garin Yobe, da misalin karfe 04:30 kowa da kowa ga hallara manyan mata ƙawayen Mama sun ci Ado, gwala-gwala nai ke wai ke kyalli da walwali, am warewa Mama da na tawagar nasu wajen cikin mutunchi, duk wacce ka kalla cikin kawayen Mom sai ka sake kalla, dan yadda suke walwali da adon gwala-gwala, events na ta tafiya MC na ƙara kambaba waje da zazzaƙar muryarta, da misalin karfe 06:30 sautin wajen ya canja, sakamakon shigowar Amarya Bhatool da Amgonta Senate, Bhatool na sanye cikin wani tsaddaden yadi, wanda kuɗinshi ya bawa 1million baya, sai kyalli take da gwala-gwalan dake wuyanta, fuskarta ta dau make-up da ya matukar kara fito da ita da kyanta, Senate na sanyi cikim arniyar babar rigar Getzner shadda fara, suna tafiya a hankali, bayansu kuma ƙawayen Bhatool ne, akwai tazara tsakaninsu, Murya Mc ce ta fito.
"Tauraruwar ziniyar da dukkan gari ya haɗu dominta❤️
Kowacce zuciya cikin farin ciki😻🎉, cikin soyayyah🥰, cikin ƙaunah❤️
Babu abinda ake marari, babu abinda ake so, sai ganin shigowar wanan amraya💃🎉
Cikin wani irin haske😻hasken da ya gama sararin samaniya❤️
A hasken da ya kai kamar na wata daren goma sha huɗu❤️ daren da inda turawa ke zaune suke cewa she look beautiful, sparkling like full moon.
Ma sha Allah fa tabarakallah🎉ahasanil kaliƙin.
Dukkan inda ka ƙure mata kallo, tun daga kan babban ɗan yatsan tafin kafarta har zuwa kanta🤭idan kana kallonan shauƙi kake ka kara kallonta🎉💃
Domin babu wani abu da zai sanya ka ji da kallon tauraruwar da asararin samaniya idam guda miliyan ne, ita kaɗai ce take hasken da kowanne haske tafi shi haske🎉🌚
Cikin irin hasken da idan allura ta faɗi a ƙasa zaka gani ba sai ka nemi abinda zaka kara haskawa da shi ba,
Wanan ita ce Amarya Bhatool, matar Senate! Aka ce matar Senate ɗa ɗaya tilo wajen manyan masu kuɗin Yobe state, Senate dan gata mai iyaye, Senate dangata mai iyayi, shine angonki Bhatool💃❤️🫶💍."
Wanan shine kirarin da Mc ta bi Bhatool da shi tun daga shigowarta har zuwa mazauninta, daga nan kuma events ya fara. Komai cikin tsari ake gudanar da shi, Mc na bawa dangin amarya dama su fito, haka ma dangin Ango, ƙawayen Mom sai barin kuɗi suke mata naira da daloli, anci ansha cikin tsari sosai da sosai, ana haka ne aka zo matakin buɗar kai, lokacin da dangin Ango zasu yi wankan amarya wajen ƙawayenta, Mama dai da tawagatar suna zaune suna kallon bidi'a kala-kala.
Ba tare da wani kwana-kwana ba, ƙawayen Mom suka siya wankan Amarya naira miliyan biyu kash, daga nan aka ci gaba da biki, ango na zubawa amarya liƙi abokansa na zuba mai liƙi, haka amarya ma na zuba ƙawayenta na zuba mai, kasancewar kamu ne ba dinner ba karfe 09:00 aka ta shi daga event ɗin baki daya, kowa ya kama hanya, abokan ango suka dakko yan uwan amarya, aka huce gida.
A gidansu Na'ima Bhatool da ƙawayenta suka sauka, ɗaki guda aka ware masu suka zauna, haka suka raba dare kowacce na waya da saurayinta, Amrah ma ta yi saurayi cikin abokan ango, wanda da alama duk abokan angon yafi su kuɗi, rafa guda na dollars ya ba ta ta yi liƙi.
Haka gidansu Senate abun sai sun barka, duk kuɗin kawayen Mom sun yaba sa tarbiya da nutsuwa irin na Mama da yan-uwata, babu hayaniya babu rawar kai, duk girma irin na gidan amma ya cika ya batse. Daga gari gari ake zuwar wa Mom, wasu ma daga wata ƙasa suka zo mata.
Shima senate part ɗin shi akwai hayaniyar mutanen, duk da dai abokansa babu wani mai kwana, Aziz da yazo daga America wanda ya bawa Amrah kuɗi.
~~~~~Washe gari
Tun safe kowanne ɓangare suka shiga nasu hada-hadar, yau Dinner ce za ayi sai karfe takwas za a fara, hakan ya rage musu yawan abubuwa. Ragowar jeren da ba a ƙarasa jiya ba aka tafi ƙarasawa, da misalin karfe daya dai-dain aka zo daukan Bhatool da kawayenta zuwa gidan kwalliyya.
A can gidan kam, masu jeren bangaren Senate ma sunzo, haka akayi jeren ciki da mutuntawa, duk wata karramawa dangin senate sun yi, basu nuna kuɗi ko ƙyama ko wani abu ba, har suka gama suka fito.
Yau ma karfe takwas dai dai dakin taro na Coral Garden event centre ya fara ɗiban jama'a, kowa cikin kaya na ke ce raini, kowa cikin ado na daukar ido, a haka kawayen Mom suka karaso tare da ita, Mc tana zuba musu na su kirarin, ana musu ɓarin kuɗi har suka isa mazauninsu.
A can ɓangaen Amarya suna gidan kwalliya ana ta kashe su da make-up, Jannah da Amrah ma duk a nan ake musu, Suhaima ce ma take yin abarta daga gida, Yaya karima ma wajen wata ƙwararriyar mai kwalliya ita ma taje, ta yi ɗinkuna na gaske na gani kasheni, masu kyau da tsada. Mussaman da ya zamana yau ita da Abdul ne zasu riƙo hannun Amarya su shigo da ita, duk da ba wasu gayya suke yi ba, sai bayan kwana ɗaya za'ayi nasu event ɗin, gobe Ladies night ne, jibi kuma nasu event ɗin daga nan sai cocktail, sai kuma Event ɗin Mom na karshe wanda tun rana za a fara shi, zuwa yamma za a ta shi daga nan Amarya zata nufi gida ta shirya akaita ɗakin mijinta.
"Yanzu mukayi waya da Azez ya ce sun kama hanya fa, amma sn turu mana motoci nan." Amrah ta faɗa. "Ni yanzu Abdul nake kira ya je ɗakko Yaya ne." Bhatool ta faɗa tana ƙara danna wayarta. "To ki kira su Furee mana naga tare suka tafi." Jannah ta faɗa, nan take Amrah ta kwashe da dariya sanan ta ce. "Kun san wani abu?."
"A'a, sai kin faɗa."
"wai Jiya Furee ta yi wani saurayi da alama ma cikin yan uwansu Senate ne, yana tambyarta sunan ta sai cewa ta yi Farha." Ai kuwa suna suka kwashe da dariya, sanan Jannah ta ce. "Allah Sarki ai ba ta ce Furee ba kam." Dai-dai lokacin Abdul ya ɗaga wayar. "Kuna ina?." Bhatool ta tambaye shi. "Na ɗakko su, yanzu zamu huce Hall ɗin."
"Mama fa?." Ta tambaya. "Mama ba zata sami zuwa ba, tun ɗazu su Ɗan-ladi da Gaggo larai suka zo suna ta faman tijara, amma su Anty zata wakilce ta kuma duk ƙawayenta zasu zo."
"Kai wayanan mutanen ba su yi ba wallahi, sai na saita musu zama." Daga haka ta kashe wayarta. "Amrah wai masu daukan namu ba su zo ba?."
"Kinga yanzu yake kirana."
"To ku ku huce dan gaskiyya sai na fara zuwa gida, wai Mama ba zata zo ba, sai na ci mutuncin su Larai wallahi."
"Bhatool ba lokaci." Amrah ta faɗa. "Allah sai naje." Daga haka ta fice zuwa mota, su ma su ka shiga zuwa gidansu na su, cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙarasa gidan lokacib su na tsaka da wata sabuwar tijarar wai an basu abinci kaɗan, babu ko sallama Bhatool ta shiga cikim gidan. "Ke lafiya mai ya kawo ki?."
"Ummah na zo ne ki shirya mu tafi."
"Bhatool maza tafi ba lokaci." Umma ta faɗa, kallonsu Bhatool ta yi sanan ta ce. "Me yasa Ummah."
"Bhatool kafin ranki ya ɓaci ki shige ki tafi."
"Tom Umma, amma dan Allah ban ruwa na sha." Ɗaki Umma ta shiga ɗakko mata ruwan, Bhatool na ganin haka ta juya wajensu, ta kai hannu ta fisge plate din abincin sanan ta ɗauke kulan. "Ku ta shi kubar gidanan, tunda babu sisin ko ciki, mugaye azzalumai, wallahi sai nayi shari'a daku a kotun abuja."
"Kizo ki kawo abincin nan kafin na sumar dake, mara tarbiya." Ɗan-ladi da Iliyasu suka haɗa baki suka faɗa. "Idan da kuɗin ku a ciki sai ku ci." Ta faɗa dai-dai lokacin da ta fice, bata ƙarasa fita ba taga almajirai waje ta juye musu, kuma gaba daya gidan babu komai sai tuwo, an basu shinkafa sun cinye sunci basu ƙoshi ba kuma ba za su ci tuwo ba, shine aka dafa musu taliya leda biyar, taji kayan haɗi ko gama zuba ta cikin faranti basuyi ba. Umma ce ta fito daga ɗaki tana cewa. "Ungo sha na maganinki." Dai-dai lokacin Bhatool ta shigo da kula babu komai ciki. "Bhatool mene haka?." Ummah ta faɗa. "Amma anyi tsinanniyar yarinya a duniya, yanzu kin zubar da abincin?." Goggo larai ta faɗa. "Ai sai kunga jami'an tsaro zaku tabbatar da tsinanniya nake."
"Wai Bhatool mene haka, me kike aikata?." Umma ta yi mata wanan tambayar. "Umma su ta shi subar gidannan, tun da su harkar arziƙi bata kawo su waje."
"Gidanku Bhatool, ina kika kai abincin?."
"Na bawa almajirai." Salati suka saki baki ɗaya, Goggo larai ta fashe da ihu tare da faɗin. "har abada bazan manta da wanan cutar da kika mun ba, wanan taliya ta ji jar miyar, taji nama, ta me star amma kika bayar, Allah wadaranki." Su sauran ma ba su iya magana ba sabida mamki da alhini. "Bhatool fita ki bar gidannan." Umma ta faɗa dai-dai lokacin kuma wayarta ta fara ringi, sunan Senate ne hakan yasa ta fice zuwa mota.
Ba wata doguwar tafiya suka yi na zuwa wajen bikin, lokacin kowa ya iso wajen ya shiga shida abokansa, cikin wami irin salo wanda yadauka hankali, ya karaɗe mediya domin abokansa sun yi watsin dala, sun yi watsin nera.
Ƙawayen Amarya ne a gaba, bayan yan taku sai kuma Amarya tare Yaya Karima da Abdul sun riƙe mata hannu, Mc ta yi gyaran murya ta fara maganaa.
Legendspen ***