ZAFIN WUTA

Chapter 7

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000093166 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000093158

 

      PAGE 35 

 

Ina karanto addu'o'inda Manzonmu ya koyar idan mutum yai mummunan mafarki, zuciyata har lokacin bata daina dokawa da ƙarfi ba, sai ma sake tsananta dokawa da tai fiye da baya, hakanan naji jikina yai sanyi sam bani da kuzari ko kaɗan. 

 

Tunanika barkayai suka dinga bijiromin na abubuwanda suka faru da ni tun wayuwar garin yau, idan da sabo ya kamata ace na saba da yanda rayuwa ke gara ni kamar kwallon ƙafa, aduk lokacinda zan wayi gari d irin ƙalubalen da zan fuskanta, sam babu wani abu na birgewa a cikin rayuwata, hakanan nike gudanar da rayuwata sam  babu farin ciki. 

 

Sake juyawa nai ɗayan sashen  ina ji a jikina dole ne in tashi in nemawa kaina mafita, ina buƙatar farin ciki kamar kowace mace, ina buƙatar samun ƴancin kai kamar kowace budurwa wacce ke gaban iyayenta, amma ta yaya zan samu hakan? na tambayi zuciyata da take saƙamin tunanika daban-daban. 

'Zan samu ƴanci kamar kowa amma sai na cire tsoro, dole sai na aro mayafin juriya na aje na haƙuri dan samun damar cimma muradina, to amma kuma ai Abba ya ce gobe zan bar gidan, ko da yake wannan ma wa ta damace zan samu dan in canza rayuwata, ban san gidan da zan rayu a cikinshi ba, haka zalika bansan wane irin mutanene a cikin gidan ba, zan tsaya imfara karantar mutanen wajen dan insan ta yanda zan gyara rayuwata kamar kowa.'  

 

Ina ta tunani daban-daban da haka har barci ya ɗauke ni me nauyi. 

 

 

BANANA ISLAND 

 

Ƙwance Mommy ta ke a kan katafaren gadonta wanda ya lashe miliyoyin kudaɗe kafin kafuwarshi a daɗin, kallon farko zakai me ka gane ba ɗan ƙasar ba ne, ko daga wace ƙasa aka ƙerashi lallai me tsananin tsada ne. 

 

Sulaima ce zaune  akan kagon kusa da Mommy wacce Doctor ke duba lafiyarta, fuskarnan ta ta tai jazur musamman saman hancinta abinka da farin mutun. 

A gefe kuma wannan Dattijuwar matar ce zaune ta yi tagumi ta na kallon yanda Mommy duk ta bi ta fice a hayyacinta. 

 

Bayan Dr. ya gama ba ta taimakon gaugawa ya juyo ya fuskanci wannan Dattijuwar ya na faɗin. 

 

"Hajjo, wai dan Allah mi yasa bakwa kiyaye lafiyar baiwar Allarnan, ta na cikin mawuyacin hali yanzu haka, jininta yayi mugun hawa, ga ciwon zuciya, mi yasa kuke barinta cikin damuwa har haka, ina Fauzan ya ke ne, nasan shi kaɗaine zai fahimci abin da nike nufi." Doctor yai maganar fuskarshi da alamun ɓacin rai gami da damuwa. 

 

"Kayya dai dakat, ai baka sa ni ba, Fauzan ɗin shine wanda yai silar shigarta wannan halin, ya na can kwance cikin mawuyacin hali rai a hannun Allah, kasande akwai shaƙuwa me tsanani tsakanin Fatima da Fauzan, halinda Fauzan ɗin ke ciki ne ya asassa ma ta tashin ciwon, wallahi muna yin bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun fitar da ita daga damuwa, amma abin ya ci tura, da zarar ta ga halin da ɗanta ke ciki sai jikin na ta ya rikice." 

Hajjo tai  maganar muryarta na jimanta lamarin. 

 

"Wai dama Hajjo har yanzu Fauzan be warke ba, na yi tunanin da kuka fita da shi India ya samu lafiya." Dr. yai maganar ya na jimanta lamarin. 

 

"Kai de bari Dakta! lamarin Fauzan se du'a'i, yanzu abin ya wuce yanda ake tunani, ciwo sai gaba ya ke ba wani sauƙi sai a wajen Allah, da zaka ga Fauzan yanzu na tabbata ƙafafuwanka ba zasu taku ta daɗin rai ba, yaronan yana ganin jarabawar rayuwa, sai de kawai muci gaba da taya shi da addu'a Allah ya yanke ma shi wannan wahala da yake ciki." 

 

Jinjina kai kawai Dr. yai cike da jimami, dan bai mance yanda aka kawo Fauzan asibitinsu ba cikin matsanancin ciwo da zafin jiki, fatan samun sauƙi yai musu tare da bada shawarwari akan yanda zasu dinga kiyaye lafiyar Mommy gudun samun matsala sannan ya tafi. 

 

Zaman shiru sukai a ɗakin kowa na tunanin zuci, da haka har barci me nauyi yai awon gaba da Hajjo, da wannan damar Sulaima tai amfani wajen sulalewa ta tafi ɗakin Fauzan dan ta ƙara ganinshi, sam hankalinta baya kwance, ga tashin hankalin yanda jikin ɗan uwanta ke tsananta, ga guma tashin hankalin yanayin Mommy ke ciki. 

 

Zuwa bakin ƙofar glass ɗin ɗakin Sulaima ta yi, tare da jingina jikinta akan ƙofar ɗakin idanuwanta na zubarda hawaye, ta na ɓatuƙar ƙaunar ɗan uwanta, sam batason abin da zai ɓata ma shi rai, ta na kiyaye abin da zai saka yai fushi da ita, shima kuma ya shaƙu da ita, ita kaɗaice abokiyar nishaɗinshi, da ita yake sirri da ita ya ke shawara, ya yarda da ita fiye da kowa. 

Ta ɗauki tsawon lokaci a hakan ta na tunani kafin daga bisani ta zabura tare da janyo ƙofar ta fito ta nufi kan stairs, da bibiyu ta ke hawa benen hakan ya bata damar hayewa cikin sauri, wa ta tsadaddiyar waya ta ɗauka akan luntsumemiyar kujerar da ke jere a ƙayataccen parloun, cikin sauri ta buɗe mabuɗan sirrin tare da laluba wa ta numbar da akai save da Pahpah, ta danna calling. 

 

Amsa kiran akai daga can ɓangaren tare da furta. 

 

    "Assalamu alaikum" 

 

"Wa,alaika salam pahpah!🥹" 

Sulaima tai maganar ta na ƙoƙarin haɗe kukanda ya sake taso ma ta. 

 

      "Sulaima lafiya dai ko! ina Mommynku ina kuma Fauzan ya na lafiya dai ko, jikin da sauƙi ko!!!." 

 

Ya jero tambayoyin cike da ruɗewa. 

 

"Pahpah dan Allah ka dawo hakanan, wallahi Yah Fauzan ya na cikin matsanancin ciwo, Pahpah kullum abin gaba yake sake yi, please idan maganin bazai samu ba ka taho hakanan, banaso yah Fauzan ya mutu bakuyi bankwana ba, Pahpah jikinshi sam babu kyawun gani, yau kwana uku kenan rabon da ya saka koda ruwa ne a cikin....! 

 

Sai kuma wani sabon kukan ya sake ɓalle ma ta. 

Cike da damuwa Ya fara rarrashinta tare da tabbatar ma ta da yana hanya yau komi dare a legos zai kwana, sannan yai ma ta albishir da ansamu maganin. 

 

Ta ɗanji daɗi jin cewa zai dawo yau, ko babu komi zai tsaya wajen ganin ko yayane Fauzan ya saka wani abu a cikinshi, dan kaf a gidan shi kaɗai ne ya isa ya taɓa Fauzan ba tare da ya ƙone ba. 

 

 

 

𝑃𝑙𝑒𝑎𝑠𝑒 𝑘𝑢𝑦𝑖 𝑚𝑎𝑛𝑎𝑔𝑒 𝑑𝑎 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑤𝑎𝑙𝑙𝑎ℎ𝑖 𝑖𝑛𝑎 𝑏𝑢𝑠𝑦 𝑛𝑒 𝑘𝑤𝑎𝑛𝑎 𝑏𝑖𝑦𝑢 𝑎𝑚𝑚𝑎 𝑖𝑛𝑠ℎ𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑑𝑎𝑔𝑎 𝑦𝑎𝑛𝑧𝑢 𝑧𝑎𝑘𝑢 𝑑𝑖𝑛𝑔𝑎 𝑠𝑎𝑚𝑢𝑛 𝑙𝑖𝑡𝑡𝑎𝑓𝑖𝑛 𝑍𝐴𝐹𝐼𝑁 𝑊𝑈𝑇𝐴 𝑎 𝑘𝑎𝑖 𝑎 𝑘𝑎𝑖.