Chapter 8
CHAPTER 35-40
بسم الله الرحمن الرحيم.
Ajiyar zuciya Pahpah ya saki lokacinda Sulaima ta kashe wayar, kallonshi farin mutum da ke zaune kan sallaya tai tare da girgiza kai sannan ya ce.
"Mudin haskenta ya sadu da ɗanka tabbas ƙarshen wahalarsa ya zo, ita kaɗaice za ta iya karya wannan mugun sihirin, sannan kuma ta bashi garkuwa da izinin ubangijinmu."
Shiru Pahpah yai tare da zurfafa a cikin tunanin yanda zai sadu da wannan tauraruwa me haske, wacce zata zamo tsanin takawar Fauzan ta hanyar samun lafiyarshi.
"Ka tashi ka je, kana tare da nasara, ka riƙe Allah domin shine kaɗai zai tallafa maka."
Wani abin al'ajabi da bammamaki, mutumin na gama maganar sai ya ɓace ɓat kamar be taɓa wanzuwa a wajen ba.
Tsam Pahpah ya tashi ya fice cikim tsoro, direct wajen motarshi ya nufa, bayan ya shiga ya saka drivar ya ja da sauri suka bar wajen.
MUBEENAH AGEGE
Can cikin barci ni ke jiyo muryar Mama sama-sama, ban buɗe ido ba sai juyi da na sake yi ina shirin gyara kwanciyata, sai na ji an jijjiga ni da ƙarfin gaske ana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, jama'a Mubeenah wai lafiyarki ƙalau kuwa? dan Allah ki tashi hakanan, rana har ta fito amma kin gagara tashi, tun asubahi nike tashinki."
Zaram na tashi zaune tun lokacin da na ji salatin da Mama ta saki, cikin sauri na buɗe idanuwana, amma abin mamaki shine, sun buɗe tar amma sam bana ganin komi, sake kai hannuna nai ina shafa idon dawa, amma abin al'ajabi sai naji ashe a buɗe suke.
"Allahu Akbar, kaji ƙudirar Ubangiji mabuwayi gagara misali, me hanawa kuma me bayarwa, Wallahi Allah Mama idanuwana basa ganin komi, duhu nike gani, zo ki duba ki gani."
Nai maganar cikin jinjina ƙarfin buwayar Ubangiji, me bayarwa kuma me hanawa aduk lokacin da ya so, idan ba Ikon Ubangijiba waye zai baka alokacin da ya so, kuma ya amsa a lokacinda ya so?.
"Ke Mubeena ban son iskanci, ta gidan ubanwa ke baki gani, alhalin ga idanuwanki nan tarrrr ma sha Allah, ki daina wasa ki taso muje kiyi sallah lokaci na wucewa."
Mama tai maganar ta na hana kanta gasgata cewa da nai bana gani.
"To Mama bara in tashi."
Nai maganar ina ƙoƙarin tashi, amma mi ta tabbata dai bana gani sam, dan kuwa ina taka ƙafata ban sauke ta a ko ina ba sai cikin kwanon da nike aje ruwa idan zan kwanta, cike da razani na janye ƙafata nai baya ina salati.
Sak Mama ta yi, ta kasa taɓuka komi domin kuwa ko ta so ko kar ta so ya tabbata bana gani.
Maganar Abba ce ta yanke min jimamin da na shiga.
"Ke Halima! wai har yanzu ita Mubeenar ba ta tashi ba, ki watsa ma ta ruwa manah, kinga rana ta soma yi, kuma ana jiranmu dan yanzu na sake yin waya da Hashimu ya sanar da ni cewa, me gidan ya dawo jiya cikin dare, muyi sauri muje dan...."
Maganarshi ta yanke ne lokacin da ya lura da Mama zaune daɓas a ƙasa, kamar ma bata cikin hayyacinda dan ya lura da yanda laɓɓanta ke motsawa.
"Halima lafiya dai ko? ko wani abun ta...."
Bai ƙarasaba ya ji ni na fashe da matsanancin kuka ina faɗin.
"Abba kana gani na ko, wallahi Abba ni bana ganinka, na zama makauniya, bana ganin komi sai duhu, dan Allah zo ka kama hannuna ka kaini waje inyo alwala banyi sallah ba".
Wa ta iriyar ashar Abba ya kutuntumo ya watsa wa Mubeenah, sannan ya ɗaura da faɗin.
"Ke abu ta kazar ubanki, ubanki ya hwaɗa ya afka ya zunduma cikin makantarnan, ni za ki mayar tsohon banza, na rantse da girman Allah sai kin buɗe idonan, ni za kiyi wa baƙin ciki Mubeenah, ni!! ni!!! Mubeenah."
Ya ƙarashe maganar ya na taƙune fuska kamar zai saka iho, ya riga da ya gama tsala lissafin yanda rayuwa zata canza mai, ya gama sadaƙarwa a yau zai zama ɗaya daga cikin masu kuɗin a arear unguwar Agege, amma lissafinshi na neman roshewa ganin halin da Mubeenah ke ciki.
Mama ce ta tashi tare da kama ni ta fitar da ni idanuwanta na zubarda hawaye, ni nasan kaf duniyata ba zan samu me sona kamar Mama ba, ƙauna tattali gami da kulawa a wajen ta kaɗai nike samunsu, ita ce kaɗai bangon da zan jingina inyi kuka kuma ta rarrasheni cike da kulawa haɗi da tausayi.
Ruwa ta zuba a buta ta kama hannuna muka nufi bayan gida, can inda tasan ina tsayawa ta aje ni tare da ajiye butar inda tasan bazan zubar ba, sannan ta fice ta bani waje.
Tsarki na yi kamar yansa na saba, sannan na tafo bango a hankali na fito waje ina sake tabbatarwa kaina na zama makauniya, banyi aune ba na ji wani abu ya ja ni, nai baya-baya na faɗa akan kayan zuba ruwanmu, ji kake "Tinjim." na afka cikin babban bahon ruwa da yake ƙarami ne bashida tsawo sai faɗi.
Abba ne ya taso daga ɗakin Mama dan ganin abin da ya faru, sai kuwa yai tozali da ni kwance male-male a cikin bahon ruwa.
"Yau ni Iroro na ga jarfa, ke dan malafar ubanki shine zaki rasa insa za ki faɗa sai cikin baho, wato ne dole sai kin tabbatar min da cewa ki na min baƙin ciki, yo baƙin ciki manah, sarai kin san wahalar da nike sha wajen samo ruwanan, kina can kina barcin asara na je na samo wai dan kiyi wanka idan zamu je gidan da za kiyi aikatau."
'Aikatau', na maimaita kalmar a zuciyata, sai kuma na zabura na tashi zaune ina lalube ina faɗin.
"Abba bara inje inyi sallah sai in shirya idan har zasu ɗauke ni a haka da makantata ni na amince zanyi aikin."
Nai maganar wani irin karsashi da ƙwarin gwuiwa na zo min.