Miji goma(ba uba goma ba ne)

Chapter 12

by @sadiyaabdulrazak954



PAGE 12


     Jin shiru babu motsinsu a tsakar gidan sai ta leƙo ta kuwa ga wayam, alamun suna cikin ɗaki, ta fito ta nufi ɗakin ta laɓe jikin labule tana sauraron su, daidai sanda Uwani take cewa"Shi ne za ki biyewa shirmenta? Ita ba ki ga kalarta ba? Kin manta da farinjininta? Ko kin manta sai da na karɓo muku taimako kafin ki samu mijin? Kina buduruwa ma kenan, ina ga kin zama bazawara? Maza ki tattara ki koma ɗakinki, kishiya ba kanki farau ba, ni ma na zauna da ita ballantana ke!".

Murja ta ce"Amma babarmu..."

Ta daka mata tsawa ta ce"Rufe mini baki! Wallahi sai kin koma, uzuri ɗaya kawai zan yi miki za ki zauna har sai ya zo biko, amma yana zuwa to wallahi ƙafarki ƙafar shi, ni za ki ja wa abun magana a gari?"

Daga nan Maryam ta ja ƙafa ta koma ɗaki jiki a sanyaye, sannan ta yi kokowa da zuciyarta da take ta faɗa mata ta zuga Murja, ta raya a ranta ƴar'uwarta ce, idan ta cuce ta kanta ta cuta, haka kuma idan an kasa gulmarta a tire ba za ta ji daɗi ba, don haka ta share su, kwananta biyu a gidan mijin ya zo, ai kuwa ko Baba ma bai shiga zancen ba, ita ce ta sasanta su, ta bi shi suka tafi, suka ci gaba da zamansu shiru abunsu.

     Nasiru ya zo ya kawowa Maryam kayan abinci, sannan ya ba ta kuɗi don a yi siyayyar jariri, a haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Allah Ya sauke ta lafiya, ta haifi ɗanta namiji, aka yi suna yaro ya ci sunan mahaifin Nasiru Yusufa, suna ce masa Abba, duk wata sai ya zo ya ba ta dubu ashirin, amma sam bai yi zancen kome ba, wanda a lokacin a yadda Maryam take ƙishin yin aure da burin ta yi zaman aure babu abin da zai hana ta yarda ta koma gidan nasa, sau tari takan tuna da Nazifi ta ce dama ya dawo ya ce ta koma da za ta zauna da Gwaggo lafiya, to amma damarta ta wuce sai dai ta gaba, sai ta ci gaba da kula da ɗanta, ta kuma koma kasuwancinta, tana ra adana ribarta.

 Taimako ɗaya da Allah Ya yi mata ma shi ne tana da farinjinin masoyan, wannan karon ma tun kafin ta yaye Abba maza suka fara sallama da ita, sai dai ta ce musu sai ta yaye ɗanta. Akwai wani Alhaji Haruna da suka haɗu da shi a kasuwa, ya fi kowa naci cikin masu sonta, don har cewa ya yi zai aure ta a hakan, amma ta ce a'a sai ta yaye, ita bai ma wani kwanta mata sosai ba, saboda yana da matarsa da ƴaƴa huɗu, ita kuma tana da kishi, sam ba ta son zama da kishiya, amma ta sani tun da ita ma yanzu ba buduruwa ba ce dole ta jingine burinta a gefe, aurenta uku da ƴaƴa biyi ba zai yiwu ta ce sai saurayi ba, don haka take ɗan kula shi.

 Sanda ta yaye Abba ta fara zancen aure sai Nasiru ya ce to zai ɗauki ɗansa, don har ma ya yi wani auren, nan Uwani ta fara subaɗaɗi tana cewa a bar mata shi, a cewarta yaron ya shiga ranta, ba za ta iya rabuwa da shi ba, ita kuma Maryam ta fi zargin wannan dubu ashirin ɗin da yake kawowa duk wata ce ta ruɗe ta, don haka ta ce a'a gara ya ɗauke shi ɗin, ba ta so a ɗora mata wahala, haka dai Nasiru ya ɗauki ɗansa, gidan iyayensa ya kai shi, tun da ba a daɗe da yin auren na shi ba, kar ya hana su cin amarci, duk sati ake kawo mata yaran nata su wuni wataran ma su kwana ɗaya sai a mayar da su, tana jin babu daɗi a ranta, saboda fargabar yadda tarbiyyar yaran za ta kasance, idan ba ƙaddara ba me zai saka uwa tana raye a raba ta da ɗanta? Haka dai take danne damuwarta tana bin su da addu'a, kwanciyar hankalinta ɗaya ce duk mariƙan yaran suna son su, ba ta ga alamar wahala a tare da su ba.

   Wata ɗaya da mayar da Abba, Alhaji Haruna ya zo da zancen aure faka-faka, ya ce sati biyu za a saka, Maryam da yake har lokacin ba sosai take son shi ba sai ta fara yi masa kwana-kwana, a wannan karon aure take son yi na har abada, saboda haka yana da kyau ta samu wanda zuciyarta ta amince da shi ɗari bisa ɗari, shi auren wanda kake yi wa so sahihi fa yana da alfanu, saboda idan zama ya yi zama saɓani ya fara shiga tsakaninku wannan son da kake yiwa mutum yana taka muhimmiyar rawa wajen haƙurtar da zuciyarka ka ci gaba da zama da shi, kana jure wasu abubuwa, saɓanin wacce ta yi auren manufa babu son miji a zuciyarta, daga wannan abin da ta aure shi don shi ya gushe, shikenan sai ta tsane shi, tun da dama babu so tun farko, idan kuwa ka tsani mutum ba za ka taɓa yi masa uzuri ba, komai ya yi na laifi sai ka yi masa hukunci.

 Ƙiri-ƙiri Uwani ta nuna ba ta son wannan auren, saboda ganin yadda Alhaji Haruna yake son Maryam kamar bai taɓa aure ba, sai bushasha yake yi mata da kuɗi kamar ba ya so, da alama duk ya fi mazajen ƴaƴanta rufin asiri, dama mijin Mardiyya shi ne abun tutiyarta da nunawa a gari ƴarta ta yi goshi tana auren mai kuɗi, sai ga shi Maryam za ta dusashe tauraruwar Mardiyyar, don haka ta ɗauki hassadar duniya ta saka a ranta, ta yi ta zuga Maryam a kan kar ta aure shi, ta ce"Ke yanzu Maryam da ajinki da kyaunki da komai za ki auri babban mutum mai mata da ƴaƴa huɗu? Ni sai nake ganin kamar kin faɗo"

Maryam ta yi murmushi ta ce"Ba faɗuwa ba ne babarmu, kin ga zaman gidan ba shi da wani amfani, kuma idan kika duba kika gani ni ma fa kullum ƙara girma nake, ban yi ƙanƙantar da za a ce Alhaji ya yi mini girma ba, saboda haka wannan ba komai ba ne, Allah dai ya ba mu zaman lafiya".

Uwani ta ce"Amma Maryam za ki iya zaman kishi kuwa? Ba mu san halin matarsa ba".

Ta ce"Babu ruwana da ita, ba zamanta nake yi ba, idan kin ji kanmu to ita ce ta so hakan".

Duk inda ta yi sai Maryam ta tare, haka dai ta rabu da ita ta zubawa sarautar Allah ido, tana jira a yi auren ta ji ta ina matsala za ta fara, ita dai ta san a yadda ta tafi haka za ta dawo, ko ta dawo da ciki ta ƙara haihuwa a gida, haka za ta yi ta rabon yara gida-gida.


Sai da Alhaji Haruna ya je wajen Baba da ƙoƙon bara kan a yi wa Maryam magana ta amince da auren da wuri, saboda babu amfanin jinkirtawar, Baba ya zaunar da Maryam ya yi mata nasiha sosai, saboda ya yaba da hankalin mutumin, kuma shi ma a yanzu ya fi so ta auri babba, kamar zai fi haƙuri da halinta, saɓanin yara da ƙuruciya kawai ake zabgawa a zaman auren, ya faɗawa Maryam shi Alhajin ya ce zai yi mata komai na kayan ɗaki, don haka ba ta da wani uzuri na cewa ba ta shirya ba, ta ce shikenan ta amince, Baba sai ya bi ta da kallon tausayi, ba ya jin daɗin wannan mace-macen auren nata, ga shi kwana biyun nan ya ganta duk a sanyaye kamar tana da wata damuwa, duka ta rage tsiwa har ma yawon bin ƙawaye.

   Yayin da Maryam ta amince da auren Alhaji Haruna, shi kuma yana can ana gumurzu a gidan shi, matar shi Rabi masifaffiyar mace ce, tun da ya yi zancen ƙara auren shikenan ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai tijara take yi, amma shi ya ce mata aure babu gudu ba ja da baya, sai ya yi, wannan ne karo na uku da yake niyyar yin aure, amma sai ta je gidan su yarinyar ta tada tarzoma har a fasa, don haka wannan karon sai ya zaɓi sanarwa Maryam halinta.

 Ranar ya zo zance yake cewa"Maryam a gaskiya ba zan ɓoye miki ba, matata ba tana da kishi sosai, tun tuni nake son ƙara aure ta hana ni, dama kuma dai lokaci bai yi ba, amma a yanzu ina ji a jikina ke ɗin ce ta aure in sha Allah! Saboda na shirya fito na fito da ita a wannan karon".

Maryam ta ce"A'a don Allah ka lallaɓata, kar ka rabu da matarka saboda ni".

Ya ce"Ba zan rabu da ita, amma aure dai babu fashi, ke kuma sai ki shirya zama da ita, kar ki ce za ki rabu da ita ta ci tuwo a kanki, ku zauna lafiya dai kawai saboda ni ma hankalina ya kwanta, tun da kin ga gida ɗaya za ku zauna".

 Maryam ta ce"Ni idan da hali ka raba mana gida mana".

Ya ce"Wallahi haka na tsara tun farko, ginina na mata biyu ne ita ma ta sani kuma tun da na gama ginawa na sanar mata zan ƙara aure".

Ta ce"To shi kenan, Allah Ya sassauta zuciyarta".

Ya amsa da amin, sannan ya nuna mata vedion gidan a waya, gida ne babba mai kyau, daga farfajiyar tsakar gida babba sai a shiga babban falo, mai ɗauke da manyan kujeru, kayan kallo da firji komai dai an saka falo ya haɗu, akwai dining a ciki, sai kitchen da banɗaki, sannan a shiga cikin gidan, ɗakin da zai saka Maryam ɗin ne a farko, ciki da falo da banɗaki a ciki, ita ma na uwar gidan haka yake, sai ɗakin shi da kuma ɗakunan yara guda biyu, sannan wani banɗakin a tsakar gida, ga bantileson mai ɗauke da shuke-shuke da famfuna, gidan ya burge ta, ta miƙa masa wayar tana cewa"Ma sha Allah ya yi kyau".

Ya ce"Zuwa gobe jibi za a gama kayan ɗakinki, sai a saka, zan ba ki kuɗi sai ki sayi kayan kitchen ko? Gobe muka yi da ƴan gidan namu za su kawo kayan lefe".

Ta ce"Allah Ya kaimu".

Ya ɗan yi jim kafin ya ce"Don Allah ku yi haƙuri da abin da ƙila ƴan'uwana za su iya yi a yayin kawo lefen, kin san da yake Sauda ƴar'uwata ce, auren gida aka yi mana, kuma ita Innar tawa ita ta riƙe ta tun tana ƙarama, da ta isa aure ta aura min, to yanzu haka tana nan tana taya ta kishi, don ban faɗa miki ba ne ba ma, amma Sauda ta yi yaji tana can gidanmu, kuma Innar ta goya mata baya ta ƙyale ta, sannan akwai wasu ƙananun maganganu da suke yi, wai ai ba zaman aure kike yi ba, ko na aure ki za ki fita, sai dai kin toshe kunnuwanki gaskiya".

Jikin Maryam ya ɗan yi sanyi ta kasa cewa komai ta tafi duniyar tunanin kalar zaman da za su yi.

Alhaji ya ce"Maryam kin yi shiru, ina son ki, kuma sannan zan kwatanta adalci daidai gwargwadon iyawata a tsakaninku, ba zan ga wata ɓaraka na ƙyale ba, amma kin san komai sai kin yi haƙuri kafin ki ci riba".

Ta ce"To Allah Ya ba mu zaman lafiya bakiɗaya".

 Suka yi sallama Maryam ta shiga gida a sanyaye, da a da ne da tuni ta juyewa Uwani komai, amma a yanzu sai ta yi shiru ta bar abun a cikinta tana fatan Allah Ya ba su zaman lafiya.

 Washegari ƴan kawo lefe suka zo, mata ne su biyar, suka kawo akwati guda huɗu, kuma babu laifi ya saka mata kaya sosai, duk da sun rage a cewarsu ai wannan kayan bai cancanci bazawara ba, ƴan'uwa da aka gayyato karɓar lefe da ƙawayen Uwani suna ta ɗaga kaya suna cewa"Ma sha Allah! Kaya sun ce".

Wata cikin masu kawo kayan ta taɓe baki ta ce"Iyyi kaya sun yi fa! Sai fatan Allah Ya sa kunun banza ya ƙare a farau-faru ɗin banza".

Wata ta ce"A to, tun da dai amaryar an ce ba mazauniya ba ce a gidan aure".

Wata cikin dangin babar Maryam ta ce"Daɗin abun dai shi ya gani ya yaba, sai a bar shi da zaɓin shi".

Wata ta ce"Kuma mutuwar aure ai ƙaddara ce, ƙaddara kuwa tana kan uban kowa, ko a yau idan uban mutum ya kwanta ya mutu uwarsa ta zama bazawara".

Wata cikin masu kawo kayan ta hasala ta ce"Kin ga kar ki zage ni, wallahi kar ki sake, dama an faɗa mana ba gidan arziƙi ba ne, ƙaddara ce da biyewa zuciya ya kawo shi".

Nan aka fara maganganu, hayaniya ta kaure a gidan, aka rabu baran-baran dutse a hannun riga, ko tukuici ba a samu damar ba su ba, suka tafi.

Wannan abu da ya faru ya ƙarawa Maryam baƙinjini a wajen dangin Alhaji Haruna, musamman mahaifiyarsa da ta cika ta yi fam kamar za ta yi bindiga, musamman idan ta kalli Sauda da yaran a gida, a cewarta ya zaɓi wata mara tarbiyya ya watsar da matarsa ta ƙuruciya da ƴaƴansa, don haka fushi take yi da shi sosai.

 A haka dai Alhaji ya toshe kunnensa, suka yi ta hidimar gabansu shi da Maryam, har ranar auren ta zo, aka ɗaura aurensu, an yi yini a gidan su Maryam saɓanin shi da babu abin da aka yi, ko abincin ƴan ɗaurin aure a can gidan matar baban shi aka yi, shi dai yana ta zumuɗin zuwan amarya babu abin da ya dame shi.

 Bayan sallar isha'i aka ɗauki Maryam aka kai ta gidan miji a karo na huɗu, wanda take fatan ya zama na ƙarshe da za a sake ɗaura aurenta, ma'ana wannan aure ne ta yi na mutu-ka-raba.

 

(To fa! Ya kuka hango zaman Maryam a irin wannan gidan?)


Littafin nan na kuɗi ne a kan naira 700 kacal!
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay

***