Chapter 13
*Reposting*
Za ku samu complete a kan Naira 700
***
PAGE 13
Alhaji Haruna har zuciyarsa ya yi niyyar kamanta adalci, saboda haka duk da Sauda tana gidansu da ya tashi siyan kazar amarci haka ya siya da nata kashin, dama a baya kashi biyi yake siya da nata da na Innarsa, yau kuwa sai ya sayi kashi uku, ya tafi gidan don ya yiwa Inna sallama kamar yadda ya saba a kowane dare, lokacin tara saura kwata, ya same su a falo, ya ƙarasa a sanyaye ya zauna yana gaishe da Inna, ta amsa fuska babu walwala, ga yaran can rakuɓe a gefe, sun nuna kamar ba su san shi ba, saɓanin da, da idan ya shigo gida a guje suke rige-rigen zuwa gare shi, yaran su huɗu ne, Momy ita ce babba shekararta goma sha ɗaya, sai mai bi mata Kausar, shekararta takwas, sai Ummi shekararta shida, sannan Nana mai shekara huɗu, daga kan Nana ya ce mata ya kamata ta ɗan yi planing don mahaifarta ta huta, ta biye masa ta saka inplan na shekara uku da ya yi expire ta cire ta sake saka wani, don haka yanzu take ganin dama shi burinsa ta tsaya da haihuwar saboda amaryarsa ta zo ta zazzago masa ƴaƴa, kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kai gefe, saboda mugun haushin shi da take ji, ya ce da babbar ƴar"Momy ko gaisuwa babu?"
Sai ta waiwaya ta kalli mahaifiyarsu, saboda tun da suka yi yajin nan kullum sai ta zaunar da su ta faɗa musu babansu yanzu ya daina son su dukansu, shiyasa zai ƙara aure, kuma shi ya kore su dukansu, sannan amaryar da zai aura muguwa ce, kashe ta za ta yi ta zama ita ce uwarsu, kuma dukansu za ta dinga yi, tana hana su abinci, shi kuma baban nasu ba zai yi komai ba, saboda ya daina son su, haka dai ta tsara musu abubuwa kala-kala daidai da tunaninsu, su kuwa hakan ya sanya musu damuwa da jin tsoron baban nasu.
Sai da ya yi magana sannan suka fara gaishe shi ɗaya bayan ɗaya, ya amsa yana ce musu"Ya makaranta?"
Sauda ta yi wani huci kamar zakanya ta tashi buguzun-buguzun ta bar falon, kasancewarta mace mai ƙiba kuma doguwa, ya bi ta da kallo, sai ya ajiyewa Inna ledarta ya bi bayan Sauda ɗin, zaune ya tarar da ita ta naɗe hannu a ƙirji, ya yi sallama tana kallon shi yana kallonta ta ƙi amsawa, ya zo ya zauna a gefen katifar da take, sai ta miƙe za ta fita, ya ce"Kin ga Sauda zauna mu yi magana".
Ba ta zauna ba, amma ta fasa fitar,shi ma sai ya tashi tsayen ya ce"Ni fa ban ƙara aure saboda kin gaza mini ba, sai don ina da ra'ayin yin hakan, kuma dama can mata biyu ne a ƙaddarar aurena, idan mai afkuwa ta afkuwa ya kamata ki ajiye komai a gefe, ki koma ɗakinki, ni sai nake ganin ba girmanki ba ne a ce yarinyar nan ta zo ta tarar kin yi yaji, kamar hakan zai janyo miki raini".
Ta yi shiru dai ba ta ce komai ba.
Ya ci gaba da faɗin"Maryam ƙanwarki ce, kuma tana da sauƙin kai, za ku zauna lafiya in sha Allah, ni dai yanzu ki wuce mu tafi gida kawai, wannan abin da kika yi sai ki jawo mini zagi a gari, nan kuwa ba ni na kore ki ba".
Ta ce"Babu inda zan je, ka je ka zauna da wacce ka zaɓa, kuma sannan zan aiko maka da yaranka, tun da ita ka zaɓa kake ganin za ta iya sai ta riƙe maka!".
Ya ce"To shikenan, ni dai ba zan yi miki dole ba, musamman ma da Inna ta goya miki baya, saboda haka ki yi duk yadda kika tsara, amma ki sani ni dai ba zan sake ki ba".
Ta ja dogon tsaki.
Ya ce"Akwai abin da kuke buƙata?"
Sai a nan ta ce"Ba na buƙatar komai daga gareka, kai kanka bana buƙatarka ballantana abun hannunka, ita da kake baƙo a wajenta ka je can ka yi mata komai!".
Ya yi ɗan murmushi ya ce"Sauda kina da kishi, amma ban taɓa zaton za ki bar gidanki saboda kishiya ba, wai har kina barazanar za ki ba ni ƴaƴana, to ki ba ni, zan riƙe su".
Ya ajiye mata ledar hannunsa, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya ajiye mata ya fice, bai tarar da kowa a falon ba, sai ledar da ya ajiyewa Inna, cike da dumuwa ya bar gidan. Amma ko da ya je gida ya tarar da amaryarsa sai ransa ya yi fess, yana son Maryam sosai, suka sha amarcinsu hankali kwance har ta mantar da shi yana cikin damuwa.
Washegari ya tafi kasuwarsa, ita kuma ta gyara gidan, tana ta baƙi jefi-jefi da maƙota da ƴan'uwa, maƙotan dai duka ƙawayen Sauda ne, don haka gulma ce kawai take kawo su, kowacce idan ta shiga ta ganowa idonta sai ta kira Sauda ta yi mata sharhi, wanda hakan bai ƙara mata komai ba, sai baƙinciki da tsanar Maryam ɗin, ita kuwa Maryam dama ta yi tunanin za a yi hakan, don haka babu wata mace da ta sakarwa fuska, kadaran-kadahan take karɓarsu.
Wajen ƙarfe biyu ta gama girki tana sallah ta ji ana buga gidan, an daɗe ana bugun saboda tana tayar da sallar aka fara, da ta idar ta taho da sauri ta buɗe, sai ta ga yara ne su huɗu da unifom a jikinsu, jikinta ya ba ta ƴaƴan mijinta ne, sai mai adaidaita sahun da ya ajiye su ya ƙaraso da waya a kunnensa yana cewa"Ai ga shi ma ta buɗe".
Don kuwa da ya ga yaran suna ta bugawa ba a buɗe ba, sai ya kira Sauda ya faɗa mata, ta kuwa harzuƙa ta miƙe tsaye tana zage-zage da cewar gidan ubanta ne da za ta hana su shiga?
Ya miƙawa Maryam babbar jakar dake hannun shi yana cewa"Ga shi mamansu ce ta ce na kawo su".
Maryam ta karɓa ta ce"To ka gaishe ta".
Ta kalli yaran ta ce"Ku shiga, sannunku da zuwa".
Babu wanda ya amsa, ballantana su gaishe ta, wannan huɗubar mahaifiyarsu ce, suka shige ɗakin kwanansu, Maryam ta biyo su da jakar kayansu ta ajiye tana cewa"Ku cire unifom, sai na yi muku wanka ku canza kaya ko?"
Momy da take babbar ta ce"A'a, mun yi wanka da safe".
Ta ce"To ku canza kaya ku fito ku ci abinci".
Suka fara kiciniyar cire kayan, ban da Momy da ta ja ta tsaya tana ta ɓata rai, sai da Maryam ta fita sanan ta fito da duka kayan cikin jakar, sai ga waya keypad ta bayyana, ta ɗauka ta shige banɗaki, ta danna ta kira babarsu a waya, Sauda tana ganin kiran ta miƙe ta shige ɗaki, don ko Inna ba ta san da wannan shirin nata ba, tana ɗagawa ta ce"Momy yaya aka yi?"
Momy ta ce"Ta ce mu yi wanka na ce mata mun yi, shi ne ta ce mu fito mu ci abinci".
Sauda ta ce"To ko me ta dafa ku ce ba kwa ci, kowa ya zaɓi abin da yake so ya ci, kin ji ko?"
Ta ce"To, amma wallahi Nana ce uwar kwaɗayi, na san ci za ta yi".
Ta ce"Ki gargaɗe ta, ki ce idan ta ci za ta mutu, ta ce doya take so ta ci, ku kuma ku zaɓi wani abun kowa na shi da ban".
Ta ce"To"
Ta ce"Ki ɓoye wayar nan fa sosai, ki saka a ƙarƙashin katifarku, kuma kar ki fita ko falo da ita".
Ta kashe wayar ta fito ta faki idon ƙannen nata ta ɓoye, sannan ta ba su kayan da za su saka, ta zaunar da su ta ce"To Umma ta ce ko me ta dafa kowa ya ce ba ya ci, ke Nana ki ce doya da ƙwai za ki ci, ke Kausar ki ce shinkafa da wake, ke ke kuma Ummi ki ce shinkafa jollop, idan kuma shinkafar ta dafa sai ki ce macaroni, wallahi Umma ta ce duk wacce ba ta ce haka ba sai ta ci ubanta".
Duk suka gyaɗa kai, sannan suka fito a tare, Maryam tana falo tana chart, ta ce"Kun fito?".
Ba su ce komai ba, ta tashi ta shiga kitchen ta juye musu taliyar da ta dafa da miya, leda ɗaya ce dama ta dafa ko ci ba ta yi ba, plate biyu ta yo ta kawo ta ajiye a gabansu tana cewa"Ku yi maza ku ci".
Daidai lokacin kiran Uwani ya shigo wayarta, ta ɗaga tana gaishe ta, Uwani ta ce"Oh! Maryam har na fara kewa, ya kike ya gidan?"
Ta yi ƴar dariya ta ce"Lafiya ƙalau".
Ta ce"Babu wata matsala dai ko? Kin san zama da kishiya".
Da a da ne sai ta faɗa mata ga shi har yaran shi sun zo, amma yanzu kuwa ta ce mata babu komai, kuma ba ta ma faɗa mata uwar gidan ta yi yaji ba, ko da ƴan kai amarya suka zo ma duk a zatonsu ɗaki ta shiga ta kulle saboda kishi.
Suna gama wayar ta juyo ta ga yaran ba su da niyyar sakkowa su ci abincin, ta ce"A'a! Ya ba ku fara ci ba? Ko sunayenku ba ku faɗa mini ba ma, ku gama ci ku zo mu yi fira ko?"
Momy ta ce"Mu ba ma cin abinci a ƙasa sai a dining, kuma ba ma son taliya".
Ta ce"Ba kwa son taliya? Kwata-kwata ba kwa ci a gidan?"
Ta ce"E".
Maryam ta ce"To me za ku ci?"
Momy ta ce"Ni tuwo nake so".
Ummi ta ce"Ni kuma jollop ɗin shinkafa".
Nana ta ce"Ni doya da ƙwai".
Kausar ta ce"Ni shinkafa da wake, da mai da yaji da salak da tumatur da albasa, da cocomba". Ta ƙarasa da karsashi, don dama Momy kowa abin da ta san ya fi so ta ce ya faɗa.
Maryam ta tsaya kallon su da mamaki, ba sai ta wahalar da kanta da tunani ba, saboda ba zai taɓa yiwuwa ta biyewa yara ta yi girki kashi-kashi ba kamar wata ƴar aiki, girki kala huɗu? Sannan wannan ai ba tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓar abincin da za su ci, don haka ta ce"Duk na ji, amma fa sai dai ku zaɓi abu guda ɗaya dukanku, saboda kun ga idan na yi girki har kala huɗu na yi almubazzaranci, don haka ku tsayar da abu ɗaya".
Duk sai suka kalli Momy tun da ita ce shugabar tawaga, ta ce"To ai mu ba ma cin taliya".
Ta ce"Na ni ba za ku ci taliya ba, ku zaɓi kala ɗaya sai na dafa muku".
Ta ce"Sai dai a yi mana tuwon shinkafa miyar agushi".
Maryam ta ce"Ni ba ni da agushi, sannan ba zan takurawa babanku ba yana kasuwa, amma akwai wake, zan yi muku miyar wake".
Da gaske Nana ba ta cin miyar wake, don haka ta taɓe fuska za ta fara kuka ta ce"Ni dai ba zan ci ba".
Kausar ta ce"Nana ba ta cin miyar wake".
Maryam ta ce"Zan dafa mata indomi".
Ta wuce kitchen ɗin, a ranta tana mamakin yadda aka sangarta yaran, ita idan ƴaƴanta ne gaskiya ba za ta saki fuskar da za su yi mata haka ba, amma su ma ɗin muddin a wajenta za su zauna to kuwa tabbas sai ta saita su. Ta ɗora tuwon da yake ta tarar da komai har farar shinkafar da akwai, da yake gas ɗin mai huɗu ne tana wanke waken sai ta ɗora miyar, sannan ta zauna ta ci taliyar.
Tana tafiya kitchen Momy ta tashi ta shige ɗakinsu, ta ɗauki waya ta shiga banɗaki ta kira Ummansu, tana ɗagawa ta zayyane mata komai, Sauda ta ce"Amma dai Allah Ya yi miki albarka Momy, yanzu kin san yadda za a yi?"
Ta ce"A'a".
Ta ce"Idan ta gama tuwon ku yi loma ɗaya ku ce babu daɗi ku ba kwa ci kun ji ko? Ko kun ji daɗi fa kar ku ci".
Momy ta ce"To Umma yunwa muke ji fa".
Ta ce"Idan kun ƙi ci sai ku shiga kitchen ku ɗauki golden morn ku haɗa ku sha, idan ya dawo ku ce masa ba ku ci komai ba yunwa kuke ji, ku ce ba ta ba ku tuwon ba".
Momy ta ce"To". Amma a sanyaye, saboda yunwa take ji.
Sauda ta ce"Ki yi haƙuri kin ji ƙawata, ni na san me zan siya muku".
Ta ce"To".
Ta ajiye wayar, sai da Maryam ta koma kitchen sannan ta sake tsarawa yaran, ta ce inji Umma, ta ce sai sun ƙi ci za ta dawo, ai kuwa suka yarda.
Sai da ta sauke tuwon ta dada indomin saboda ta manta, ta zubo ta kawo musu,lokacin har ƙarfe uku ta gota, ta ajiye ta ɗakkowa Nana indomi, ita kam ana ajiyewa ta fara ci ta manta da gargaɗin yayarsu saboda yunwa take ji, kuma dama duka-duka shekararta huɗu, su kuwa manyan ba su saɓa ba, loma ɗaya kowa ya yi a layi, idan wannan ya ci, sai wannan ya ci, sai suka tsaya suna kallon tv, Maryam ta ce"Ya dai? Ku ci mana".
Momy ta ce"Ni dai ba na ci, na ji babu daɗi, ko Kausar?"
Su ma suka haɗa baki wajen faɗin"E babu daɗi".
Ran Maryam ya ɓaci, lallai sun yi sa'a a wannan karon zama ta zo na mutu-ka-raba, da babu abin da zai hana ta fesawa babbarsu mari, ba ta ce komai ba, ta kwashe ta kai kitchen, babbar ta shige ɗaki, duk suka bi ta, babu jimawa kuma ta fito ta shiga kitchen ɗin Maryam ta bi bayanta, ta tarar tana haɗa golden morn, ta haɗa shi kofi uku ta ƙwala musu kira, suka fito suka ɗauka suka koma ɗaki, ita kuwa Nana sai ta zauna a nan falon tana kallo.
Maryam ta cika da mamakin yaran sosai, ta kuma saka a ranta ta san zaman da za ta yi da su.
Da yamma da ta yi baƙi sai ta ba su taliyar, tuwon kuma ta rufe musu shi, tana jira babansu ya dawo ta sanar masa ta ga matakin da zai ɗauka.
LITTAFIN NAN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 700
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
***