ZAFIN WUTA

Chapter 9

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000180223 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000180215

 

      CHAFTER 40-45 

 

بسم الله الرحمن الرحيم. 

 

Tsit Abba yai jin maganar da nai, sai kuma ya was he baki tare da faɗin. 

 

   "Yauwa Mubeenah, ko ke fa, to yanzu kiyi sauri ki shirya zuwa anjima bayan Ummanku ta gama abin kari sai kiyi mu kama hanya dan mu isa da wuri." ya ƙarashe maganar tare sa taimakamin na fito daga cikin bahon jikina na tsiyayarda ruwa, sake zuba min ruwa yai a buta  sannan ya damƙamin a hannuna ya na ta rarrashina gami da lallaɓawa, sai naji jikina yai sanyi ƙalau, duk da ba ganin shi nike ba amma a iya maganar da yai min na fuskanci lallai ya ji daɗin maganar da na faɗa, sai na shiga zargin kaina akan ƙin bin umirninsa da nike a baya, wataƙila hakan ne ya saka ya tsaneni saboda kafiya da baƙin taurin kai irin nawa. 

 

Ban san sanda bakina ya furta. "Abba dan Allah ka yafe min duk abin da nai maka, bazan sake ba, na yi danasanin wanda nai maka a baya, nasan da ace na bi umurninka da na auri abokinka da yanzu nima kana so na kamar yanda kake son su Yaya Habiba, daga yau bazan sake saɓama umuninka ba in sha Allah." 

 

Kasaƙe Abba yai jin  maganar da nayi, sai jikinshi yai sanyi, duk wanda ya taɓa zuwa gidanmu koda na wuni ɗaya ne, to yasan rashin jituwar da ke tsakanina da Abba, tun maƙota na zuwa bada haƙuri idan yana dukana har takai da suk girman unguwarmu babu me ko kallon inda muke idan wani abu ya haɗo ni. 

 

Bai ce komi ba sai juyawa da yai ya shige ɗakin Umma wacce dukkan abin da ke faruwa akan idonta, indai wajen iya laɓe da jin ƙwam ne, to Umma ita ce kan gaba, bata yarda gulma ko tsugudidi su wuce ta, a haka ma wai  dan a Legos muke ta na tsoron ƴan iskan unguwarmu, dan abu ƙalilan sai ka ji ance ansakawa mutum taya an ƙone shi ƙurmus,  musamman idan wani abu ya haɗa yare da hausawa. 

 

"Wallahi kar ka yarda da abin da ta gaya maka, yaudara ce kawai, so take tai mana baƙin cikin cin arziki shiyasa ta kulle idon, yo ita makantar haukace da zata sameta lokaci ɗaya, ade bincika zaka samu wani abun ta shafa dan baƙin munafurci irin nata." Umma tai maganar ta na shanye ƙananun idanuwanta irinna kwararrun ƴan gulma da munafurci. 

 

"Ubanta ya zurma ya afka ya zunduma ya faɗa cikin shafawa ido wani dan makancewa, ita yanzu dan kutumar abu ta kazanta har ta yi wayon sanin makirci, to aniyarta ta bita, na fi ƙarfin ta yaudare ni wallahi, zan gwada ma ta ba abanza nike zaune a legos ba, nima tantirin kaina ne, iskanci sai de mu koyawa wasu badai mu a koya mamu ba." Abba yafi cikin tada jijiyoyin wuya, daga jin abin da Umma ta faɗa shikenan har ya yarda ya  hau kai ya zauna daram,dama ba tun yau ya saba irin haka ba, sau da dama hakan kan kasance, lafiya lau za'ayi magana da shi amma da zarar Umma ta ce ba haka ba babu bincike ba lissafi zai hau kai ya zauna akan yanda ta ce hakanne gaskiya. 

 

 

Mamace ta zo ta kama ni ta kaini ɗaki tare da yimin shimfiɗa da saka min hijabi, alƙibla ta fuskantar da ni tare da bani umarnin yin sallah. 

 

Ina kabbara Sallah wani irin rauni ya baibayeni, sai na ji ina buƙatar tsiyayarda damuwata a gaban Mahallicina me rahama, nasan zai sauƙaƙamin ta wani ɓangaren, aiko na shiga zubda hawaye masu zafi yayinda nike gabatar da Sallah cikin nutsuwa da kamala, kuka me ƙarfi ya kubcemin lokacinda na duƙar da gaɓoɓina aƙasa nakai sujjadah, kuka da addu'a nai sosai   har sai da naji nauyin da ya tokaremin ƙirji ya  sauka sannan na ɗago naci gaba da Sallar cikin karsashi har na sallame, bayan na kammala azkar na hau karatun alƙur'ani me girma, da yake harda ce da ni, dandanan nishaɗi ya baibaye, tabbas karanta littafi me tsarki babbar rahamace, babu abin da yake saka ni nishaɗi kamar inji ina karanto littafi me tsarki tiryan-tiryan. 

 

 

Na ɗauki lokaci me tsawo ina karatu, har sai da muryata ta disashe sosai sannan nai addu'a tare da shafawa nai zaune abuna ina nazarin rayuwa, wato Allah alhakim, wa ta hikimace ta ubangiji wannan makantar da ya ɗauramin, godiya nai a gareshi ta hanyar yin tazbihi harma da salatin Annabi, duk safiyar duniya da zan wayi gari da ciwo ko babu sai na yi tarin aiyuka kamarsu, share ɗakin Mama da na Umma, share tsakar gida, hura wutar ɗaura abin kari, wanke-wanke, wankin kayanda aka ɓata, idan ka cire kayan Mama hatta na  Abba nice zan wankesu kullum ranar duniya, aƙalla Yaya Sumayya na daka kaya kala uku duk rana, haka zan haɗa in wanke, wani bin Abba ya na zundumamin zagi Umma kuma na mita haka zan zage inyi aiyukana babu me cemin sannu sai ma zagi da nike sha wajen Abba, amma nice yau zaune a ɗaki ina hutawa kamar yanda kowa ke yi, babban abin da yai min daɗi be wuce yanda yau bazanje shago ba, sam bani son zuwa shagonan saboda ƴan iskan da ke wajen, amma banda damar daina hakan, sai gashi yau babu zuwa shago saboda lalurar makanta. 

 

Ban san na ɗauki tsawon lokaci ina tunani ba sai da Abba ya kwaɗo min kira, firgigit na farka daga duniyar tunani da na lula, da laluben hanya har na kawo ƙofar ɗakin. 

 

"Gani Abba." 

 

"Amshi wannan kunun ki shanye sai kiyi sauri kizo muje." 

 

"To Abba nagode." 

 

Na faɗa tare da lalubawa har na kai inda hannunshi ya ke na amshi kofin kunun, juyawa yai abinshi, ni kuma na zame na zauna  a wajen tare da kafa kofin a baki na shiga shan kunun, ina son abu me ruwa sosai hakan ya bani damar shanye kunun duka. 

 

Lalubawa na sake yi ina bin bango har nakai wajen jakar da nike ajiye kaya, da lalube ba buɗe ta na ɗauki kedar thank you wacce nike ajiye a gefen jakar, laluba ƙasan jakar nai harna lalubo wa ta  ƴar siririyar chain, danƙe shi nai a hannuna kamar wani zai ƙwacemin, sannan na saka hannuna na kakkaɓe jakar tawa na janyo ta zuwa jikin bango na aje nima na zauna zaman shiru, har yanzu zuciyata ba ta daina dokawa da matsanancin ƙarfi ba, kuma ina jin wani irin sanyi me kashe gaɓoɓi ya na baibaye ni, ga wa ta iriyar kasala me sakar da gaɓoɓi da ta saukomin. 

 

Shiru nai ina sauraran bugun zuciyata harna tsawon lokaci, ban san adadin mintunan da na kwashe ba, sai da na jiyo muryar Abba ya na faɗin. 

 

    "Mubeenah, ke Mubeenah ki fito idan kin gama ke nake jira mu yi mu tafi lokaci ya na ja." 

 

Zumbur ta tashi kamar dama jiran kiranshi nike. 

 

    "Abba dan Allah ka taimaka ka ɗaukar min jakar tunda bana ganin hanya." 

 

Bai musa ba ya shigo ya ɗauki jakar tare da kama hannuna muka fito, bai saki hannuna ba sai ji nai ya na faɗin. 

 

"To Mubeena ga mutanen gidana zasuyi sallama da ke." 

 

Murmushi nai sannan na ce. 

   "Mama nasan kuka kike yi, dan ina iya jiyo zafin zubar hawayenki a cikin zuciyata, dan Allah ki kwantar da hankalinki babu abin da zai sameni sai alkairi, ina ji a jikina wannan tafiyar ita ce zata zamo tsanin da zan taka wajen ganin na cimma muradai da mafarkaina, haƙiƙa Mama ke uwace a gare ni, a duk inda nike zan kasance cikin kwanciyar hankali matsawar za ki ch gaba da yi min addu'a kamar yanda kika saba, zan yi kewar kulawarki a gareni, Allah ya baki haƙurin jure rashina uwa ta gari me maida ɗiyarta kamar sarauniya saboda soyayya da kulawa🥹." 

 

Kuka ne ya kubcewa Mama me tsananin ƙarfi, yayinda na matso inda muke ta riƙe hannuna gam ta na faɗin. 

 

"Ibrahim ka ji tsoron Allah karka rabani da Mubeenah, wallahi ina jinta kamar ƴar da na tsugunna na haifa, ka ji tausayin halin lalurar da ta ke ciki kabarmin ita, wallahi nayi alƙawarin zan ɗauki dukannin ɗawainiyarta." 

 

   "To munafuka ƴar baƙin ciki me baƙin hali, ai dama batun yau ba nasan kedin munafuka ce, yo munafuka manah idan ba munafurci da baƙin ciki ba, ina ruwanki da shiga sha'anin uba da ƴa, wannan ai kinibibine irin na fulanin ruga." Umma tai zaram ta faɗi jin maganar da Mama ke yi na neman yin tasiri a zuciyar Abba, dan ta lura kamar jikinshi ya ɗan yi danyi. 

 

Cike da macin rai Mama ta saki hannuna ta juyo wajen Umma ta na faɗi.  

   "Ke Umma ki kiyaye bakin ki😡, kisan abin da za ki dinga faɗa, ina ruwanki, wa ya saka da ke, ban san shigar shigula, ki kiyaye ni wallahi kar ki bari in waiwayo ta kanki dan abi  ba zai yi maki daɗi ba, ina ɗaga maki ƙafane kawai dan a zauna lafiya amma badan ina tsoronki ba, daga yau kar in sake ji kin tsomamin wannan baƙin bakin na ki me kama da anzunguro kan kare ta taga, ki shiga hankalinki." 

 

Mama ta yi maganar ɓacin rai da hasala na bayyana a fuskarta, yayin da Umma tai murus sai walimar idanu ta ke  yana shege lahira, shi kanshi Abba mamakin Mama ne ya daskarar sa shi a tsaye, dan bai taɓa tunanin ta na da zafi har haka ba, lallai an ƙure haƙurin damo, ya faɗi a zuciyarshi. 

 

Juyowa ta yi wajen shi tare da faɗin. 

   "Tabbas ban isa in hanaka zartar da hukunci akan Mubeena ba, amma zan tuna maka gaji tsoron Allah, wannan baiwar da kake wulaƙanta rayuwarka ita ce rufin asirinka, kuma amanace a wajenka, muddin ka zalunceta Allah ba zai barka ba, ka je ka yi duk yanda kaga dama da ita." Mama na gama faɗin hakan ta zo wajena ta damƙamin wani abu a cikin hannuna sannan ta shafa fuskata ta juya fuuuuu ta shige ɗakinta. 

 

Da sauri Umma ta matso kusa da inda muke ta fara jan hannun Abba wanda ke riƙe da jaka ta ta na turamu waje wai kar Mama ta fito ta hanamu tafiya. 

 

Ina tuntume da komi haka Abba ya ja hannuna har muka fice sannan ta saki hannunshi ta dawo cikin gida ta kaɗa su Yaya Habiba zuwa cikin ɗaki  suka shige harda kullo ƙofa. 

 

Ina tuntuɓe da komi haka Abba ke jaye da hannuwana har muka shiga cikin unguwarmu sosai inda mutane keta hada-hadarsu su na kaiwa da komowa, a Legos babu ƴan zaman banza kowa fitowa ya ke ya nemi na kanshi dan rufawa kai asiri. 

 

Munyi tafiya sosai kafin mu samu abin hawa, nan Abba ya lalubo wayarshi wacce ta ci duniya duk ta sha ɗauri da lobali ya lalubo number Yah Hashim ya kirashi dan ya yiwa me abin hawan kwatancin inda za'a ajemu. 

 

Hawa mukai bayan mun tsadance muka tafi, har lokacin ban daina jin sautin bugun zuciyata ba a cikin kunnuwana, sannan sanyin jikina sai daɗa ƙaruwa ya ke kamar wacce ta shiga cikin na'urar sanyi. 

 

A daidai farkon shiga BANANA ISLAND aka sauke mu, Abba ya sake kiran Ya Hashim, kafin ya zo sai da muka ɗauki mintuna atsaye, tun ina jin daɗin tsayuwar har ta gundure ni, hakan ya saka nace cikin sanyin murya. 

 

  "Abba dan Allah ka samo mana inda zamu ɗan zauna, na gaji da tsayuwa wallahi." 

 

Waige-waige ya shiga yi kamar me neman wani abu, wa ta bishiya me kyau ya hanga a gefenmu, hakan ya saka ya ja hannuna muka je can muka zauna ya na mitar jimawar da Hashim yai be zo ba. 

 

 

Ƙungurmin daji ne me cike da munanan halittu iri daban-daban, wa ta iriyar guguwace me haɗi da ƙura ta taso da iska me tsananin ƙarfi, saboda tsananin ƙarfin iskar guguwar sai da halittun  da ke wajen suka shiga neman wajen ɓuya, sauti marar daɗin ji me kama da tsawa me firgitarwa ne ya cika dajin gaba ɗaya, a daidai wajen wa ta tshohuwar bishiyar kuka me rassa da jijiyoyi da yawa wannan guguwar ta tsaya, a hankali yayyafin ruwa ya fara sauka a cikin guguwar da ke ɓacewa ta na komawa ruwa, farace tas tas farin har ya yi yawa kai da ganin irin hasken nata kasan  ba dai mutum ba sai dai jinsin aljannu, fara ce kuma doguwa me yalwar baƙin gashi da tsananin tsawo ta bayyana fuskarta a murtuke, idanuwana sun kaɗa sun sauya launi zuwa launin shuɗi me haske, cike da ɓacin rai ta buɗe murya cikin amo marar daɗin ji ta kwala kiran. 

 

"Zizzau! Zizzau!! Zizzau!!!." 

 

A yanda ta ke magana sautinta na fita da amo me tsoratarwa, bakinta kuma na feso da feshin ruwa masu zafin gaske, wannan bishiyar kukarce ta shiga girgiza da tsananin ƙarfi, kafin wani hayaƙi ya bayyana wani baƙin gajeren aljani mumunan gaske ya bayyana, duƙawa yai cike da girmama ya fara kirari gami da fadanci. 

 

Dakatar da shi wannan aljanar ta yi cike da facin rai ta ke faɗin. 

 

  "Waye wanda ya aikeka yin aiki akan goɗiyata? tabbas za ka fuskanci hukunci me tsanani saboda saɓa umurnina da kuma karya dokar da na gindaya muku akan aiki da waɗacan butulun bil Adaman waɗanda basu san komi ba sai cutar da ƴan uwansu da yaɗa zalunci a doran ƙasa, yanzu-yanzu da ƙarfin ikon ubangiji na baka izini kaje ka karya aikin da kai, sannan kuma kadawo ka kai kanka wajen ruwan hukunci." 

 

Bata jira abin da zai ce ba ta ɓacewa daga wajen, nan take ruwan ya ɗauke gaba daya kamar be taɓa wanzuwa ba. 

 

Cikin hanzari wannan baƙin aljanin yai girgiza tare da ɓacewa ɓat, bai bayyana a ko ina ba sai akan bishiyar da Abba da Mubeena suke zaune su na hutawa. 

 

Shuuuuuuu, wani abu ya gifta ta gefen idon Mubeenah, yayin da baƙin hayaƙi.