ZAFIN WUTA

Chapter 10

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000165665 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000165657

 

   CHAPTER 45-50 

بسم الله الرحمن الرحيم. 

Ya mamaye wajen, tare da iskar guguwa me tsanani, hakan ya yi daidai da tsayuwar jibgegiyar motar da Ya Hashim ke ciki, wasu irin baƙin ruwa masu tsananin azabe suka shiga zubowa daga idanuwana gaba ɗaya hankalina ya gushe saboda ruɗani da kuma azabar da idanuwanta ke ma ta, Abba ne ya juyo ya na kare fuskarshi daga yashin da guguwar ta ɗebo, sai ya ganni a wannan halin, cike da firgici ya soma ja d baya ya na girgiza kai ganin yanda baƙin ruwa ke tsiyaya daga idanuwana. 

 

Fitowar Yaya Hashim daga mota ya yi daidai da ɓacewar guguwar haɗe da ɓacewar wannan ruwan daga kan fuskata kamar ba au taɓa wanzuwa ba. 

 

A hankali na ke buɗe idanuwa waɗanda sukaimin nauyi, abin al'ajabi sai na ga Abba da Yaya Hashim tarrrr, sake  rufe idon nawa nai sai kuma na sake ganinsu, da matsananin sauri na miƙe tsaye zumbur ina dube-dube amma stil ina ganin komi clear. 

 

   "Allahu akbar kabeeran, Allah na gode maka, Allah kai ne abin godiya, Alhamdulillah, Alhamdulillah." 

 

Na faɗa ina sake maimaitawa cike da farin cikin yanda ganina ya dawo. 

 

   Sakin baki Abba yai ya na bina da kallo me cike da mamaki da kuma tsoro, ga zallar al'abin abin da ya gani yana zuba daga idona. 

 

Yah Hashim ne ya katse shi ta hanyar dafa kafaɗunshi ya na faɗin   "Wai Abba lafiya?."  

 

Sannan ya dawo hayyacinshi tare da basarwa ya miƙe tsaye ya na bin shawar da zuciyarshi ta bashi akan b waske kawai ya samu ya rabu da ni lafiya. 

 

A gaggauce Ya Hashim yai mana jagora zuwa gaban motar, har lokacin fuskata ɗauke da annashuwa da farin ciki, cike da ɗauki na matsa gaban motar ina jiran ya buɗe  min da mota itace ƙarshen abin da nike son hawa a rayuwata, ina bala'in son inganni a cikin mota, amma babu halin hakan, iyakata da ita sai gani daga nesa. 

 

Tun da muka fara shiga cikin tsararriyar unguwar bugun zuciyata ya sauya salo, numfashina na yau shirin ɗaukewa amma ban bashi damar ɗaukewarba nike janyo shi da sauri, wato malam duniya da arziƙi su na inda suke, tsayawa baku labarin yanda unguwar ta kai ƙarshe a haɗuwa ɓa ta lokacine, sai dai kawai ince kugi imagin. 

 

Daidai wani ƙaton get na alfarma wanda ya lashe maƙudai wajen kafuwarshi Yaya Hashim ya tsaya da motar tare da fito da wani card ya miƙawa ɗaya daga cikin jibga-jibgan jaruman escort ɗin da ke  zagaye da get ɗin. 

 

Bayan am bamu damar shiga cikin gidan ta hanyar buɗe manah wannan makeken get ɗin, kai tsaye Yaya Hashim ya danna kan motar cikin makeken ƙeraren gidan wanda yakai ƙarshe wajen haɗuwa. 

 

    "Muƙuƙut, maƙwat." 

Abba da ya hangame baki tare da karkace kai ke ta faman haɗiyar yawu, lissafi da kwancewa kawai ya ke a kwanyarshi, tare sa wasu irin tunanika da ke bijiro ma shi. 

 

Ni kuwa sake rakuɓewa nai ina ƙara kallon yanda aka narke dukiya wajen gida wannan gida me kama d aljannar duniya, tun da nike ban taɓa ganin gida wanda ya kama ƙafar wannan wajen haɗuwa da tsaruwa ba. 

 

 

 

 

 

BANANA ISLAND. 

 

Zazzaune suke su huɗu akan lallausan carpet, gabansu an cike shi da kayan break fast na alfarma, kallo ɗa ya zakai musu ka gane basu cikin walwala. 

 

Nisawa kamulallen mutum yai tare da cigaba da maganar da yake wacce ta saka sauran nutsuwa. 

 

     "Wallahi hajjo inda kika ga mutumin ba za ki ce ba mutum ba ne, saboda kamala da dattako irin na shi, ya tabbatar min da idan har muka samo wacce ta amince zata yi wannan aiki to babu makawa Fauzan zai warke ya samu lafiya kamar kowa,   abin da ke bani tsoro yanzu ɗaya ne, shin ta yaya zamu samu wacce za ta amince da aikin alhalin ko mu da muke iyayenshi ba komi zamu iya yi ma shi ba, ni kaina jiya da na kusanci inda ya ke sai da na ƙone wallahi." 

 

Yai maganar ya na kallon hannunshi da yai jazur ga kuma alamar konuwa ta tashi a hannun na shi. 

 

   

 

   "Ya Allah gareka muka dogara, Allah ka bamu mafita akan yanda zamu shawo kan ciwon wannan bawa naka wanda yake cikin matsanancin hali." 

 

  Hajjo tai maganar fuskarta na jimamin lamarin. 

 

Mommy ce ta ɗan muskuta tare da gyara kishingiɗar da tai ta buɗe baki cikin ƙarfin hali ta na faɗin. 

 

   "In sha Allah za'a dace dan kuwa jiya na yi magana da wannan yaron Hashim me wanki da guga akan ina so ya binciko min yarinya me hankali da nutsuwa a can cikin unguwanin talakawa, ya amsamin da in sha Allah za'a samu, yanzu haka na tabbatar da su na hanya dan kuwa munyi waya yau da asuba ya sake tabbatar min da ansamu kuma ƴar uwarshi ce, ya na da yaƙini akan zata iya, to na bashi umarni akan ya ɗaukominsu yanzu da safenan kafin anjima Mu'allim ya zo." 

 

Jinjina kawuna sukai a zuciyoyinsu su na addu'ar Allah ya sa a dace, indai kuɗi za su yi aiki to a shirye suke wajen ganin sun salwantar da ko nawa ne dan samun lafiyar sanyin idaniyarsu. 

 

 

 

Bayan isowarmu da kamar mintuna goma, amma shiru babu wanda ya leƙomu, mamaki, gidadanci gami da ƙauya ci sun gama daskare man kawunanmu ni da Abba, idan Abba ya kafe abu ɗaya da ido tofa ba zai janye idonsa ba har sai ya gamsu da bayanin da kwanyarshi ke ma shi na adadin kuɗaɗen da abun ya lashe kafin wanzuwarshi, duk da iskan AC da fankoki ma su wurwurawa da tsanani  gudu hakan bai yi nasarar hana gumi tsatstsafowa Abba ba, duk bayan sakanni sai ya kai hannunshi ya shafce gumin da ke barazanar jiƙeshi, sai zare jajayen koɗaɗɗun idanuwansa ya ke ya na shege lafiya, lissafi tun ya na yinshi ya na tafiya daidai har busy yaiwa brain ɗinshi yawa ta daina bashi haɗin kai saboda yanda ya takurata da lissafe-lissafe. 

 

Tsinewa rashin siyo calculator ya saka a cikin aljihu saboda irin haka da yayi yafi sau shurin masaƙi, ni kuwa tun lokacin da akai mana iso zuwa wannan danƙareren ɗakin na alfarma wanda ya ke cike da kayan ƙawa da more rayuwa jikina yai sanyi, sai na soma tunanin anya kuwa a cikin duniyar mutane mu ke, ko dai duniyar aljannu Yaya Hashim ya kawo mu, tun ina kallon kayan ƙawa da more rayuwar da aka wadata ɗakin da su cikin tsoro, mamaki gami da al'ajabj, har na ware ina bawa idanuwana abinci nima nabi sahun Abba wajen buɗe idanuwana ina kallon kayan ban mamaki, wato malam arziƙi na inda yake, talaka bawan Allah inji hausawa sukace Talaka buzun banza indan ta mutan gari sai ya mutu. 

 

Saƙe-saƙe da lissafe-lisafe babu wanda banyi ba, amma sam hankali da brein ɗina sun gaza lissafo min adadin yawan maƙudan kuɗaɗen da aka narka wajen gida wannan gida. 

 

Wa ta dattijuwar ma ta ce ta shigo da kayan uniform a jikinta, a bayanta matasan ƴan mata ne suma sanye cikin uniform kalar na ta, sai Yaya Hashim da ke biye da su waya kare a kunenshi da alama waya ya ke. 

 

Cike da fara'a matar ta ƙaraso inda muke tare da bawa ƴan matan umarnin ajiye treyn da ke hannuwansu wanda ya ke shaƙe tab da kuloli da jug na alfarma. 

 

Gaishe mu tai tare da ƙare manah kallo ganin irin shigar da ke jikinmu, duk da ba kallon raini ko ƙasƙanci tai mana ba amma sai naji duk na muzanta, musamman dana ɗaga kai na kalli yanda kayan uniform ɗin jikinta suka sha guga suka kwanta kuf, sannan fatarta luwai gwanin kyau dan harda siririn glashi a idonta, yaƙe kawai nai ma ta ina sinne kaina ina jin wani iri, atamfar jikina na kalla wacce tana ɗaya daga cikin kayan da nike ji da su, Yaya Sumayya ce ta bani ita a wani zuwa da sukai Katsina biki suka dawo da kaya niƙi-niƙi wanda ƴan uwan Umma suka basu, shine ta ɗaukota ta bani saboda rigar ta yi daidai da ni, saboda bani da ƙiba sam sai dai inada cikar jiki da ƙira me jan hankali.  

 

Janye ƙafafuwa nai tare da ƙudundune su a cikin hijabi, dan ina ɗago kai naga matar ta kafe ƙafafuwan nawa da ido, ba tun yau ba nasan Allah yai mani halitar ƙafa me kyau da tsari, sautari idan na ina ina zaune da Mama takan janyo ƙafafuwa ta ɗaura a kan cinyarta ta na shafawa wai burgeta suke. 

 

  Abbana yai saurin saukowa ƙasa bayan ya amsa gaisuwar matar cike da fara'a kamar bakinshi zai yage, bayan ta gabayar mana da waɗanan kuloli wanda na tabbata cike suke da abinci na alfarma, godiya Abba ya shiga zundumawa kamar sabon maroƙi, nannaɗe hannun riga ya soma yi tare da haɗiyar yawu ji kake "Maƙwat". 

 

Kiciniyar buɗe food flasck ɗin ya soma amma ya kasa, gudun kar ya je yai ɓarna ya sa ya kalle ni tare da faɗin. 

   "Ke Mubeenah sauko ki buɗe mana coolar muyi mu ci kafin mutan gidan su fito, dan wallahi Allah cikina ya kwakware kamar ban taɓa cin komi ba, dama dai ɗan ruwan kunu ne wanda Umma ta dama kuma kinsan halinta da baƙar ruwar tsiya ɗan kaɗan ta sammin." 

 

  Banja da nisa ba na sauko, dan nasan halin Abba tsaf zai dalle ni maruka babu ruwanshi dan yasha faɗi da bakinshi cewa shi abin kunya gaba ya bashi ba bayaba, iskanci da abin kunya gadonshi sukai. 

 

    Da ƙyar na iya buɗe food flask ɗin waɗanda suke ta faman ɗaukar ido da walwali, zazzafan peper soup ne wanda ke ta faman tashin ƙamshi me tado tsohuwar yunwa, ɗayar kuma soyayyen dankalin turawa wanda aka soya da kwai, jug ɗin kuma kunun madara ne fari sol sai daƙƙuwa yakemin, ban san sanda nima na bi sahun Abba wajen haɗiyar yawuba. 

 

Abba bai jira na zuba a plate ba ya suri cinyar kaza ba tare da yayi bisimilla ba ya dirar ma ta, ganin haka ya saka nima nai maza na zanyo plate na warci ƙirji da fuffuke na saka tare da ɗan tattare hijabina gudun kar ta ɓaci nai bisimilla tare da far ma ta, lokacin da ɗanɗanon naman ya ratsa kwanyata sai da nai hooking na wucin gadi, idan ma rantsuwa nai to bazanyi kaffara ba tunda nike ban taɓa cin kaza me makamancin ɗadin wannanba, ga shi ta dahu luɓus tai taushi gwanin ɗadi wajen ci, ina ci ina jinjina kwarewar wacce ta sarrafa wannan girki, ba maki ɗari ba ni dai har maki dubu ɗari na bata wallahi. 

 

Jug ɗin kunun na janyo na tsiyaya a ƙaramin cup, tare da zuba dankalin shima a plate ɗin da nike cin kaza, harga Allah ina da karah da kawaici amma banda wajen abinci, ina bawa cikina muhimmanci sosai, bare  nasan idan na tsaya sanya tsaf Abba wai wawure abincinan tas ya barni da haɗiyar yawu, shi yasa nima ban tsaya cutar kainaba na saki jiki na cika tunbina tsaf. 

 

Abin mamaki duk irin mugun cin Abba sai da ya gaji ya ture kazar nan ya koma kan kunun madara, shima ya ɗaɗɗaka sosai amma bai shanye ba, yo ta ina zai iya shanye wannan kayan gara waɗanda ƙamshinsu kaɗai ya isa ya ƙosar da mutum bare ace ya ci, wani abu ɗaya da na hasaso shine, tabbas idan dai ɓangaren masu girki za'a ɗaukeni aiki zan zage in koyi irin waɗanan abubuwan dama na daɗe da burin zuwa koyan girki amma sai Umma ta sakamin mugunta, har makaranta abokin Abba ya taɓa samomin ni da ɗiyarshi amma ta shiga ta fita ta hanani zuwa sai aka ƙaƙabamin zaman shago cikin yare. 

 

Duk abin da muke Yaya Hashim na zaune a gefe yana kallonmu, kunya gami da takaicin halin Abba duk ya cikashi, dama yasan za'ayi haka shi yasa koda wasa bai taɓa nuna ga irin gidan da ya ke aiki ba dan yasan dole wa ta rana irin haka za ta faru. 

 

Bayan na gama ne na suɗe hannuna tas kaɗi da lashe pink lips ɗina kamar banci komi ba, sai lokacin hankalina yakai wajen Abba wanda ya wani bararraje kamar gidanshi, duk ya ɗiga musu miya a jikin carpet da gabanshi rigarshi da ya ɓata kamar wani ƙaramin yaro. 

Kunya ce ta kama ni ganin yanda tai, ina tunanin inda zan samo ma shi ko da tsumma ne ya goge jikinshi kafin masu gidan su iso, amma kash na makara dan kuwa ban gama tunanin mafita hancina ya shaƙomin wani irin sanyayyen daddaɗan turare me saukar da nutsu....✍️