ZAFIN WUTA

Chapter 11

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000142698 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000142690

 

     CHAPTER 50-55 

 

بسم الله الرحمن الرحيم. 

 

Me saukar danutsuwa gami da nishaɗi, kafin ingama tunani akan daɗin ƙamshi turare wa ta matashi wacce ta ƙawatu cikin uban ado kamar wacce za ta je gasar kyau ta bayyana a parloun, gayu iya gayi ta yi shi amma kuma kallo ɗaya nai ma ta na tabbatar da ta na tare da matsananciyar damuwa, fuskarta fayau babu komi akanta sai man leɓe me sheƙi, idanuwanta duk sun zurma can ciki da alama tayi rashin lafiya saboda sautari akan samu irin wannan ramarne wajen wanda yai rashin lafiya, ko me fama da matsananciyar damuwa. 

 

Siririyar sallama ta yi idanuwanta na akanmu, amsa ma ta na yi ina janye idanuwa daga kallonta, kallon secons biyu tai mana sannan ta ɗauke kai zuwa inda Yaya Hashim ke zaune, cike da girmama ya zamo daga kujerar tare da faɗin. 

   "Ranki ya daɗe Hajiya Sulaima barka da wannan lokacin." 

 

A taƙaice ta amsa tare da bashi umurnin mu biyo bayanta, babu ɓata lokaci yai manah inkiya akan mu taso da sauri. 

 

Hakanan kawai na ji gabana ya tsananta dokawa da tsananin ƙarfi, sannan kuma kasala ta baibaye ni da ƙyar na samu na miƙe akan ƙafafuwana. 

Abbama tuni ya miƙe ya na ta faman sakin gyatsa da buɗaɗɗiyar muryarshi.  Rufawa Yaya Hashim baya mukai har zuwa wa ta ƙofa ta glass wacce akaiwa ado da kalar gorlding, sai ɗaukar ido ta ke, bayan wannan wacce Yaya Hashim ya kira da Sulaima ta shiga muma muka rufa ma ta baya ni da Abba fuskokinmu fal mamakin irin wannan dukiya da aka narka, a wani ƙayataccen makeken parlou wanda ya gaji da gaɗuwa muka ɓulla, su uku ne zaune akan ƙayataccin kujerun alfarwa waɗanda aka ƙawata wajen da su, Dattijuwa ce zaune kusa da wa ta mata wacce taɗan jingina da jikin Dattijuwar, sai wa ni kamulallen mutum zaune a kujerar kusa da su, kusa da mutumin wacce aka kira da Sulaima ta nufa tare da zaunawa ƙasan ƙafafuwanshi. 

 

  Cike ca fara'a Dattijuwar ta ke mana sannu da zuwa, yayin da na sake shiga wani irin yanayi marar misaltuwa ga zazzaɓi da ke shirin rufar ma ni nan take, a ƙasƙance muka rakuɓe ni da Abba, mu na jinmu wani iri ganin yanda muka samu mutanen wajen kamar sarakuna saboda ado da kwalliya, mu kuma sai na dinga ganinmu kamar bayi duƙe a gaban sarki ko yarima. 

 

  Abba kamar zai taune harshe wajen gaisarda su,ni kuwa cike da nutsuwa na gaidasu ba tare da na kallesu ba. 

 

   Mommy ce ta ɗago a hankali ta na gyara zamanta tare da kafe ni da ido kamar me kokonto a kaina, sai kuma ta kalli Pahpah wanda shima dai idonshi a kaina ya ke, ita kuma Hajjo hankalinta na wajen Abba wanda ke ta faman zare idanuwa ya na ƙarewa duk abin da idonshi ya sauka akanshi kallo, idan ya kalli abu sai ya lissafi idadin kimanin kuɗaɗaɗen da abin zai iya lashewa sannan ya jinjina kai ya koma wajen wani abun, bayan kamar min tuna biyu da zamanma Pahpah ya kalli Yaya Hashim tare sa gyaran murya sannan ya ce. 

 

    "Masha Allah, Hisham wannan ita ce ƙanwar ta ka ko? gaskiya na yaba da hankalinta sosai, kuma ina da yaƙini akan za ta iya, nutsuwarta da kamalarta sun burge ni ainun, sannan ina fatan itace za ta zame mana abin alfahari anan gaba." 

 

"Dararammm" ƙirjina ya doka da tsananin ƙarfi, yayinda zuciyata ke kokowar fitowa saboda razani da fargabar da nike tsintar kaina a gaban waɗanan mutane. 

 

   Aje numfashin Pahpah ya yi daidai da tabbatuwar lissafin da zuciya da kwanyar Abba ya haɗe waje ɗaya, tare da gamsar da kanshi wannan ita ce sakayyar yanda gobenshi da ta iyalanshi za ta kasance, dan haka sai ya aro bargon nutsuwa ya yafawa kanshi, tare da ƙoƙarin hana idanuwanshi kalle-kallen abubuwan da suke neman caza tunaninshi. 

 

  Nutsuwarshi ta yi daidai ta kallonshi da Pahpah yai tare da fara yi ma shi magana ya na karantar yanayinshi. 

 

Babban abin da ya burge bai wuce yanda naga Abba ya kame kamar ba shi ba ya na zayyano zantuka masu ma'ana da dattako, sai na ji wani sanyi da farin ciki ya baibaiyane yau ɗaya Abba ya ɓoye hallayarshi a gaban mutane. 

 

⭐⭐⭐⭐ 

BAYAN AWANNI BIYU. 

⭐⭐⭐⭐ 

 

Zaune nike akan mafefen royal bed ɗin da ya mamaye ɗakin, ya yinda idanuwa ke zubarda hawaye wanda ni kaina bansan na minene ba, amma zuciyata ta tilasta ni amincewa sa lallai Abba baya so na, ban taɓa kawo afkuwar irin wannan lamarin nan kurkusa a rayuwata ba, ban san mi yasa a kaina Abba ya ke kasancewa me son kanshi ba, muddin lamari ya shafe ni to babu makawa sai Abba ya nuna son kai akaina. 

 

   Ɗaure fuska na yi tare da furta "Abba kenan, ina mai tabbatar maka daga wannan karon rayuwata ta canza, Abba daga yau bazan sake kasancewa cikin baƙin cikin abubuwanda kake yiminba, daga yau zan tsaya tsayin daka wajen ganin na inganta rayuwta kamar ko wace mace." Na yi maganar kamar Abban na gabana ko ancemin ya na jin abin da nike faɗa. 

 

Rigar da aka aje kusa da ni marar nauyi na ɗauka, sai da na tabbatar da babu me kallona sannan na shiga warware ƙaton towel ɗin da aka kawomin wai in ɗaura idan zan shiga wanka, a jikin ƙaton madubin da ke shaƙe da kayan kwalliya na kalla, ina sake ƙarewa surar jikina kallo ta cikin gashin, wani irin daɗi ne da sanyi ne ya baibaye ni domin kuwa ni kaina nasan Allah yayimin baiwar tsarin zubin hallitta me ɗaukar hankali, sai na ji zuciyata na min wasu saƙe-saƙe aiko nai saurin yin A'uziyya tare da hanama kaina sake yarda da yin makamancin wannan tunanin, cikin sauri na zura rigar tare da  mulke jikina da lallausan losion wanda naga an jera, ban tsaya jiran komi ba na ɗauki veil ɗin rigar na ɗaure kaina da shi, sai na kawo hijabina na saka, kallon kaina nai a madubi sai naga na yi wani irin kyau na musamman wanda zan rantse ban taɓa yin irinshi ba, tunawa da wannan matar wacce na ji sun kira da Mommy ta ce inyi sauri ta na jirana, ya saka nai hanzarin juyawa dan infita, sai de kuma na mance inda ƙofar ta ke, duk inda na taɓa sai inga ashe ba ƙofar ba ne, tashin hankali ne ya baibaye ganin ƙofa ta ɓacewa ganina, da ƙyar na rarrashi kaina banyi kuka ba, amma kuma daf ni ke da rafka ihu ko za'a samu  wanda zai kawo min ɗauki idan ya jiyo ni. 

 

    Ƙarar buɗe abu na ji, cikin sauri na ɗaga kaina dan ganin minene, sai na sauke udanuwa akan wacce na ji an kira da Sulaima, ajiyar zuciya na saki ina godiya ga Allah da ya kawo min ɗauki. 

 

Guntun murmushi ta sakarmin tare da ƙarasowa inda nike ta na min magana da turanci, aiko gaba na sake tsallen bugu, dan harga Allah nasan ina jin turanci amma da na ji yanda ta ke nata turancin cike da kwarewa da iyayi sai na kasa fahimtar mi ta ke nufi. 

 

 

    "Oh sorry, Mubeenah ko! dama Mommy ce ta ce ki zo muje idan kin ƙarasa, tun ɗazu muke jiranki amma shiru baki fito ba." 

 

Zurum na miƙe tsaye ba tare da na yi magana ba, dan sai na tsinci kaina cikin tsoron buɗe baki inyi magana kar inyi ba daidaiba in kwafsa. 

 

Ganin na miƙe tsaye ya saka ta ɗauke kai daga kallona da ta ke, a ranta ta ke yabawa da irin kyawun da Allah yai min, sai de rashin gyara da ƙarancin wayewa ya disashe ƙyalin kyawun nawa, amma duk da haka kallon farko za'a sakani a cikin jerin kyawawa. 

 

Bin bayanta ni ke kaina a ƙasa har muka isa wani ɗan ƙaramin parlou wanda babu komi a cikinsa saga na'urar Ac sai ƙaramin fridge me kyau da tsari sai kujeru masu taushi. ganinmu ya saka Mommy da Hajjo miƙewa tsaye, bayan mun ƙarasa na zame na sake gaidasu ta hanyar yin jimla. 

  Bayan sun amsa Hajjo ta matso kusa da ni tare da kama hanuna ta na faɗin. 

 

    "Mu je jikata yarinyar kirki, Allah ya albarkaci rayuwarki ya haskaka ki da saiken alkairi." 

Amsawa na yi a cikin zuciyata ina yaba karamci irin na waɗanan mutanen. 

 

Mommy ce gaba sai ni da Hajjo da Sulaima a bayanta, sai da tai ɗan jimmm sannan ta tura ƙofar glashin tare sa Bisimilla ta tura kanta ciki, haka Sulaima  ta rufa ma ta baya, yayinda Hajjo ta tura kanta tare da janyo hanuna nima na shiga. 

 

Wa ni irin mummunan bugu ƙirjina yau, wanda saura taƙi ɗaya rak ya ragewa zuciyata ta wuntsilo ta maƙogarona zuwa waje, ban san lokacin da na duƙe a wajenba na shiga maida numfashi da tsananin sauri, hannunawa dafe da ƙirjina, dokawar da zuciyata ke yi na barazanar toshe magudanar numfashina, yayin da wa ta iriyar zufa tare da sanyi suka lulluɓe ni lokaci guda, juyowar Mommy da duƙowar Hajjo a kaina ta na jijjigani ya yi daidai ta isowar Pahpah wajen, cikin hanzari ya matso kusa da ni fuskarshi na bayyanar da annuri gami da tausayina a lokaci ɗaya, kafin kowa ya samu damar cewa komi Pahpah ya duƙa tare da kamo hannuwana ya miƙar da ni tsaye, sai da ya tabbatar da na samu nutsuwa sannan cikin taushin murya gami da rarrashi ya ke faɗin. 

 

   "Ki nutsu! nutsu kinji mah doughter, ki tausayawa halin da ɗan uwanki musulmi, kuma wanda ke amsa suna miji a gareki yanzu ya ke ciki, ke kaɗaice za ki iya ceto rayuwarshi da taimakon ubangijinmu, na baki yardata 100% a karo na farko a cikin rayuwata da na yarda da wani mutum na daban har na yi marabada shi a cikin familynah." 

 

Duk da yanda ƙafafuwana ke rawa su na barazanar kayarda ni, amma sauraren kalaman da suka ci gaba da fitowa daga bakin Pahpah, wanda nike wa kallon mutum me daraja da karamci, sai na ji zuciyata na bani kwarin gwuiwa, hakan ya saka na shiga gyaɗa ma shi kai, ban san wane zaren ƙaddara bane ya janyo ni zuwa cikin waɗannan ahali masu karamci, ban san cewa amincewar da na yi ba zai zama mabuɗin buɗe ƙofofin ƙaddararon rayuwata, haka kawai nike ji a jikina daga yau kuma yanzu rayuwata ta sauya, sauyi sosai wanda ya banbanta da irin faɗi tashi da tarin ƙalubalen da na fuskanta a rayuwata. 

 

Cike da tausaya Pahpah ya janyo hannuna zuwa ainahin cikin ɗakin, wanda shigata cikinshi ya zaftare abubuwa da dama daga ratuwa da burukana, ɗakin da ya zama wajen da zan kafa tarihin wa ta rayuwa me cike da rikitattun al'amurra. 

 

Duk taƙo ɗaya da zanyi, ina aje ƙafata ne tare da bugawar zuciya me tsananin ƙarfi, sannan kuma ina jin wani irin ZAFI me kama da ZAFIN WUTA🔥🔥🔥  ya na fuskanto ni, a daidai lokacin da na sauke takona na ƙarshe, a lokacin ne zuciyata ta tsaya cak da bugawa, gangar jikina ta kafe akan ƙafafuwa, a sa'ilin da idanuwa suka sauka abin abin da ya nemi hargitsa duniyata a lokacinne kwanyata ta shiga maimaitomin tariyar mafarkan da suka addabe ni a cikin barci musamman kwanakinnan.....✍️ 

 

 

ALHAMDULILLAH🙏💃 YAU DAI ALLAH YA AMINCE NA KAMMALA FREE PAGE, YANZU ZAMU SHIGA AINAHIN CIKIN LABARIN BA TARE DA ƁATA LOKACI BA.