Introduction
by @reza12
[9/26, 10:17 AM] S Reza: *_TSINUWAR UWA_*
_By S Reza_
*GARGAƊI⚠️* _Kuskure ne yin amfani da wani bangare daga cikin wannan littafin ba tare da izini ba. Ban yarda wani ya sauya ko abu ɗaya daga cikin saba. Haka zaluka idan na kama wani/wata ya ɗora min littafi a YouTube channel ba tare da izini ba zan ɗauki mummunan mataki a kansa wanda ba zai masa daɗi ba🙏_-
*TAMBAYA DAGA MAI RUBUTU ⁉️* Shin wai me yake kawo yin tsinuwa? Yaya ma ake yin tsinuwar? Laifin ƴaƴa ne ko laifin iyaye ne? Shin ma wai da gaske ne ana yin tsinuwar? To idan anyi me ke biyo bayan yin tsinuwar? Shin da gaske tsinuwa na kama wanda akaiwa tun anan gidan duniya ko sai an je lahira? To shi wanda yayi tsinuwar yana wanyewa lafiya ko dai shi ba shi da laifin komai? Shin kun taɓa ganin rayuwar wanda iyayen sa suka tsine masa? Idan kun taɓa gani to yaya rayuwar take? Yana yin nasara a rayuwarsa ko dai taɓewa yake yi? Mu buɗe kunuwa mu ɗauki darasi mai muhimmanci a wannan tafiyar, Kuzo mu shiga cikin wannan littafin na TSINUWAR UWA wanda nai masa taken DAMA TA UKU, domin jin amsoshin duk waɗannan tambayoyin. Bada ɓata lokaci ba duk kanku zai buɗe in sha Allah.