Page 8
by @reza12
Sosai gabanta ke faɗuwa kana ƙara kallon ikon Allah, azuciyarta tana cika da mamakin wai Jamila da jamilu ne ke aikata wannan ɗan yen aikin, ganin basu ganta bane yasa ta sake leƙawa, ta ja musu kofar ta koma da baya har zuwa cikin ɗakin Aida tana jin wani irin tsoro a ranta. Waya ta ɗauko ta kira number Aida tana ɗagawa Aida ta ce "Yauwa yanzu nake son na kira ki, ki duba Email ɗinki zakiga sako, sannan maganar aikin Baby and me ya taso, yanzu haka maganar muka gama yi da Oga Fita, kuma an yanke shawarar Fita zai zo gidanku domin yayi magana da iyayenki, ya sanar da su gaskiyar magana, domin sanadin abun da ya faru yana son kawo matsala a aikin da za'ayi, yanzu haka mutane sai ƙara rura wutar abun suke yi. Cikin wata irin murya ta ce "Aida ina cikin gidan ki kizo yanzu". Aida cike da mamaki ta ce "Wani gida kuma ba nace miki karki fito yanzu ba, Kinsan ilar take tattare da fitowar taki kuwa, mai yasa ba kya da tunani ne wani lokaci, sosai Aida ta rikice har tana masifa, ita dai Siyama tasan za'ayi haka. Siyama ta katse ta da faɗin "Na riga na fito kawai kizo. Cikin mamaki Aida ke tambayarta lafiya kuwa take ya taji muryarta haka. Siyama dai ta katse wayar tana tunanin abun yi, shin ta sanar wa da Aida ne ko dai ta bari babu ruwanta, ko kuma ta samu Jamila da jamilu ɗin tayi musu faɗa da nasiha, sosai take ta sake-saƙe har taji ana sallama. Amsawa tayi tana bada izinin a shigo. Jamila ce ta shigo tana ganin Siyama ta tsuguna har ƙasa tana gai da ta. Siyama ta amsa tana binta da kallo. Ta ce "Na shigo gidan ban ga kowa ba, kuma ga gidan a buɗe, shine nace bari nazo na huta kafin ku dawo. Jamila tace "Eh anty Aida bata dade da fita ba, shi kuma Jamilu baya jin dad'i ne, yana kwance shine naje kula da shi har barci ya ɗauke ne. Tun da ta fara magana Siyama ke ta kallon bakin ta, tana jin abun da take faɗa, a zuciyarta tana mamakin ashe dai yarinyar ta iya magana har haka. A fili kuwa ta ɗanyi alamar tausayi ta ce "Aiya to Allah ya bashi lafiya amma ai asibiti ya kamata kuje ko? Ta ce "Kawai fa ciwon ne kuma na ɗan lokaci ne, wani lokaci yana masa haka dama. Siyama dai ta amsa da to Allah ya sawaƙe. Haka Ta bar ɗakin bata jima ba sai gata da abun sha harda soyayyen nama da cincin. Siyama ta ce "Nagode. Har Jamila ta juya zata fita Siyama ta ce "Am Jamila minti ɗaya mana please? Jamila ta dawo ta zauna ba tare da tayi magana ba. Siyama ta kalleta sosai ganin ko Fati bata kai ba, sosai take tunanin anya kuwa wannan uwa ɗaya uba ɗaya suke da Jamilu da kuma Aida ɗin kuwa! Ita sai yanzu ma ta tsaya ta ƙarewa yarinyar kallo, gata dai masha Allah amma ta ɓata rayuwar ta. Siyama ta ce "Idan akwai kuɗi a gurin ki, please kije waje a kwai mai mashin da ya kawo ni, to ban fito da kuɗi ba kuma yana jira na. Da sauri ta miƙe tayi waje Siyama tabi bayan ta da kallo. Gashi dai bayan nata ma ba wani girma suka yi ba, domin irin dogwayen yaran nan ne, marasa jiki. Ajiyar zuciya ta sauke ta ɗauki nama ɗaya ta kai bakin ta. Lokaci ɗaya kuma abun da tazo yi ya dawo mata. Waya ta ɗauko ta buɗe data, sai ga sako daga email. Tana budewa taga daga campanin Baby and me ne, nan take ta shiga karantawa. Bayani ne akan sun shirya zasu fara aiki da ita, kuma ranar Laraba mai zuwa, kuma aikin na kwana uku ne, kwana ɗaya a kamfanin su dake Lagos, kwana biyun kuma duk a Maroco zasu yi, sosai take mamaki. A fili tace "Lallai baku da hankali wacce Siyama ce zata tafi har wani guri har kwana uku. Take taja wani gajeren tsaki tana ci gaba da kallon dokokin aikin nasu da suka turo mata, ita sosai take mamaki wai dama haka aikin Model ɗin yake ne. Ita fa a tunaninta kawai zaka je kamfane kayi musu hoton kayan da suke sai dawa sai kawai a sallame kane, amma shine harda kwana. Tana cikin haka taji sallamar Jamila ta ce mata "Anty yana ta zagi da kyar ya karɓi kuɗin ma fa" Siyama ta ce "Ai dole yayi faɗa yafa dade a gurin. Jamila dai bata ƙara cewa komai ba. Ganin haka yasa Siyama cewa "Dama kin ƙara masa kuɗi akan wanda yace ko? Ta girgiza kai! Siyama tace tom nawa kika basa tace "Yace wai ɗari huɗu shine na basa dubu daya ya bani ɗari biyar wai ɗari ladan jira. Ta faɗa tana miƙa mata canjin ɗari biyar ɗin. Siyama tace "Ai da kin bar masa gaba ɗaya kawai, to yanzu ai wannan naki ne ba nawa ba, sannan kina da account? Ta ɗaga kai. Siyama tace to bani sai na dawo miki da kuɗin ki harda kyautar da nayi niyar yi miki ko?
Jamila ta girgiza kai ta ce "Wannan ma ai kuɗin ki ne, Anty Aida tace naki ne, shine yasa na baki chanji ɗin. Siyama da ta gano nufinta sai tayi murmushi tace "To kije na bar miki, kuma ki bani account ɗin naki kinji. Haka Jamila ta bata account ta tura mata dubu hamsin, tayi godiya ta bar cikin ɗakin. Sai a lokacin Siyama ta kalli uban kukadeden dake cikin account ɗinta. Ita fa sai ma yanzu ta tuna da cewar tun da aka fara wannan abun babu wanda ta bawa ko sisi, ita kanta bata samu natsuwar ci ba, kamata yayi ta fara siye bakin mutane da kuɗi, domin dai a kwai su, kuma sun fara zuwa ma kenan, domin ko ɗazu kuɗin da Baby and me suka rubuta na fement ɗin ranar ma kawai masu yawa ne. Da sallama Aida ta turo ƙofar ɗakin ta shigo hannunta rike da leda fara mai dan girma, sai Jamila da jamilu biye a bayanta kowa da reƙe da leda. Jamilu ya gaida Siyama sannan suka ajiye kayan suka fita. Aida cikin kulawa ta ce "Me ya faru naji muryarki alamar damuwa? Siyama dai sai bin Aida da kallo take bata ce komai ba har ta fara tsarguwa. Ta ce "Wai lafiya kuwa meye a jikin nawa? Ta faɗa tana bin jikinta da kallo. Siyama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Babu komai, ina so ne kawai na haɗu da wannan tsohon banzan Olusha, wallahi sai ya faɗa min a gidan oban waye mukayi haka da shi. Aida ta ce "Matsala ta dake kenan wallahi rashin nazari, ke yanzu idan aka ganki a gurin wannan mutumin me kike tunani zai faru, za'a ce kinje neman yafiya ko kinje ki masa wani abun. Kinga dan Allah bama wannan ba, yanzu wani kokari kikayi ta bangaren ki, yanzu fa kusan kwana goma fa. Bama wannan ba, kin duba sakon aikin naku ko? Kuma kinga lokaci kaɗan suka bayar hakan yasa Oga Fita ya yanke shawarar zuwa ya samu iyayanki da Umma. Domin nasan dai ke babu abun da kikayi. Siyama ta ce "Karki damu babu wanda zai zo gidanmu, nasan abun yi. Amma kuma Aida wannan aikin nasu kinji fa wai harda kwana, kuma harda barin ƙasa fa? Aida tayi dariya ta ce "To ke da meyi nufin ki, to ai ke dan ma a iya Afirka kika tsaya ne, bari ki fara aga aikin ki yayi kyau kigani har Jamani da Chaina da Faransa da Ingila za'a kiraki, yanzu Kinsan Adawiya ma tana Ingila kuwa? Siyama ta waro ido ta ce "Ingila dai? Aida tayi dariya tace "In sha Allah Siyama sai kin zama Model ɗin duniya ba iya Afirka ba. Siyama dai tayi shiru tana hango kanta tare da manyan Model irin su Razina da Alexander da Laila da kuma Oluwalu da kuma wanda take gani a matsayin madubi ko kuma tace yawan kallon aikinsa yasa ta fara sha'awar aikin Model, wanda take bin sa a duk wani kafa sadarwa da take yi Wato Adam Rezor. Sosai ta shiga tunanin Allah yasa watarana aiki ya haɗa ta da shi domin kuwa ita fan ɗin sa ce. Aida ta ce "Yanzu ga shawara? Kibi duk wani dankinki mai faɗa aji ki musu kyautar yanke talauci akan su zo su samu Umma su sanar da ita cewar Sana'ar Model sana'a ce kamar kowacce, kuma musulmai da Yahudawa da Kirista duk suna yi, kice su shawo kanta har ta yarda. Sosai Siyama tayi na'am da wannan shawarar haka ta kama hanyar gida tana tunanin rashin fadawa Aida halinda taga Jamila da jamilu a ciki, wata zuciyar kuma ta ce "To idan kuma ta sani fa! Daidai ta kusa fita Aida ta tsayar da ita tana zuwa ta ce "Kinga dan Allah maganar tafiya a ƙafa da wani boye-ɓoye duk ya ƙare yanzu. Acikin mutocinki wallahi sai kin ɗauki ɗaya kinje da ita gida. Wai ke an faɗa miki matsoraci na zama gwani ne, wa ya ce miki a haka zaki zama wata aba, kamata yayi ace izuwa yanzu sai abun da kika faɗa a gidan ku, amma kin tsaya kina tsoro. Siyama tayi murmushi tana jin wani ƙwarin gwuiwa amma gefe ɗaya tana cewa Aida baki san wacce Umma bane wallahi. Suna tsaye sai ga Jamila da jamilu sun fito da ledojin ɗazu sun bode wata arniyar mota sun zuba kayan a ciki. Aida ta ce "Waccer zaki ɗauka itace daidai ke. Siyama dai sai taji anya zata iya kuwa. Haka Aida tai mata dole har ta dauki motar ta fita da ita. Haka tana tafiya tana ƙara sakawa kanta ƙwarin gwuiwa, lokacin da ta shigo unguwar su ta New ariya dake Abuja, kasancewar unguwar dama ta yaku bayi ce, yasa duk inda ta wuce sai an ƙara kallonta, sosai ta dake tana kallon gabanta. Daidai tazo ta saitin gidan su Ibrahim zata wuce shi kuma ya fito, kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kai, shi kuma ya kafe ta da ido ganin ita ne yasa ya biyo bayanta da gudu. Ganin yana Binta yasa ta ƙara gudu hakan yasa mutane keta kauce mata, wasu na zagi wasu na Allah ya sawaƙe. Tana zuwa kofar gidan su ta sauƙa da kanta ta buɗe gidan kasancewar akwai gurin ajiye mota zai iya ɗaukar motoci uku, yasa ta shiga da motar, tana fitowa da niyar shiga gida sai taga Ibrahim yana haki na gudun da yayi. "Bani hanya na wuce? Ta faɗa tana harararsa. Ya ce "Siyama kashe ni kike son yi ne? Tsaya kiji abun da zance miki please? Lokaci ɗaya Siyama ta saki murmushi tunowa da tayi da shawarar ta ta ɗazu. Ta ce "Ina jinka" ya ce "Siyama dan Allah idan wasa kike min wallahi na horu haka, mutuwa kawai ya rage ban yi ba, wallahi ban san cewar san da nake miki har ya kai haka ba sai da kika fara min wannan wasan, dan Allah a tsayar da wasan haka, wallahi nayi alƙawarin idan har muka dawo kamar da zan zama miki duk abun da kike so. Kallonsa kawai take tana tunanin wai ita maima ya kaita fara wannan abun da wannan wawan ne. Ta ce "Yanzu da na baka miliyan biyar da mota da kuma na yarda na dawo soyayya da kai wanne ka tsaɓa? Lokaci ɗaya ya miƙe tsaye ya ce "Wallahi Siyama ke nake so ba kuɗin kiba, na zaɓeki, bana son komai naki sai ke ɗin. Lokaci ɗaya Siyama ta waro ido waje tace "Kai lallai na yarda kai wawa ne kuma dolo kamar yadda ake faɗa. To ni wallahi ko dubu biyar nafi so a kanka kaji ma da kyau kenan. Ta ce "Zan baka miliyan goma da mota kaima kaje ka gina kanka amma dan Allah ka barni nayi rayuwata please. Ibrahim ya ce "Wallahi Siyama ko duk abun da kika mallaka zaki bani akan na daina sonki ba zan iya ba, ni Ke ɗin nake so, kuma domin Allah nake sonki. Lokaci ɗaya Siyama ta zuba masa ido, sai kuma wani tunani ya ɗauketa na minti biyu, ta shiga tunanin ko dai wannan shine soyayyar gaskiya da ake cewa, ko dai ta yarda da shine in yaso ta gina shi sai kawai ta auresa ta dinga juyashi kamar ita ce matar, to ai kuma bata son sa, ina zata kai son mutumin da ta gama narkewa a cikin sa, duk da bai san tana yi ba, to amma idan ta yarda ta auri Ibrahim bata muzanta ba. Kuwa, kaman ita ta auri wawa. Lokaci ɗaya ta dawo tunaninta ta ce "Kai wawa ne, kaje gida ko ka samu abokinka kayi shawara da shi, ko kaje ka samu wannan tsohuwar kakar taka kayi shawara da ita, idan ka gama ina jiranka, domin dai na fahimci kai baka san me kake yi ba har yanzu. Tana faɗa ta kama hanyar gida ta barsa tsaye yana kallonta. Tana shiga cikin palon taga Umma da da Nasiru da Yaya Bala suna zaune sai Fati da take cin abinci.
****** *YAYA BALA* Lokaci da suka je ɗakin Siyama sai suka tarar bata nan hakan ya ƙara ɓata ran Umma sosai, ta shiga faɗin "Yanzu shi kenan Siyama tafi ƙarfinmu ko Bala, muna gidan nan da ita sai ta saka ƙafa ta fita nata gurin babu wanda ya sani ko, to wallahi na gaji ba zan iya ba, ka kira min ita yanzu duk inda take tazo gida ina son ganin ta. Sosai Umma tayi faɗa Yaya Bala dai sukai mata shiru domin shima harda shi take haɗawa. Haka Umma ta dawo Palo tana jiran a kira mata Siyama. Yaya Bala ya kalli Nasiru ya ce "Ɗauko wayarka ka kira ta" Nasiru ya shiga ɗaki da niyyar ɗaukar wayar, koda ya ɗauko baida kati a ciki, hakan yasa Yaya Bala yace a barta ai zata dawo duk ma inda taje. Yaya Bala ya kalli Umma cikin kwantar da murya ya ce "Umma magana nake so muyi akan karatun Nasiru da Siyama. Umma ta juyo ta kallesa har yanzu ranta a ɓace yake. Ta ce "Ita Siyama yanzu wani karatu kuma ya rage mata, yarinyar da tafi ƙarfin iyayenta, yarinyar da take da gaban kanta, kuma yanzu maganar aure zaka yi kawai ba karatu ba, ina so ka samu shi yaron da take tsayuwa da shi ya ruro idan da gaske yake kawai ayi mata aure mu huta, domin ni na gaji da wannan halin nata. Yaya Bala ya sauke ajiyar zuciya ya ce "To Umma shi kuma Nasiru fa, kinga yanzu suna shekarar karshe ne, kuma har yanzu hannunsa bai warke ba, gashi yanzu maganar kuɗi ne, bamu biya kudin jarabawar ba har yanzu kuma gashi ciwon nasa sai an ƙara komawa asibiti, ni dai nawa Alhamdu Lillah, shima sabo da yana da ƙanjiki ne ciwo ko yaya yake a jiki sai yaƙi warkewa. Umma tayi shiru tana tunanin lokacin da mahaifin su wato Al-Hasan shima haka yake da ƙanjiki koyaya yaji ciwo to ya fara ƙaruwa kenan ko yaƙi warkewa, sai sun sha fama sosai. Tabbas shi Nasiru da Siyama suka gado, itama haka ciwo yake mata ya bata wahala sosai. Umma ta kalli Yaya Bala ta ce "To ko shi Nasiru zai bar karatun ne har bayan shekara idan ya warke, kaga sai muji da kuɗin maganin ko? Domin kaga yanzu idan ba hakan a kayi ba zamu shiga cikin matsala. Yaya Bala ya ce "A'a fa Umma yanzu maganar barin karatu har sai wata shekarar ba dabara bace, domin idan shekarar ta dawo sai mun biya komai da muka biya a baya, kuma shi kansa ba zai ji daɗin karatun ba. Umma tayi shiru cen ta ce "To ko zaka je gurin masu gidan naku su bada kuɗin hayar wannan shekarar ne idan yaso kaga ko shekarar ta ƙare sun biya kenan ko? Yaya Bala yayi murmushi ya ce "Umma ko wata biyar bai yi bafa da suka bamu na waccer shekarar, kuma shima da yaya suka haɗa mana, yanzu kuwa muna zuwa zasu ce ai shekarar bata yi ba, kawai dai Umma bari na kira shi Nasiru ɗin muji ta bakin sa. Daga nan yaya Bala ya shiga kiran Nasiru sai gashi ya fito rike da waya a hannu, hannun ciwon nasa ya kumbura sosai babu ko kyawun gani. Bayan ya zauna Umma tace ya tashi ya kira mata Fati. Bayan sun zauna ta mayar musu da duk yanda sukayi, Nasiru ya ɗago da sauri jin abun da ake ciki. Ya ce "Yaya shekara mai zuwa fa cikin jiniyoyina fa zan shiga duk abokaina lokacin sun tafi sun barni, gaskiya Yaya a'a ba zan iya jira har wata shekara ba. Umma ta ce "To da wani hannun zaka yi karatun da rubutun ana magana kana faɗin ba zaka iya ba kamar wani karamin yaro, ko baka fahimci matsalar da ake ciki bane, duk akan maganar kuɗi ne, yanzu ma asibiti za'a koma a kan wannan hannun naka amma kazo kana abu kamar karamin yaro. Nasiru dai ya cuno baki ya shiga haɗa rai. Fati dai tayi shiru tana sauraronsu. Bayan kamar minti biyu Umma ta ce "To ko za'a saka wancen gidan a kasuwa ne, idan yaso sauran kudin sai ka fara wani kasuwancin da shi, tunda kaga aikinku ba kullum ake samu ba ko? Da sauri Yaya Bala ya ce "No a'a Umma ba zamu sayar da abun da muka mallaka na gado ba. Ya ce "Umma idan muka sayar da gidan zamu zo muyi da na sani, domin gidan Nasiru nake so idan Allah ya kai mu lokacin auransa sai kawai a gyara ya shiga. Cikin faɗa Umma ta ce "To Allah zai hore muku in sha Allah kafin lokacin ku siya wani, yanzu yaya kake so ayi, wannan dai gida naku ne, bayan shi baku da wani abu da za'a sayar asamu lafiya da kuma ci gaban karatun ku, to yanzu ni dai na gama magana aje a sayar Allah zai hore, lokacin da ka sayi wannan gidan kasan zaka samu kuɗin ne, Allah ne yaso kuma ya nufa har ka siya, sabo da haka ku dinga kyautata zato mai kyau ga ubangijinku shine ke yi a lokacin da babu mai baka. Sosai Umma ta shiga faɗa cikin na nasiha hardai suka yarda akan za'a sayar. Bayan an amince ne yaya Bala ya ce "To Umma yanzu mu sanarwa da Kawu Inuwa da Baba (wato Husaini ƙanin mahaifinsu shi suke cewa Baba) Umma ta ce "Eh ai dole zasu sani. Fati dai tuni ta tashi ta shiga cikin gurin Binta da ta bari tana ƙarasa abincin nasu, ganin bata gama bane yasa ta ɗauki kwano ta ɗebo kaɗan domin yunwa take ji. Haka ta fito palon ta zauna Umma ta bita da kallo domin kuwa tasan ba'a gama ba ta ɗebo. Umma ta sake cewa da Yaya Bala "Yanzu wacce sana'ar kake ganin zaka fara ? Kafin yayi magana suka ga an turo ƙofar an shigo, gaba ɗaya suka mai da kallonsu ga ƙofar. Siyama ce riƙe da kin mota a hannu. Itama kallonsu take, ganin yadda suka haɗu family amma babu ita a ciki sannan babu Anty Zainab. Sallama tayi tana kallon hannun yaya Nasiru da yayi wani irin kumburi wanda bata taɓa kula ba. Kusa da shi taje ta zauna tana ta kallon hannun. Umma dai tun kallo ɗaya bata ƙara bi ta kanta ba. Yaya Bala a karon farko da zai yi magana da ita kenan tun da abun ya faru. Ya ce "Daga ina kike? Wa kika fadawa zaki fita? Kamar daga sama taji tambayoyin nasa domin sai yanzu ya shiga sha'anin ta tun da komai ya baiyana. Sai da ta tabbatar da ta haɗa maganar a bakin ta tsabar rudewa kafin ta iya cewa "Dama da dama dama naje gurin mutumin da yayi min Sherri ne ku... "Wani tsawa da Umma ta daka mata ne yasa ta bata san lokacin da ta zamo ƙasa ba. Sosai ran Umma ya ɓaci jin tana neman raina musu wayo wai yayi mata Sherri. Ta ce "Da baki je kin sanar da shi komai ba yaya za'ayi ya sani, idan baki fito kin faɗi gaskiyar inda kika je ba, Allah zan shayar dake ruwan mamaki, kuma daga nan zaki haɗa kayan ki ki koma gurin shi arnen uban naki. Umma ta faɗa tana miƙewa tsaye domin Umma nada zafi sosai, abu kaɗan ke ɓata mata rai. Yaya Bala da shima saida ya tsorata da irin wannan tsawar da Umma tayi ya ce "Wannan makullin motar ta waye? Siyama da ta gama tsorata ta ce "Mota ta ce" kallon-kallo aka fara yi a palon. Ya ce "Waye ya baki? Sai a lokacin Siyama ta ɗago ta kalli Umma ganin ita take kallo sai tayi saurin yin ƙasa da kai, sosai take son aro jarunta tasa a kanta amma da ta haɗa ido da Umma sai ta kasa, tabbas tsoron da Umma ta saka musu nata tun suna yara yayi tasiri akan Siyama, domin duk yadda takai da son yin magana mai ma'ana da ta kalli Umma sai komai ya kwance mata. Sosai Umma ta daure bata sharara mata mari ba jin ana tambayarta ta yi shiru.
Yaya Bala ya ƙara maimaita tambayar ta ce "Tawa ce da na samu bayan nazo ta biyu" Sosai yanzu harda Yaya Bala ɗin suke mamaki. Ita dai Umma bata fahimta ba, haka kawai sai a bata mota dan tazo ta biyu dole akwai dai wani bayanin. A lokacin wayar Siyama ta shiga ƙara ta duba taga Aida sai ta kalli Umma da Itama ita take kallo suna haɗa ido ta kawar da nata. Yaya Bala yace ki ɗaga mana. Kafin ta ɗaga kiran ya katse. Nan sai ga wani kiran. Tana ɗagawa Aida ta ce "Ke a kwai matsala fa, babu yadda banyi da Oga Fita ba amma yace Wallahi sai na kawo su gidan ku, wai masu aikin ne suka matsa sosai, shi kuma baya so ki rasa aikin yanzu haka gamu a hanya, domin kina fita yazo Allah ne ma yayi ba zaku haɗu ba. Siyama ta gama shiga ruɗu ta ce "No dan Allah karki kawo shi please " Aida kuwa ta miƙawa Oga Fita waya shi kuwa ya ce "Naga ke ɗin ce har yanzu baki yi serus bane, kawai yau ayi komai. Yana faɗa ya ka she wayar. Lokaci ɗaya hawaye suka zubowa Siyama. Yaya Bala ya riga Umma yin magana ya ce "Su waye zasu zo?" Ba tare da ta kalli kowa ba ta ce "Oganmu ne zaizo yayi muku bayani domin ni bazaku yarda da niba. Umma dai sai kawai taji Siyama ɗin ta bata tausayi ganin tana hawaye. Binta ce ta fito daga kicin tana faɗin an gama abinci a kawo yanzu ne? Yaya Bala ya ce "Bari tukunna baƙi zasu zo yanzu sai kawai a kawo idan sun zo. Yaya Bala ya dawo da kallon sa izuwa ga Siyama ya ce "Kenan shine yasaka ki a wannan abun shi ogan naki?* Lokaci ɗaya Siyama ta tuno da wanda yasa mata kwadayin abun, sai kawai taji wani irin ƙwarin gwuiwa yazo mata ta ce "Babu wanda ya saka ni, kawai ina son abun ne tun ba yanzu ba. Ta faɗa a dake. Binta dai sai bin Siyama da kallo take, sannan a karo na farko da take wa Yaya Bala kallon ƙurulla tun bayan da Momy (wato mahaifiyarta) ta ɗarsa mata a kan cewar ta dinga manne masa komai tai masa ko Allah zai sa ta maye gurbin matarsa Zainab. Farko Binta taji tsaro domin bata taba harsaso haka a ranta ba, kuma tana ganin yayi mata girma, mai zai hana ace Nasiru amma Yaya Bala ina zata kai shi. Sai da Momy tai mata dogon bayani sosai kamar yadda itama akai mata akan cewar ai yanzu Siyama zata fara samun kuɗi na bam mamaki domin yanzu ta zama salebiriti. Hakan yasa take so aci kuɗin da ƴarta. Sosai Binta ta yarda Duk da bata jin sonsa ko na ɗugo ɗaya. Yaya Bala ya ce "Siyama shekarar ki nawa? Kin gama karatu? Mai muka rageki dashi da har kika zaɓi wannan aikin na zubar da mutunci? Siyama ta ce "Yaya wallahi babu abun da kuka rageni da shi, kuma banyi komai ba sai sabo da ku, duk abun da nake yi sabo da kune wallahi yaya. Yanzu haka na mallaki abubuwa da dama harda motoci da kuɗaɗen da ban san a dadin su ba, kuma yanzu haka na samu wani aiki shine nake tsoron tambayar ku, dan Allah karku hana ni, wallahi zan kula da kaina nasan me nake yi, please dan Allah yaya, kuma wannan maganar da tsohon nan yayi duk ƙaryace wasu maƙiyan nawa ne suka haɗa baki dashi domin aci mani mutunci amma zan gano koma su waye, kuma zaku gani please Umma. Ba Nasiru da Fati da Binta ba, har Umma da Yaya Bala saida suka shiga mamaki. Lokaci ɗaya Nasiru ya tashi daga ƙasa ya zauna a ransa yana jin ya samu mota. Ita kuwa Binta gaba ɗaya ma ruɗewa taso yi, domin kaɗan ya rage ta nuna kanta a gurin. Yaya Bala ma dai jin abun da take cewa yasa ya kalli Umma. Umma ce ta fara buɗe baki zata yi magana suka ji anyi sallama. Amsawa akayi kafin Aida ta shigo, sai Oga Fita sai wani mutumi sanye da bakaken kaya. Guri aka basu suka zauna aka shiga gaisawa. Fita baya jin Hausa shida baƙon nasu. Umma kuma bata jin turanci. Hakan yasa lokacin da suka gai data sai kawai ta ɗaga musu hannu. Yaya Bala yasa Binta da Fati suje su fito musu da abinci. Lokaci ɗaya Siyama ta tuno da Jamil da jamilu yanzu haka suna cen suna aikata iskancin su, kallon Aida tayi ganin tana ta sunne kai, lokaci ɗaya suka haɗa ido kowa na tausayin junan su da irin nufinsa. Yaya Bala yayi wa su fita tayin abinci. Suka sha abun sha suka ce a ƙoshe suke. Yaya Bala dai sai kallon Siyama yake akan tayi musu bayanin mutanen, kaman kuwa tasan abun da yake nufi ta fara jawabi.
Ta nuna Oga Fita tace "Wannan shine Oga Fita ogan mu. Ta nuna Aida ta ce "Wannan sunanta Aida abokiyar aiki nace, kuma ƙawata. Waccen kuma ban san sa ba. Ta nuna gurin da wannan mai baƙaƙen kayan yake. Umma sai kallo Aida take ganinta kyakkyawa da ita, a ranta tana faɗin Sai dai babu kyawun zuciya. Oga Fita ya fara maganar abun da ya kawo su. Ya fara basu labarin yadda akayi yasan Siyama da kuma lokacin da suka fara aiki tare, har dalilin da yasa suka ƙirƙiri iyayen ƙarya akan tana tsoron a gano cewar itace a gidan su domin tana tsoro sosai. Har dai lokacin da ta samu nasarar zuwa ta biyu da irin kyautar da ta samu da kuma aikin da ta samu na Model. Sannan ya warware musu gaskiyar magana akan abun da Olusha yayi cewar ƙarya ne. Yana yi Nasiru na fassarawa Umma. Bayan ya gama jawabin ne ya ɗora da faɗin abun da ya sani iya gaskiyar sa akan aikin Model..."Aikin Modelling aiki ne mai kyau wanda mutum zai tara kuɗi sosai, kuma mutum zai zama salebiriti a duniya, duk inda ka shiga za'a san ka. Kuma aikin kowa nayi muddin kana da jiki mai kyau. Saboda haka ina baku shawarar da kuyi hakuri kubar Siyama ta fara wannan aikin zakuyi alfahari da ita kuma zaku samu kuɗi. Fita ya nuna wannan mutumin ya ce "Wannan ɗaya daga cikin mutanen da zata yi aiki a campanin su ne, to suna ta damu na akan sai tazo an fara ni kuma na sanar da shi cewar ai tana da ɗan matsala da iyayenta ne, shine ya ce azo tare da shi yaji meye matsalar ku. Ya ƙarasa yana bawa mutumin damar yin magana. Mutun ya ɗaga musu hannu ya fara da faɗin "My name is Dele Ali I'm from England London, I'm the manager of the Baby and me Company for Nigeria and Marocco. Yaci gaba da faɗin...mun ga Siyama a taron kyau na nan ƙasa Nigeria kuma tayi kyau da irin kalar da muke so mu dora a fuskar tallan kayan mu, shine muka zo neman yarda ta da ta iyayen ta, zamu yi aiki da ita a duk inda muke da gurbin kamfani. Kuma mun dauki nauyin baku jari daga garemu, harda gida kyauta anan garin Abuja duk daga garemu. Sosai Nasiru yake aikin fassara, ita dai Umma sai saurara take har aka zo karshe. Binta kuma ta gama cika da mamakin jin irin abun Alkairin dake tunkaro wannan ahalin. Kafin kowa yayi magana Oga Fita ya ɗora da faɗin... "Yarinyar ku tana da hankali domin tasan me take yi, kar kuji komai a kanta ko ni na yarda da ita...📝
Love all One love Comments Ana shering Love my fan's By S-Reza writer [9/26, 10:17 AM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*
_By S-Reza✍️_