Tsinuwar uwa

Page 1️⃣1

by @reza12

Binta ta ce "Yaya dama karaya kayi ne? Ai ina ce targaɗe ne, kawo na gyara maka na iya" ta faɗa tana ruƙo hannun nasa. Yaya Bala kuwa sai yanzu ya tuna da cewar Mommy fa ta iya gyaran karaya da targaɗe to amma bai san ita Binta yau she ta koya ba. Ya ce "Tashi ki fita daga ɗakin nan yanzu?" Ta ce "Yaya ɗaurin da a kai maka ɗin ne bai yi ba ina zuwa ka gani, karka tashi kaji yanzu zan dawo" Tana faɗa tana miƙe wa da sauri ta bar ɗakin ta nufi ɗakin su, shi dai ya bita da kallo bai ce komai ba. Bata yi sallama ba ta shiga duba jakarta ta kwaso wasu kwalabai gudu uku ita dai Fati tana ta raka ta da ido. Haka ta koma ta same sa a gurin da ta barshi. Toilet ta shiga ta fara dube-dube sai ta ɗauko wata singlet ɗin sa ta ce "Yaya kana son wannan rigar? Ya kalli rigar da kyau ya ce "Meye kike yi haka a ina kika koyo gyaran karaya?" Ta ce "Yaya kenan kai dai tsaya ka ganewa idon ka. Sai ta shiga duba inda zata ga tsunma, ganin bata samu bane ta cire hular kanta shi dai ya bita da kallo yana ta mamaki. Gashin ta yake kallo ganin sa baki ƙirin kuma a wanke gashi babu laifi yana da tsayi kasancewar babu kitso akan, har wani ƙamshi ke fita daga cikin gashin, lokaci ɗaya ya tuno da Anty Zainab itama haka take da gashi har ma yafi wannan tsayi, sannan takan buɗe gashin kan nata idan suna su biyu, domin yana son mace mai gashi sosai kuma bai cika son yaga mace na yin kitso ba, yafi son ganin gashi a haka. Kallonsa ya kai gurin da hoton ta yake ita kaɗai sanye da doguwar riga ta saka glas ta riƙe gife da gefen glas ɗin da hannu biyu tana murmushi. Kallon gurin da yake kallo tayi sai ta sauke ajiyar zuciya a zuciya ta ce "Lallai a kwai Binta kina da aiki". Yana ta kallon hoton har ta jona ruwa ya ɗan yi zafi ƙadan, kafin ta cire ganin har lokacin yana kallon hoton harda hawaye ne, yasa ta tsoma hular tata a cikin ruwan ta ɗan matse kafin ta danna masa da ɗan karfi wanda yasa da sauri ya dawo da kallonsa gareta. Tayi ɗan murmushi ta ce "Yaya bari kaga aikin ƴar gado". Haka ta wanke masa jinin ta ɗan danddana hannun da ruwan zafi kafin ta ja masa hannun, ganin yadda yake yi ne ta ke yi da gaiyya amma ya dake, haka ta shafa masa wannan mayukan da ta ɗebo, sannan ta yi amfani da igiyar da ya ware ɗazu ta wanke ta ɗaure masa. Tana gamawa ta ce "In sha Allah sati ɗaya za'a warware ɗaurin. Ya ce "Idan kuwa kaka ɓata min hannu zan koya miki hankali, je ki kawo min abinci".Tayi dariya ta ce "Yaya bani da hankali dama?" Ya ce "Nace ki kawo min abinci ko? Ta ce "Ni dai Allah yaya ka daina ce min bani da hankali, to me nake yi na rashin hankali?" Ta faɗa harda bubbuga ƙafa a ƙasa ita a dole zata yi shaƙwaɓa. Yaya Bala da mamaki yake kallonta har abun yaso basa dariya amma ya dake. A ransa yana mamakin Binta yana tunanin Allah yasa dai ba sonsa take ba, domin kwana biyu gaba daya ya lura da ita. Ya haɗe rai ya ce "Yau she na fara wasa da ke Binta? Kin raina ni ko? Ya faɗa yana tamke fuska. Ita kuwa Binta ta ƙara maraireciwa ta ce "To yaya haka kawai sai kace min mahaukaciya, yanzu fa na gama maka gyara ko na gode baka ce ba, kuma baka biya kuɗin gyara ba shine zaka ce min mahaukaciya. Yaya Bala tsabar mamaki bai san dariya ta kufce masa ba. Shi yaushe ya ce mata mahaukaciya. Ganin harda kukanta yasa ya ce "Ok tom naji ke ba mahaukaciya ba ce, kuma na gode sosai, sannan nawa ne kuɗin aikin. Jin haka yasa Binta sakin dariya da karfi harda riƙe ciki ta ce "Yaya kaga nasa kayi dariya, kuma kuɗin aiki na dubu goma ne amma ka ajiye min a gurinka ka tara min idan ciwon bai gyaru ba na sake gyarawa shima sai ka ajiye min har na tara da yawa. Tana faɗa ta bar ɗakin tana dariya. Waro ido yayi yana kallonta amma har ta bar ɗakin. Dariya yayi yana kallon hannunsa da har ya daina masa zugi sai wani sanyi yake masa da alamar man da ta shafa a gurin ne. Rabonsa da ya samu kansa a cikin farin ciki haka tun kafin rasuwar Anty Zainab. Kwantawa yayi yana jira ta kawo masa abincin.

**** *IBRAHIM* Lokacin da ya dawo daga aikin Hajja ta tare shi da zancen da Haladu yayi mata na karbar kuɗin da Siyama ta ce ya rubuto zata basa tayi masa. Amma Ibrahim ya ce shi sam ba dan kuɗi yake sonta ba, kuma duk abun da ya taɓa bata ya bata domin Allah da kuma son da yake mata ne. Shima ya shiga tambayar Hajja ɗin akan taje gidan su Siyama ɗin. Tsabar haushi da takaici yasa Hajja faɗin. "To bari kaji wallahi babu inda zanje, idan kuma kana son naje to sai kaje ka ƙarbo mana wannan kuɗin, haba Ibrahim kai idan baka buƙata ai mu muna da buƙata, yarinyar nan tace bata sonka to dole ne kayi hakuri kowa yaje yayi rayuwarsa mana. Ibrahim da baya son jin kalmar wai Siyama bata son sa kuwa wani irin ɓacin rai ne ke taso masa yana jin zai iya cewa komai ga Hajja idan ya tsaya sauraronta, hakan yasa ya barta a gurin tana cigaba da faɗa. Washegari kuwa sai ga Haladu yazo da takarda ya rubuto abubuwan da yaga sun dace, aka duba kuɗi totall nera dubu talatin da biyu harda ɗari biyu da ashirin. Hajja da kuwa bayan Nana ta sanar da ita yawan kuɗin ne yasa ta riƙe baki tana faɗin "Kuma gaba ɗaya zata bayar? Haladu ya ce "Ai Hajja wannan ma iya wanda na sani ne, ina so shima ya fadi sauran kinga ko dubu hamsin da wani abu aka kai ya ya isa yaja jari ya manta da ita. Haka suka runtuma zuwa ɗakin Ibrahim da yau yace bashi da lafiya ba zai je aiki ba. Kwance suka samesa yana kallon sama duk ya rame, domin tun da abun ya faru baya wani cin abinci da yawa. Zama Haladu yayi ya ce "Ta shi malam duba ka gani meye ban saka ba, harda tsiren da kake sintirin saya mata duk ran juma'a na ɗari uku-uku na saka kuma shima iya wanda na gani ne, ai kwara a ramawa kura aniyar ta, kai da nine kai wallahi har wanda ban bata Bama sai na saka. Haladu ya faɗa yana miƙa masa takardar. Ibrahim ya ce "Wai meye ne duk kunzo zaku dame ni, ni barci nake ji dan Allah ku fita min" Haladu ya tura masa takardar gabansa yana faɗin, kai ɗin banza nasha wahalar rubutun kace na fita. Dole ya mike ya amshi takardar yana dubawa. Ibrahim na gama kalla ya yaga ta yana sakin tsaki. Ya ce "Ni wallahi matsala ta dai kai Haladu kwaɗayi da shegen son kuɗi, kai a tunaninka kuɗi ko wani abu zai sa na rabu da Siyama ne, nifa wallahi sai dai ko mutuwa nayi, amma muddin an barni a raye to babu mai iya rabani da siyamata, kuma maganar kuɗi ni ba domin ta biyani nayi ba, siyama ba zata iya biyena abun da nayi mata ba har sai ta yarda zata aure ni. Hajja da ta gama ƙuluwa tace "Haladu ku rabu dashi ai bari ba shegiya bace da ubanta, yunwa da damuwa ba ƙannen ubansa babe, ta shi ka tafi sannunka da ƙoƙari kaji mun gode. Haka Haladu ya tafi yana mamakin anya kuwa abakinsa bai samu tabin hankali ba, duk da cewar dama kamar dai yana da ɗan matsala. Haka suka manta da shi har dare, ganin bai fito bane yasa Hajja ƙara leƙasa, ta ganshi zaune ya dafe kai. Ta karasa ciki taga yana kuka yasa waya a gaba alamar dai Siyama yake kira. Lokaci ɗaya Hajja ta tausaya masa, ta zauna tana lallashin sa, tasa Nana ta kawo masa abinci amma sam yaki ci, sai sunan Siyama yake kira, sosai fa Hajja da Nana suka tsorata, har dare yaki cin abinci, karshe ma ya fara amai yana tari. Da safe ta kira masa mai dan shagon gurin magani yayi masa allura bayan an bashi baƙin shayi ya sha. Shima a shagon Haladu aka karbo, ko kuɗin maganin ma shine ya dauki nauyin biya. Haka jikin nasa ya ƙara sauki har washe gari da ya tashi da wani irin ciwon zuciya wai shi dole sai yaga Siyama, gashi baya iya tafiya, kuma sai riƙe zuciya yake yi, hakan yasa Hajja ta zari hijjabi sai gidan su.

Lokacin da ta dawo daga gidan su Siyama da kuka ta shigo domin kuwa taga duk abun da yake faruwa a gaban ta. Yanzu kam ta tabbatar sai dai Ibrahim ya mutu idan a kan Siyama ɗin ne. Lokacin da ya ga Hajja na kuka sai ya ƙara ruɗewa yana tambayar meye ya samu Siyama ɗin, Bama meye ya samu Ita Hajja ɗin da taje gidan ba a'a shi dai siyamarsa. Sosai Hajja ke kuka tama rasa ta ina zata fara yi musa bayani. Nana ta ce "Hajja ko Siyama ɗin ta mutu ne?" Lokaci ɗaya Ibrahim ya miƙe zaune yana sakarwa Nana mari tass a bakinta! Ta riƙe bakin tana kallonsa shima ya na kallonta kowa yaƙi yin magana sai hannu ɗaya da ya riƙe zuciyar sa. Nana ta ja dogon tsaki ta tashi ta bar ɗakin tana faɗin "Allah yasa ma ta mutu mota ta take tsinanniyar kowa ya huta, ƴar banza mai girman kai" Ibrahim ya bita da kallo yana ƙara cigaba da tari yana kallon Hajja da take ta kuka, a ransa yana jin zai iya ɓalla Nana a gidan tabbas kuwa. Ya ce "Wai Hajja ba zaki min magana bane, kinzo kin sani a gaba sai kuka kike baki ce min komai ba, kina so sai zuciyata ta fashe ne kafin ki sanar dani. Itama cikin Irin ihun da yayi ta ce "Dan ubanka zuciyar taka ta fashe ko yanzu wawa mara hankali kawai kaje kana hauka akan yarinyar da bata ragawa kowa ba har iyayenta, wacce babu wanda ya isa da ita, to ni wallahi ma ko tace zata aure ka ba zan yarda ba, me za'ayi da irin marasa tarbiyya da rashin ganin girman iyayensa, yarinyar da a gabana uwarta na faɗa tana faɗa, to wallahi kamaji bada niba. Tana rufe baki Siyama ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin "Eh fadi ki ƙara tsohuwar muna fuka ashe gulma ya kai ki gidan namu.

Kwallon-kallo aka tsaya ana yi tsakanin Siyama da Hajja da IB. Da sauri ya miƙe tsaye yana kallonta kamar dai gizo take masa. Ganin kowa yayi shiru ne yasa Ibrahim ɗin faɗin "Siyamata kece da gaske ko dai gizo ne?" Ya faɗa yana ƙoƙarin kamo hannunta. Ita dai Hajja tayi mutuwar tsaye domin tsoro take ji, yanzu-yanzu ta gama da iyayenta ma bare ita, hakan yasa ta takure agefe ta kasa cewa komai. "Da sauri ta ture hannunsa tana faɗin "Kai wawa soko ɗan dolo-dolo, saurareni kaji, gargaɗi nazo nayi muku kai da wannan tsohon magulmaciyar taka. Ta faɗa tana nuna Hajja da hannu kamar zata tsokale mata ido. Taci gaba da faɗin... Na rantse da girman Allah idan baku fita daga sabgata ba zan sa a kulle wannan soloɓiyon jikan naki, kuma ƙullewar da bazaki sake ganinsa ba. Kai kuma ɗan dolo, ba kana yin abu kamar wawa ba, kana yi kamar baka da zuciya ba, to wallahi muddin ka ƙara nuna ka sanni na rantse sai na aikata abun da na faɗa maka. Daga yau ko nace daga yanzu idan na fita daga gidan nan to babu ni babu ku, karku ƙara nuna kun taɓa ganina, idan ma wani ya kiraku daga gidan mu kace kai yanzu ka daina sona, koma waye kana dai jina ko? Ta karasa tana daka masa tsawa kuma tana kama kunne alamar gargaɗi. Ibrahim da yaji ciwon zuciyar da ke damunsa ya tafi dalilin ganin Siyama ya ce "Siyama kome zaki min sai dai kiyi amma wallahi ba zan daina sonki ba, nima ba yin kaina bane laifin zuciyata ne, kuma zan cigaba da faɗa miki cewar ina sonki, kuma ba zan daina ba har sai kin aureni kamar yadda kika min alƙawari, dan Allah Siyamata abar wannan wasan na horu haka, baki san abun da nake ji bane, ni kaina wani lokaci sai nake jin inama zuciyata tamin adalci ta manta da ke, amma kullum sai ƙara sonki take yi. Siyama da ta gama zuwa ƙarshe da ɓacin rai ta ce "Kai dai anyi ɗan marasa zuciya wawa kawai, kai ni duk duniya a kwai wata halittar da zai ce baya sona amma na dage har haka ne dan uban mutum ko waye shi. Ibrahim ya ce "Nima ke ɗaya ce duk duniyar nan wallahi wacce zan iya mutuwa a kanta". Ya faɗa yana ƙara matsowa kusa da ita. Ita dai Hajja gaba ɗaya sai sauraronsu take, kamar tace da Ibrahim yayi shiru karta kashe su a cikin ɗakin domin taga a lamar zata iya. Siyama ta ce "Ni ɗin ƙanwar uwarka ce da bazaka iya rabuwa da Ni ba? Ibrahim da yake jin daɗin hirar da suke yi ya ce "Kinfi nan Siyama, wallahi kin wuce ƙanwar uwata a zuciyata, ni yanzu ki faɗa min abun da zan miki domin ki tabbatar da irin son da nake miki wallahi ko me kike so zanyi in dai akan ki ne. Ta ce "Wai kai mutum ne kuwa?" Ya ce "Mutum ne mana kamar ke Siyamata. Siyama kamar tayi kuka ta ce "So nake ka rabu dani, ka faɗa daga kan miliyan ashirin zuwa ƙasa fadi yadda kake so yanzu na baka ka manta da ni, domin naga kamar talauci ne duk ya cika maka ƙwaƙwalwa da baka san daidai da rashin ba. Ta faɗa tana bin dakin da wani irin kallon raini harda toshe hanci. Sai a lokacin Hajja tayi magana ta ce "kinga ajiye mana duk abun da kika yi niyya, na miki alƙawarin ba zai ƙara ko kallon hanyar da kike ba" Hajja ta faɗa a tsorace. Ko kallonta Siyama bata yi ba.

Siyama ta kalli Ibrahim tana jira yace wani abu. Sai ya ce "Ni Siyamata tafi ƙarfin kuɗi a gurina, idan har zan amshi kuɗi akan son da nake mata to na ci amanar so, kuma shugaban masoya zai yi fushi da ni" Cikin zafin zuciya ta ce "Da kai da shugaban masoyan duk kunci kutumar ubanku, banza sakali, dolo ƙazami wawa mahaukaci" Ya ce "Siyama karfa ki manta ke kika koya min sonki, ke kika nemi da mu fara soyayya, to bayan na yarda da ke na gama zurmawa a sonki shine yanzu zaki nuna wai wasa kike min, to ni dai da gaske nake ina sonki. Siyama da ta rasa me zata ƙara cewa ta buɗe jakarta ta kwaso kuɗi rafar biyar dubu ɗari biyar kenan ta watsa masa ta ce "Ibrahim wannan shine gargadin karshe tsakaninmu, idan kaji to shi kenan, tana faɗa ta miƙe zata fita amma Ibrahim ya jawo ta jikinsa, ai kuwa ta faɗo kan gadon sa, ta hau kansa. Ganin haka yasa Hajja fita da gudu tana ihun kiran Nana. Sosai ya manneta a jikinsa yana shaƙar sassanyan ƙamshin turatenta da ya kama ɗakin tun ɗazu da ta shigo. Sosai ta shiga ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa hakan yasa ta sakar masa cizo amma ko a jikinsa, sai ma ƙara matseta da yake yi yana ƙara tabbatar mata da cewar yana sonta. A haka Haladu da Nana da Hajja suka zo suka samesu, Siyama tayi-tayi har ta haƙura ta fara kuka domin ta matsu sosai. Shi kuwa wani irin sanyi da natsuwar zuciya ya samu kansa a ciki har yake nema ya shagala barci ya ɗauke sa. Yana jin an shigo ya saketa yana miƙewa. Ita kuwa da kuka ya cika mata baki ta fashe da shi tana gyara rigar ta da ta tattare. Hajja ta ce "Ibrahim ka fara hauka ne, meye wannan ɗin kayi, ko ka zama mahaukaci ne. Ta faɗa tana kallon Siyama da ta miƙe tsaye tana gyare-gyare. Ta juyo ta kalli Ibrahim ya sakar mata murmushi ta ce "Zaka san ka haɗa jiki dani, ba dai kai wawa ɗan iska dole shege ba ka jira dawowa ta" ya ce "Dan Allah ki dawo da wuri please Siyamata" ya faɗa da dan ƙarfi domin har ta bar gidan.

Suna fita Hajja ta ɗauke shi da mari ta ƙara masa tana faɗin "Yanzu kasan me zata aikata mana ne, me yasa baka da tunanine Ibrahim yaushe ka zama ɗan iska a cikin gida zaka kama musu yarinya haka ake so ɗin" sosai Hajja tai masa kace-kace, kuma tace karya kuskura ya leƙa ko waje. Tana gamawa ta kwashe kuɗin tana nunawa Haladu da yake ta kallonsu tun da yazo. Hajja ta ce "Haladu yanzu nawa kenan wannan kuɗin. Ya ce "Hajja guda biyar ne sun kama dubu ɗari biyar kenan" Hajja ta waro ido tana kama baki ta ce "Ɗari biyar dai Haladu? Haladu yayi dariya ya ce "Allah ne ya baku" "Yanzu zamu iya taɓawa nifa ina tsoro karta dawo tace a bata kayanta? Kafin Haladu yayi magana Ibrahim ya wafce kuɗin ya saka a ƙarƙashin katifarsa ya ce "Babu wanda zai taɓa mata kuɗi mayar mata da shi za'ayi. Haladu ya ce "To wallahi baka isa ba, ina ruwanka kai ne ka bayar, kai dai kaje da rashin zuciyarka yarinya ta zageka ta zagi uwarka a gaban ka, ai ni wallahi ka bagama bani mamaki. Ibrahim ya ce "To ko kaima zaka zaga ne ka gani? Haladu ya ce "Ba zan zaga ba domin nasan illar hakan amma kuɗi ne dai sai ka bayar anbawa masu hankali su hajja. Ibrahim yace "To zoka ƙwata. Haladu ya ce "Yanzu kuwa" Haka suka shiga dambe har sai da Haladu ya ciro kuɗin ya mikawa su hajja raba ɗaya ya ce zai ajiye musu sauran sabo da kar ya zo ya kwashe. Hajja dai sai godiya take duk da har yanzu tana tsoro, ita dai Nana har ta fara lissafin abubuwan siya.

****** *AIDA" Sai da ta tabbatar da duk wata shedar ta da yake nuna cewar Adawiya da Badawiya ne suka saka wannan tsohon banzan Olusha yayi wannan aikin hakan yasa ta samu Oga Fita ta sanar masa, shima yayi mamaki ai kuwa nan take ya haɗa mintin aka taru ya tambayi Badau kasancewar ita Adawiya bata nan. Farko tayi musu amma ganin shedar da Aida ta kawo yasa ta tabbatar. Nan take Oga Fita ya wanketa tass akan yanzu gashi sun jawo mata zagi agurin iyayenta da jama'ar gari. Sannan yace "Zasu yi vedio su ƙaryata kansu. Nan fa Badawiya tace ba zata iya ba. Haka zaman ya watse akan ita dai wallahi ba zata yi video ba. Ai lukacin da Adawiya ta samu labari daga gurin Badawiya, lokacin har ta sa hannu a VIP London, dama tana neman yadda za'ayi ta bar team ɗin su na Farin gida, kuma dama sunyi magana da shugaban Magazing akan zata mayar da Badau taci gaba da aiki a tare da su a matsayin ta, ita ta samu wani aikin. Alesx da haushin ta yake ji tun lokacin da yayi mata maganar Aikin karshen shekara tace ba zata yi ba. Bai nuna mata komai ba yace ta kawo hotunan ƴar uwar tata.

Sosai Adawiya ta kira Oga Fita suka yi kace-kace har tana ƙara sanar da shi cewar zata ƙara yin wani sabon Video ɗin akan shi Oga Fita ɗin yana kwanciya ne da duk members ɗin team ɗin su kafin ya ɗauke su harda ita Siyama ɗin, kuma harda ita kanta Adawiya ɗin. Sosai Oga Fita ya shiga tashin hankali domin shi ba rabuwar da sukayi da su bane matsalar ko faɗin cewar zata ce yana kwanciya da su ba, a'a shi abu biyu yake tsoro, na ɗaya Siyama da iyayenta, domin ya tsorata da Umma da ya ganta. Na biyu kuma jin cewar Adawiya ta shiga VIP London, sosai yake mamaki da tsoro. Haka dai a ka rabu tsakanin team da Adawiya da Badawiya. Haka kuwa ta tattara komai nasu sai England London tarar da ita a cen.

Hakan yasa sunan Aida ya shiga cikin waɗanda zasu yi tala ga Baby and me. Yanzu haka ita da Nusee da Sarah ne zasu fara zuwa gurin domin saka hannu kuma a ƙara koya musu duk wasu abubuwan da zasu yi. Ganin har lokacin da aka bawa Siyama ya wuce ne yasa suka ce kawai a fara aikin da sauran Medels ɗin, idan yaso duk lokacin da ita Siyama ɗin ta shirya zasu yi aiki da ita. Akan haka aka tsaya, Aida tana ta kiran Siyama domin ta sanar da ita amma bata amsawa, sai kawai ta tura mata message. Da sauri ta fito Palo tana kallon Jamila da ta fito daga kicin riƙe da kofin shayi tana sha. "Kar dai kice min baki gama girkin ba? Jamila tayi dariya ta ce "Harma munci namu ke kawai ya rage" Ta ce "Ina Jamilu? "Ya shiga wanka tun ɗazu nima shi nake jira" Da mamaki Aida ta ce "Ina zaku je da kike jiransa? Jamila ta buɗe mata kanta ba tare da tace komai ba. Sai Aida ta ce "Auf sorry ni bama Na manta munyi maganar wankin kai daku ba. Ta ce "Yauwa zan bar muku wannan farar motar, kuma karku tsaya a ko'ina, kuna gamawa ku dawo gida, zan kara muku kuɗi yanzu, karfa ku tsaya a ko'ina" Jamila ta amsa da tom. Haka ta shiga cin abincin tana sauri, kafin ta gama Jamilu ya fito cikin shirin sa na kayan ƴan kwallo yana kallon Aida ya ce "Anty baki tafi ba har yanzu ƙarfe tara saura fa?" Haka ta gama kafin ta wanke hannu ta ƙara jaddada musu cewar karsu tsaya a ko'ina ana gama gyara mata kan shima yayi askin su dawo gida, suka amsa da to kafin ta rungume su ɗaya bayan ɗaya suka rakata har gurin motarta ta shiga ta nufi team ɗin su. Tana barin gidan Jamila da jamilu suka koma ciki. Bata fi minti biyar da fita ba motar Siyama ta shigo gidan. Bata tsaya komai ba ta shige cikin ta nufi ɗakin Aida duk ranta a ɓace. Tun daga palon take jiyo Nishi a ɗakin Jamila, hakan yasa abun da ta gani ranar ya fado mata, take ta nufi ɗakin tana tunanin wai kullum haka suke yi ne, anya kuwa Aida bata sani ba, da mamaki taga ɗakin a buɗe, ta leka ta samesu kamar ranar yau ma dai sex suke yi, sosai wannan karan ta tsaya tana ta kallonsu har ta manta da abun da ya kawota, sosai taji tana neman rasa control ɗin ta, hakan yasa ta ciro wayarta ta shiga camera ta fara ɗaukarsu vedio. Haka ta juya ta fita ganin haka tasan Aida bata gida, hakan yasa ta bar gidan itama.

Aida kuwa tare suka tafi su uku kowacce da motarta. Bayan sun isa gurin ne, aka tabbatar da cewar zasu iya, nan suka saka hannu, kafin aka shigar dasu wani ƙaton abu mai kamar irin abun gurin wanka, amma wannan a zagaye yake kamar saiko. Da mamaki sukaga ruwan zafi ne a ciki sai tururi yake yi, gashi ruwan kamar yalo kamar kore. Haka dai Nusee ta fara shiga sai Sarah sai ita Aida ɗin. Jin ruwan ba zafi  sosai ne yasa suka sake. Sunyi a ƙalla minti talatin kafin aka ce su fito. Nan ma aka basu wani ruwa mai kaman mai aka ce su shafe jikinsu, su dai komai aka ce sai yi suke, suna sanye da bra da banti kawai a jikinsu. Lokacin da suka kalli jikinsu suka ga sun kara wani haske da kyau. Bayan sun gama shafe jikinsu aka basu wani ruwa irin na da suka shiga ciki amma wannan normal ruwane su shiga ciki irin dai na ɗaxu. Bayan sun fito aka basu wasu kayan suka saka, aka fara yin hotuna. Ita Sarah tallan fauda suka ɗauketa wanda uwa da ƴarta zasu iya yin amfani da shi a lokaci guda, za'a dinga ɗora hotonta a jikin fauda ɗin. Ita kuma Nusee tallan man shafawa ne nata itace za'a dinga ɗora hotonta a jikin man ita da yarinyar da aka bata mai kyau da ita suka yi hoton yarinyar sai dariya take yi. Ita kuma Aida turare ne shima duk na kampanin Baby and me ne, wannan shine karo na farko da suka fito da turare na Baby and me hakan yasa suka zaɓi ita Aida ɗin ganin ita ba fara mace. Nan aka shiga nuna musu yadda kowacce zata tsaya a dauki hoto, sannan sati mai zuwa kuma za'ayi vedio domin fara haɗawa, kasancewar tallan nasu yana shiga gidajen talabijin da na rediyo harma online da dai sauransu. Haka dai kowacce ta dawo gida cike da farin ciki.

****** ADAWIYA Duk da yadda take kallon haɗuwar gurin amma hakan bai sa ta shagala da kallo ba saboda karma a raina ta. Sunyi tafiya mai tsayi a linta kafin suka isa wani ɗaki, suna shiga ta ga ɗaya daga cikin mutanen da suka zo gurin ta. Tana shiga ya miƙe tsaye suka yi hannu da manager ita kuma ya ɗaga mata hannu. Kallon ɗakin take ko tace ofishin da ya cika da hutunan fina-finai na batsa wanda wasu daga ciki ma duk ta kalla. Sosai sunan wani fim ya ɗauki hankalin ta ganin hoton wani saurayi Model ɗan ƙasar Faransa. Tasan yaron sun taɓa yin aiki da shi a nan Ingila a Magazing, amma bata san ya shiga VIP London ba, kallon hoton tayi taga a she ma film ɗin sabo ne, domin ba'a sake shi ba. Maganar da mutumin yayi ce ta dawo da Adawiya cikin tunaninta ya ce "Ga dokokin aikin VIP" Ya faɗa yana turawa manager ɗin wata zungureriyar takarda. Manager ya shiga karantawa yana yi yana kallon Adawiya da mutumin cike da mamaki. Sai da ya gama kafin ya share zufar da yayi ya ce "Zamu iya yin magana da ita mu biyu? Mutumin ya ce *Yes don't worry"  Yana faɗa ya nuna musu wani ɗan Ƙaramin daki gefe da su. Adawiya ta ce "No ba sai munje ko ina ba, nasan komai game da aikin kawai asa hannu" manager ya kalleta da kyau ya ce "No Madam ki dai ƙara ki sake dubawa yanzu da kanki. Haka ta ƙarɓa ta shiga dubawa sama-sama ta karanta abun da idonta ya kai wanda bata kalla ba kuma ya wuce. Nan take ta saka hannu shima manager babu yadda ya iya ya saka hannu. Take aka bata wasu takardu akan taje ta ƙara cike su. Bayan sun gama mutumin ya ce ta biyo shi ita kaɗai. Nan suka shiga tafiya saida suka yi nisa kafin suka iso gurin ɗaya mutumin. Ya bata wasu kaya ta saka. Nan ta saka kayan wanda basu da maraba da tsirara. Wani dakin hoto ta shiga, ai kuwa tana shiga ta tarar da mata da maza sun kai goma ana ta hoto, yanayin shigar dai ba'a cewa komai. Domin dama haka shigar Medels yake musamman ma yan VIP. Ba'a tsaya da ita a nan ba suka shiga wani ɗaki bayan mata da mazan sun gama mata barka da zuwa. Suna shiga wani na miji yabi bayan su da abun ɗaukar video. Suna shiga taga ɗaki ne harda gano da komai. Kwanciya ya ce tayi, ta kwanta tana kallon namijin da shima ya zagayo kusa da ita babu komai a jikinsa sai ƙaramin wandon maza.  Mutumin da suka shigo tare ya ce "Sau nawa kika taɓa yin sex? Ta haɗiye yawon tsoro tana tunanin to ina ruwansu da sanin wannan tace "Bata sani ba"  Kallon Namijin yayi ya ce "Zata iya yi kuwa? Ya ce "Eh zata iya. Ya kalli mai ɗaukar video ɗin ya ce muje zuwa. Ya fara ƙoƙarin cire mata ɗan fanti dake jikinta sai ta riƙe, domin har ga Allah ta tsorata da namijin ganin sai jiki duk a murɗe kamar ɗan dambe.Wata tsawa mutumin ya daga mata yana cewa zata ɓata musu aiki gwaji za'a kawai idan har ta iya cin gwajin to za'a fara aiki da ita kwanan nan, idan kuma bata ci gwajin ba za'a ci gaba da bin ta a hankali har ta saba. Sosai ta tsorata a fili ta ce "Sex ne gwajin?" Ya ce "Yes baki gani a jikin takardar da kika sa hannu bane? Gabanta ya ba da wani rass...📝

_To masoya S Reza, wannan shine karshen free page Kaman yadda nayi alƙawari. Nera ɗari biyar kawai zaki biya a saka ki a cikin group aci gaba da posting. Kuma yanzu haka ba tsayawa zan yi da posting ba, domin wasu sun fara biyan nasu, idan kin biya sai na tura miki wanda akayi ba kyanan sai kuma a ci gaba da ga inda aka tsaya. Ba sai na ce muku komai akan wannan labarin ba kunsan za'a samu darasi mai muhimmanci, sanna akwai aikin da na sani a ɓangarorin cikin labarin kaman yadda kuka gani, Jamil da jamilu abun da suke yi Aida ta sani, Adawiya da Badawiya sun samu madafa, Siyama da Ibrahim me zai faru, Hamm ba sai na cika ku da surutu ba mu haɗu a VIP. Ga account number da za'a biya ɗari biyar 8100785178 Opay Adam Salisu. Sai a tura da shedar biya ta wannan lambar ***. Idan ma katin waya zaki turo shima kiyi magana wa wannan number. Idan kika biya kudi akan wannan littafin wallahi ina sheda miki cewar baki faɗi ba domin zaki kwashi ruwan darasin rayuwa. Sai na ganku ƴan amanar S Reza_ 🥰

Love all One love Comments Ana shering Love my fan's By S-Reza write [9/26, 10:17 AM] S Reza: TSINUWAR UWA