Chapter 23
SAUTIN ƘARSHE
BY AMANARCOOL
YOTA/021
Under Yota's Amazing Pens
Book 1
Page 23
Misalin ƙarfe uku da rabi na dare, zaune yake a gaban Malaminsa ya zuba masa ido yana kallon yadda yake gudanar da baƙin aikinsa, wata ƙwarya Malamin ya ɗakko da wasu ruwa mara kyan gani a ciki, ya ajiye a gabansa. Ya ɗakko wani garin magani ya zuba a cikin ruwan, nan take suka canza launi, wani turare ya sake ɗakkowa cikin wata ƙaramar kwalba ya zuba. Sai ga ruwan sun koma kalar ja, wani hayaƙi ya dinga tashi a cikin ƙwaryar yana yi sama. Lokaci ɗaya ɗakin ya surmuƙe da hayaƙin, kusan minti biyar suba a haka, sai kuma ya fara washe wa, hayaƙin ya daina tashi. Malamin ya yi wani murmushin da yake bayyanar da tsantsar mugunta da rashin imani. Ya ce "Alhaji, aikinka ya kammala, ka zuba ido ka gani kai ne da nasara a cikin wannan tafiyar da za a yi. Jinin matar nan yana da kyau sosai, ga ta da yaron ciki sai muka haɗa duka har da shi muka yi amfani ni, shi ya sa akinmu ya tafi daidai yadda ake buƙata." Ya kai ƙarshen maganar yana ɗakko wani ƙullin magani ya ce "Karɓi wannan maganin, ka je a zuba shi a cikin magungunan da ake sarrafawa kamar yadda aka saba. Sai dai yanzu ka da a sake taɓa kowa sai bayan wata ɗaya, saboda gara a dinga yi ana kawar da hankalin al'umma kar su farga da abin da yake faruwa, duk da ba su da wannan damar."
Mutumin da aka kira da Alhaji ya sauke numfashi ya ce "To shikenan Malam, ina godiya sosai da sosai, za a yi kamar yadda ka buƙata, gara ana yin ɓaddasau, musamman ma wannan karon da mutum uku muka taɓa lokaci ɗaya."
Dariya Malamin ya yi ya ce "Ai ko mutum goma kuka taɓa lokaci ɗaya babu wanda zai yi magana, ko kamanta waye ni? Kai dai ka je ka ci gaba da amfani da maganin nan da na baka, salin alin za mu dinga amfani da jinin mutane muna biya muku buƙatunku da shi, za mu ci gaba da rufe bakin jama'a, ta yadda duk abin da zai faru ba za su yi magana ba, ko su tsaurara bincike ba, sai dai akwai wata matsala da naga tana ƙoƙarin kunno kai. Duk da ban ida tabbatarwa ba, amma naga alamunta, kuma zan yi ƙoƙarin kawar da ita kafin faruwarta."
"Matsala kuma Malam? Wace irin matsala?"
Dariya ya yi ya ce "Kar ka damu, ka kwantar da hankalinka, wani mutum ne na fara gani yana ƙoƙarin ba mu matsala amma zan yi maganinsa."
Ajiyar zuciya mutumin ya sauke ya ce "To shikenan Malam, ai nasan tunda ina da kai ba zan taɓa jin kunya ba."
"Kai da jin kunya ai sai idan ba na raye Alaji." Ya ce yana murmushi.
Cikin jin daɗi ya ajiye masa maƙudan kuɗaɗe sannan ya yi masa sallama ya tafi.
.....
Daga Mammy har Zahra babu wanda ya iya komawa bacci a cikinsu, kiran sallar farko a kan kunnensu a ka yi shi, bayan sun idar da sallar asuba ne Mammy ta yi shiru ta zubawa gawar Ilham ido tana kallonta, Zahra ta dube ta da rinannun idanunta da suka kumbura saboda kuka ta ce "Mammy ki sanar da su Yaya da Uncle"
Ajiyar zuciya Mammy ta yi ta ce "Zahra ina tunanin yadda zan sanar da su ne, wallahi ina jin tausayin iyayen yarinyar nan fiye da Sudais, ya za su ji? Yarinyar ita kaɗai Allah ya basu, daga ita ba su sake haihuwa ba sai bayan wasu shekaru. A lokacin da suka fitar da rai da sake samun haihuwa sai gashi Allah ya sake basu wata haihuwar, suna murna da farin ciki, lokaci ɗaya aka nemi yaro aka rasa. Shekaru huɗu kenan da faruwar lamarin nan yanzu kuma ƴar da suke kallo suna jin sanyi a ransu ita ma sun rasa ta." Ta ƙarasa maganar hawaye na zuba daga idanunta. Cikin kuka Zahra ta ce "Duk da haka Mammy haƙuri za ki yi ki sanar musu, idan ba za ki iya kiran Uncle ba ki kira Yaya Sudais ko Yaya Faruk ki gaya musu."
Ba tare da Mammy ta yi magana ba ta ɗakko wayarta ta turawa Sudais saƙo sannan ta ajiye wayar.
Sudais ana idar da sallar asuba bai daɗe zaune a masallaci ba ya dawo gida, yana zaune bakin gado yana tunanin rashin lafiyar Ilham, tare da tambayar kansa wane magani ne ta sha? Saƙo ya ji ya shiga wayarsa ko da ya duba yaga Mammy ce, buɗe saƙon ya yi. "Sudais ka zo maza yanzu Allah ya yi wa Ilham rasuwa jiya cikin dare."
Shi ne abin da idonsa ya gane masa, murza idonsa ya yi ya sake kallon screen ɗin wayar da kyau, babu shiri ya kira wayar Mammy, tunda daga yanayin muryata ya tabbatar da saƙon da ta turo masa gaskiya ne, kashe wayar ya yi, ya kasa magana. "Ilham ta rasu? Ilham ta rasu? Ilham ta rasu?" Ya tambaya har sau uku. Duk sanyi Acn dake cikin ɗakin bai hana shi yin gumi ba, lokaci ɗaya fuskarsa ta sauya daga fari zuwa ja, idanunsa suka yi jajur. Saƙo ya turawa Faruk da Hanif, ya gamawa ya fice daga ɗakin ba tare daya tsaya canza kaya ba. Yana fita harabar gidan yaga Faruk ya shigo cikin tashi hankali, da alama yana masallaci ne yaga saƙon Sudais "Yaya yanzu naga saƙonka, da gaske Ilham ta rasu?" Sudais bai tsaya bashi amsa ba ya nufi motarsa, da sauri Faruk ya karɓi makullin motar daga hannunsa, saboda a wannan halin da yake ciki idan ya yi tuƙi da kansa komai zai iya faruwa, mazaunin direba ya shiga, Sudais ya zauna a gefensa ya dafe kansa. Murya a sanyaye Faruk ya ce "Ina zamu je Yaya?"
"Asibiti" ya bashi amsa. Faruk ya ja motar suka tafi asibitin.
Lokacin da Faruk ya sanar da Uncle, bai sanar da Momy ba ya shirya ya tafi asibitin, bayan an gama duk abin da za a yi aka basu gawar Ilham suka wuce gida da ita, sai a lokacin ne ya kira Momy ya sanar da ita abin da ke faruwa. Kamar wata ƙaramar yarinya haka dinga ihu tana kuka, ta ce "Za ta zo gidan" amma Uncle ya ce "Kar ta zo saboda ya san idan ta zo ƙara ɗaga wa mutane hankali za ta yi." Sai da Mammy ta ce masa "Ya bari ta zo ta yi bankwana da ƴarta, tare da yi mata addu'a" sannan ya amince ta zo. Ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba a lokacin da ta yi tozali da gawar Ilham, don sai da ta suma a gurin, bayan ta farfaɗo ne Uncle ya sa aka mayar da ita gida. Cikin ƙanƙanin lokaci labarin rasuwar Ilham ya zagaya dangi da ma sauran jama'ar garin, da misalin ƙarfe goma na safe aka yi jana'izarta. Duk wanda ya kalli Sudais ya san yana cikin tashin hankali mara misaltawa, gaisuwa ma da hannu ko ya gyaɗa kai yake amsata. Hanif ne yake ta bashi haƙuri. Alhaji Sardauna ya zo tare da su Alhaji Badaru duk da su aka yi jana'iza, sun daɗe a gurin suna yi masa nasiha da nuna masa muhimmancin haƙuri, sannan suka yi masa sallama suka tafi.
.....
"Allah mai iko, Lantana Zalihan ce ta ba ki wannan labarin?"
Lantana ta ce "Eh wallahi Malam, sai ma ka ga yadda take ba ni labarin tana kuka, ni narasa me mutane suka ɗauki duniyar nan ne? Gabaɗaya babu Allah a ransu." Ya yi murmushi ya ce "Hmmm, wai har kin manta abin da ya faru da aminina? Ko ko ni kin manta abin da ya faru da ni? Kar ki manta ba don Allah na ya nufi ina da tsawon rai ba da yanzu na daɗe da zama toka a ƙabari, shekaru ashirin ba wasa ba. Duk da tsawon wannan lokacin na tabbatar da mutanen nan sun san ina raye da ba za su bar ni ba, shi ya sa nake cewa ni da Abuja har abada. Ina fatan Allah ya toni asirinsu, kuma in sha Allah duk na samu wata damar da zan iya ba da gudummawata akan mutanen nan sai na yi."
Ajiyar zuciyai ta sauke ta ce "Malam ni har yanzu ka kasa sanar da ni taƙamammen me mutanen nan suke aikatawa ne, kodayake ko ma me ye ai yanzu ya wuce, ba na tunanin har yanzu tsawon waɗan nan shekaru a ce suna aikata shi." Kallonta ya yi, ya girgiza kai tare da yin murmushi mai ciwo ya ce "Ke dai a yi sha'ani kawai, har yanzu babu abin da suka daina, sai ma ci gaba da suka ƙara samu. Allah dai ya toni asirinsu, kuma duk ranar dana samu dama sai na bawa kowa mamaki."
Lantana ta ce "Wane mamaki kuma? Wai ma tukuna wace damar kake magana? Kai da da ƙyar kasha a hannunsu." Ya ce "Lantana kenan, a yanzu da zan samu dama, ina mai tabbatar miki akwai abin da idan na fitar da shi ƙaryarsu ta ƙare."
"Menene shi Malam?" Ta tambaya tana kallonsa.
Ya nisa ya ce "Ba zan sabar dake ko me ye ba, ki jira idan lokacin daya kamata ki sani ya yi za ki sani."
"Wane lokacin kenan?" Ta sake jefo masa tambaya. "Lokacin da Allah zai kawo wanda nake jira, na san komai daren daɗewa zai neme ni." Daga haka ya tashi ya ɗauki buta ya shiga banɗaki.
....
Tunda Abbi ya sanar da ita labarin mutuwar matar Sudais, gabaɗaya sai ta ji hankalinta ya tashi matuƙa, sosai mutuwar ta dake ta duk da ta wani fannin abin jin daɗi ne a gare ta, amma sam ba ta ji ta yi farin ciki da hakan ba.
Ƙarfe tara na dare Sudais na zaune a ɗakinsa ya sunkuyar da kansa ƙasa, a cikin wuni ɗaya ya yi wata irin rama ta ban mamaki. Kira ne ya shigo wayarsa, yana jin wayar na faman ruri amma ya yi banza da ita. Daga ƙarshe ya kashe wayar ma gabaɗaya.
Bin wayar Zuhura ta yi da kallon ganin bai daga ba, sake kira ta yi ta ce wayar a kashe. Ta ce "Allah Sarki! Bawan Allah, wallahi na tausaya maka masoyi, Allah ya ba ka haƙuri, irin wannan rashin na kumfayakun yana da zafi."
Sudais kuwa yana nan zaune Zahra za ta shigo ɗakin da sallama hannunta ɗauke da tiren abinci, durƙusawa ta yi ta ajiye tiren ta ce "Sannu yaya, ya ƙarin haƙuri? Allah ya sa ta huta." Bai ce mata uffan ba, sai alama da ya yi mata da ta fita da abincin. Ɗaukar tiren ta yi ta juya za ta bar ɗakin, ta ji ya ce "Zahra"
Juyowa ta yi a hankali ta ce "Na'am Yaya"
"Kina da masaniya akan maganin da aka ce Ilham ta sha?" Girgiza kai ta yi ta ce "A'a Yaya, ban da masaniya a kai, na dai san ranar da muka je gurin Momy a hanyarmu ta dawo ne kanta ya uzzura mata da ciwo, sai muka shiga wani asibiti aka duba ta tare da ba ta magani." "Za ki iya gane maganin da aka ba ta?" Ya tambaya yana tsare ta da ido.
Zahra ta ce "Eh"
Tashi ya yi a hankali, ya je inda ya ajiye kwalin maganin ya ɗakko su ya ce "Duba ki gani sune?" Kallo ɗaya ta yi musu ta ce "Eh sune".
"Wace asibiti ce?" Shiru ta yi tana nazari, amma ta kasa tuna sunan asibitin, ta ce "Wallahi Yaya na manta sunan asibitin" ya kalle ta da kyau ya ce "Ok" daga haka ta bar ɗakin.
....
"Ma'u" Inna ta kira sunanta tana tsare ta da ido
Cikin matsanancin tsoro ta ɗago da kanta suka haɗa ido da Inna, da sauri ta duƙar da kanta ƙasa, tana mazurai da ido, cikin tashin hankali Inna ta ce "Innalillahi wa inna ilaihim raji'un, Ma'u me zan gani haka? Don Allah ki rufa mini asiri, ki ce mini abin da nake gani a idona ba gaskiya ba ne. Ma'u duk wata alama da take bayyanar da mace mai ciki, ta bayyana a gare ki. Ki gaya mini garin yaya hakan ta faru? Ma'u wa ya yi miki ciki?"
"Ciki kuma!?" Suka ji Aliyu ya faɗa da ƙarfi, a razane Ma'u ta ɗago da kanta ta kalli bakin ƙofa inda yake a tsaye.
Mun kusa kammala book 1, book 2 na kuɗi ne, ga mai buƙatar ci gaba da bibiyar wannan littafin zai iya tura 1k ɗinsa, 1019533255 Nafisa Muhammad UBA, sai a tura mini shaidar biya.
Amanarcool
***