Halimatus’sadiya (sakayya)

12

by @102565813543784586917

Asim yayi shiru bai tanka shi ba har suka dawo gida suka wuce sallah magriba.


Da zumudin sa ya shriya zai je wurin masoyiyar sa dan bata amsar tambayar ta sai da ya gama shiryawa ya naimi key din motar shi sama da kasa ya rasa.

Ya fito parloun a hassale ya ce "Kai Asif bana son wasan banza where is my car key?


Asif ya dubai shi ya ce "Na ma kama da barawon mukulun mota."


Asim ya ce "Look i'm in haste ina ka aje min su ban abuna."


Asfi ya dau system din tare da crossing leg ya ce "Keeping asking." Ya maida kan shi saman syetem.


Rai ba ce ya nufo Asif ya chakumai shi yana ce wa "Kar ka bata min rai.'


Ahmad dake zaune a prlourn ya mike da niyar raba su ya ce "Haba Asim mi yayi zafi haka?


Asif ya tabe fuksa ya cigaba  da amfani da ita. Asim kuma ya koma daki yagama dubai duban sa bai gan shi ba bai ga na Asif ba bai ga na buba ba ya fito parlourn ya tambayi Ahmad ina car key din ka ara min zan fita.


Ahmada ya ce "Sorry my car has broke down."


"Dam it."

Zai fita Ahmad ya tambaye shi "Wai ina zaka? 


Bai bashi amsa ba ya wuce. Part din Umma ya wuce, ba ta parlou ya wuce kitchen in da ya jiyo muryar ta.


Ya karasa ciki ya na kiran ta. "Umma kuma zata fito ta ce "Lfy Asim ka ke kira na tin daga parlour?¿


Ya ce "Umma dan Allah key din motan ki na ke so?


Umma ta ce "Lfy ni ban gane ba dazu Asif ya amshe shi."


Asim ya ce what! Ki ka bashi. 

Ya juya rai ba ce zai fita ta dagatar da shi amma ina zuciyar na ta shi ba karamin haushin danuwansa ta ke yi ba ya wuce dakin su. Ya bangaje kofar ya shigo ciki Asif na ganin haka da sauri ya wuce daki ya sa key. 


Asim ya buga kofar a hasalle ya na ce wa ka ban key din motar umma kar in bata ma rai.


Asif ya ce "Ka dauka in ka ganshi."


Ran shi ba karamin ba ci yayi ba yana ta masifar shi Ahmad na bashi hakuri duk da bai so yayi kutse dan yasan kafin dare za su hadai  kai.


Har dai a ka kira sallah isha’I anajin Asim da Asif. Karshe ya wuce massallaci bayan an gama sallah ya yanke shawara tafiya akan machine.


Har cikin layin mai machine din ya kawo shi ya sauka daga kan machine ya fiddo kudi a aljihun gaban rigar shi ya bashi kudi sannnan ya wuce kofar gidan su halimatu. Ya aiki wani yaro ciki.


Halimatu na bisa tabarma ta na sallah yaron ya shigo ya isar da sakon nusaiba ta ce ka ce ga tanan fitowa. Yaron ya gyada kai ya wuce ya fadi wa Asim Asim ya bashi tukici ya wuce shi kuma ya jira har sai da ta gama sallah sannna ta fito.


Ta na fitowa kamar kullun kanta a sadda ta gasihe shi ya amsa. Shi kuma ya tambayi su umma ta ce suna nan lfy.


Ya ce "Masha Allah, aikin da ki ka bani na nemo wasu wasu kuma sun ki zama on my minute brain."


Ta ce toh ina sauraran ka.


Ya ce "Fatan in na amsa daidai za a min tukuici."


Ta jingina jikin bango ta re da tambayar shi wani kalar tuikuici ka ke so.


Ya ce s"Soyyar ki bana."


Shiru ba ta bashi amsa ba ya fara mata bayani kamar haka;


With my little knowledge na san dai Aure ibada ne duk in da a ka ce ibada ana nufin bauta kuma sunnah manzon Allah SAW ne. In the afternoon I reserch on it so kin san goggle zai baka different scholers da yanda suka dau ma’anar sa kuma wannan brain din nawa karamin byte ga rai shi ba duka yayi capturing ba.


Sai ya dagata yana kallon ta duk da har yanzu kan ta a saddai yake.


Ya ce "Hello are you here??

Ta gyda mashi kai.

Ya ce "Naji kin yi shiru."

Ta ce "Ina sauraran ka."


Ya ce "Ok, cikin abubuwan da na duba da su akwai hadisai da yawa wanda suka yi Magana gamaida aure sai dai na manta wasu but what I could remember akwai hadisin da manzon Allah SAW ta ce da sahabai kuyi aure ku haihaifa ina so in yi alfahari da al’umma ta ranar tashin alkiyama kin ga da ni da ke ta dalilin aure mu ka zo duniya.

Sai kuma hadisin da manzon Allah ya ce... 

..Sorry ni ban iya larabci ba so I just grap the meaning.


Ba tace da shi komi ba ya cigaba.


Manzon Allah ya ce **Jin dadin duniya kadan ne kuma rabin sa shi ne ka samu mata ta gari**  Kin ga ke nan in na aure ki na samu rabin jin dadin duniya. 


Sai last hadith da zan iya tunawa shi ne.. hmm ya ma. 


Ya dan rike goshin sa yana Nazari kafin ya ce "Yes, na dai manta ya hadisin yake but a fahimta ta in dan namiji ya yi aure ya cika 50percent na addinin sa sauran 50percent bautar Allah ne. so that all what I know, fatan zan samu marks da yawa.


Sai a lokacin ta dago kai sai dai ba ta bari suka hada ido ba ta ce "Sai dai kuma banji ka kawo reference wanda shine ginshinkin rayuwar mu musanman musulmi."


Ana gizo ke saka Asim ya dubai ta sai dai ta kauda kai ya shiga Nazari yana ta cracking brain din sa amma ya kasa gano answer ya ce "Na hakura na faadi ki fadi min answer."


Ta ce "Mi yasa za ka yi saurin bada gari."

Ya ce "Sbd ban san answer ba."


Ta ce "Aikin ka na biyu ke nan."

Ya ce "A min gafara wannan ma da ya na samai shi ki taimaka ki fadi min kin ji."


Ta ce "Al’qur’ani."


Sai alokacin hakan ya fado mashi ya ce"Wannan haka yake kwatakwata tunani na bai kawo haka ba, Alqur'ani shi ne ginshikin rayuwar mu kuma mabudun kowace masalaha sai dai ni ba gwani ba ne a alqur’ani ba ban yi harda ba balle in san tafsir din shi iya tilawa kadai muka tsaya.


Ta ce "Cikin surarul ra'ad aya ta 38 Allah ya na cewa "Hakika mun aika manzonninmu  gabanin ka mun sanya masu mataye da zuria." 


Sannan a suratun rum aya ta 21 "Daga ayoyin sa ya hallita muku matan aure daga kanku domin ku nutsu zuwa gare ta, kuma ya sanya soyyaya da rahama a tsakanin ku."


Sannan aya ta daya da ta uku cikin nisa’i

Dan numfashin da zata maida ya ce "A gaskiya da zan samai ki a matsayin mata da na fi kowa alfahari ko ba komi zan kara sanin addini ta wurin ki da yaran da zamu Haifa.


Ba ta ce mashi komi ba ya ambaci sunan ta ta dago sai dai har yanzu bata da wannan courage din da zata iya kallon fuskar sa.


Ya ce "Dan Allah ki kara sanar da ni gamaida aure tin da yau tofic din da mu ke Magana akai.


Bata ce mashi komi ba har sai da ya hada ta da Allah kafin ta ce "Kamar yanda ka ce Aure sunnan manzo Allah ne, manzon Allah ya ce "Duk wanda ya kyamaci ko yaki sunnah ta baya tare da ni haka ya fada wa wasu sahabai guda uku da suka ce, dayan su yace azumi zai yi har karshen rayuwar sa na biyun kuma yace sallah dare zai cigaba da yi na ukun kuma ya ce zai kauracewa mata dan yana so ya shagalta da ibada. 


Da manzon Allah Saw ya ji haka sai ya sa a ka kira su ya ce duk cikin ku na fi ku jin tsoran Allah kuma na fi ku jin tsoran sa kuma a haka ina yin aure na ina yin azumi ina sallah dare wanda ya kyamaci sunnanh ta baya tare da ni.


Ha ka kuma manzon Allah ya ce a na auren mace dan abubuwa guda hudu, dan kudin ta, Dan gidansu kila ta fito daga babban gida dan kyaunta ko kuma dan addinin ta. 


Miyasa za ka zabai ni bayan ni talakace baba na ma talakka ne, gidan mu ba wani babban gidaba ne ko kuma sannane sannan duk kyawawan matan Kano miyasa sai ni? 


Miyasa sai yar' aikin gidan kawun ka wadda wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa??


Ya furzar da numfashi shima yana jingina da bangon da ta ke jingine sai dai ya bar tazara a tsakanin su kafin ya ce"Na dade da jin hadisin amma kin manta karshen hadisin manzon allah ya ce amma ka zabi mai addinin, wannan itace duka amsar tambayar ki, ban da mu dan wai baku da kudi ko kuma gidan ku dan a fatawar da na ji duk daren da dai wa wannan kyawunnata zai gushe haka kudin ta zata ma Gadara da shi amma addini ya na nan ba zai taba gushaiwa ba. 


Ban damu ba dan wai baku da kudi ko wani abu sannan talakka ba shi ne wanda bai da kudi ba a’a talakka shi ne wanda bai da tarbiya da ladabi ita kuma tarbiya ba a sayen ta ba a saida ta sai dai akoye ta. 


Dan Allah ba dan ni ba sai dan giran Allah wanda ya hallice mu ki yarda zaki aure ni.


Gaban ta ne ya fadi, dan a duk lokacin da ya mata maganar aure wulkancin yan gidan su ta ke tunawa dan yana da wasun suke daukar talakka a kaskance duk da ba wani sanin su tayi sosai ba amma dabiun su Idan sun zo gidan kawu mala.


Ya katse ta daga tunanin ta, "Amira bi ki ce komi ba. Sunanan da ya fara lakana mata domin ya na jin nauyin kiran sunanta mussnmsn ta na dauke da sunanan mahaifiyar shi.


Ta ce "Ka nai mi izini wurin mahaifina."

 Daga haka tayi azamar tafiya. 


Da sauri ya shiga gaban ta ya ce Ay ya yarje min yanzu yardar ki kawai nake nema. 


Ta tambaye shi ka fadawa iyayen ka. 


Ya girgiza mata kai ta ce a duk lokacin da ka fada masu kuma suka yarda toh a lokacin zan karbi tayin da ka min. Daga haka ta bi ta gaban sa ta wuce cikin gida wanda ya bi ta da ido dan tabbass ya san ba karamin ruwa ya ibo wurin mahaifin sa amma ba zai bar halimatu ta kufce masa ba zai yi duk karfin sa ya samu halimatu ko da zai bar komi na sa ya dawo rayuwa irin ta su. Ya wuce a kan hanya ya tuna da wayar da ya siya mata dan zantukar da suka yi hankalin shi bai kai ya tambaye ta ina wayar ba ga kuma dare ya yi sai kawai ya wuce gida.


Ya na dawo wa gida ya shiga part din umman su ya mata sai da safe bayan ya ce da ita ya fasa tafiya gobe sai jibi ta tambaye shi dalili, a Zahiri yace mata flight din da yayi booking na Sunday ne a badini kuwa bai so ya tafi batare da ya fadawa masoyiyar ta sa gamaida tafiyar sa ba kuma ya sa ta ta fara amfani da wayar da ya siya mata.


Ya na shiga part din su ya iske su duka a parlour sallama ya musu ya wuce ba tare da ya kalli ko daya daga cikin su ba ya wuce dakin su. 


He took a quick cool shower cause the wether is hot, change into pjs bounced on his bed, ya dan lumshe idon sa iskan fanka na bukun sa chan ya lula tunanin masoyiyar sa haka har bacci ya dauke su sai da suka shigo hayaniyar su ya falkar da shi a lokacin ya tuna bai yi addu' a ba. Ya tashi zaune zai fara addu'a ya ga Asif ya zauna a dayen gefen ya na azamar kwanciya. 


Tsaki Asim ya ja ya mike ya koma gadon su Hamza fuska a daure ya ce wa hamza "Matsa."


Hamza kam na ganin haka ya san yau an ji ta kan su daman in sun yi fada ba sa taba yarda su kwana gado daya sai dai kowa ya kwana wuri daban musanmana Asif da ke da zuciya har barin dakin ya nayi ya koma parlour. 


Hamza ya matsa mashi ya zauna yana addu’a. Asif ganin haka ya yi dariya yana ce wa "Haba dude daga ba ka ga key din moto na ka ba dan zaka wurin budurwa sai ka zo ka na ta mana dacin rai ba dai ka kanta yanzu ba."


Asim yayi banza da shi Asif kuma ya kyalkyale da dariya. Buba da ya sallame sallah ya ce "Asif miyasa ka iya neman rigima?


Asim ya tofa adduar ya kwanta. Asif ya kara bushewa da dariya kafin ya ce "Ba ruwanka tsakanina da shi ne wai fah a kan budurwa ya ke ta wani dacin rai."


Buba ya ce "Na ji ba ruwana a tsakanin ku but gaskiya ka rage kyeta. 


Dariya yayi  yace "Zo mu kwanta in ba ka lbr, ay ina gaya ma ka wata aka samu da tafi da zuciyar dan uwana nan ta ke. First sight love fah. 


Buba ya karaso ya kwanta saman gadon. Asim da hamza duk suna jin su suka ki tanka masu. 


Buba yace "Toh wannan wace ce. Asif yayi murmishi ya ce "Wa ta mai sa’a ce?


 Kai dai ku sa shi a addu'a dan ta na neman zautar da shi. 


Buba yayi murishi yace 'Ka manta kwankin baya ka gama haukan Kursum sai da ga baya tayi casting din ka."


Asif ya buga taski ya ce "Kai fah dan rainin sense ne miya kawo maganar baya, mtsww ni ka ma bata min rai sai da safe." Ya kwanta. 


Buba yayi dariya kafin yace "Yanzu dai kun fasa neman twins da zaku aura?


Ya ce "Eh an fasa ko da akwai abin da zaka iya, ina ruwanka da kalal matayen da zamu aura."


Buba ya ce "Na ga da kuna ra.."


Asif ya katse shi "Kuma yanzu mun fasa ko ana dole malan don’t disturb me I wanna sleep." 


Daga haka ya daga hannun yayi addu'a buba ma haka suka kwanta.


Asim dai idan sa biyu sai dai ya rufe su maganar halimatu ke kai kwao cikin brain din sa, Ke nan ta na son sa ko kuma ba za ta fara san shi ba har sai ya fadawa iyayen sa? Haka dai ya cigaba da tambayar kan sa ya na sake sake har bacci ya dauke shi.