13
Da Asuba daman Asim ke tada da su ya tada kowa ban da Asif ya wuce war sa masallaci bai ta kan sa ba.
Sai da gari ya waye ya dawo ya koma bacci .
Wurin 10 saura ya tashi, toilet ya shiga ya wanke bakin sa da fuskarsa sannan ya wuce part din Hajiya Shafa ya gaishe ta sai ya wuce part din umma.
A karamin parlor ya iske su ita da Asif sai Jannat. Ya kauda kai ya gaishe da Umma ya wuce kitchen. Ya budai warmer din da ke tsakaniyar dakalin kitchen din sannan ya koma wurin cabinat ya bude ya dauko plate da fork ya wuce wurin warmes din ya bude ta biyun ya zuba sh¹¹uredded iris sannnan ya sa egg sauce.
Har ya dau plate din ya aje ya nufi wurin fridge ya dauko 2 egg daga crete din sa ya dawo ya dauko karamin bowl ya fasa eggs din ya dauko knife yayi dicing din oninons with ball pepper ya sa seasoning yayi wishking ya koma ya dauko pan ya wuce wurin cooker ya gasa kwian ya dora saman plate din ya hada coffe ya dau plate din a hannu daman sa, dayan kuma ya dau coffe din sa ya fito nan wurin su.
Yana karaso wa zai zauna Umma ta ce "Duk kwain da ke cikin sauce din bai ishe ka sai ka kara soya wani."
Ya ce "Umma 2 ne fah."
Umma ta ce "Koma nawa ne, aikin ku kawai ku ci ku kara gaba. Daman dazu shima Asif din ya soya na shi kai ma ka zo ka soya."
Asif ya ce "Daga ya ga na soya shima da kilbibi ya soya na shi."
Asim ya Harare shi kafin ya ce "Kai waye da za ayi gasa da kai. Mtsww."
Umma ta ce "Ni fah bana son wannan fadan na ku, shike nan ba ranar Allah da zata zo ba ku yi fada ba haba mana ku yi hankali bana shekara 28 kuna wani fada kamar yara ko Hamza da ke karamin ku bai yi.
Asif yace "Umma kin san yanda yake da hana wali sai shegan na ci."
Asim ya ce "Kai ni ka ke ce wa haka, zan farfasa ma baki, ka kiyaye ni. "
Umma ta ce "Ku dai ku ka sani."
Shiru na wani dakika kafin Umma ta ce "An kawo min karan ku kai Asif kai ne karami amma kullun kai ne da jan fada."
Asim ya ce "Sai kuma na taba yaro a ce ba haka ba bayan a san gaskiya."
Asif ya kyalkyale da dariya.
Umma ta kwabe Asif "Kai bana son shegantaka, miyasa jiya ka dau car key din sa kuma ka dawo ka dau nawa?
Asif ya ce "Ohh jiya ya zo ya na neman car key din sa bai gansa ba ya dora min laifi."
Umma ta ce 'Ay an ce min kai ka dauka."
Asif ya zaro ido yana ce wa "Wani na ukun ne ya gaya miki, mi zan yi da car key din sa?
Asim ya ce "Ni na san kai ka dauke shi dan haka ban abu na."
Asif yayi karamar dariya ya ce "Na ma kama da barawo."
Asim ya ce "Ka yi."
Jannat dai bin su ta ke da kallo tare da yin dariya ba tare da daya ya gan ta ba.
Umma ta ce "Toh kai ina ka je jiya ba ma jiya ba kwana biyu ina ka ke zuwa da dare?
Kafin ya bata amsa Asif ya ce "Wurin budurwar sa bana."
Jahillar harara Asim ya wulla masa. Umma kuma ta kalli Asim cikin mamaki har ma jannant da ta tashi zaune dan kwance ta ke saman kujera jin Asif ya ce budurwa ta tashi zaune ta dubi Asim.
Umma ta tambaya da mamaki "Wata mai sa'ar ce ko kuma biyullace irin ku ta ma koffi a zuciyar ka."
Asif ya ce "Ko daya."
Asim rai bace ya ce "Ka san Allah ka kara Magana a nan sai na basa ma baki."
Asif yayi dariyar kyeta yana ce wa "Ay na ga baka da bakin Magana sai na ari na ka."
Asim ya ce "Ka cigaba ka gani."
Umma ta ce "Kai Asif tashi ka wuce ka tafi aikin ka."
Asif ya ce "Umma kin manta yau satuday."
Umma ta ce "Ohh haka ne toh ka yi shiru ban son jin bakin ka ka bari wanda na tambaya ya ban amsa."
Ta dubi Asim tana ce wa fadi min wacece?
Ya ida shanye coffe din na sa ya aje cup din kafin ya ce "Umma kin ga har 10 tayi ban fita ba amma in sha Allah in na dawo za mu yi Magana daman na bari sai na dawo daga tafiyar sai na fada maki amma waccen dan tonan sirin mai zubar baki."
Umma tayi murmishi tana ce wa "Kun fi kusa."
Ya mike ya na cewa "Umma ni zan wuce."
Umma ta ce "Zo dawo ka dauke min plate din nan wa zai dauke ma."
Ya dubi jannat ya ce "Jannat dauke su." Daga haka ya wuce ya bar parlour.
Yana fita umma ta ce "Asif bani labarin yarinyar nan?
Yayi murmishi ya ce "A'a umma kun fi kusa da shi."
Ta ce "Ka da Allah ya sa ka fada min."
Ya ce "A'a Umma dan wlh kwana nan Asim kamar wanda ake wa wani ni dai bari na wuce kasuwa." Ya ida maganar yana mikewa.
Umma ta ce "Toh sai ka dawo."
Ya amsa da amin ya wuce.
Jannat ta dawo daga kai plate din kitchen ta nace wa "Umma su fa in dai za su yi aiki a kitchen in ka shiga sai ka ga ba yanda ka so ba, kwai kadai ya soya amma kin ga yan da ya bata kitchen din."
Umma ta ce "Sai ki gyara."
Jannat ta zauna ta nace wa "Ga dai binta chan za ta gyara."
Umma ta ce "Ke kin fi karfin gyara wa ke nan."
Ta girgiza kai kafin ta ce "Umma wai kunne na ya ji Asim na da budurwa."
Umma ta ce "Nima dai abin da mamaki ko da yake daman dole wata rana ya nemo matar shi, shi kuma Asif dan rawar kai ya kasa tsayawa ya zabi mace shi ne wacce shine waccen. Allah dai ya ba su ta gari kuma Allah baku mazaje na gari."
Asif ya wuce daki shima ya kimtsa har zai fita ya dawo ya budai wadrop ya dauko irin yadin da Asim ya sa ya chanza na jikin sa. Asim na ganin haka ya tube waccen ya dauko wasu ya sa shima.
Asif ya ce "Dadin abin dai iri daya sun fi yawa."
Asim yay tsaki ya budai locker sa ya duba kayan da Asif bai da irin su ya dauko ya sa duk da mostly in daya zai Dinka kaya yana yi wa dan uwan sa.
Ya dauko vent colour yadi ya sa.
Asif ya ce "Wai kai.. shi ke nan." Ya matso kusa da shi yana embarcing din sa ya ce"Haba Dude mi ne ne abin fushi bayan ka san every weekend our outfit is the same.
Asim ya ce "Bana san irin haka ka dai na min irin wasan nan."
Asif ya ce "Okay na ji na dai na."
Asim ya ce "Allah sa da gaske." Ya ida maganar tare da kai hannun sa saman wuyan rigar ya cire kayan ya dauko irin kayan Asif din ya sa suka yi combing gashin su kowa ya sa hula hular ma iri daya ba abinda ya chanza suka fito su ka iske Abdullahi a parlourn murmishi kawai yayi masu.
Suka wuce part din Umma suka mata sallama ta masu addu'a sannan su ka wuce bayan sun wuce Umma ta tabo jannant ta na nuna su.
Bayan sun fita Umma ta ce "Kin ga biyullen nna yanzu suka gama fada kamar ba an shirya ba amma ji ko 30 minute ba ayi ba sun shirya."
Jannat tayi murmishi ta na cewa ka su dai a ke ji.
Baranda suka wuce suka ga ayan da zai shigo ciki Asim ya bashi wayar sa ya masu hoto sannan suka wuce kasuwa a motar Asif.
Da yamma bayan sun tashi a kasuwa suka yi sallah magriba da ganan ya wuce da su gidan su Halimatu kasancewa shi ke tuki.
Asif ya dubai shi tare da tambayar shi ina kuma za muyi.
Asim ya ce "Zuwa zan yi in saida ka in huta da takurar ka."
Duka suka yi dariya. Asif ya ce "Toh shi ke nan muje ka sai da ni nima sai na huta da kai."
Asim yayi murmishi ya cigaba da tuki. Bayan wasu dakiki yayi parking. Ya na parking Asif ya dubai shi ya ce "Ohh na gane yau ka kawo ni wurin ta ko kai fa."
Bai ba shi amsa ba ya budai kofar ya fita shima Asif ya fito ya rufe kofar suka shiga cikin lungun gidan su.
Suna kan tafiya Asif na dubai dubain layin kasancewa da sauran hasken gari bai ida duhu ba yana mamakin mi dan uwansa ya gani a wurin Halimatu da zai so ta, amma ko da yake an ce zuciya ba ta da kashi. Haka ya cigaba da sake sake a zuciyar sa har suka isa.
Asim ya tura yaro kamar kullun ya shiga ciki, ya isar da sakon yau ita ta amsa shi ya wuce.
Kafin ta fito Huzaifah ya karaso yayi mamakin ganin su biyu.
Ya tsugunnan ya gaishe su. Suka amsa. Daga nan Asim ya bashi hannu su ka yi musabaha tare da tambayr shi ya yake.
Huzaifah ya amsa "Ina lfy, rankayadadai wannan dan'uwanka ne?
Asim ya dubi Asif ya ce "A'a dan biyu na ne."
Huzaifah ya saki baki yana kallon Asif wanda sai yanzu yaga kamar ta su har ta baci dan da farko bai kalli fuskarsa ba kasancewa ya sadar da kansa. Yana so ya tabbatar wa kan sa Asim biyu ne ko kuma mutane daban daban ne."
Sallamar halimatu ta dagatar da shi da sauri ya juyo ya kalle ta yana ce wa "Halima kalla yan biyu masu kama."
Karamin murmishi ta mashi tare da ce wa wuce ciki. Ya gyada mata kai sannan yayi masu waeving bye. Asim ya mayar mashi.
Bayan shigar shi ta gaishe su suka amsa sannan Asim ya ce "Yau dai gani ni da dan'uwana."
Asif ya ce "Kullun ana ban labarin ki nace ya kawo ni in ga macen nan mai sa'a."
Karamin murmishi ta mashi kafin ta ce "Sannun ka da zuwa."
Asif ya ce "Sannu mai sunnan Umma."
Asim ya ce "Huzaifah na mamakin ganin mu."
Asif ya ce "Kamar ya kasa yarda da abin da idon sa ya gani."
Halimatu ta ce "Toh ay kamar ta ku ta baci, sai wanda ya san ku zai iya gane ku."
Asif ya ce "Ay ke kin samu za ki iya ganai mu."
Ta ce "A'a ni ba zan iya ganai ku ba."
Asif ya ce "Ay kuwa zaki iya tin da kina rike da zuciyar dan uwana."
Harara Asim ya wulla mashi duk da akwai duhun dare. Asif ya ce "Toh yanzu tin da mun sa kaya irin daya sai ki banbance mu."
Asim ya ce "Dude koma mota tin da yar kure ka zo yi."
Asif ya ce "A'a shi ke nan ni zan koma mai sunnan Umma."
Halimatu ta ce "A'a ya zaka tafi ana fira."
Ya ce "Ay ba a bukata ta a nan."
Ta ce "waya ce ma."
Asim ye ce "Kai koh.."
Asif yayi karamar dariya ita kuma tayi murmishi. Asim ya ce "Toh naji yanzu ina wayar ki?
Tayi alamar tambaya.
Ya ce "Wadda na siya maki."
Ta amsa shi "Tana ciki."
Ya ce "Good yanzu ki je ki dauko ta in ki ka fito ba tare da mun yi Magana ba sai ki banbance mu."
Tayi karamar dariya tana ce wa "Ni taya zan iya banbace ku ga duhun dare."
Asif ya ce "A'a ay zaki haska da torch din wayar."
Ta ce "Ba zan iya ba."
Asim "Ya ce kin ga jiya kin ban task I completed it, now is your turn."
Ta ce "Tin da kunna ce a kan haka." Ta juya ta koma ciki.
Ta na shiga Asif ya ce "Dude har waya ke nan ka siya mata, dagaske dai auren ta za kayi."
Asim ya ce "Ba auren ta zan yi zan tsaya bata lokaci na ay bata lokaci na bar maku tin da ku yan wahalane ku ta bata lokaci kun san ba auren mutun zaku yi ba."
Halimatu na shiga ciki Huzaifah ya tarbe ta da ce wa "Halima wai yan biyune ko kuma shi ya zo a kala biyu irin na film?
Nusaiba ta ce "Kai dai huzaifah sai a hankali tin dazu ake ce ma yan biyu ne masu kama daya."
Halimatu ta amsa shi da "Eh" ta wuce cikin daki ta dauko ledar wayar ta budai kwalin ta ta dauko ta ta kunna ta, Asee mai bi ma huzaifah wadda da ga ita sai shi, ta biyo ta dakin. Halimatu zata mike ta ce "Halima in zo mu je tare nima in gan su??
Halimatu ta amsa ta da "A'a." ta nufi kofa.
Asee…