Chapter 24
Jikin Ma'u ya ɗauki rawa, ta fara girgiza kai tana kallonsa cikin tashin hankali.
A hankali ya shiga cikin ɗakin ya tsaya a kanta yana ƙare mata kallo, ya mayar da dubansa ga Inna ya ce "Inna abin da kunnuwana suka ji kin faɗa da gaske ne?"
Ajiyar zuciya ta sauke, cikin damuwa ta ce "Gadanga ban tabbatar ba, sai dai duk wasu alamu da suke nuna hakan na gane su a tattare da ita, shi ya sa hankalina ya tashi na tsare ta ina tuhumarta, wallahi Gadanga ina tsoron abin da nake gudu in bashi ne ya faru ba, ina fargabar a ce azzaluman mutanen nan zun taɓa yarinyar nan." Da sauri Ma'u ta girgiza kanta tana kuka ta ce "Wallahi Inna, na rantse da girman Allah babu abin da suka yi mini, wallahi bayan mutum ɗaya da ya mare ni a cikinsu babu wanda hannunsa ya taɓa jikina." Aliyu ya kalli agogon hannunsa ya ga ƙarfe goma na safe, ya mayar da dubansa ga Ma'u ya ce "Ɗakko hijabanki biyo ni." Daga haka ya fice daga ɗakin, tashi ta yi kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, ta ɗauki wani cakuɗaɗɗen hijabinta ta ta saka, sum-sum tabi bayansa. Shiru Inna ta yi tana tambayar kanta to me ya kawo wannan canjin a jikin Ma'u? Ta san tunda har ta rantse tabbas babu babu abin da suka yi mata. "To amma me ya kawo mata wannan sauyin?" Ta sake tambayar kanta.
Wata ƙaramar asibiti dake wajen gari ya je da ita. Suna zaune a gaban likita bayan ya gama yi mata gwajin ciki, ɓaro-ɓaro sakamakon ya bayyana tana ɗauke da juna biyu har na tsawon watanni uku. Tunda Ma'u ta ji abin da likitan ya faɗa ta fara kuka, domin ta san yau Yaya Aliyu kashe zai yi. Wani mugun kallo Aliyu ya yi mata, muryarsa babu alamar sauƙi ya ce "Ta tashi su tafi gida."
....
Daga gidan Momy har na su Mammy ɗinke yake da jama'a ƴan zaman makoki, tunda aka yi rasuwar nan fuskar Zahra a kumbure take saboda kuka. Gabaɗaya Sudais ya kasa cin abinci, yau da safe Mammy ta lura da bai fito ba, da kanta ta same shi a part ɗinsa ta dinga rarrashinsa. Da ƙyar ta samu ya sha tea kaɗan, ta ce masa "Ya yi haƙuri ya tashi ya shirya ya fita wajen zaman makoki." Ya jinjina mata kai. Tana fita kiran Zuhura ya sake shigowa wayarsa. Kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ɗauka ya kara a kunnensa ba tare da ya yi magana ba. Muryar a sanyaye ta yi masa sallama, bayan ya amsa ne ta yi masa gaisuwa, godiya ya yi mata, har za ta kashe wayar ta ji ya ce "Zuhura ranar kin ce kin haɗu da wata mai kama da ni ko? A ina kika haɗu da ita?" Sai da gabanta ya faɗi da jin tambayar da ya yi mata. Kuma ta yi mamakin me ya sa ya yi mata tambayar a cikin wannan halin da yake ciki.
Ta ce "Amm a hospital ɗinmu ne ganta, ita da wata matashiyar budurwa da kaɗan ta girme ta, kuma abin mamaki hadda ɗayar tana da yanayi da kai, sai dai ita wadda make ba ka labari tafi kama da kai sak."
"Ok thanks" daga haka ya kashe wayarsa yana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihim raji'un." Dafe kansa ya yi, ya furzar da iska mai zafi, ya so ya tambaye ta me suka je yi a asibitin? Amma gudun kar ta yi zancen da wani ya sa shi yin shiru, tuna ya yi lokacin da Zuhura ta ce masa ta ga mai kama da shi, date ɗin daidai ne da ranar da suka je gidan Momy. Lokaci ɗaya idanunsa suka ƙara canza launi, a hankali ya tashi ya shiga ban ɗaki ya sakarwa kanshi ruwa.
.....
Durƙushe take a tsakiyar ɗakin, kanta na kallon ƙasa tsabar firgicin da take ciki ya hana ta ɗago da kanta ta kalli mutanen dake ɗakin, jikinta na rawa kamar wadda aka jefa ta cikin ruwan ƙanƙara. Hawaye na kwarara a cikin idonta babu ƙaƙƙautawa, gabaɗaya sun jiƙa cakuɗaɗɗen hijabin dake jikinta. Wani irin sautin kuka take yi mai firgitarwa da taɓa zuciyar mai sauraro, kallo ɗaya za ka yi mata ka san ba ta cikin nutsuwarta. Cikin buɗaɗɗiyar muryarsa ya daka mata tsawa "Dan ubanki ba za ki daina wannan kukan ba ki yi mana bayani?" Ya yi maganar cikin tsananin ɓacin rai da fushin zuciya. Sake fashewa ta yi da wani irin kuka mai tsuma zuciya, ta kasa magana. A hankali ta ɗago da rinannun idanunta tana kallonsu, haɗe hannayenta guri ɗaya ta yi alamar neman afuwa. Ganin ba za ta yi magana ba ya sa a fusace ya sake cewa "Idan ba ki gaya mini gaskiya ba yanzu nan zan murɗe miki wuya ki mutu kowa ma ya huta, kuma wallahi idan kika yi mini ƙarya sai na yi gunduwa-gunduwa da namanki a gurin nan".
Numfashinta har tashi sama yake yi tsabar tashin hankali da take ciki, "Yaya don Allah ku yarda da ni." Ta yi maganar muryarta na rawa, wani sabon kukan na sake ƙwace mata, sannan ta ci gaba da faɗin "Wallahi ban san yadda aka yi haka ta faru ba, Allah shi ne shaidata ban taɓa aikata zina ba, kuma ban taɓa sanin wani ɗa namiji ba, Mama ban taɓa ba…" Tsawar da Aliyu ya daka mata ne ya sa ta yin shiru ba tare da ta shirya ba. "Asma'u, idan na sake tambayarki ba ki faɗa mini gaskiya ba wallahi sai na lahira ya fiki jin daɗi, dan ubanki shi cikin a ruwa kika sha shi?".
"Innalillahi wa'inna ilaihim raji'un, Allah kai ne Allah. Ya Ubangijin jin ƙai da rahama, Allah ka dube ni ka ɗauki rayuwat...." Ba ta ƙarasa maganar ba ta ji saukar tagwayen mari a kan fuskarta, ganinta ne ya ɗauke na wucin gadi. Aliyu ya kwance bel ɗin wandonsa zai duke ta da sauri Inna ta riƙe shi tana kuka mai cin rai. "Inna don Allah ki rabu dani in kashe ta, me ye amfanin rayuwar Asma'u? Muna zamanmu hankali kwance ta je garin neman maganarta ta ɗakko mana abin kunya, kuma tsabar rainin hankali take cewa ba ta san yadda aka yi ba".
Zaunar da shi Inna ta yi, ta dube shi da kyau ta ce "Gadanga ina tunanin kafi kowa sanin halin Ma'u, sannan ka san abin da za ta iya aikawa da wanda ba za ta iya ba, ba wai ina kare ta ba ne, ko kuma ina goyon bayanta ba. A matsayina na mahaifiyarta na san Ma'u ba za ta taɓa aikata wannan ɗanyen aikin ba, wallahi ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba Ma'u ba za ta aikata zina ba, zan iya yarda a ce mini tana doke-doken yaran mutane ko ta yi wata tijarar saboda rigimarta amma ban da wannan abin. Sai dai ina cikin ruɗani da tashin hankalin yadda aka yi aka haihu a ragaya. Ina mamakin yadda ciki ya iya bayyana a jikinta, kowa ya san a garin nan Ma'u ba ta hulɗa da maza, babu ruwanta da maza. Ba ta dogon yawo sai in aiken ta aka yi, ko za ta je makaran..." "Na sani Inna! Inna na san da haka, to amma ya aka yi ciki ya bayyana a gare ta a matsayinta na budurwa wadda ba ta taɓa yin aure ba?" Aliyu ya katse Inna da tambaya.
"Wannan shi ne abin da na ke son sani da fahimta, amma wallahi Gadanga Ma'u ba za ta taɓa aikata zina ba". Cewar Inna tana sake rushewa da kuka.
"Ke dan uwarki ki yi mana bayanin yadda aka yi kika samu ciki?". Aliyu ya faɗa yana kallon Ma'u fuskarsa tamau babu alamar tausayi a tattare da shi.
"Wallahi Allah Yaya ban sani ba". Tashi ya yi da ƙarfi ya tunkare ta gadan-gadan. "Ka da ka taɓa ta Gadanga." Cewar Inna tana kallon fuskar Ma'u, cikin damuwa ta ce "Taso ki zauna a kusa da ni."
Tashi ta yi da ƙyar ta isa bakin gadon ta zauna, Inna ta dube ta da kyau ta ce "Ma'u, ki dubi girman Allah, ki tausaya mana ki gaya mana gaskiya, kin ce azzaluman mutanen can ba su taɓa ki ba, kuma wallahi tunda har kika rantse a kan hakan na yarda da basu taɓa kin ba, domin da sun taɓa ki ba za ki ɓoye ba har ki saka kanki a cikin wannan ƙangin ba, sai dai ina mamakin ta yadda aka yi ciki ya bayyana a jikinki har na watanni uku. Idan ban yi kuren lissafi ba watanni uku kenan da faruwar waccan abin, Ma'u ki sanar damu gaskiyar abin da yake faruwa. Waye ya yi miki wannan abin?" Cikin kuka ta sake nanata musu cewar ƴan ta'addan nan basu yi mata komai ba.
A harzuƙe Aliyu ya ce "Inna don Allah ki bari in wujijiga yarinyar nan, wannan sako-sakon da kike yi mata ne ya sa take yi wa mutane yawo da hankali, idan ba can ta samo shi to a ina ta same shi?" Ya yi maganar yana kallonta.
Shiru ta yi, ta kasa magana, Inna ta ce "Ke muke saurare"
"Inna ni ma ban san yadda aka yi cikin ya samu ba, don Allah ku yi haƙuri, ku yi mini addu'a, ni mutuwa ma zan yi kowa ya wuta."
"Ai da za ki mutum a yanzu ba ƙaramin farin ciki za mu yi ba!" Cewar Aliyu ya fita ya bar ɗakin a fusace, domin idan ya tsaya takaici ne zai kashe tunda Inna ba bari za ta yi ya hukunta ta ba.
.....
Sosai Momy ta shiga cikin damuwa, ta rame, duk ta keɓe ita kaɗai sai ta yi kuka ba na wasa ba, tsahon tabon dake zuciyarta na shekaru huɗu da suka wuce ya taso ya haɗe mata da mutuwar Ilham, gabaɗaya ta dawo wata iri kamar ba ita ba. Dady ma ƙoƙari ne yake yi da nuna jarumta, amma ba ƙaramar damuwa yake ciki ba.
Saddik da ya samu labarin rasuwarta shi kansa ya shiga cikin damuwa sosai. A haka dai har aka yi sadakar bakwai.
Sudais ya ƙara zama shiru, ko kaɗan baya son hayaniya, mutuwar Ilham ba ƙaramin dukansa ta yi ba, bai taɓa tunanin ya damu da ita har haka ba sai yanzu da ba ta raye, idan ya zauna baya da aiki sai tunanin kyawawan halayenta, da yadda take haƙuri da shi. Daidai da rana ɗaya ba ta taɓa nuna fushinta akan abin da yake yi mata ba. Ya ɗaukarwa kan shi alwashin sai bibiyi wane irin magani ne aka ba ta a asibitin nan ta sha da har ya yi sanadiyar rasa ta da kuma abin da yake cikinta.
....
Sati ɗaya kenan, Aliyu ya daina shiga harkar Ma'u, ya daina yi mata magana. Idan ta gaishe shi baya amsawa, daga ƙarshe ma ya yi mata gargaɗi akan idan ta sake yi masa magana sai ya yi mata tsinannen duka.
Inna ta zubawa sarautar Allah ido, tunda daga ranar ba ta sake tambayarta waya yi mata cikin ba, sai dai tana cikin tsananin damuwa, da tunanin idan jama'a suka farga da cikin nan me za su ce? Wane irin kallo za a yi wa Ma'un? Duk da ta san da yawa za su alaƙanta cikin da abin da ya faru da ita. Ma'u ba ƙaramar azaba take sha ba, laulayi sosai cikin nan ya zo mata da shi, komai ta ci sai ta amayar da shi, gabaɗaya ta rame, ta yi haske sosai.
Ku yi haƙuri da wannan ba yawa ba na jin daɗi ne