BABI NA ƊAYA — M-ARROW
Abuja
Katafaren fili ne da ya ƙunshi wani babban ɗakin taro na musamman mai suna The V.I.P. Imperial Conference Hall. Wuri ne da aka tsara daki-daki cikin tsarin zamani, cike da dukkan manyan kayan more rayuwa da fasahohin da suka dace da tarukan manyan shugabanni da attajiran duniya.
Daukacin mutanen da ke cikin zauren taron sun maida hankalinsu gaba ɗaya kan wata katafariyar na'urar sadarwa ta zamani da ke manne a bangon gabashin ɗakin, wato The Smart Interactive Holographic Display.
A gabanta kuwa, Comrade Aliyu A. Manga, The Deputy Director of Human Rights Commission, ya tsaya daram cikin cikakkiyar ƙwarewa, yana gabatar da bayanai masu cike da hujjoji da ƙididdiga. Yana nuna bayanai da yatsansa a kan holographic display ɗin, yana bayyana yadda sabon tsarin zai gudana da kuma amfanin da zai haifar wa al'umma.
A gefe guda kuma...
Shi yana zaune cikin zallar ƙasaita da cikakkiyar nutsuwa.
Ya jingina faffaɗan bayansa da lallausar kujerar fata ta alfarma, yana ɗan lila jikinsa a hankali. Lokaci zuwa lokaci yana juyawa kaɗan hagu da dama, kamar wanda babu abin da ya dame shi.
Ƙafarsa ɗaya tana kan ɗaya.
Idanunsa kuma a lumshe suke, tamkar mai barci.
A tsakanin dogayen yatsunsa masu ƙarfi kuwa, yana sarrafa wani tsadadden Golden Executive Pen, yana juyawa cikin natsuwa kamar wani abu da ya saba yi.
Duk da cewa idanunsa a rufe suke, babu kalma ko guda daga cikin bayanan da ke kubuce masa.
Kowace magana...
Kowace hujja...
Kowace gardama...
Duk suna shiga kunnuwansa daki-daki.
Sai dai duk mai lura da yadda jijiyoyin wuyansa suka fito suka miƙe, da yadda yake matse muƙamuƙansa lokaci zuwa lokaci, zai fahimci cewa ba kwanciyar hankali ne ke lullube shi ba...
A'a.
Wani irin tafasasshen fushi ne da ke ci gaba da taruwa a zuciyarsa, yana jiran lokacin da zai balle.
Ba zato ba tsammani...
Ɗaya daga cikin manyan attajiran kamfanoni ya miƙe tsaye cikin isa da nuna ƙarfin iko. Ya zaro idanu, sannan ya katse bayanin da Comrade Aliyu A. Manga yake yi.
Cikin kakkausar murya ya ce:
"What kind of nonsense policy is this? Me ake nufi da wannan tsarin? Bayan mun riga mun sauke farashin kayayyakinmu a baya, yanzu kuma ana so mu sake rage wani sabon farashi? No! This is absolutely impossible! Idan manufarku ita ce ku kassara kamfanoninmu, ku durƙusar da tattalin arziƙinmu, then forget it! Ba za mu taɓa amincewa da irin wannan tursasawar ba. If the poor can't afford our products, let them work harder and make more money. Amma mu kam ba za mu yi asarar biliyoyin Naira saboda wani sentimental decision ba!"
Da jin waɗannan kalamai masu cike da raini da rashin mutunci, Comrade Aliyu ya dakatar da bayaninsa.
A hankali ya juya ya kalli mutumin.
Sai dai kafin ya yi magana...
Idanunsa suka sauka kan mutumin da har yanzu yake zaune cikin nutsuwa.
Har yanzu idanunsa a lumshe suke.
Amma kallo ɗaya kacal da Aliyu ya yi masa...
Sai ya ji ƙirjinsa ya buga da ƙarfi.
Dum!
Dum!!
Tsagwaran fushin da ke kwance a kan kyakkyawar fuskarsa ya isa ya firgita kowane mutum mai hankali.
Ba hayaniya yake yi ba...
Ba ihu yake yi ba...
Amma irin shurun nan nasa ya fi kowace irin hayaniya razanarwa.
Hayaniya ta mamaye ɗaukacin ɗakin taron.
Kowane attajiri na ta bayyana rashin amincewarsa da sabon tsarin.
Wasu na bugun tebur.
Wasu na ɗaga murya.
Wasu kuma na musayar zafafan kalamai.
Sai dai...
Ba su san cewa a wannan lokacin sun riga sun taka layin da bai kamata su taka ba.
Cikin wani irin motsi mai cike da ƙarfi da kwarjini...
Ya miƙe tsaye lokaci guda.
Daram!
Tsayuwar da ya yi kaɗai ta isa ta sanya gaba ɗaya ɗakin taron ya yi tsit.
Tsayuwar namiji cikakke.
Dogon mutum.
Faffaɗan kirji.
Jiki irin na jarumin dakarun musamman.
Kafin wani ya kai ga ɗaukar numfashi...
Ya ɗaga damtsen hannunsa.
Wani gigitaccen naushi ya sauka a tsakiyar katafaren teburin taron.
Ji ka ji...
DUUMMMM!!!
Wani irin amon gigitaccen naushi ne ya kaure cikin ɗakin taron, har ya girgiza ilahirin The V.I.P. Imperial Conference Hall.
A take, katafaren teburin da aka ƙera da tsadadden katako na musamman—wanda kuɗinsa ya kai miliyoyin Naira—ya tsatstsage gida biyu, ƙananan ɓangarorinsa suka watse a kan tebur da ƙasa.
Sautin fashewar katakon ya gauraye da amo mai razanarwa, wanda ya sanya gaba ɗayan zauren taron yin tsit, tamkar an datse numfashin kowa.
Idanun manyan attajiran da suka cika ɗakin suka zaro lokaci guda.
Wasu suka zabura daga kujerunsu.
Wasu kuma suka ji wani irin sanyi mai haɗe da tsoro yana ratsa ƙasusuwansu.
Ba don sun ga ya bugi teburin ba...
Sai don sun fahimci irin ƙarfin da ke ɓoye a cikin mutumin da ke tsaye a gabansu.
A hankali ya ɗaga dogon yatsansa na dama.
Ya shiga nuna su...
Ɗaya bayan ɗaya...
Kowanne cikin idanu.
Fuskarsa babu ko ɗigon murmushi.
Babu alamun sassauci.
Sai wata irin tafasasshiyar fusata da ke bayyana a kan kyakkyawar fuskarsa mai cike da kwarjini da kamalar jinin sarauta.
his striking amber eyes masu haske suna yawo daga fuska zuwa fuska.
Duk inda idanunsa suka sauka...
Zuciyar wanda suke kallo sai ta buga da ƙarfi.
Cikin wata murya mai zurfi, sanyi, amma cike da ikon da ya sa ƙashin bayansu yin sanyi, ya fara magana a hankali, sautin na fita da kauri.
"Listen carefully... this is my final warning."
Ya ɗan dakata.
Sannan ya ci gaba cikin kakkausar murya.
"Duk kamfanin da aka sake kama yana cutar da al'umma ta hanyar ƙara farashi ba bisa ƙa'ida ba, I will personally order the immediate seizure of that company. Ba zan yi ƙasa a gwiwa ba. This is not a threat... it is a promise."
Ya sake nuna su da yatsansa.
"Don't ever make the mistake of testing my authority. Kada wani ya sake sa ni na juyo ta kansa. Because the consequences... will be beyond your imagination."
Kalaman nasa ba su da yawa...
Amma nauyinsu ya fi na bindiga.
Ya sauke hannunsa a hankali.
Sai kuma ya juya cikin zafin nama.
A yayin da zai taka gaba...
Sai ya jefa wata irin zabgegiyar harbi da ƙafarsa zuwa kujerar da yake zaune a kai.
Kujerar ta tashi sama tamkar ƙwallo.
Ta haye sama na ɗan lokaci kafin ta bugi katafaren bangon gilashin da ke bayansa.
Gilashin zamani mai kauri ya watse caca-caca.
Ƙananan gutsattsarin gilashi suka watse ko'ina cikin ɗakin.
Wani irin shiru ya mamaye wurin.
Babu wanda ya kuskura ya motsa.
Babu wanda ya kuskura ya yi magana.
Kowa ya tsaya cak...
Yana kallon mutumin da ke tsaye a gabansu tamkar ba ɗan adam ba ne.
Wasu daga cikin attajiran suka dafe ƙirjinsu.
Wasu kuma suka haɗiye yawu da ƙyar.
A wannan lokacin ne suka fahimci cewa ikon M-ARROW ba ya tsaya kan mukami kawai...
Har da hali.
Har da ƙarfin zuciya.
Har da ikon aiwatar da abin da ya faɗa.
Ba tare da ya sake waiwayensu ba...
Ya juya ya nufi ƙofar fita.
Takunsa masu ƙarfi suna amsa amo cikin ilahirin ɗakin taron.
Tap... Tap... Tap!...
Kowane taku nasa yana ƙara sanya tsoro cikin zukatan waɗanda ya bari a baya.
Yana tafiya yana gyara necktie ɗinsa da hannunsa ɗaya, yayin da fuskarsa ke nuna cewa har yanzu wutar da ke tafasa a zuciyarsa ba ta lafa ba.
yana isa bakin ƙofar fita...
Daukacin jami'an tsaronsa, sanye da baƙaƙen suit, riƙe da manyan makamai na zamani, suka miƙe lokaci guda.
"Good afternoon, Sir!"
Duk suka faɗa cikin murya ɗaya tare da kamewa.
Ko kallonsu bai yi ba.
Ya wuce kai tsaye.
Jami'ai biyu suka yi saurin rigarsa, suka buɗe masa ƙofar motarsa ta alfarma.
Ya shiga ciki cikin ƙasaita ba tare da ya waiwaya ba.
Nan take direba ya zauna a mazauninsa.
Wani jami'in tsaro ya shiga kujerar gaba.
Sauran motocin tsaro biyu suka ɗauki matsayinsu; ɗaya a gaba, ɗaya a baya.
Cikin daƙiƙu kaɗan...
Ayarin motocin ya fice daga The V.I.P. Imperial Conference Hall cikin tsari irin na shugaban ƙasa, yayin da fitilun motocin ke walƙiya, suka bar ɗaukacin attajiran cikin tsananin fargaba da tashin hankali.
A cikin mintuna kaɗan...
Ayarin motocin ya isa ƙofar Shadum Estate.
Tun kafin motocin su ƙaraso bakin The Main Arrow Gate, katafaren get ɗin alfarma ya riga ya gano motocin ta hanyar Advanced AI Security Scanning System.
Na'urorin tantancewa suka fara aiki cikin daƙiƙu kaɗan, suka tabbatar da sahihancin motocin, sannan ƙofar ta buɗe kanta kai tsaye ba tare da wani jami'i ya taɓa ta ba.
Ayarin motocin ya kutsa ciki cikin tsari.
Shadum Estate ba Estate ba ne na yau da kullum.
Daula ce.
Wani katafaren birni ne da aka gina a cikin Abuja domin mutum ɗaya.
Jami'an tsaro kala uku ne ke gadinsa dare da rana.
A get na farko akwai dakarun sojoji masu cikakken shiri.
A mataki na biyu kuwa, Mobile Police Special Unit ne ke sintiri da manyan makamai na zamani.
Sai kuma mataki na ƙarshe...
Dogarai masu jinin sarauta, sanye da kayan gargajiya masu matuƙar kima, suna tsaye kyam tamkar mutum-mutumi.
Su ne masu tsaron ainihin cikin gidan.
A tsakiyar Estate ɗin akwai wani katafaren roundabout, wanda aka kawata da tsadaddun furanni da bishiyoyin ado daga ƙasashe daban-daban.
Ko kallon wurin kaɗai...
Ya isa ya sa mutum ya manta cewa yana Najeriya.
Motocin suka zagaya roundabout ɗin cikin ƙwarewa, suka nufi katafaren Luxury Parking Lot, mai ɗaukar sama da motoci hamsin lokaci guda.
Direban bai ma gama daidaita parking ba...
M-ARROW ya buɗe murfin motar da ƙarfi.
ya zuro kafafunsa duka biyu a tare ya yi wani irin durowa gami da mike tsaye daram yadda.
yadda ya yin zai tabbatar maka da cewa jarumi ne na gaske.
Har yanzu kyakkyawan fuskarsa yana ɗauke da zafin fushin da bai huce ba.
Michael, shugaban jami'an tsaronsa, ya yi saurin fitowa.
Sai dai da ya ga oga ya fito kafin parking ya kammala...
Ya fahimci abu ɗaya.
"The Boss is still extremely angry..."
Bai kuskura ya yi magana ba.
Sai kawai ya bi bayansa cikin nutsuwa.
M-ARROW ya nufi wata hanyar sirri da ke bayan katafaren ginin.
A cikin daƙiƙu kaɗan...
Ya shiga wani katafaren Private Duplex Wing, wanda ba kowa ke da damar shiga cikinsa ba sai shi kaɗai.
Da ya kutsa ciki ta bayan ginin...
ya bayyana a bayan wani katafaren falon alfarma.
Falon ya ƙunshi haɗaɗɗun kujeru na musamman da aka ƙera na musamman daga ƙasashen Turai.
One-Way Bulletproof Glass ne ya raba inda yake da babban falon.
Mutanen da ke cikin falon ba za su iya ganinsa ba.
Amma shi...
Yana ganin komai da ke faruwa.
Ma'aikatan gidan suna ta gudanar da aikinsu cikin natsuwa.
Ba wai saboda akwai ƙura ba.
A'a.
Hasali ma komai na cikin falon yana walƙiya tamkar yanzu aka fito da shi daga masana'anta.
Kai tsaye ya ƙarasa gaban katafaren Royal Staircase.
Ba tare da ya rage gudu ba...
Ya riƙa haɗa matakala bibbiyu.
Har ya isa bene na sama.
...
(Ya Ilahi! Ni Rasheedat S Director, anya kuwa yau ban bi mutumin da ya fi ƙarfina ba ni? Masoya, wallahi na fara zargin ba a duniyar mutane nake ba. Da ace a gidan su Feeryal nake, da tuni na rantse aljanu ne suka yi garkuwa da ni suka kawo ni ƙasarsu! 🤣🤣 Amma ai na rantse sai na kawo muku rahoto tass! Ko zan suma, ko alkalamina zai karye, ni kam sai na gano abin da wannan bawan Allah yake ɓoyewa. Ku dai ku riƙe hannuna sosai, domin ni kaina idan na yi kuskuren kallon wani ɓangare na wannan gida na biyu, zan iya manta abin da na zo yi!🙌😂)
Ya isa gaban wata ƙofa mai matuƙar ƙyalli.
Na rantse...
Har na kasa tantance ko gilashi ce...
Ko zinariya...
Ko kuwa wata fasaha ce da ban taɓa gani ba.
Ya ɗora tafin hannunsa.
Click!
Ƙofar ta buɗe cikin nutsuwa.
Ya shiga.
Masoya...
Da na ɗaga ido...
Sai na ji numfashina ya tsaya!
Wallahi ba zan iya kwatanta muku abin da idanuwana suka gani ba.
Master Bedroom ɗin nan...
Ba ɗakin kwana ba ne.
Tamkar wani Royal Presidential Suite ne na gidan sarautar da ba a taɓa nuna wa duniya ba.
Na yi saurin gyara riƙon alkalamina.
Na kuma tunatar da kaina cewa...
"Rasheedat, ba yawon buɗe ido kika zo yi ba... rahoto kika zo ɗauka!" 🤣
M-ARROW kuwa bai tsaya kallon komai ba.
Kai tsaye ya isa bakin makeken gadonsa.
Ya ɗauki laptop ɗinsa.
Sannan ya buɗe wani drawer na sirri.
Ya fito da wasu classified files masu matuƙar muhimmanci.
Daga nan...
Ya juya.
Ya fice daga ɗakin kamar yadda ya shigo.
Ba tare da ko mutum ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ya san ya shigo ko ya fita ba.
Da fitowarsa daga cikin sashin, ya sake bi ta hanyar sirrin da ya shigo tun farko.
Har ya fice daga katafaren ginin gaba ɗaya...
Ba tare da mutanen da ke cikin babban falon sun san cewa ya taɓa shigowa ko fita ba.
Iya ma'aikatan da ke gudanar da ayyukansu a farfajiyar Shadum Estate ne kawai suka hango gilmawar wucewarsa.
Tun kafin ya ƙaraso Luxury Parking Lot...
Jami'an tsaro suka ruga gare shi cikin ladabi da girmamawa.
Ba tare da ya ce komai ba, suka karɓi Laptop ɗin da kuma Classified Files ɗin da ke hannunsa.
Michael kuwa ya riga ya buɗe masa ƙofar motar.
M-ARROW ya shiga ciki cikin ƙasaita, ya zauna ba tare da ya waiwayi kowa ba.
Michael ya karɓi laptop ɗin da fayilolin daga hannun sauran jami'an, ya shirya su cikin tsari a gefensa, sannan ya rufe murfin motar cikin sauri.
Shi ma ya zagaya ya shiga kujerar gabansa.
Direba ya tayar da motar...
Ayarin motocin ya sake fita daga Shadum Estate cikin cikakken tsari.
Motar M-ARROW tana tsakiya.
Motar jami'an tsaro ɗaya na gaba.
Ɗaya kuma na baya.
Blue lights ɗinsu na walƙiya yayin da suke yanke titi cikin matsanancin gudu.
M-ARROW ya sake jingina bayansa da kujerar fata ta alfarma.
Ya lumshe idanunsa.
Har yanzu kuma...
Fushin da ke cin zuciyarsa bai ko ɗan lafa ba.
A cikin motar shiru ne ya mamaye komai.
Sai sautin injin motar da kuma gudun da suke fesa wa a kan titin Abuja.
Can...
Wayarsa ta alfarma VERTU Agent Q Supreme ta shiga ruri.
Wata sassanyar ƙarar ring tone mai matuƙar daɗin ji ta cika cikin motar.
Kiran farko...
Ya ƙare.
Ko motsi bai yi ba.
Kiran na biyu...
Shi ma ya ƙare.
Har yanzu idanunsa a lumshe suke.
Kiran na uku ya sake shigowa ba kakkautawa.
Michael ya ɗan waigo cikin girmamawa.
Ya rage muryarsa ƙasa sosai.
"Sorry, Sir... your phone is ringing."
Ya san sarai cewa oga ba mutum ba ne mai son hayaniya ko yawan magana.
Musamman idan yana cikin irin wannan yanayin.
Saboda haka, bai ƙara cewa komai ba.
Shi kuwa mai kiran...
Ya ci gaba da sake kira.
Amma M-ARROW bai motsa ko da yatsarsa ba........!
Wannan mutumin ba zan sake kallonsa da ido ɗaya ba idan akwai idon da yafi biyu to da shi zan rika kallon sa! 😂😂
Ku riƙe hannuna sosai, domin labarin yanzu ne yake fara nuna mana ainihin FARASHIN RAYUWA! 🔥📖
Muje zuwa Fans wasan yanzu aka fara! 🤸🏻♀️😂 Shi fa wannan yasin ba irin sauran mutane bane!
Mommyn Twins ce