Tushen Ƙaddara
by @aiimarvoice
A TSAKANIN ZUCIYA DA KADDARA
_Aiimar Voice/Talk_
*01*
A ciki. Wata ranar Litinin ce, ranar ba ta da zafi sosai, iska kuwa tana kadawa a hankali tana motsa ganyen bishiyoyin mangwaro da ke tsaye a bakin gidan. Hayaniyar yaran unguwar ta cika ko'ina; wasu suna tsalle tsalle, wasu suna buga ƙwallo, wasu kuma suna guje-guje suna ta nishadi da murna.
A tsakiyar wannan hayaniyar ne wani ƙaramin yaro mai kimanin shekaru takwas ya fito daga cikin gidan su, riƙe da wata ƙaramar leda a hannunsa.
Sunansa Abdurrahman, amma kusan kowa a unguwar yana kiransa da Aiimar.
Aiimar ba shi da yawan magana. Yaro ne mai natsuwa, wanda ko da yake yana cikin yara masu hayaniya, ba kasafai yake shiga rigima ba. Idan aka samu matsala, shi ne na farko da zai yi ƙoƙarin sasanta su.
Ya tsaya a ƙofar gidan yana kallon yaran da ke wasa.
Sai ya ga wata yarinya ta fito daga gidan da ke ƙetaren hanya.
Tana sanye da wata doguwar riga mai launin ruwan hoda, kanta a ɗaure da ɗan ƙaramin mayafi. Hannunta ɗauke da kwandon roba, yayin da take kallon yaran da ke wasa.
Sunanta Shamsiyya.
Amma saboda ita ce autar gidansu, kusan kowa yana kiranta da Autar Mama.
"Aiimar!"
Muryar ɗaya daga cikin yaran ta katse tunaninsa.
Murmushi yayi sannan ya kallesa "Zo mu buga ƙwallo!"
Aiimar ya juya ya kalle su yace "Ku fara, zan zo."
Ya sake maida kallonsa akan Shamsiyya.
A wannan lokacin kuwa ita ma ta ɗago kai cikin murmushi suka kalli cikin idanun juna.
Shamsiyya ta saki wani murmushi.
Aiimar kuwa sai yayi saurin kawar da kansa kamar wanda aka kama yana aikata wani laifi.
"Me ya sa kake kallonta?"
Wata murya ce daga bayansa take tambayarsa, Aiimar ya juya da sauri cikin tsoro, Ɗan uwansa ne, Salisu, yana tsaye yana dariya.
"Ba kallonta nake ba." Aiimar ya amsa fuskarsa a yamutse
Salisu ne ya sake tambayarsa "To me kake yi?"
"Ba Komai." Aiimar ya amsa yana sake maida kallonsa a kan Autar Mama
Salisu ne ya ƙara fashewa da dariya.
"To ka daina kallon Autar Mama dai."
Aiimar ya daure fuska. "Ni ba kallonta nake ba."
"To shikenan." Salisu ya amsa sannan ya juya yana tafiya, waigowa yayi sannan ya ƙara da cewa "Amma dai kasan na gan ka ko."
Aiimar ne ya ɗauki ƙaramin dutse ya jefa masa, kaucewa Salisu yayi sannan ya ruga da gudu.
A gefe guda kuma juyawa Shamsiyya tayi ta shige gidan su.
"Autar Mama!"
Mahaifiyarta ta kira ta daga cikin ɗaki.
"Na'am Mama."
"Kin kai wa Babanku maganin da ya ce ki kai?"
"Na kai." Autar mama ta amsa
"To zo ki taimaka min."
Shamsiyya ta ajiye kwandon sannan ta zauna kusa da mahaifiyarta.
"Mama..." Shamsiyya ta kira mahaifiyarta tana murmushi.
"Na'am Autata"
Shamsiyya ce ta nisa sannan tace "Yau Aiimar ya zo."
Mahaifiyarta ta kalle ta tace "Aiimar?"
Gyada kai shamsiyya tayi tace "Eh."
"To me ya faru?" Mama ta tambayeta tana murmushi
"Ba komai." Shamsiyya ta amsa tana saukar da kanta kasa, Ta yi shiru.
Mahaifiyar ta yi murmushi sannan ta tambayeta "Kin san shi kenan?"
Shamsiyya ta gyada kai alamun Eh, Sannan ta kara da "Shi ne ɗan gidan Malam Abdul."
"Na sani." Mama ta amsa tana sake kallon Shamsiyya
"Yana da kirki." Shamoce ta fadi haka tana wasa da yan yatsunta.
Mahaifiyarta ta yi dariya.
"Kin san yana da kirki tun yanzu?"
Shamsiyya ta sunkuyar da kai.
"Mama..."
Mamace tayi murmushi sannan tace "To shikenan, ban ce komai ba."
Ta shafa kanta tace "Allah yayi miki albark"
"Amma ki je ki yi karatunki. Ba kullum akeyin wasa ba."
Shamsiyya ta tashi tana murmushi.
"To Mama."
______________________________
Shekarun suna tafiya.
Abin dai ya fara ne daga kallon juna daga nesa, yanzu ya koma ana gaisawa.
Gaisuwa ta koma abota.
Abota kuma ta zama wata irin kusanci da babu wanda ya san lokacin da ta fara.
Suna makaranta ɗaya.
Idan Aiimar ya manta da littafinsa, Shamsiyya takan bashi aron nata.
Idan Shamsiyya ta kasa fahimtar darasi, Aiimar yana zama domin koya mata.
Idan aka basu aikin gida, sukan haɗu a ƙarƙashin bishiyar su yi shi tare.
Wata rana, bayan sun gama karatu, Shamsiyya ta ɗaga kai ta kalli Aiimar.
"Aiimar."
"Na'am?"
"Me kake son zama idan ka girma?"
Aiimar ya ɗan yi tunani sannan yace "Ban sani ba."
Kallonsa ta sakeyi sannan tace "karkaji tsoro kawai ka faɗa ."
Murmushi Aiimar yayi sannan yace "Zan zama babban mutum."
Shamsiyya ta fashe da dariya har tana dafe cikinta sannan tace masa "Ni ban tambaye ka ko za ka zama ƙaramin mutum ko babban mutum ba."
Aiimar ya yi murmushi ya bita da kallo zuciyarshi fal da farin ciki sannan yace "To zan zama mutum mai kuɗi."
Cike da mamaki Autar mama ta kallesa sannan tace "Me za ka yi da kuɗin?"
"Zan gina babban gida." Ya fadi tare da nunawa da hannunsa
"Sai me kuma?" Ta sake tambayarsa
Aiimar ya amsa yana murmushi "Zan sayi mota."
"Sai me kuma?" Ta sake tambayarsa
Aiimar ya kalle ta. "Zan..." Sai ya yi shiru.
"Zakayi me?" Ta sake tambayarsa
"Zan taimaki Mama." Aiimar ya amsa
Shamsiyya ta yi murmushi tace "Allah Ya sa."
"Amin." Aiimar ya amsa yana murmushi
"Ni kuma zan zama malama." Cewar Autar Mama
"Malama?" Aiimar ya amsa yana nuna alamun tambaya a fuskarsa
Amsawa tayi cike da kwarin gwiwa "Eh."
"Me za ki koyar?"
"Yara zan koyar" ta amsa masa tana murmushi, murmushin shima Aiimar, "To idan kin zama malama, ni zan zo makarantar ki."
"Me za ka yi?"
"Zan dinga kawo miki abinci."
Shamsiyya ta yi dariya.
"Ni ba ƙarama ba ce."
"Na sani."
"To me ya sa za ka kawo min abinci?"
"Saboda nasanki ba kkasafi kike cin abinci ba."
Shamsiyya ta yi shiru, Sai murmushi ya bayyana a fuskarta.
---
Wata rana da yamma, Aiimar yana zaune a bakin ƙofar gidansu yana gyara wata motar kara.
Sai Shamsiyya ta zo.
"Aiimar."
Ya ɗago kai ya amsa,
"Na'am."
"Zo mu je."
"Ina?"
"Kasuwar Mama ta ce in je in sayo mata wani abu."
"To me ya sa kika zo wajena?"
"Saboda ina tsoron tafiya ni kaɗai."
Aiimar ya tashi.
"Mu je to"
Suka fara tafiya.
Ba su yi nisa ba sai wani ɗan yaro ya zo yana ta zagin Shamsiyya saboda wata ƙaramar rigima da suka yi kwanakin baya.
Aiimar ne ya tsaya yana kallonea tare da fadin "Ka daina."
Yaron ya kalle shi.
"Me za ka yi?"
"Na ce ka daina."
"Fadan ba naka ba ne." Yaron ya fadi
Aiimar ne ya matsa kusa da shi sannan ya fada masa,
"Amma ba zan bar ka kana zagin ta ba."
Shamsiyya ta kama hannunsa.
"Aiimar, mu tafi."
Ya kalle ta, sannan ya juya suka tafi.
Suna tafiya, Shamsiyya ta yi shiru na ɗan lokaci.
Sai ta ce:
"Na gode."
Ya kalleta yace "Da me?"
"Da ka tsaya min."
Aiimar ya yi murmushi.
"Ba komai."
Tun daga wannan rana, Shamsiyya ta fara kallon Aiimar da wani sabon salo.
Ba wai kawai abokin wasa ba ne.
Ba wai kawai abokin karatu ba ne.
A hankali, ya fara zama mutum na musamman a zuciyarta.
Amma su kansu ba su fahimci hakan ba.
Har yanzu yara ne.
Rayuwa tana gabansu.
Ba su san cewa shekaru masu zuwa za su kawo musu abubuwan da ba su taɓa zato ba.
Ba su san cewa ranar da za su fara magana kan aure za ta zo ba.
Kuma ba su san cewa wata rana za su zauna a gaban sakamakon wani gwaji, su ji kalma ɗaya da za ta girgiza duniyar da suka gina tun suna yara ba
A wannan lokacin, abin da Aiimar ya sani kawai shi ne idan ya ga Shamsiyya, zuciyarsa tana samun wani irin farin ciki da ba zai iya bayyana shi ba.
Shi kuwa abin da Shamsiyya ta sani shi ne, idan Aiimar bai zo makaranta ba, ranar ba ta samun sukuni ko farin ciki.
Soyayyar su ba ta fara da furucin "Ina sonki ko inasonka ba"
Ba ta fara da saƙonnin waya ba.
Ba ta fara da alkawarin aure ba.
Ta fara ne da ƙananan abubuwa.
Taimako.
Gaisuwa.
Murmushi.
Kallon juna.
Kuma wata ƙaramar kulawa da ba su san cewa wata rana za ta zama babbar soyayya ba.
A ƙarƙashin bishiyar mangwaro kuwa, wani sabon babi na rayuwarsu ya fara.
Ba su san wanda ya riƙe alƙalamin ba.
Amma sunansa...
KADDARA.
Aiimar....