Page 45
💫MARYAMA💫
45.
Lokacin da na farka akan gadon asibiti na tsinci kaina, gefe dani wata jami'ar police ce zaune bisa kujera da kakin polisawa a jikinta, abubuwan da suka faru ne suka fara dawowa cikin kwakwalwata tamkar yanzu ya ke faruwa.
Kuka mai sauti na saki har ina yi kamar zan shide Cikin kuka na ce, "Siyama ya zaki min haka? Ya zaki kawo ni garin da ban san kowa ba sannan ki tafi ki barni tafiya na har abada? Dan Allah kice min bake wannan motar ta kashe ba, ki ce min kina zuwa wani abu zaki amsa ki dawo, dan Allah Siyama ki ce man zaki dawoooo".
Na fada ina kara fashewa da kuka hadi da daukar filon da kaina ke bisa na danne kaina dake barazanar tsagewa dashi.
Babu shiri police din ta garzaya neman likita dan tana ganin kamar wannan patient din ta samu mental problem ganin abubuwan da take yi, a tare suka dawo da likitan. Da gaggawa ya danna alluran bacci cikin karin ruwan da aka daura wa Maryama, shure shure ta dinga yi har bacci ya kuma daukarta, wayar Maryama dake hannun police dince tayi kara alamar shigowar kira, babu bata lokaci jami'ar tsaron ta dauka dan dama abin da suke jira kenan,."Hello" ta fada cikin muryarta mai kauri.
Dan matsar da wayar ya yi daga kunnenshi yana bata fuska na sakan biyu sannan ya mayar zuwa kunnenshi, "Hello" ta cigaba da fada, a bangaren Sadeeq dake zaune a palonshi abun duniya yayi masa yawa dan ya gama zagaye duk wasu tituna dake garin patakot bai ga mommy da khadija ba, dama tunaninshi airport suka nufa nanma ya zagaye kaf cikinta bai gansu ba. Tunanin Maryama kuma na manne daya bangaren zuciyarshi dan haka ya kirata, amma maimakon ta dauka sabanin tunaninshi wata murya mai kama da ta gardawa ce ta amsa mashi kiran....
Bayanin da matar ta cigaba da mashi ne yasashi mikewa babu shiri har yana tuntube da glass table dake gefenshi, a rikice yake tambayarta wanne asibiti suke kuma mai ya sameta.
Sunan asibitin ta sanar dashi hadi da cewa," Wani accident akayi a gabanta shine dalilin sumarta, kuma ana kyautata zaton tana da alaka da wacce accident din ya ritsa da ita kamar yadda na'urar cctv dake bisa hanyar ta tabbatar...
Bai jira ya gama jin abin da take fade ba ya katse wayar ba tare da ya rufe ko kofar palon ba ya afka motarshi hadi da bata wuta ya figeta a guje, da hanzari mai gadi ya wangale masa kofa ganin yanayin mai gidannasa yau babu sauki. Ikon Allah ne kawai ya isar da Sadeeq asibitin nan lafiya, dan gaba daya bashi da control, gashi duhun magriba ya fara.
A harabar asibitin ma ko parking mai kyau bai yiba ya fita da sassarfa ya nufi inda aka kwatanta mashi Maryama ta na can.
Tana kwance sambal da ita, cikin awanni kadan har ta zabge ta yi wani fayau sai dogon hanci kawai kake gani a fuskar. Zuba mata idanu yayi bayan ya ja kujera ya zauna a bakin gadon. Bacci take yi amma ko a baccin kasan babu kwanciyar hankali tattare da ita dan sai yamutsa fuska ta ke yi....
Hannunta daya ya kama ya rike gam cikin nashi yanajin abubuwa masu yawa suna yawo a kansa maganganun Mommy suna dawo masa daya bayan daya tamkar yanzu take karanta masa su....Shin zuwa da yayi wajen Maryama yanzu na nufin ya zabe ta kan iyayenshi? ko dai ya abin yake? Zuciyarshi ke tambayarshi, kafin ya samo amsa Maryama ta farka a firgice zata kwala kara amma sai ta yi shiru ganin kamar sadeeq zaune kusa da ita, mafarki nake yine? ta tambayi kanta, a hankali idanunta suka fara washewa ta sauke su tarwai bisa fuskarsa.
Shi din ne dai ba gizo ya ke mata ba. Ruwan da ake kara mata ta fincike da karfi ta hantsilo kasa kamar mahaukaciya, cikin kiftawar ido ta aikata hakan shiyasa Sadeeq bai ankara ba.
Da hanzari ya rikota ganin abin da tayi, yace, "Pretty, are you ohk?".
Kuka ta fashe dashi tana fadawa jikinsa hadi da nuna masa kofa da hannunta da rawar harshe ta ke fadin, "Si...Siy..Siyama..Ta mutu mota ya bugeta ta zama pieces akan kwalta shikenan ta tafi ta barni ban san kowa ba an..."
"Shhhiiit" Sadeeq ya fada yana daura hannunsa saman lebenta, a hankali ya ce, "Kina dani anan Maryama. Stop worrying your self, kowa lokacin sa yake jira and duk inda Allah ya kaddara ajalinka yake to fa sai kaje can. Mu mata fatan samun rahama kawai."
Dago kai tayi tana kallonshi, cikin sanyin tace, "You mean kana tare dani duk da abin mamarka tace?".
Lumshe idanu yayi for 30sec har ta cire tsammanin zai furta wani abu taga ya gyada mata kai yana kara damketa, wani irin ajiyar zuciya Maryama ta sauke gami da mayar da kanta jikinsa ta kwantar. Bayanta yake shafawa gently, take bacci ya kuma daukarta dama alluran bai sake ta ba yanayin firgicin da take ciki ne ya hana mata baccin cikin salama.
Kwantar da ita yayi saman gadon, sannan ya juyo ga yar sandan suka fara magana akan gawar siyama da ke mutuary da kuma case din dake ofishin yan sanda....
**********
Wasa wasa aka nemi Maryama aka rasa duk inda ake tsammanin zata je anje babu ita babu labarinta, a bangaren Jabeer kuwa sai dai sauki daga Allah dan ciwo gaba gaba yake har ya zuwa yanzu bai farfado ba, numfashin da yake fitarwa ne kawai ya bambanta shi da gawa amma zahiri kwance yake komai sai an mishi, Iyayensu ba karamar tashin hankali suke ciki ba, Innarmu tayi kuka har kamar idanunta zasu tsiyaye. Tayi addu'a har ta rasa abin da zata roka.
Baffa da shike namiji ne yafita juriya amma shima a hankali abin ke shigarsa musamman duk sanda ya zo yaga wannan marayan Allah da babu uwa babu uba kwance...Umaimah ma taji sauki sosai saidai tun daga lokacin har yanzu bata da aiki sai kuka, ko abinci bata iya ci, idan an tambayeta abin da ya faru kuwa bata iya fadin komai sai kuka. Ganin haka ne ya sa su Innarmu barinta a cewar su duk ranar da ta sami nutsuwa zata basu labari, ko da baffanmu yazowa Inna da shawarar kai cigiyar Maryama gidajen radiyo da talabijin murmushin takaici tayi tace.
"Basai ka wahal da kanka ba baffansu,duk inda Maryama take na tabbata ta na lafiya qalau kuma da saninta ta tafi koma ina ne saidai all what I know shine watarana zata dawo da kafafunta zata dawo ta nememu da kanta, a lokacin ta yi karatu irin wadda ya kamata, duniya ta bata ilimi mai kyau amma ina mata addu'ar karta dawo a kurarren lokaci. Ni na haifi maryama a cikina na reneta da iya baiwar tarbiyar da ubangiji ya bani iko.
Dan haka nasan wacece ita,ban sani ba ko wani laifi nayiwa ubangiji na, ban sani ba ko ita din jarabawatace,ban san......" kuka ne yaci karfinta ta ringa rera abinta. bafyfanmu bai katseta ba dan yasan tabbas tana bukatar kukan kozata sami saukin radadin da takeji a matsayinta na uwa...
Sallamar Umaimah ne ya sa Innarmu tsagaitawa da kukan da take yi, cikin rashin kuzari ta iso gareta gami da durkusawa kasan guiwowinta hawaye na zirara bisa kuncinta tace,"Dan Allah Innarmu ki daina kuka. Tabbas Maryama tayi kuskure a rayuwarta amma kukan ki ba komai zai jawo mata ba face shiga masifa da bala'i.
Innarmu ke uwa ce ta gari hawayenki masifa ce akan Maryama, ki daina dan Allah."
Dago idanunta da suka rine tamkar gautar da yaji rana Inna tayi ta suke su bisa fuskar Umaimah, cike da bada umarni tace,
"Umaimah me ya faru? Me ya faru a waccan bakar ranar? Me maryama ta aikata,? Ina Maryama ta tafi?".
Kasa Umaimah tayi da kai wasu hawayen suna zirarar mata, kamar bazata ce komai ba, har tsawon wani lokaci sai kuma ta dago tana goge fuskarta da bayan hannayenta tace, "Abin da ya faru shi...ne kanwar ummar mu basira ce tazo gidanmu ranar suna tadi da Ummarmu shine naji tana bata labarin yadda zata hana aure na da yusuff a cewarta bazan taba yin aure inje inji dadi ba, wai yusuf yana da abin yi kuma inda zansha wahala take so inje. Ina tsaye bansan tazo fita ba kawai ta ganni wai ina mata labe nan suka dinga dukana da basira har suka jimin ciwo kuma suka hanani yin kuka, dana samu na gudu kawai na tafi gidan Maryama...Sh...Shi..n.." kuka ne yaci karfinta ta kasa karasa maganar, cike da rudani Innarmu ta ce, "sai kuma me Umaimah".
"Shine na samu ta rike gaban rigar Hamma Jabeer......"nan ta basu labarin gaba daya abinda ya faru da ta gani daga farko har karshe. Hannu Inna ta dora a ka zata kurma ihu kawai ta hango gadon da Jabeer ke kwance bisa yana rawa kar kar kar kar kamar ana jijjigasa. Ba Innarmu dake shirin kuka ba hatta Baffa da yayi mutuwar tsaye a wajen sakamakon labarin da Umaimah ta bayar yanzu a tamanin ya tafi gaban gadon.
"Jabeer, cewar inna tana tabashi, "Jabeeru" baffa ma ya ambaci sunanshi, "Hamma jay" cewar umaimah tana kuka.
A hankali wasu hawaye suka ziraro daga cikin idonshi dake rufe ruf suka hau ta saman dogon hancinsa da shi kadai ya ragewa fuskar suka cigaba da gangarawa sannan ya diga dill saman filon da ya ke kwance..." Ya fardado" cewar Innarmu wani irin dariyan farin ciki yana kufce mata mai hade da hawaye, hannu baffa ya daga sama ya ce, "Alhamdulillahi"...Yayinda Umaimah ta juya da wani irin gudu ta nufi ofishin likita...