Page 41/42
*SANADIN HIJIRA*
BY
Ummu Fadeela
Chapter.... 41/42
Rawa jikin Abeey ya dauka sai jijjiga yake, idanunshi a kan Alburhan da ya kafe shi da idanu shima. "Akhee Fadlallah, ko ba ka yi farin ciki da halartata daurin auren GUDAN JINI BA?" Wani irin gingirigim Abeey ya ji a tsakiyar kanshi, sai kuma kwanyarshi ta fara maimaita kalmar 'GUDAN JINI' da Alburhan ya ambata. A ina ya san wannan kalmar? Tabbas ya san wannan kalmar.
Timmm! Karar fadowar Hosni daga rikon da aka mashi a sama ya dawar dashi duniyar zahiri. Waige-waige ya fara amma wayam, babu Alburhan babu labarinshi. Da sassarfa ya nufi inda Hosni yake, sai kakarin mutuwa yake yi; ya yi hanzarin dagoshi. "Hosni! Hosni!" Kawai yake ambata. Da kyar ya iya furta, "Ruwa Fadlallah, ruwa." Ruwan ya garzaya ya dauko hadi da daga kanshi ya fara bashi, tas ya shanye gorar ruwan yana maida numfashi.
"Cikin wannan tashin hankalin kake rayuwa Fadlallah? Wannan bakar masifar kake gani amma har yanzu kake zaune ragas da kai ba ka bi jeji ba? Lallai na yarda da maganar SITTI da ta ce babu tsokar zuciya a gangar jikinka, Fadlallah."
Sarawa kan Abeey ya kuma yi, ya dafe kan da hanzari. "SITTI," ya ambata. "Tsokar zuciya? Gudan jini? Me yasa abubuwa suke son kwabe mini lokaci guda ne?" Ya fada yana buga gefen katifar gadonshi.
Knocking kofa akayi, sai kuma aka bude Umma ta shigo cikin shiga ta alfarma sai baza kamshi take. Tana kallon Abeey ta ce, "Sorry Yallabai, ban san kuna tare da wani ba. Dama zan ce ne kusan kai kadai ake jira fa; daga tsakar gida ina iya jiyo muryar maroki yana ta ambaton sunanka. Baban ango kawai ake jira." Ta karashe in a naughty way.
Gyara zaman hularshi ya yi yana kamewa tamkar ba shi ne a cikin tashin hankali ba, ya ce, "Gani nan tafe Hajiya, wani karamin accident Hosni ya samu a nan shi ya sa."
"Allah ya kiyaye," ta fada tana wucewa.
Ko a wajen daurin auren ma sosai Abeey ya kame tamkar ba shi ba, amma sai baza idanu yake ta ina zai ga Alburhan, ta ina zai bullo masa? Tun yana baza idanu har ya gaji ya hakura. Alkawarin Allah ya cika; a yau din, a kuma wannan lokaci, dubban jama'a suka shaida daurin auren Badariya da Aminullahi.
Babu wani shagalin da ya rage, amarya ma a nan cikin gidan nasu zata tare a bangaren Al'ameen, inda Umma ta zage Abeey kuma ya fidda kudi sosai, ta mata kayan daki na gani na fada, komai ya ji. Dakin Aminu ne kawai ba a taba ba, amma hatta kujerun da ke palo duka an canza su.
Karfe tara na dare ya shigo gidan a gajiye tibis, yana rike da babbar rigarshi. Tun bayan gama daurin auren bai huta ba sai yanzu da ya tabbatar duk abokananshi da suka halarci daurin auren daga bangarori daban-daban sun koma, wadanda zasu kara kwana kuma sun samu masauki. Ko yanzu ma daga airport yake; sai da ya ga tashin wasu abokananshi biyu zuwa Mexico, su Dr. Wunti kuma suka wuce Maiduguri, sannan ya juyo.
A hankali ya bude dakin, ido hudu suka yi da ita. Tana zaune bakin gado ta yi shiru tamkar mai hankali; idan ba sarkar da ke kafarta kaga ni ba, babu ta yadda zaka yarda mahaukaciyace. Tunda Al'ameen ya dawo, Dr. Shettima ya daina samun damar yi mata allurar dake kara haukata jininta ta yi ta duka da buge-buge. A bangaren Umma kuwa, tana nan tana dura mata some kwayoyin da har yau babu wanda ya sani; maganin gargajiyar da Abeey ke kawowa ma still har gobe zubarwa take yi.
Durkuso ya yi a gaban gadon yana kallonta, murya ciki-ciki ya ce, "Ummie!" Idanunta tsaye kyam tamkar shi take kallo, amma hankalinta babu kwatakwata, ma bata san da wanzuwarshi a wajen ba. "Ummie, yau Aminullahinki ya zama babban mutum. Yau wani nauyi ya hau kanshi; a yau aka daura mishi aure amma baki sani ba, balle ki sanya mishi albarka." Dan shiru ya yi yana maida numfashi tsawon lokaci, sannan ya ci gaba, "Duk da haka baz..."
Magar tasa ce ta yanke sakamakon karar kwanciyarta da ya ji da karfi dake nuna faduwa ta yi daga zaune. "Ya Allah!" Ya nufeta da sauri ganin baccinta take yi hankali kwance. Gyara mata kwanciyar ya yi sannan ya mata addu'o'i, ya ja mata duvet. Ya dade jingine da wall na dakin kafin karar wayarshi ta dawar dashi tunaninshi. "Badar!" Ya fada saman labbanshi, sannan ya kama handle din ya bude. A hankali yake takawa har ya kama karfen benen ya haura sama, duk jikinshi babu dadi; babu irin wannan karsashi da zumudi na sababbin angwaye a tattare dashi.
Kai da kawowa kawai Umma ke yi tsakanin palon. "Kuma bai kiraki a waya ba har yanzu?"
"Ke Anty, kina gani sai kiranshi nake bai dagawa, kuma kina tambayata bai kiraki ba? Ko fa irin kiran bayan auren nan ya ce min 'Baby an daura' bai yi ba. Gashi kawayena har suka gaji da jira suka tafi, bai shigo da nashi abokan ba. Na shiga uku na lalace Anty, wallahi su Zuby da dariya suka dinga yi."
"Eh, ba shakka akwai matsala. To ban da abunshi, haka ake yi? A daura maka aure da zukekiyar mata haka amma har karfe goma baka shigo gida ba, kuma ba sakon gaggawa? Ah, gaskiya ba lafiya, ni dai ban taba ganin haka ba tunda uwata ta haifeni. Mu da aka aurar tun zamanin jin kunya da guje-guje ma kenan, bare ku da kowa ya kawo jiki an ci an koshi."
"Ni dai Anty ki barni in nemo shi kawai, yanzu haka ma wani abu ya sameshi amma kin hanani fita. Ni dai kawai ki barni." Bude kofa akayi ya shigo, gajiyayyun idanunshi suka sauka a kanta. Ta sha ado cikin fari da golden din lace, amma fuskar ta yi kaca-kaca dasu maskara da jambaki saboda kukan da take tun dazu. Da wani irin gudu ta tafi ta kamkame Al'ameen, da ya ji ta a bazata; saura kadan su fadi tsabar nauyinta, ya yi saurin rike gefen kujera yana gyara tsayuwarshi da kyau.
"Innalillahi, ni Fanta na ga bone oh oh! Yaran zamani babu ta ido. Yo mu a zamaninmu ai sai mace ta yi watanni ma miji bai kama hannunta ba," ta fada tana rabawa ta gefe zata wuce abunta.
Al'ameen da ya yakice Badar a jikinshi ya ce, "Barka da dare Umma, ya hayaniyar jama'a?"
"Mun gode Allah dannan, hayaniya ya kare amma ka daga mana hankali. To, abu ne da bamusan me hakan ke nufi ba; ka tafi ka yi difff abinka, amarya da kawayenya suna ta jira amma shiru kamar an aiki bawa garinsu. Yanzu dai dare ya yi, kawai ku kwanta; da safe Abeey zai maku magana, dama shi ya aiko a kiraku kuma nazo na tadda wannan tashin hankalin." Daga haka ta raba gefen kujera ta wuce abunta.
"Sojanaaa! Duk ka bani tsoro, ina ka tafi?" Ta fada tana kuma faduwa jikinshi.
"Ya Salam! Badar, haka ake karbar ango idan ya shigo?" Yana tsattsareta da idanu.
"Sojana, ai kai ne."
"Ni ne me?" Dan kallonshi ta yi, sai kuma ta zaro idanu. "Wait, wai ina leda?"
"Leda?"
"Kaza mana Sojana! Ko ka manta ana shigowa amarya da kaza?" Ta fada tana turo baki gaba. Shafa goshi ya yi zuwa saman kanshi; shi kwatakwata ma ya manta, abubuwa sun sha mishi kai. "Sojana, ni komai nawa daban. Baka shigo da wuri ba, and ka shigo kuma babu kaza; ba fa haka ake yi ba." Kawai sai hawaye shaaarr.
Lakace mata hanci ya yi yana kakaro murmushi, dan ba karamin gajiya ya yi ba, ya ce, "Oh my darling wife, karki bata wa Soja kwalliya. Ba dai kaza kike so ba? Ohk, kin samu, ke naki ma daban da na kowacce amarya, ango special gashi zaki samu. Oya, let's go!"
Hannunta ya kama direct zuwa kitchen dake palon bayan ya ajiye babbar rigarshi saman kujera. Ta cikin ma ya cire, daga shi sai singlet da dogon wando. Karewa kitchen din da komai na cikinshi sabone dal ya yi da kallo; sai kamshin sababbin kwanuka ke tashi, an jere komai a muhallinshi. Freezer ya bude ya fitar da dakwalon kaza da ya riga ya daskare, ya jefa cikin baho ya ajiye bakin sink bayan ya bude ruwan.
Harde hannu Badar ta yi a kirji ta jingina da cabinet tana kallonshi with much surprise. Juyowa ya yi ya ce, "Oh, what next?"
Tana dagowa da dariyar jin dadi a fuskarta, "Like serious, tunda ka fara ai sai ka gama."
"Zaki gani kuma."
Ita dai bata ce komai ba har ya gama hada ingredients din. Ya zo ya wanke kazar ciki da waje tas-tas, ya zo ya shafe ta da hadin koina ya ji sosai, sannan ya bude oven ya durata ciki; ya daidaita 180°C din da yake so, ya zo ya wanke hannu. "Sai me kuma?"
Still with smile da ya ki barin fuskarta ta ce, "Amm ehmm yes, saura ka hada fresh milk."
Da hanzari ya gwalo idanu, "Fresh what?"
"Ehh, fresh milk, da shi ake hadowa ai."
"You are joking, wife. Wannan ko fridge na Abeey zan je in dauko maki. Beside, na san akwai su a palo, kina son wahal da ni ne kawai," ya karashe yana kwabe fuska. Kwabe fuskar ita ma ta yi, "Sojanaa, ango made nake son sha ai."
Jingina ya yi da cabinet din shi ma yana lumshe idanunshi, kanshi na sarawa kadan-kadan. Ta matso hadi da kamo hannunshi da kwantar da kanta saman kafadarshi, tana murza hannun a hankali. Cikinsu babu wanda ya kara yin magana, sai sakon da yake tura mishi a tafin hannu yake karba; yana kara lumshe ido da taunar lebe, haka har kazar ta gasu kamshi ya bade koina. Gloves ya sanya a hannu ya bude oven din, ya janyo kazar gami da daurata saman circle tray da ya ajiye. Table knife da fork ya dauka sai glass cup guda biyu duka ya ajiye a wani tray din daban. Dauko kazar ya yi zuwa satin fuskarta yana kallon ta, "Your kazar amarci is ready, wife."
"Woww, I like it!" Ta sanya hannu biyu ta karba. Ta juya, shi kuma ya dauko cups da sauran tarkacen ya biyota da shi. Saman dining ya ajiye, ita pula ta bude fridge ta dauko gorar ruwa da Hollandia yoghurt sai Bullet energy drink da ta san shi ne fav nashi.
"Let me freshen up kafin kazar amaryata ya yi sanyi." Dariya ta yi; dadi kamar zai hadiyeta. Tunda suke tare da Soja tsawon shekaru, bai taba tsayuwa ya nuna mata kulawa irin na yau ba. Jin ta take a sama cikin cloud, kamar ta fi sauran matan duniya sa'a. "As you wish, Sojana."
Direct bedroom nashi ya wuce, sai da ya yi wanka ya yi duk abun da ya saba kafin kwanciya bacci sannan ya fito cikin kayan bacci. A lokacin sha daya na dare ya wuce. Badar na zaune yadda ya barta, ta baza tagumi gaban kazar amarci kamar mai kirga adadin kasusuwan dake jikin kazar.
Duk marmarinta da yadda ta nace, bata wani ci kazar dayawa ba, ta ji ya fita a kanta. Zagewa Al'ameen ya yi ya ci sosai, dan rabonshi da abinci tun bayan liyafar daurin aure; shi ma bai wani ci na kirki ba, dan haka ya saki jiki ya ci sosai ya kora da drink. Yoghurt din ma bata wani sha ba ta tashi. "Nima zan yi wanka, Soja."
Bayan wucewarta, press up ya dinga yi a palon dan rage nauyin abun da ya ci, sannan ya wuce dakinshi bayan ya kashe komai na palon.
Time da Badar ta fito, palon dim yake da duhu. Cike da mamaki take kallon koina. "Yanzu ni zan kai kaina kenan? Wannan wacce irin amaryace haka, Sojana!" Ta fada kasa-kasa tana kada kai da nufar hanyar dakinshi. Dakin ma babu isashen haske sai dim light dake saman bedside; tana iya hango yadda ya yi daidai saman gadon, alama baccinshi yake sha. Duk yadda gangar jikinta ke son ganin bai mata adalci ba, zuciyata ta ki aminta da hakan; soyayyarshi ke rinjayar rashin dai-dai din da take hasashen ya mata. Gefen gadon ta hau ta kwanta lamo.
A kan agogon dake nuna karfe bakwai da rabi na safe idanunta suka sauka, sai kuma ta bi hasken rana dake shigowa ta window da kallo tana mutsuke idanunta. Gefen da yake kwance ta duba, babu kowa sai kamshinsa da ya manne a jikin komai na dakin. Kafafunta ta saukar kasa ta taka zuwa bakin toilet, knocking ta yi sau uku, shiru; hakan yasa ta tura kofar tana wurga idanu, nan ma wayam baya nan. Idanunta ne ya kai kan wani karamin takarda dake kusa da filon da ta tashi. Da sassarfa ta iso, hannu na rawa ta bude ta fara bin content din da kallo kamar idanunta zasu zubo kasa. Tana kaiwa karshe ta zube nan bakin gadon ta fashe da wani marayan kuka...
Da wani irin mamaki take saurarenta, kafin cike da tashin hankali ta ce, "Yanzu Magajiya, abun da tsinanniyar yarinyar nan ta maki kenan? To ko dai aljanun gareta da gaske? Idan ba aljanu ba, Magajiya, ina dalili zata dinga maida wadanda suka dauke ta mata? Ah, yau na ga ikon Allah! Kuma kikace shi yaron arziki gareshi kamar Dangote amma ya dawar da yarinyar?"
"Ke Titi, ana gaba kina komawa baya. Ina fada maki yaron arzikinsa sai ya siye Abuja gaba dayanta ya rushe ya gina sabo; kaftin din Sifen ne fa duka! To wallahi dai yarinya ta yi mana bakin ciki. Duk ba ma wannan ba, al'amari fa ya kara rikicewar da duk wanda ya zo ya dauke ta dawar da ita yake, ina fada miki duk ta maidasu mata. Ga dai sauran kowa ta gane kanta daya, a cikin su ma an dauketa zaman gida, amma wannan dai abun ya ci tura. To ni yanzu na yanke shawarar maidota gaskiya; ina dalili zan ta ciyar da katuwar a banza bata shigar min da komai, a'a ni ba asararriya bace, ahto."
"To kema kin ce wani abu. Gaskiya dai ba zaki ta ciyar da katuwar kuma babu riba ba, ina dalili ina dan mafari? Sai dai zancen ki dawar da ita ma fa bata taso ba; wa kike tunanin zai biya mata kudin jirgi? Hajiya Babba ko ni, ko kuma ke da banzar bata samar maki komai ba? Ai kawai korata zaki yi ta shiga duniya, eheee! Na tabbata a titin Spain zata samu mai sauke mata duk aljanun dake kanta, ko da ko kukar bulukiya ce!"
"Kuma fa kin kawo shawara, Titi. Ai ni shaff na mance da zancen kudin jirgi za a biya mata. Kinga bari in aika banza titi yanzu kuwa, dan ba a bori da sanyin jiki." Kittt ta kashe wayar ta mike tana murtuke fuska.
Ina zaune na hada kai da guiwa, abun duniya ya min yawa. Ji nake kamar rayuwata ta zo karshe, astagfirullah, tamkar ni kadai ce rayuwa ta juyawa baya. Anya akwai wace ta taba shiga gararin rayuwa kamata kuwa a wannan duniya? Kululululu! Cikina ya bada sautin a karo na barkatai. Bayan hannu nasa ina sharar hawayen da ke ziraromin gami da shafa cikina; yau kwana biyu kenan rabona da abinci, Mummy ta daina bani a cewarta ta gaji da asara. Sauran kowa ita ke ciyar da kanta. Nawwara kuwa, tun bayan da ta warke ban kara ganinta a gidan ba; ko ina ta shiga, Allah masani.
Kamar wace aka hankado ta fado dakin tana muzurai. A rikice na mike jikina na rawa; a zatona dukan da ta saba yi mani ne yau ma zata min. "Wuce muje," ta fada tana nuna min kofa. Jiki na rawa na yunkura na rarumi hijabin da nake sallah dashi zan daura saman doguwar rigar kantin dake jikina. Tun ban saka ba ta tura keyata da hannunta. "Wuce ki bar min gida, kuma kar in kara ganin wannan mummunar fuskar taki a nan! Dama baki shigo da komai ba, kuma hacking zaki fitar min dake gida."
Wani irin tsinkewar zuciya mai tafe da faduwar gaba ne suka sameni lokaci guda, har na yi taga-taga zan fadi amma na koma na tsaya. Hannuna ta fara ja zuwa kofar fita. "Ki yi wa girman Allah da darajar ma'aiki S.A.W Mummy ki rufa min asiri! Ina zanje? Wa na sani a kasar nan? Na shiga uku, laifin me na aikata duniya yake guduna haka? Mummy kar ki fitar da ni! Maahh, ina kika tafi? Ki dawo gareni, ki dawo gareni dan Allah!" Cikin matsanancin kuka nake magana ina rike duk abun da na yi karo dashi a hanya, amma haka Mummy ta yakice ni da karfin tsiya hadi da hankadoni waje.
Wani irin katantanwa na yi tsabar karfin yadda ta turoni, garabb na ji na fada kan abu. A anna na dago jajayen idanuna, na bi kafarshi da kallo kafin in daga sama har kan fuskarshi da ke hade murtuk kamar hadarin August. Wani tsallen zuciyata ta yi, kawai na mai da kaina bisa kafafunshi na kife............