Chapter 6/7
by @smauta
Page 6/7
Yau kimanin satin su manar daya da dawowa hutu duk wani gidan dangi da abokan arziki daya kamata su zagaya sunje,halim tayi matukar farin ciki akan wannan ziyarar koba komai ta debe kewa saidai lokutta da dama tana tunani tace inama itace a damshin manar ganin duk inda sukaje ana marhaba da ita wasu zata ce masu yan uwar mamarta ne wasu na babanta…….
Mahaifiyar ta ta rasu duk da har yanzu daga babanta har dangin mamar tata ba wanda ya fada mata silar mutuwar mamar tata,so tari takan kusanci babanta da tambayar amma basu kareta ta dadi kakar ta kuma data haifi mamarta basa shan inuwa ɗaya da ita uwa uba kanwar mamar tata kwalli daya tall shiyasa idan kanason tashin hankalin halim to ace zataje hutu gidan kakarta…….
Tunanin me kikeyi halima? firgigi ta dawo hayyacin ta kwalla ta goge bakomai kaka,a'a zonan kaka ta jawo halima kusa da ita ko zaman gidan nan ya isheki dama shi yasa nace anya zaki iya zama damu har sati biyu halima mudai talakawa ne ba lallai ma abinda muke baki kinaci ba kina son shi ko?a'a kaka wlh bakomai idan ma inason wani abu ai inada kudi zan siya naci,to meke sakaki tunani ina lura dake kwana biyu bakya sake jikin ki a gidan ko wani yana faruwa dake ne wanda bansani ba????
Kwalla ta goge ta fada kan kafadar kaka sannan tace ina tunanin mamata ne,kaka banida kowa sai Allah sai mahaifina duk wani abu najin dadin rayuwa ina samunshi amma rashin mahaifiya ta akusa dani ya tsagaita man da komai dangin mamata basa sona bansan ina zan raba naji dadi ba,ganinan rayuwa kawai nake bansan ina na dosa ba mahaifina yaki aure mata dayawa nason shi kaka yaki basu dama sai yace mata macuta ne kaka har na fara zargin ko mata yake……kull kar in ji kar ingani wannan maganar banza ta fito a bakin ki mahaifi da mahaifiya ko mahaukata ne sunansu iyaye……….
Banason shashancin banza wannan maganar ki cire ta a ranki kita addu'a kinsan mutuwa lokaci gareta idan yayi ba tsumi ba dabara sai ka tafi?tace eh kaka,to haka aure yake idan lokacin auren nashi yayi kina zaune zayayi kuma da kike ganin mata na tururuwa akan shi kowace yana jaraba halin nata ya tabbatar da idan ya aure ta din cuta zata shigo baya sai yasa yake nesa nesa da mata,kuma duk kinsan saboda me yake haka halima?a'a kaka saboda ke neeeee………
Ni kuma kaka eh,yana tausayin ki ne yasan kinyi rayuwa ta maraici bazai so kuma yanzu da girma yazo maki ba kuma ya kara jefaki a wani maraicin abinda zan gayamaki kita taya mahaifin ki da addu'a da yan uwar mamarki kina zaune Allah zai share maki hawayen ki , Allah baya bacci kuma da zuciya yake amfani muddin kin rike addu'a halima bazaki tabe ba ki rike addu'a a duk inda kika shiga,Baga manar nan ba ita ba uwa ba uba ni kadai take gani taji dadi a duniyar nan amma kinga tanasa damuwa a ranta?a'a to saike da kike ma a inuwar mahaifi ki gode Allah kinji ko,tashi kije kiyi sallah kuzo kujeman kasuwa……..
Marece suka tafi kasuwa suna tafe suna fira halim ta kalli manar tace mutuniyya ta tunda muka dawo kasar nan banji an maki sallama ba,kema ai banji an maki sallamar ba,suleja aiba garin mu bane🤣🤣indai da gasken kinada shi ya biyoki nan din mana daria halim tayi tace keeee badai tare zamuje abuja ba zaki gani danma dady aida kullum ina tare dashi……..
Manar tace karyar banza kawai shekarar mu nawa tare niko waya banji kinayi da saurayi ni zakima alako yanzu dai nan suleja zan samo maki wani kidan rage zafi ki fara soyayyar nan kema kiji me akeji,wai dan Allah manar mi akeji dadi mana kiji duk duniya ba wadda takaiki ai soyayya tayi yarinya 🤣🤣✌️
To yan matan amarya sai yanzu kuka dawo kaka wlh halim ta tsaidamu wai sai mun zagaye kasuwa,kika biye mata kuma kuna ganin marece yayi jibi dai zaku tafi in huta mgn kaka kin gaji damu ai bakujin magana,kaka dake fa zan tafi Allah tsari kakata Aisha abuja garin masu kudi haka kawai a filleman kai ban zuwa itama wannan dazan barki ku tafi tare dan kinzo gidanmu da ba inda zataje kuma da mijina nada rai Allah baya bari alhaji baiso ko nan da can manar taje,haka ya hore mu shi yasa nima kunga ba inda nake zuwa……..
***ABUJA NIGERIA***
Haba dan Allah saki jikin ki mana,ke naki in saki din halim nan ne gidanku wai ehen nan ne mana muje jakar hannun manar halim taja suka dumfaro wata katafariyar kofa wacce da kanta ta bude suka shigo,tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai,masu kudi na kaya gida ne karshen kallon yaro ko a china ita dai bata tabacin karo da gida mai girman wnn ba tabbas baban halim ba karamin attajiri bane wane mutum inji mutuwa…….
Halim na gaba manar na biye da ita kowane sassa na zuciyar ta na bugawa dam dam dam bada dan da halim suke tare ba tsaf zata ce wannan gidan na yan yankar kai ne,addu'a duk wacce tazo bakin ta yinta takeyi steps ta hau tana biye da ita wani sabon parlour suka kara shiga anan halim.ta samu wuri ta zauna seat,zama tayi ta ajiye hand bag dinta gefe kinga nan ko,da kai manar tayi alamar eh nan dady yake zama idan ya bar office dinshi dake nan cikin gida nan ne Bus stop dinshi idan yanajin raha yan kirkin nakanshi nan zan zauna muna fira dashi sosai amma duk ranar da fa yan kirkin basu kai ina zuwa zai korani🤣🤣🤣
Dole ya koraki ai halim bakin ki baya shuru alamar bude kofa sukaji halim tayi mata signal gashinan zai fito kara gyara zama tayi daidai ta dago idon ta daidai dadyn halim na budo kofar da zata sadashi da parlourn nashi kai tsaye,da sauri halim da buga wani uban ihu tayi kanshi da gudu tace daddyyyyyy,kyam yake tsaye a wurin yasa hannunshi biyu yayi hugging dinta back,wani sanyi yaji yana tsara mashi zuciya a duk lokacin daya rungume diyar tashi yakanji kaso tamanin na damuwar shi ya tafi saboda a kaf duniyar nan halim ita kadai ce sanyin idaniyan shi………
Tun fitowar shi gaban manar ya tsinke ya fadi zunbur ta mike tsaye,jikinta na wani irin ciri ba wanda ya lura da ita hannunta ta dora saman bakin ta da kirjin ta,tana karanta addu'ar neman tsari daga shaidan wanene take gani tsaye gabanta a matsayin uba ga halim idon ta ne ko kuwa tunanin shi ne yasa har ta zautu yake mata gizo,a ranta take kara maimaita sunan shi oga oga………
Sai lokacin halim ta saki dadyn nata tace daddy this is my friend manar danake baka labarin ta zata zauna damu har mu idasa hutun mu kafin mu koma school,sarai ya gane yarinyar maza gumbar dutse kenan kallon kallo da manar daddyn halin ya ankarar da halim tace dady hold up you two know each other?cikin ran manar tace mutumin dana dade ina crushing ya ceci Rayuwa ta baban kawata ne kenan?i can't let halim find out that,aa bamusan juna baaaa………..
Lokacim daya ta gigice ce a wurin wani sihirtaccen murmushi dady ya saki sannan ya lalle su duka biyun yace have fun😊
Ta gefen halim ya wuce ya bude wata kofar wata ajiyar zuciya da manar ta sauke har saida halim ta kalle ta sannan tace lets go ki saki jikin ki haka dady yake amma yanada kirki sosai,da kyar take daga kafar ta dan tayi mata wani balain nauyi kanta ya kulle a ranta tace ga koshi kuma ga kwanan yunwa ya Allahu….