BABAN KAWATA

Chapter 8

by @smauta




Manar naam babe meke damunki is there anything wrong?a'a no me kika gani halim am tired ne, I need rest munyo tafiyar marece umm kedai kika sani,nidai danaje gidanku ban darare kaina ba amma kinzo nan kinaman kamar bakuwa,halim kiyi hakuri ban taba zuwa gida irin wannan ba to zamu sace ki ne?🙄🙄🙄🙄






Hmmmmm ga toilet nan ki shiga kiyi wanka zan kawo maki abinci a nan wannan tsoron naki bazaki iya sauka kasa ba nasani🙄ficewa halim tayi tabar ta sai lokacin ta zauna kan gadon ta furzo wata zazzafar ajiyar zuciya,hannu ta daga sama tace Allah ka taimakeni ka rufaman asiri kabani ikon danne abinda nakeji game da mutumin nan ya Allah, Allah na rokeka idan son da nake mashi ba alheri bane Allah ka sassauta man ya Allah😭😭




Koda ta fito daga wankan halim har ta kawo mata abinciccika kala kala zama tayi ta fara cin abincin dadin shi na ratsa ta saida taci tayi nattt sannan tabar wurin gaban akwatin ta taje ta shiga cicciro kayanta tana sakawa a wardrobe tsaf ta kimtsa komai sannan ta jawo rigar baccin ta datazo Mata har gwuiwa ta saka,gaban mirror ta tsaya tsaf ta kalli kanta samun kanta tayi yau da admiring beauty dinta,wani body splash nata taciro ta feffesa…………….





Tun tana jiran shigowar halim har tagaji kayan dataci abinci ta dauko har tazo kofa ta tuno bata saka hijab ba ta koma kamar munafuka haka takebin ko ina da kallo sadaf sadaf ita dai taga kofa amma batasan inane ba a hankali tasa hannu ta bude kofar corridor data gani yasa ta saki ajiyar zuciya cigaba da takowa tayi tana wuce dogon corridor din motsin mutum taji daga gefen ta kofa ce a bude abinda take hange a wurin sai books da akayi jeransu kamar Library, zuciyar ta na kara ingiza ta taje ilai haka akai kuwa kanta tsaye ta kusa cikin wurin bataga kowa ba amma tanajin alamar akwai mutum a wurin…………….





Tray din hannunta ta ajiye akan desk tacigaba da takawa sadaf sadaf bayanshi kawai ta hanga tsaye da jallabiya har kasa hannunta ta dora kan bakinta jikinta yashiga rawa kyaf kyaf kyaf,wani reverse yayi tun shigowar ta yaji ta,ido cikin ido yake kallon ta from head to toe hannunta ba abinda yakeyi sai rawa da gudu ta daka kwana ta fice dakin bayanta ya biyo da sauri a gaban desk yaga kayan abinci dauko su yayi ya biyota yasan kitchen take nema,koda manar ta fito ba inda ta zarce sai gaban wata kofa da tana budewa taga bakomai bane sai kitchen datake nema…..



Gaban fridge tayi ma kanta masauki tana sauke ajiyar zuciya wata iriyar zufa ce take mata sallama daga cikin sumar kanta har zuwa kasan kafafun ta abayar jikinta ta cire tana share zufar kanta,kitt ya budo kofar kitchen rike da tray 4 eyes ya karayi da ita tana goge zufa tsoki yaja yakai tray gun wanke wanke direct ita yake nufowa bako canjin hanya dayasa jikinta yashiga tsuma,yana daf da zuwa kusa da ita tace dan Allah kayi hakuri 😭😭💕




Tsamm ya dauke ta ya dora akan Mable top na kitchen kura mata ido yayi na mintina kadan yafara cewa hey don't play the stranger?i thought you forgot me,or you want to hide something??I didn't know you were halims dad oga👏you should call me uncle,me kike zuwa kinayi a gidana China,wannan letter ya zaro ta daga aljihun shi ya damka mata a hannu kece kika rubata ta,kingano diyata a school dinku take kika ƙulla ƙawance da ita dan ki ganni cikin sauƙi baby girl?…………..

Well karanta nan abinda kika rubuta a cikin letter gani gaki,manar jikinta ya shiga rawa ta kasa magana ba magana nake maki ba?So when did you start crushing on me????……….kujera ya jawo ya zauna gabanta am asking you kinaman shuru,aaaaaa tun ranar dana fara ganin ka, wayace ki fara sona?nayi maki kama da yaran kanana da kike kulawa am i your mate ya jefa mata tambayar………




Shuru tayi hannu yasa ya anshi letter hannunta sannan yace duk zuwan da kikeyi ina gani a Camera ta har letter nan da kikaje kika jefa nagani naso lokacin da na karanta letter nan nima in hadu dake amma is too late kinzo lokacin da zuciya ta tayi sanyi da lokacin ne nayi alkawarin zane ki da bulala marar kunyar yarinya kina zuwa gidana ki tadama matata hankali idan da itace ta tsinci letter nan ta ganoki fa….….





Sumburar baki manar tayi kalmar matar dayace ne ya tsaya mata a makoko kara matsota yayi sosai yace babu girl is that jealous i see? jealous of what?I don't have the right to be jealous of anything, hannunta ya damke da karfi yayi murmushi sannan yace jealous doesn't look good on good girls karki fara abinda bazaki iya ba manar,zan baki shawara ki rike ƙawancen ku da kyau karki rufe idonki akaina bazan taba son kawar diyata ba put this on your head,I know what you're thinking you're my daughter's best friend,it's late you should go to sleep ya fice daga kitchen din gaba ɗaya bayanta ta jingina ta saki wani siririn kuka he's right he's my best friends dad i can't do this to her but why won't my heart listen😭😭😭😭……….





Agogon kitchen ta kalla da kyar ta sauko hijabin ta taja ta fito gaba daya conversation dinsu ya dagula mata lissafi dama duk zaryar datakeyi a boye gidanshi yasani?har letter datayi yana nan ajiye da ita kuma akwai number ta a ciki meyasa bai kirata ba? da gasken yake bazai taba son kawar diyar shi ba?mene aibun haka bafa haramun ne ba a musulunci,halim zata yarda na auri babanta tafiya kawai takeyi batasan inda takesa kafar ta ba,wani mahaukacin jiri ke dibar ta abinda ta dade tanaso dama yana tare da ita amma kuma taren mai hadari,idan halim tagano mezataman wata zuciyar na ingizata da tayi hakuri wata kuma tana ingiza ta akan karta barshi…………..





Kicibus sukayi da kawarta keeee ina kikaje kinsa hankalina ya tashi ina kika sani a gidan nan da zaki fita bodyguards din dady fa basuda mutunci yanaga kina kuka wani ya tabaki a cikinsu?wani sabon kuka ya kwace ma manar har tana shashsheka ta kasa magana taya zata fada ma kawarta aminiyarta tanason babanta bazata iya kuma bazata daina son Shi ba,dady dady juyowa yayi ya kallesu manar nata rizga kuka kagani ko dady daga zuwa nasan wannan yan banzan bodyguards din naka ne suka ganta basu santa ba,kazama shaida kowaye ya tabata saika koreshi aiki……..





Kamar a mafarki manar taji yace ki gano ko waye gobe ki kawo shi office take her to your room ya bude kofa yabarsu nan sai lokacin manar ta dago tace bafa wani ne yaman wani abu ba kitchen naje kofar ta rufeni bansan yazanyi ba inata kuka ina kiranki bakiji ba sai dakyar nasamu ta bude shine nake kuka,gskia na yarda ke yar fari ce kofar ce tasaki kuka me kikaje yi a kitchen?plates nakai aida kin bari cook dinmu tazo zata dauke komai daga yanzu ko spoon aka kawo maki kibar daukewa zasu dawo da kansu su dauke kinji ko bari kukan tou muje ciki haka taja kawarta zuri zuri suka wuce dakin su sunama juna wani irin so da basusan kalar shi ba………






Da asuba manar ce ta tashi halim don suyi sallah after ma sungama sallah bacci suka koma manar ta riga halim tashi hakan ya bata damar kara ficewa daga dakin tana addu'ar Allah yasa ta kara haduwa dashi saidai hakar ta bata cimma ruwa duk iya inda kafarta zata iya zagayawa ta zaga amma batayi kicibus da gogan ba hakan yasa ta dawo kafar ta a sagale ta shige toilet,karar ruwan toilet dinne ma ya tashi halim taga har 11pm……..