BABAN KAWATA

Chapter 9

by @smauta



11:45pm.  
Manar ce zauna kan gado tana kallan message din data tura mashi jiya da dare bayan ta saci number sa a wayar halim yayi mata reply yanzu 
_"Idan kin dage akan kina sona baby girl fine amma kisani mutum na farko dazan sanar itace halim kin yarda?



"Manar?" muryar Halim ce
ta shigo da cup biyu na hot chocolate gashi kisha manar tayi gaggawa ta rufe wayar ta kar halim ta kamata,halim ta zauna kusa da ita. "Kin san me a'a, dady tun mutuwar maman na  
bai taba kallon wata mace ba da sunan so amma yau da safe zuciyar Manar ta buga "Me... me ya faru?"  
"Na ganshi yana murmushi yana kallon wayarsa, raina yana bani wata mace kamar tashigo rayuwar shi,nakumaji yana cewa baby girl karki dagulaman lissafi na dade banganshi cikin irin wnn yanayin ba manar...........

Manar ta rufe bakinta da hannu hawaye na neman kufce mata
_Ya Allah... me zan yi?_

Karar bude kofar ne yasa dukkansu biyu suka firgita dady ne yashigo fuskar nan daure yace kun tashi muryar shi har tsakiyar kanta takaita,Yes daddy manar a sanyaye tace good morning, morning how's your night?fine,halim tace dady kanason wani abu kara shigowa yayi idanunsa suka hadu dana manar tsawon mintina kadan,bakomai naji kamar magana anan dinne shiyasa nashigo ashe kune,get ready zakiman rakiya supermarket...........






A harabar gidan nasu suka tarar dady na jiransu kallo daya yayi masu ya dauke kai dan baiso ta fito da manar ba duk idan halim na nan zaije supermarket tare suke zuwa zai bata list ɗin abinda yake bukata ita zata shiga ta siyo mashi ya zauna mota,gaba yayi suna biye dashi har gaban wata katuwar mota dady kaine zakayi driving yes my dear ko kene zakiyi?a'a da sauri ta bude gaban motar ta shige manar ta kame a owners corner sanyin AC da kamshin turaren shi na rasa mata kai,har gaban wata supermarket sukayi parking dashboard dinsa ya bude ya ciro list da 🏧 card yaba halim idan kuna bukatar wani abu kuma ku dauko da sauri ta rungume dady hakan yaba manar damar gane bashiga zaiyi ba kenan? let's go manar, ouch halim kaina na ciwo bazan iya sauka ba kinsan yadda kaina yakeman muna school shine nakeji, subhanallahi baki fadaman ba kuma aida bamu fito ba a ciki ana siyar da magani bari zan siyo maki zauna kawai a motan,ko gezau baiba sarai yagane karya takeyi 😂 💔...............




Idon shi na kan halim har ta shige supermarket sannan ya juyo da akalar shi wurin manar keeee ya daka mata tsawa bance ki fita a harka ta ba? number na kika dauka zaki matsaman da messages na banza,da karfin hali irin na maiyin makauniyar soyayya manar tace nasan kana sona tunda har kana karanta message dina kana magana bakasan kanayi ba,kaima kana mafarkina kamar yadda nakeyin naka?wani marayan murmushi ya saki yace ohhhh really,ina tausaya maki saboda dalili daya kina kawar diyata amma dana dade da kashe ki a inda ko gawar ki bazaa gani ba fitsararriya kawai,niba fitsararriya bace yazakayi da zuciyar data kamu da sonka a lokacin da ban san ma na fara ba,zan iya barin komai nawa a rayuwa in rabu da kowa dan in rayuwa dakai,kasan irin son da nake maka,nasan kasani amma ka shareni😭😭😭😭ka taimaka ka soni koda kwatan yadda nake sonka ne Khalil.................




Khalil ya kara maimaitawa keeee ni kike kiran sunana kai tsaye?manar ta share hawayen da suka zubo mata tace ban tabajin nauyin ka ko so daya a raina ba kullum ina maka kallo na abokin rayuwata ne,banga dalilin dazaisa kace bazan kira sunan ka ba a duk sigar da nakeso ba,samun kanshi yayi da daga hannunshi yashiga goge mata hawayen sannan yace shiiii rayuwar shi baison kuka,stop crying kinaji na ta daga kai alamar eh,lallashin ta yashiga yi sannan yace am your best friends dad bazan taba kallon ki a cikin masu sona ba ina maki kallon diya ta dana haifa mind you ki samu samari daidai ke bani ba idan kika kara nuna kina sona zanyi kasa kasa dake a takeeee.........




Ya juya ya barta tana share hawayen ta halim ya hango dauke da jakunkuna wasu kuma ana biye da ita,har cikin boot ta saka sannan ta shigo motar manar meyafaru,ciwon kan ne yasaki kuka?zaki karama kanki wani ciwon,ko dady yayi maki wani abu ne a'a halim wani abu ne ya fadaman a ido ga ciwon kai,yana jinsu baice komai ba ya figi motar suka wuce gidansu.................




Cikin zuciyar ta take cewa na zabi na boye maki damuwata halim ba kowane so ake samu da sauki ba,sai nasha wahala sai nayi hakuri saikuma na boye nema na daga karshe na bayyana maki samu koda kuwa karshen zai hassalaki kawata nasan daga baya zaki fahimci damuwata,ta kara sautin kukan ta mai tsuma zuciyaaaa.........






Har sukazo gida bai kara bi ta kansu ba,yana kallo yadda halim duk ta rikice kan kawar tata,gaba yayi yabarsu nan suka shigo har daki ta kaita sannan ta dauko ledar maganin ta bata koda tasha fitowa tayi tabar mata dakin dan tasamu hutu,dady ta hango zaune dinning table a wannan lokacin ba abinda yake tunani a ranshi irin karfin halin manar sai yanzu fa yake tabbatar da cewa dagaske take son nashi,ya zaiyi da yarinyar nan kawar diyar shi ya diyar tashi zata kalli abun shekara nawa daya cire aure a ranshi?zai aure ta ne ko kuwa ta wata hanyar banza zai dasa mata son shi,tunani yake kala kala ya kasa ba kanshi ansa ne yasa ya mike kai tsaye ya nufi dakin shi don yana bukatar hutu yanzu............



A round 4pm wayar halim tayi ringing bodyguard din daddy ne yasa ta dauka
Daddy????ta tashi a firgigi manar tace lafiya meya faru dashi tanajin kanta na mata wani tsauuuu,muryar bodyguards dinne ta dawo dasu hayyacinsu oga ya fadi a toilet gamunan a hanya zamuje asibiti ki biyomu a baya sunan asibitin ya fada mata sannan ya datse kiran..............



Kara kiranshi tayi yana numfashi dady eh yanayi amma jikin da zafi sosai wani ihu ta buga kuna royal hospital dinne yanzu eh miss halim gamu a bakin gate basu tsaya wani shiri ba dukkan su suka fada mota halim ta figesu a mugun guje.........



Hospital



Daddy ne suka tarar dashi a kwance hannunsa sanye da drip bodyguard dinne yake mata bayani doctor yace ciwon ciki ne mai tsanani yakeyi temperature jikinshi takai 40°kuma yana yawan aiki bai huta ba,ya kamata ya zauna a asibitin na tsawon 24hours,halim kuka ta fashe dashi ta fada jikin manar hakuri take bata itama idan za'a tona ranta ita kadai tasan tashin hankalin da take ciki,kiyi hakuri ta juya ta kalli bodyguards din tunda kuka kawo shi a haka yake Yes ma subhanallahi ta furta a ranta,halim na'am kije gida ki hado mashi black tea ki taho da habbatusssuda da zuma yana farkawa ya fara sha zaya samu sauki nizan zauna maki dashi a nan In Shaa Allah daddy zai samu sauki kinji jeki ina nan kome kenan zamuyi waya..............





Jiki a sanyaye ta fito tana gab da fita taga doctor daya duba dady nata sun dauki kusan 1hour yana mata bayanin ciwon baban nata harda stress baya hutawa sai wurin 5:40 tabar asibitin ta nufi hanyar gida har lokacin manar na nan zaune kusada gadon nashi tanata mashi addu'a tana tofa wa akanshi, zuciyar ta na bugawa tace wannan gwaji ne daga Allah dakin shuru sai karar na'urorin dakin dake aiki,tashi tayi ta dauko towel ta jikashi da wuri tana shafa masa a gashin shi,tana cikin hakan ne ya farka da sauri ta kara matsawa kusa dashi ka farka,karkaman haka dan Allah karka tafi kabarni wlh idan ta tafi kashe kaina zanyi bodyguards dinshi dake tsaye cikin dakin yayima alama da ya fita,fita yayi ya yunkura zai tashi batasan ma tayi ba ta kama hannun shi kamar yaro ta zaunar dashi,me kikeyi anan shine tambayar farko daya fara mata, muryar sa tayi rauni sosai ta marasa lafiya dan Allah kadaina mgn ka kwanta jikinka ba karfi dariyar karfin hali kawai yayi mata ruwa ta dauko tace sha ruwa Please amsa yayi ba gardama ya kafa bakin shi saida yasha ruwan enough sannan,yace meyasaki kuka saboda banida lafiya ko saboda halim?samun kanta tayi da cewa duka,karya katse ta ne yasa yace saboda ni kike nan,manar tayi shuru hawaye na cigaba da kai kawo a saman kyakkyawar fuskar ta hannun shi ya daga ya shafo ruwan hawayen sannan yace cry cry baby duk yau kuka kikeyi ko,manar kinsan menene SO?



Bari in fada maki ke kina wani irin so mafi muni a cikin soyayya sai tari ya sarke shi da sauri ta masto dan Allah karka mutu dan Allah shhhh bazan mutu ba inda dalilin rayuwa a yanzu kodan saboda diyata kwal daya halim where is she? Nace taje gida ta kawo tea da habbatusssauda,kada kanshi yayi alamar gamsuwa,tana zaune kan kujera halim ta budo kofar da gudu dady ka tashi manar baiyi wani abu ba duk tausayin kawar ta ya kamata lokaci daya,har kan gadon ta zauna tace dady doctor yace wannan ciwon naka gaba dayan shi stress pls and pls kodan ni Ka rage banida kowa sai kai dady idan ka tafi wazan kama,hannunshi ya manar yace wannan zata zamar maki uwa uba koda babu raina kidaina tunanin mutuwa me kika kawoman Black tea,bani insha saiki kirawoman doctor inason ganin shi........