Chapter 12
BOOK TWO
PAGE 01
بسم الله الرحمن الرحيم
Kwance ya ke akan bed wanda ya kasance na glass me kwari, gaba ɗaya jikinshi babu kyan gani saboda tako'ina ƙonuwace duk ta dalje, yayinta gangar jikinshi ta ke a buɗe sai iya al'aurarshi kaɗai aka rufe da wani ɗan kyalle fari, ba yau na saba ganin ƙuna ba amma wannan da na gani ta bala'in ɗaga min hankali, da ya ke gaf sosai nike da shi hakan ya bawa zafin hucin wutar da ke cinshi fesomin, wani irin jah da baya nai jikina na karkarwa, yayinda harshena yai nauyin wajen furta koda kalma ɗaya ce, da ƙyar nai nasarar janyo kalmar.
" Innalillahi, ZAFIN WUTA🔥 ke fitowa daga jikinshi." Na faɗi ina durƙushewa ƙasa a daidai saitin inda Mommy ta ke tsaye ta na sharer hawayen da suka ƙi tsayawa, kama ni ta yi tare da miƙar da ni tsaye sannan ta matse min kafaɗun da tsananin ƙarfin ta na jijjiga ni yayinda matsanancin tashin hankali ya baibaye fuskarta.
Wa ta irinyar fizga na yi na kwace kaina daga riƙon da taimin, yayin da nai baya-baya kamar zan faɗi sai kuma na tsaya ƙyam akan ƙafafuwana, wa ta iriyar iska me sanyin gaskece ta baibaye ɗakin, yayinda idanuwa suka sauya launi zuwa kalar shuɗi, da wa ni irin hanzari na sada kaina da inda Fauzan ke kwance ya na barcin azaba, ban san y akai ba sai dai kawai na g hannuna ya ɗaga da kanshi bai suka ako ina ba sai akan fuskarshi wacce batad maraba da kwarangwal sai fatar dake rufe da ita, saukar hannuna ke da wuya wani irin hayaƙi wanda ke fitar da wuta ya tashi yasa, sake yawata hannuna nai a fuskar ta shi, aiko duk inda na saka hannuna sai wannan baƙin yahaƙin ya tashi yai sama, idan yai sama sai ya ɓace ɓat, wa ta iriyar ajiyar zuciyar salama Fauzan ya sauke, yayinda fuskarsi tai wani irin haske fayau, wannan baƙin ƙunar duk ya ɓace, a hankali ya fara buɗe idonshi, hanuna nakai saiyin idon na shi na danna da tsananin ƙarfi ina sakin nishi da gurnani, sai ga wani abu na tsiyayowa marar kyan ganni.
Mamaki da tsoro ne ya ya baibaye fuskokin Mommy, Sulaima, Pahpah da Hajjo, yayinda suke ganin yanda hayaƙi ke fita daga jikinshi ni kuma wannan hallitar wacce na gani a cikin mafarkina ce nike gani a zahiri kwance akan wannan bawan Allan ta na cinye tsokar jikinshi, idan ta cinye tsokar sai ta hura ma ahi wutar cikin bakinshi a wajen sai ta koma wani wajen kuma.
Hannuna nakan fuskarshi jikina ya fara karkarwa, ban janye hannun nawa ba har sai da ƙafafuwana suka lankwashe kansu sukai nasarar kayar da ni ƙasa, wani irin turirin sanyi ne ya fara fitowa daga ƙofofin gargasar jikina ya na yin sama ganyar da wannan hayaƙin ya bi, zubewa nai a kasan wajen a sume.
A can cikin daji kuma bayan Sarauniya Zubudiyyace ta biyo bayan baƙin Aljani Zuka wanda jikinshi ya ƙone sosai da sosai, gudu ya ke tsulawa ya na ketawa ta jikin manya-manyan bishiyu amma sai da Sarauniya ɗiyar sarkin ruwa ta cimmashi, ba tai wata-wata ba ta saka ƙafarta me fitar da tururin ƙanƙara ta danna bindinshi, wa ta iriyar ƙarar azaba ya saki wacce sai da ta karaɗe baƙin dajin, aiko nan ƙananun ƴaƴan aljannu da tsunsaye harma da hallitun da ke rayuwa ciki suka dinga guduwa domin neman wajen ɓuya, dan sarai sun san wacece Sarauniya Zubudiyya ƴar sarkin ruwa, ba ta barin bashi ga duk wanda yai ba daidai ba, launin azabobi iri-iri ta dinga ganawa Zuka wanda tun ya na da ƙarfin karewa har ya haƙura ya saduda ta azabtar da shi yanda ya kamata, sannan ta umurci wasu aljannu akan su kai ma ta shi bakin kogon hukunci.
Duk wannan dambarwar da aka gudanar ina ganin komi a cikin barcina, yayinda a zahiri na shiga yin wa ta iriyar jijjiga ina burgima, Hajjo ce ta matso inda nike ta shiga tofa min addu'o'i, cikin ikon Allah na koma daidai na daina birgimar na daina gurnani sai barci me nauyi da yai gaba da ni.
Kallon su Pahpah da mamaki ya gama kashe ta yi tare da faɗin.
"Ko zo muje da yardar Ubangiji babu abin da zai faru, sai ma nasara da za'a samu".
Haka Hajjo ta kaɗa kawunansu suka fice suka barmu, bayan kusan mintuna talatin da faɗuwata na farfaro, amma jikina ta ko ina ciwo ya ke min, ga hannuna da yai wani irin jawur sai azabar zafi ya ke min.
Addu'ar tashi daga barci na karanto tare da tashi zaune ina murza ido, buɗe idona ke da wuya na ganni awannan ɗakin wanda nai zaton mafarki na yi, a sukwane na kai dubana zuwa wajen gadon da wannan bawan Allan ya ke kwance, aiko karaf idanuwana suka sarƙafe a cikin na shi, wani irin hantsalowa zuciyata tai kamar me shirin fitowa waje, ya na nan kwance kamar gawa, jikinshi ko ina yayi baƙi wasu uwaren kuma duk sun kwalje su na fitar da ruwa irin na ƙonuwa, wa ni irin sanyi ne ke fitowa daga rinannun idanuwanshi ya na shiga cikin nawa idon, da kyar na samu na janye idona daga kallonshi zuciyata na dokawa da ƙarfi, ga wa ta iriyar kasala da ta baibaye ni na gagara ɗaga koda hannuna ne, sai de lumshe ido da nai ina sauraron bugun zuciyata da ya haɗu da wa ta zuciyar wacce ba tawa ba suka dinga dokawa a tare a cikin ƙirjina.
Ɓangaren Fauzan ma haka ya cinci kanshi cikin wani yanayi me wuyar fassarawa, yayin da wa ta iriyar nutsuwa ta baibaye ruhinshi, ga wani irin sanyi me daɗi irin wanda ya daɗe ya na buƙatar samu dan samu sassauci daga halin azabar da ya shiga, amma hakan bai samu ba sai yanzu, bugu da ƙari wani irin dokawa da zuciyar ta dinga yi a cikin ƙirjinshi wanda a baya tai ma shi nauyi kamar andanne ma shi ita da ƙaton dutse, sannan kuma kallon wannan kyakkywar halitar ta wa ta saka shi cikin wani yanayi wanda ya mance da shi a ɗan tsukinan saboda azabar ZAFIN WUTAR da yake barazanar tafiya da rayuwarshi.
A hankali ya lumshe idanuwanshi ya na jin wannan sanyin na safkar ma shi da kasala wacce ke barazanar sauya yanayinshi zuwa wani abu daban.
Wasu manyan zungura-zunguran jajayen aljannune suka ɗauki Zuka zuwa kogin hutunta wanda yai wa Sarki ko Sarauniya laifi, ya na turjewa gami da bayar da haƙuri amma sam babu ki babu gani suka cicciɓeshi suka wular a cikin wannan kogin wanda ke kwance sai lunƙaya ya ke yana fitar da tururin sanyi.
Lokacin da fatar jikinshi ke sulluɓewa saboda tsananin sanyin azabar da ake gana ma shi, lokacin ne yai alƙawari gami da alwashi akan wasu mutane guda biyu.
AGEGE.
Tun bayan dawowar Abba wanda Yaya Haisam yai ma shi rakiya saboda yanda ya ruɗe ya kuma tsorata da irin gigitacciyar kyautar da Alhaji Abdallah me gwalagwalai yai ma shi.
Rungume ya ke da ɓakar ƙatuwar jakar da aka loda manya manyan kuɗaɗe wanda suke barazanar ɗauke ji da ganinshi.....✍️