ZAFIN WUTA

Chapter 13

by @maryamstar248

Version:1.0 StartHTML:0000000156 EndHTML:0000098000 StartFragment:0000000469 EndFragment:0000097992

 

         CHAPTER 2 

بسم الله الرحمن الرحيم 

Sai faman zare idanuwa ya ke yana shege lahira, gumin ruɗu da farin ciki sai karyo ma shi ya ke tun daga cikin kai ya na bin fuskarshi, a tsakiyar gida ya zauna sai ƙara ƙanƙame jakar ya ke kamar wani zai kwace, Umma ce ta fara fitowa kamar wacce aka hankaɗo, zaninta a hannu sai faman ɗaurashi ta ke amma yaƙi ya bata haɗin kai wajen ɗautuwa ta daɗi, ya yinda ta ke ta faman washe washeshen bakinta kamar zai  rabe biyu, matsowa ta yi kusa da Abba tare da yunƙurin  janyo jakar za ta ƙwace, wani irin wawan bahagon mari Abba ya sauke ma ta tare da sake ƙanƙame jakarshi ya na juya ma ta baya. 

 

Sak Umma tai jin saukar gigitacen marin da ya kusa tarwatse ji da ganinta, lokaci guda ta kai ƙasa taɓas ta na ƙifta idanuwanta. 

 

Mama na tsaye ƙofar ɗakinta bata ce komi ba dan ita yau ta fita harkar kowa na gidan saboda rabata da ni da Abba yai, a hakama wai dan batasan abin da ya faruba a can gidan aikatau ɗin. 

 

Ganin Abba ya kasa magana ya saka Yaya Hashim fara yi musu bayanin komi dalla-dalla. 

 

Abin da ya faru bayan Pahpah ya tabbatar da Abba ne Babana. 

 

      Musabaha sukai bakin Abba kamar zai ɓare, sannan Pahpah ya nemi da su keɓe ya na da muhimmiyar magana,  ba musu Abba ya bishi jiki na rawa. 

 

    "Amm dama Malam ba komi ne ya saka na nemi keɓewa da kai ba sai wa ta alfarma da nike nema a wajenka, nasan abin da nauyi amma  kuma insha Allah ina abin zai zama alkairi a goben yaranmu." 

 

      "Haba Alhajin Allah, ai kawai ka yi maganarka kanka tsaye babu kwana, yo Allah na tuba ai kawuce neman alfarma a wajen talaka irina sai dai ka bada umurni." 

 

Jinjina kai Pahpah ya yi tare da nazarin maganar Abba sannan ya nisa ya ce. 

 

        "Ita yarinyar da za ta yi aikin jinya ƴarka ce???." 

 

Sai da gaban Abba yai mummumar bugawa, wa ni tunani ya gifta ta cikin kanshi,  sannan ya yi saurin waske wa ya ce. 

 

     "Am..ih...ih yarinyata ce, duk duniya bata da wani uba da ya wuce ni." 

 

"Ma sha Allah, to ina neman aurenta, ka bawa ɗana aurenta." 

 

Kwalalo ido Abba ya yi tare da zamo ɗuwawunshi daga kan sopa ya shiba in ina kafin da kyar ya ce. 

 

"Aure kuma, aure fa kace Alhajin Allah." 

 

  Abba yai maganar wani irin farin cikina baibaye fuskarshi. 

 

"Ih aurenta nike nemawa ɗana  Fauzan wanda shine za ta yi jinyar, to ganin ita yanzu yarinyace matashiya bai kamata ace ta keɓanta da wanda ba muharraminta ba ne, sannan kuma akwai wasu dalilan da ya saka na ce haka, na kuma yaba da nutsuwar ita yarinyar, ka yanke ma ta sadaki daga milion daƴa har zuwa inda tunanika ya yanke." 

 

Naman fuskar Abba ne  ya shiga rawa, yayinda jajayen idanuwanshi suka yo waje, lissafi da kwancewa ya shiga yi a kwanyarshi, amma duk yanda ya so ya lissafa adadin da zai faɗa abin ya gagara, da kyar ya fizgo maganar daga bakinshi ya na haɗiyar yawu ya ce. 

 

        "Alhajin Allah ai ina ganin da kuɗin tambaya da na lefo da sadakin ku bada miliyan biyar kawai Allah ya basu zaman lafiya." 

 

"To babu laifi hakan, zan bada milion goma gaba ɗaya, amma banda lefe wannan kam mu zamuyi ma ta, yanzu ka sanar da wakilanta da waɗanɗa suka kamata su sa ni, zuwa anjima bayan sallar la'asar sai a ɗaura auren dan da buƙatar ayi shi cikin gaugawa saboda akwai wasu magunguna da wani babban me bada magani a India ya bani, kuma ya tabbatar min da idan akai amfani da maganin ta hanyar da ya dace in sha Allah za'a samu dacewa." 

 

"Allah sarki, to idan babu damuwa mi zai hana a ɗaura ayanzu kawai sai Yayanta Hashimu ya wakilceta, tunda maganar gaskiya mu ba ƴannan bane, a ƙarance za'a iya ɗaukar sati ɗaya ba tare da an haɗo kan dangi ba saboda kowa da inda ya ke rayuwa." 

 

Pahpah amincewa yai ba tare da ya ja zancen ba, shi ta samun lafiyar ɗan shi kawai ya ke. 

 

Limamin da ke jan Sallah a cikin masallacin cikin gidan aka kira tare da tsirarun ma'aika masu nutsuwa da hankali sai Yaya Hashim, su ne waɗanda suka shaida ɗauruwar igiyoyi uku kwarara akan MUHAMMAD FAUZAN ABDALLAH, da amaryarsa MUBARAKHA MUHAMMAD IBRAHIM. 

 

Auren da ya ɗaurewa mutanen da suka shada kai, domin kuwa abin da ɗaure kai musamman da sukaga Abba a matsayin uban amarya, a kaf garin Legos babu wanda bai san wanene ABDALLAH ME GWALAGWALAIBA. 

 

Cike da fatan samawa Fauzan mafita Pahpah ke addu'ar Allah ya dawwamar da albarka a cikin aure, tare da fatan ƙulluwar alaƙa me tsananin ƙarfi a tsakanin ma'auratan biyu, waɗanda akaiwa kutse cikin rayuwarsu aka zartar da hukunci ba tare da amincewa ko sahalewar su ba, tausayina ne ya luluɓe Pahpah ya na ganin kamar an shiga haƙƙina da yawa, duba da zamanin yanzu da ƴan mata da yawa su keyiwa kamsu zaɓin abokan rayuwa. 

 

Abba bakinan har kunne ya na ta gandala da godiya ga Allah da ya kawo shi wannan rana wacce za ta kafa tarihi a rayuwarshi, ranar da baƙin talauci me kama da ZAFIN WUTA zai yaye, arziƙi dawamamme ya maye gurbinsa, albarkar da ya daɗe da ɗebemin yau ita ce ya ke zundumamin babu ƙaƙƙautawa, albarkar da niban san yana yi ba, tun da ba agaban idona ya ke ba. 

 

Numfashi Yaya Hashim ya sauke tare da satar kallon inda Mama ke tsaye ta na aiko musu da mugun kallo wanda ya nemi ya hautsina ma shi hanjin ciki, Abbama kallonta ya ke duk jikinshi ya yi sanyi, sai yanzu yaga rashin kyautawar abin da ya aikata ma ta, sanin kanshi ne akaf gidan babh wanda mukai sabo da shaƙuwa da shi irin Mama, komi na samo Mama, idan wani abu ya same ni to Mama ce zata zauna tare da ni. 

 

Umma kuwa dukda cewa ta maru ba kaɗanba, dan Abba ya shammaceta lokacin da tazo karɓar jakar hannunshi, ya ƙe ta shiga yi ta na nuna murna da farin cikin auren da aka ɗaura min babu shiri, ta na ganin hakan shine ya dace da ni tunda bani da wani gata. 

 

Shigewa ɗaki Mama ta yi tare da fashewa da kukan baƙin cikin halin Abba, ta tabbata kuɗi ya gani ya bayar da aurena haka kamar auren kaza, ta yi kuka harta godewa Allah kafin daga bisani ta shiga jero addu'oin nema min kariya aduk inda nike......✍️