CHAPTER 1
AMARYAR GADO
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
AISHA SANI ABDULLAHI
Xayyeesherthul-humaerath
©️2026
Jan hankali: Wannan littafi ƙirƙirarriyar riga ce da aka saka wa kowace ƙaddara da ke cikinsa suna. Kada wani labari ko sirri da aka bayyana a cikinsa ya sa a fassara shi da rayuwar wani na gaske.
Gargaɗi: Haƙƙin wallafar littafin na marubuciya ce kaɗai. Ba a yarda a juye shi zuwa wani harshe, ko a canza shi zuwa sautin murya (audio) ba tare da rubutacciyar yarjejeniya ba.
SHAFI NA ƊAYA
Zaune suke a cikin mota, Ahmad ya zura mata idanu, ko kyaftawa baya yi, yana sakin murmushi. Farida ta gyara zamanta, tana sa hannunta a fuskarsa ta ce, “Yah Ahmad, wannan kallon fa? Kamar yau ka fara ganina ne wai?”
Murmushi ya yi yana cewa, “To Reedah, in ban kalle ki ba wa kike so in kalla? Ko kin fi so in je in ta kallon wasu matan a waje?”
Nan take yanayinta ya sauya, ta ɓata rai cikin shagwaɓa ta fara faɗin, “A kan me? Ni wallahi aa. Ni kaɗai za ka kalla, ni kaɗai na ishe ka. Kuma ai ina addu’a duk ranar da ka sa kyawawan idanunka ka kalli wata, to makancewa za su yi.”
Ahmad ya buɗe baki ya ce, “Ah! Lamarin har ya kai ga munin hakan? Ni me ma zai kai ni kallon wasu mata bayan ina da ke? Kin san meye?”
Farida ta girgiza kai.
“A idanuna kin fi dukkanin sauran matan da ke duniya kyau. A kullum ji nake ana ƙara mini so da ƙaunarki cikin zuciya. Duk da cewa auren haɗi za a yi mana kamar yadda aka saba yi wa kowa, amma ni ji nake a raina dama can kece kika cancanci zama mata a gare ni, kuma kece zaɓin raina. Ina fatan na rayu da ke har ranar da numfashi zai bar gangar jikina. Ina son ki, Reedah.”
Farida ta yi ajiyar numfashi ta ce, “Ni sai nake ganin kamar tun muna cikin ciki iyayenmu suka kulla wannan soyayyar. Ni dai fatana kawai, kar wata rana ka ji a ranka ba ka so na, ka ji wata kake so, ko ka tafi ka bar ni. Ba zan iya rayuwa ba babu kai, Yah Ahmad. Ka gama yi wa zuciyata sabo da soyayyarka.”
Hannunta ya riƙe ya haɗa da nasa ya ce, “Mutuwa ka raba, Reedah. Na miki alƙawari ba zan taɓa barinki ba sai ranar da numfashi ya bar jikina.”
Farida ta saki murmushi ta ce, “Ni ma haka, ina sonka Yah Ahmad ɗina. Yanzu yaushe ne tafiyarku?”
Ahmad ya ce, “gobe da safe ne, amma fa da ace da yadda zan yi, gaskiya ba zan je ba. Amma sun jaddada cewa wajibi ne ga duk wani ma’aikaci.”
Farida ta ja dogon numfashi tana cewa, “Allah Ya sa hakan ne mafi alkhairi. Ya kai ku lafiya, Ya dawo da ku lafiya.”
“Ameen, Reedah na. Ki kula min da kanki, kin ji kuma…”
Knocking window ɗin da aka fara yi musu ne ya katse shi ba tare da ya ƙarasa maganar ba, ya ɗage glass ɗin. Sufyan ne tsaye, ya ja gajeren tsaki.
“Baba na kiranka.” Yana faɗa ya juya zai tafi, Ahmad ya bude kofar ya fita Farida ma ta fita ya ƙwalawa Sufyan kira.
“Miye haka ne, Sufyan? Kai ba za ka canja halinka ba? To wa kake yi wa tsakin?” Ahmad ya faɗa.
Wurgawa Farida wani mummunan kallo Sufyan ya yi, ita ma ta bi sa da harara.
“Ni fa ka daina bina da irin wannan kallon raini, don ni ba sa’arka ba ce. Mutum sai shegen faɗin raini banza da wofi.”
Cikin fushi Sufyan ya ce, “Kar ki kuskura ki fara, kina nan gari guda a wajen.”
Ahmad ya ce, “Oh, a gabana ma ba za ku daina irin wannan halin ba? Ina wajen? Sufyan, ai ta girme ka, sannan ko ba komai, wacce zan aura ce. Kamar ni take a gare ka. Ka kiyayi ɓacin raina.”
Sufyan ya ce, “Ai ni wallahi na gode Allah da wannan haɗin ya tsaya a kanku. Kuma kai da aka tashi ma sai aka ba ka wacce ta fi kowa muni a gidan nan. Ga ta jibgegiyya kamar gari gudu, ko in ce jikar Samudawa. Wannan ai sai ta dinga ba ka tsoro. Muni har yana magana, wallahi an cuce…”
Kafin ya ƙarasa, Farida ta fashe da kuka ta shige cikin gida a guje. Ahmad na daga hannu ya falla wa Sufyan mari.
“A kan waccer mummunar bogazar za ka mare ni?” Sufyan ya faɗa, hannunsa yana riƙe da kumatunsa.
Ahmad ya ce, “Oh, wai ci gaba da faɗin hakan ka yi? Wai kai yaushe za ka yi hankali ne, Sufyan? Wa ya ce maka kyawun fuska ko sura ake dubawa wajen aure? Wannan babban kuskure ne, kuma in ka biye wa wannan tunanin za ka yi da-na-sani.”
Ahmad na gama faɗin hakan ya wuce ya bi bayan Farida ciki.
Tana shiga ta faɗa jikin Inno a falo tana kuka.
Su uku ne zaune suna hira Kawu hamza, Baba Haruna sai Inno.
Baba Haruna ya ce, “Ke kuma mene ne haka? Me ya faru?”
Inno ta ɗaga ta ta ce, “Faridatu, lafiya?”
Kawu Hamza ya ce, “Yoo, zai wuce. Shagwaɓar autanci ce ta tashi.”
Cikin muryar kuka Farida ta ce, “Wai Sufyan ne yake cewa an cuce Yah Ahmad da aka ba sa ni, wai ni mummuna ce kuma mai kiran Samudawa.” Ta ƙarasa maganar tana ƙara fashewa da kuka, daidai lokacin da Ahmad ya shiga falon.
Cikin fushi Baba Haruna ya ce, “Wai shi wannan yaron wani iri ne? Ko don ya ga ana ƙyale sa ne? Zan ɗauki mataki kuwa.”
Ahmad ya ce, “Baba, ai ma na yi masa nasiha, ya ji In Sha Allah. Reedah, ki yi haƙuri. Kin san har yanzu wautar yarinta na tare da Sufyan.”
Inno ta ɗaga ta tana share mata hawaye ta ce, “Yoo, ai ni sai yanzu na fahimci cewa Sufyanu na baƙin ciki ne da ni, domin kaf jikokin gidan nan babu wacce ta yo ni sak ta ko ina illa Faridatu. Kuma in dai batun kyau ne, ai ba a faɗa mana ba. Sai dai hassada, kila baƙin cikin rashin cewa ba shi zai same ki ba ne yake wannan ƙurarin. Kwantar da hankalinki.”
Ahmad ya ce, “Baba, gani. Sufyan ya ce kana kirana.”
“Eh, amma yanzu bari kawai ka ɗauki Farida ku ɗan fita, ka kawar mata da baƙin ran da wancen mashirmacin ya sa ta.” Cewar Baba Haruna.
Inno ta ce, “Yawwa Haruna, ai ko ka kyauta. A je a sha wannan kayan sanyin ickirim yake ko me? Ni ma kar a manta da ni, a riƙo mini da nawa fisabilillah, don ya na yi mini.”
Dukansu sai da suka dara.
Farida ta ɗago tana dariya ta ce, “Ice cream fa ake cewa.”
Inno ta ce, “Ohho dai, ni a tawo min da nawa. Ina son abin.”
Cikin sigar tsokana Ahmad ya ce, “Inno dai akwai baƙin kwaɗayi.”
“Ka faɗa wa iyayenku.”
Dariya suka yi dukansu, suka fice daga falon.
Suna fita ba inda suka nufa sai Crispy Creme. Suka shiga suka sa order. Bayan an kawo musu, sun fara sha ne Farida ta ce, “Yah Ahmad, in tambaye ka?”
Ahmad ya gyaɗa kai. “Ina ji, Reedah.”
“Ni kaina na san ni ba kyakkyawa ba ce. Don Allah, ba ka ji a ranka cewa da gaske an cuce ka da aka ba ka ni ba? Musamman yadda kai ka kasance farin fata kuma kyak…”
Kafin ta ƙarasa ya rufe mata baki.
“Kar in ƙara ji. Kar ki ƙara sa wa a ranki cewa wai ba ki da kyau. Babu halittar da Allah Ya yi mummuna. Kowa mai kyau ne, sai dai kowa da yadda yake nuna nasa kyawun. In ba ki so kanki, kin ji a ranki ke mai kyau ba ce, so kike wani ya faɗa miki? Aa, ki so kanki a duk yadda kike. Kuma ni har cikin raina nake faɗa miki, ban taɓa ganin muni a tattare da ke ba. A kullum ƙara yi mini kyau kike, kuma ina son ki a duk yadda za ki kasance. Sannan mafi maƙurar kyau ai yana ga zuciya, ba ga surar jiki ba.”
Farida ta numfasa. “Na gode, Yah Ahmad.”
Wasa da dariya ya dinga janta da shi har sai da ya tabbatar walwalarta ta dawo. Suka yi hotuna, tukun suka yi wa Inno takeaway, suka nufi hanyar gida.
Washegari da safe, Ahmad zai tafi, ya kira Farida za su yi sallama. Gaba ɗaya ji suka yi ba sa son rabuwa. Hakan ya sa tun da ya shiga mota suke waya har sai da network ya ɗauke.