MATAR GIDA PAGE 8
MATAR GIDA 008
SHUUKRAN/022
P8
Karfe tara da rabi Ɗalha ya yi parking a kofar kamfani,harda sanyin Ac dake cikin motar Ɗalha ya jiƙe da zufa shakaf saboda rashin wanka da bai yi ba,ga kuma damuwa da yake ciki na rashin zuwa aiki da wuri yau,harda ya san yau ɗin yana da meeting mai muhimmanci amma babu yadda ya iya,ba tare da ɓata lokaci ba ya fita daga motar hannusa riƙe da jakar kanbuta,tafiyar mintina shidda ne daga kofar kamfanin zuwa ofishinsa,bayan shigar sa office,zama ya yi kan kujerar sa yana mai da numfashi,a hankali ya rintse idanunsa,buɗe kofar da aka yi ne yasa ya buɗe ido yana bin wanda ya shiga office ɗin da ido abokinsa ne Muhsin,har Muhsin ya samu waje ya zauna Ɗalha na binsa da ido kamar yau ya fara ganinsa,bayan Muhsin ya zauna ne ya mayar da dubansa ga Ɗalha ya ce ''Mallam ya aka yi sai yanzu ka shigo?tun ɗazu ana ta kiran ka baka ɗaga waya Allah yasa dai lafiya'' ɓoyayyar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke kafin ya ce ''lafiya ƙlau'' shiru ya yi kamar bazai ce komai ba sai kuma ya fara magana cikin sanyin murya ya ce ''na gaji da ƙazantar Amirah Muhsin duk yadda na yi ta gyara abin ya gagara,a takaice dai jiya ya ce ta je gidansu na yi mata saki ɗaya'' Ɗalha ya yi shiru sai kuma ya ce ''saboda rashin imani irin na Amirah ta tafi ta bar min yara har Fauziyya da ke shan nono ta tafi ta barta,na yi ta kiran layin ta bata ɗaga wayar daga karshe ma ta kashe wayarta gaba ɗaya,na kira ƙaninta Kabir dan naji ko ta je gida amma da alama bata tafi gida ba,hasilima basu san bata gidana ba,and da safe nan na biya gidan Husnah da alama ita ma bata san na saki Amirah ba'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''ban san yadda zan yi da yaran ba,daren jiya ban samu barci mai kyau ba,na tashi karfe shidda na fara yi masu shirin makaranta amma kaga sai yanzu na samu daman zuwa office ko wanka fa ban yi ba and ban ci komai ba,saboda babu lokaci'' wata irin murmushin gefin baki Muhsin ya yi kafin ya ce ''yanzu ka gane matar ka bata da kazanta kenan kwana ɗaya rak duba yadda ka koma'' Muhsin ya yi shiru yana kallon Ɗalha kamar yadda shi ma yake kallonsa Muhsin ya daura da ''magana ta gaskiya matar ka tana kokari wajen kula da yara harda yaran sun yi mata yawa amma still tana kokari sosai wajen kula da su'' Muhsin ya yi shiru na wasu ƴan sakanni kafin ya daura da ''ina ganin is better ka dawo da matar ka,ko saboda yara da kuma aikin ka,ka gode Allah baƙin da zamu yi meeting da su basu samu daman zuwa ba,oga ya ɗaga meeting sai nan sati biyu masu zuwa'' Ɗalha da ya rufe ido shiru yana sauraran Muhsin ya gyra zama tare da buɗe idanunsa ya ce ''an ɗaga meeting amma ka yi ta kirana kamar kana bina bashi'' Muhsin ya yi murmushi ya ce ''oga ne ke son magana da kai a lokacin,da baka ɗaga waya ba shine ya sanar da ni cewar sai nan da shi biyu za'a yi meeting ɗin'' Ɗalha ya dauki wayarsa tare da faɗin ''bara na kirata Allah yasa ta kunna waya'' Muhsin dai sai kallonsa kawai yake Ɗalha ya kira layin Amirah kusan sau biyar amma wayar a kashe,hakan yasa ya ajiye wayar tare da mayar da dubansa ga Muhsin ya ce ''har yanzu wayarta a kashe'' Muhsin ya ce ''ka kara Ammi ka sanar da ita abinda ka aikata,is better su sani because yanayin da ƙasar nan ke ciki ba ka da tabbacin tana cikin koshin lafiya ko akasin haka,so ina ganin zai fi kyau ka faɗa masu abinda ke faruwa'' numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''Ammi will be mad at me man''! ya faɗa tare da dafe kansa da hannu biyu cikin yanayin damuwa
Taɓe baki Muhsin ya yi kafin ya ce ''kafin ka sake ta ya kamata ka yi wannan tunanin ba yanzu ba,aikin gama ya gama aiy so just tell her'' Ɗalha ya dauke waya ya ce ''bazan iya kiran Ammi ba,zan kira Husnah kawai na faɗa mata in yaso ita sai ta faɗama Ammi'' ya kare magana tare da manna waya a kunne bayan ya yi dailing number Husnah,har wayar ta tsinke Husnah bata ɗaga ba hakan yasa ya ajiye wayar shiru kan tabir dake gabansa, Muhsin ya ce ''is like you are not seriuos kai da ka ke niman matar ka ka ke yin kira ɗaya'' wani kallo Ɗalha ya yiwa Muhsin kafin ya ce ''duk abinda nake saboda yarana na ke yi ba dan ina so zama da Amirah ba'' baki sake Muhsin ke kallon Ɗalha kafin ya ce ''da alama baka daku ba''Ɗalha na shirin magana wayar sa yi ƙara alamar shigar kira Husnah ce ke kiransa bayan ya amsa kiran ne Husnah ta yi magana cikin murmushi ta ce ''aiy ta yi barci,baka daɗe da fita ba barci ya dauke ta'' Ɗalha ya ce ''ok ya yi kyau'' yadda ya yi magana yasa Husnah faɗin ''lafiya kuwa yaya you sound somehow'' shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya yi mata bayanin abinda ke faruwa bayan ta gama sauraran Ɗalha Husnah ta ce ''yanzu ina ta tafi yayah in bata gidansu kuma bata je can gida ba to ina ta tafi?" Ɗalha ya ce ''ban sani ba Husnah the worst part is bata da ƙawaye bata da ƙawa ko ɗaya'' murya can ƙasa Husnah ta ce ''kai ka hanata ƙawaye yayah ka rabata da kowa'' Ɗalha ya yi saurin kawar da zancen ta hanyar faɗin ''just call Ammi and tell her ƙila tana can gida'' Husnah ta ce ''bana tunanin ta je gidan Ammi,da ta je da tuni Ammi ta kiraka'' cike ƙosawa Ɗalha ya ce ''oky call her Please now'' daga haka ya kashe waya shi dai Muhsin kallon Ɗalha kawai yake har sannan yana mamakin abinda Ɗalha ya faɗa da ya ce saboda yara zai dawo da Amirah kenan da ba yaran bazai dawo da ita ba
Unaisa ce zaune cikin ɗakin mahaifiyarta inda mahaifiyarta ke yi mata nasiha kan zamantakewar aure da kuma yadda zata riƙe yaran Ɗalha kamar ƴaƴanta,duk wata nasihar da Mama ke yiwa Unaisa gaba ɗaya hankalin ta baya wajen hasilima chat take da wata ƙawarta kan yadda za su tsara braidal shower,Aisha dake zaune can gefin tana linkin kaya gaba ɗaya hankalinta na kan Unaisa dake chat harda murmushi,haushi da takaici yasa Aisha faɗin ''bani wayar'' Unaisa ta so yiwa Aisha rashin kunya amma ganin babu alamar wasa a fuskar Aisha yasa ta miƙa mata wayar,nan dai ita ma Aisha ta daura nata nasihar Mama ta na yi itama tana yi,a can wajen Ɗalha kuwa bayan Husnah ta kira Ammi ta sanar da ita halin da ake ciki,nan take ta kira Ammi ta kira Ɗalha sosai ta nuna masa ɓacin ranta ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,ta kuma ce masa kafin safiyar gobe tana son ya dawo Amirah gidansa yaje na nemo ta duk inda take ya dawo da ita,cike da kiɗima Ɗalha ya ce ''Ammi ban san inda take ba bayan na gama waya da Husnah na kira Kabir ya ce min bata gidan mahaifinta'' Ammi bata ce masa komai ba ta kashe wayarta,Ammi bata daɗe da kashe waya ba Abba mahaifin Ɗalha ya kira,ganin kiran mahaifinsa ji ya yi numfashin sa na neman tsayawa,sai da ya saita nitsuwarsa kafin ya amsa kiran,bayan sun gama gaisawa ne Abba ya ce ''Hajiya ta sami ni da wata batu kan matarka'' Ɗalha ya ɗanyi shiru na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''eh haka ne Abba'' Abba ya ce ''me ya yi zafi haka Ɗalha me Amirah ta yi maka da zaka yanke wannan hukunci ba tare da niman shawarar ɗaya daga cikin mu ba ni da mahaifiyarka?" Ɗalha ya yi shiru ya ƙasa cewa komai Abba ya ce ''yanzu ina Amirah take?" Ɗalha ya ce ''ban sani ba Abba na yi ta kiran wayarta a kashe tun jiya'' Abba ya ce ''gaskiya baka kyauta ba da ka yanke hukunci ba tare da shawara ba,ka kira ƙawayenta da ƴan uwanta duk sun ce maka bata tare da su?" Ɗalha ya ce ''duk na kira su Abba'' Abba ya ce ''to ka ƙara bincika mu ma zamu taya ka a nan insha allah'' Ɗalha ya yiwa Abba godiya daga haka Abba ya kashe wayar sa,shiru Ɗalha ya yi yana tunanin kalaman da Ammi ta yi masa,akwai shaƙuwa sosai tsakanin Amirah da Ammi,Ammi ta dauki Amirah tamkar ƴarta da haifa duk sanda Ɗalha da Amirah suka je ganin gida,a gidan Ammi Amirah da yara ke uni,muryar Muhsin ne ya katsewa Ɗalha tunanin yadda ya ce ''ina ganin muje office ɗinta mu duba may be har yanzu tana gari'' shiru Ɗalha ya yi ya kafe Muhsin da ido yana tunanin ko sun je office me za su ce,hakan yasa ya ce ''me za mu ce masu? tambayar su zamu yi ko ta je aiki yau? aiy sai su yi tunanin akwai matsala'' murmushi Muhsin ya yi kafin ya ce ''ba ka son a san ka sake ta ne?" ɗan jimm Ɗalha ya yi kafin ya yi magana cikin yanayi na ɗan ɓacewar rai ya ce ''ba haka bane amma tsakani da Allah me zan ce masu?ina niman matata na saketa bata je gidansu ba kuma bata gidan iyayena ba ko me zan ce masu?" cikin kwantar da murya Muhsin ya ce ''clam down ba haka na ke nufi ba'' shiru Muhsin ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''ok ni zan je office ɗin zan ce masu kai nake son gani wayar ka bata shiga so ina son ganin ita Amirah mu yi magana tunda kai ban same ka ba'' ɗage kafaɗu Ɗalha ya yi ya ce ''ok fine''daga haka Muhsin ya fita ɗaga office ɗin,kamar yadda ya faɗa bayan tafiyarsa kamfanin da Amirah ke aiki tambayar office ɗinta ya yi aka nuna masa,abokiyar aikin Amirah ya samu zaune kan kujerar ta,bayan sun gaisa ne ya gabatar da kansa a wajenta matsayin abokin mijin Amirah,kamar yadda ya faɗawa Ɗalha hakan ya yi,amma bayan ya gama jero mata zance ta yi murmushi ta ce ''ikon Allah Amirah ta dauki hutun annaul leave,Allah ya sa dai lafiya saboda tun safe nake kiran wayarta amma baya shiga'' Muhsin ya ce ''ƙila sun yi tafiya ne amma zan cigaba da kiran layin sa'' daga nan ya yi mata sallama ya fita daga office ɗin jiki babu kwari ya koma office ya yiwa Ɗalha bayani,zuwa yanzu jikin Ɗalha ya fara sanyi, ko dai da gaske baya kyauta mata ne ƙila yana cutan ta kamar yadda take faɗa,bai taɓa kawo Amirah zata iya rabuwa da shi ba bare ƴaƴanta da take mugun so har bata iya ɓoye soyayyar ta kan ƴaƴanta,amma an waye gari ya sake ta bata bashi hakuri ba bata yi kuka ba,ta yi tafiyarta ta bar masa yaran gaba ɗaya,sannan babu wanda ta faɗawa inda take,ɗazu bayan fitar Muhsin Ɗalha ya kira Nasir yayan Amirah ya faɗa masa komai babu abinda ya ɓoye masa,daga yadda Nasir ke amsa masa magana Ɗalha ya fahimce ran Nasir ya ɓaci sosai, haka dai ya daure har suka gama magana yadda Nasir ya tabbar masa Amirah bata je gida ba
SHUUKRAN