BABI NA BIYU
By Rasheedat S Director
A haka motocin suka ci gaba da yanke hanya cikin matsanancin gudu...
Har suka nufi hanyar Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja.
Kiran ya sake dawowa.
A karo na huɗu...
Na biyar...
A wannan karon...
M-ARROW ya ja wani dogon tsaki.
“Mtschh...”
Ba tare da ya buɗe idanunsa ba, ya miƙa hannu ya ɗauki wayar.
Ya danna amsa.
Ya kai ta kunnensa.
Shiru...
Sai numfashinsa mai ɗauke da zafin fushi.
Daga cikin wayar ne wata dattijuwar murya mai cike da iko ta fito.
"Hello, Son... where are you? An gaya mini ka shigo gida amma ka sake fita nan take. Bana son ka ɗauki dukkan nauyin ƙasar nan ka ɗora a kanka. Ka bar wannan al’amari a hannuna.
ranar Monday zan sa a shirya min zama da mutanen nan. Komai zai warware. Kana ji na?"
M-ARROW bai amsa ba.
Sai kawai ya furzar da wata iska mai zafi ta hancinsa.
Dad ya ci gaba da magana.
"Son... yaushe za ka daina sadaukar da rayuwarka saboda mutane ne? Kai ma kana da haƙƙin samun kwanciyar hankali. Allah ya san niyyarka, kuma zai saka maka da alkhairi. Ya baka ladar niyyar ka.
Ka tuna lokacin da nake mulki... na yi iya ƙoƙarina domin talakawa, amma daga ƙarshe suka juya mini baya.
ga mahaifiyarka ta yi ta kiranka baka ɗaga ba. Kana sa ta cikin damuwa."
Kafin M-ARROW ya yi magana...
Sai wata murya mai taushi ta karɓi wayar.
"Hello, Arrow..."
Mom ta faɗa cikin tsananin son jin muryar ɗan nata.
Muryarta cike take da damuwa.
"Lafiya kuwa? security's sun gaya mini ka shigo gida amma ban gan ka ba. Me ya sa ba ka ɗaga kirana ba? Kana saka ni cikin damuwa. Please, Arrow... ka bar waɗannan matsalolin ka dawo gida. in kula da kai, ya isa haka yanzu kam kana bukatar nutsuwa da hutu na musamman."
Ta sauke numfashi cike da damuwa irin na uwa mai santsar ƙaunar ɗanta.
kana ta cigaba da magana
"Ko kuma ka tafi UK. Zan zo da kaina in zauna tare da kai. Ka bar Dad ɗin ku zai kula da komai a nan. Don Allah, kada ka lalata kanka saboda wasu mutane.”
M-ARROW ya matse idanunsa da ƙarfi.
Ya sauke wani numfashi mai nauyi.
A hankali, cikin sanyin murya amma har yanzu fushinsa bai lafa ba, ya ce,
“Mom... I'll call you later.”
Shi kaɗai ya faɗa.
Daga nan ya katse kiran.
Ya kashe wayar gaba ɗaya.
Sannan ya jefar da ita a gefensa.
Ba tare da ya sake cewa komai ba.
A wannan lokacin kuma...
Ayarin motocin ya iso Nnamdi Azikiwe International Airport.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba, M-ARROW ya sauka daga motar.
Jami’an tsaronsa suka kewaye shi cikin tsari.
Kai tsaye ya nufi katafaren Private Jet ɗinsa.
Mintuna kaɗan bayan ya shiga...
Ƙofofin jirgin suka rufe.
Injinansa suka fara ruri.
Daga bisani...
Jirgin ya buɗe fikafikansa.
Cikin daƙiƙu kaɗan...
Ya ɗaga sama, ya bar ƙasar Abuja a ƙasa.
A ɓangaren iyayensa kuwa...
Mom ta zaro wayar daga kunnenta a hankali, idanunta cike da mamaki da damuwa.
Ta ɗan kalli fuskar wayar na wasu daƙiƙu, tamkar tana sa ran ɗan nata zai sake kiran ta.
Sai ta ɗaga idonta ta kalli Dad.
Fuskarta cike da tsantsar damuwa.
Cikin sanyin murya ta ce,
"Alhaji... kar yaron nan ya kashe duk wayoyinsa fa. Ka san halinsa. Duk lokacin da ransa ya ɓaci, yana katse hulɗa da kowa. Zai kashe duk wayoyinsa, mu rasa hanyar samun sa gaba ɗaya."
Ta sauke numfashi mai nauyi.
"Wallahi mutanen nan za su lalata mini kwakwalwar yarona. Ko mu da muka taɓa shugabanci, ba mu taɓa ɗaukar dukkan damuwar mutane muka ɗora ta a zukatanmu har ta hana mu walwala ba."
Muryarta ta fara rawa.
Idanunta suka cika da ƙwalla.
"Please, Alhaji... ka yi wani abu. Bana so ɗana ya cigaba da shiga cikin irin wannan damuwar. Wallahi ba zan iya jurewa ba."
Ta girgiza kanta cikin takaici.
"Ba zai zama bawan mutane a kowane lokaci ba. Kullum yana sadaukar da lokacinsa saboda wasu. Ba shi da lokacin kansa... balle namu mu iyayensa."
Ta yi shiru na wasu daƙiƙu.
Sai ta ci gaba da magana cikin muryar da ta nuna tsantsar ƙaunar uwa.
"Ni yanzu na gaji. Ina son ɗana ya dawo kusa da ni. Ya huta. Ya yi rayuwar da ta dace da shi. He's a prince, Alhaji... jinin sarauta ne ke yawo a jikinsa, ba jinin wahala ba."
Ta share hawayen da suka fara taruwa a gefen idanunta.
"Ɗana... ba bawan talakawa ba ne. Ya isa haka. Ya yi abin da ya kamata ya yi. Yanzu lokaci ya yi da zai rayu domin kansa."
Dad ya kalli matarsa cikin natsuwa.
Ya san wannan ba magana ce ta fushi ba...
Maganar zuciyar uwa ce.
A hankali ya kai hannu ya dafa kafaɗarta, yana bubbugawa cikin lallashi.
Sannan ya ce,
"Ki kwantar da hankalinki."
Ya ɗan yi murmushi mai laushi.
"Ko kin mance ɗan naki sadauki ne jinin Arrow Shadum ne ke yawo a jikinsa."
Ya ɗan jingina da kujerarsa.
"Kin san halinsa. Idan ya yanke shawara, ba abu ne mai sauƙi a sauya masa ra’ayi ba. Ban san dalilin da ya sa ya zaɓi irin wannan rayuwar ba, alhali an haife shi cikin alfarma da iko.
Da zai so, zai iya rayuwa ba tare da ya damu da matsalolin kowa ba... amma zuciyarsa ta fi karkata ga talakawa fiye da yadda take karkata ga kansa."
Ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba.
"Duk da haka... zai dawo. Jinin sarauta baya ɓacewa. Za mu ba shi duk abin da yake buƙata domin hankalinsa ya kwanta."
Mom ta gyaɗa kai a hankali.
Sai dai damuwar da ke cikin zuciyarta ba ta ragu ba.
Ta sake ɗaukar wayarta.
Ta sake danna lambar M-ARROW.
Bayan ƴan daƙiƙu...
Sai ta ji muryar na’ura.
“The number you are trying to reach is switched off.”
Ta runtse idanunta cikin takaici.
Ta sauke wayar a hankali.
Dad ya karɓi wayar daga hannunta.
Ya ce cikin kwantar da hankali,
"Ya yi fushi ne kawai. Give him some time. Da zarar zuciyarsa ta huce... shi da kansa zai kunna wayarsa."
Mom ba ta ce komai ba.
Sai dai ta jingina bayanta da kujerar da take zaune.
A zuciyarta...
Ta ci gaba da ɗora laifin wannan rayuwar da ɗanta ke ciki a kan mutanen da yake sadaukar da kansa saboda su.
Musamman...
Talakawan da yake ganin kare musu haƙƙinsu shi ne babban aikinsa.
A gare ta...
Ta fi son ganin ɗanta yana murmushi...
Fiye da ganin duniya gaba ɗaya tana yabonsa.
A cikin Private Jet ɗinsa kuwa...
Yana zaune kafafunsa a harɗe ya yin da his striking amber eyes suke a lumshe.
yana ɗan kaɗa ƙafarsa a hankali.
ya yin da bayansa ke kwance kijin lallausar kujerar fata ta alfarma.
Sai dai duk wanda ya kalli fuskarsa a wannan lokacin, zai fahimci cewa duk da jirgin yana ci gaba da shawagi cikin sararin samaniya...
Ransa kuwa har yanzu yana cikin wutar da bai huce ba.
Numfashinsa mai zafi na fita ta hancinsa a hankali.
Ɗakin jirgin ya mamaye da cikakken shiru.
Sai ƙaramar ƙarar injinan Private Jet ɗin da ke ci gaba da aikin yanke sararin sama.
Katsam...
Wata wayarsa daban, wadda ke cikin aljihun Suit ɗinsa, ta fara ringing.
Ba ita ce wayar da ya kashe ɗazu ba.
Wata ce daban...
Wayar da ba kasafai wani yake da lambarta ba.
A hankali ya saka hannu cikin aljihunsa.
Ya ciro wayar.
Da niyyar ya kashe ta kamar yadda ya kashe ɗayar.
Amma...
Kafin yatsarsa ta taɓa fuskar wayar...
Idanunsa suka sauka kan lambar da ke haskawa.
Babu suna.
Babu hoto.
Sai jerin lambobi kawai.
Lambar da...
Shekaru uku kenan da ya goge daga cikin Contact List ɗinsa...
Har yau bai taɓa mantawa da ita ba.
Lokaci guda...
Idanunsa masu launin amber suka tsaya cak a kanta.
Tamkar ba lamba yake kallo ba...
Tamkar fuskar mai kiran yake gani a gabansa.
Wani irin abu ya motsa a cikin zuciyarsa.
Abin da ya daɗe yana zaton ya mutu...
Sai ya motsa..
Kiran farko ya yanke.
Bai motsa ba.
Sai wani ya sake shigowa.
Har yanzu idanunsa na kan wayar.
Kamar wanda ya manta cewa yana cikin jirgi.
Ko numfashinsa ma ya sauya.
Kiran na biyu na dab da yankewa...
A hankali...
Cikin nutsuwarsa, ya ɗaga yatsansa.
Ya danna amsa.
Ya kai wayar kunnensa.
Amma...
Bai ce komai ba.
Shiru ya mamaye layin.
Daƙiƙa ɗaya...zuwa biyu...ana uku
Sai numfashin wani ya ɗan kaɗa a can ɗayan gefen.
Daga bisani...
Wata murya ta mace ta fito.
Raunatacciya.
Kasasshiya.
Muryar da kuka ya gaji da ita.
Ta kira sunansa cikin sanyin murya.
"...Arrow!..."
Kalmar kaɗai...
Ta isa ta sauya abin da ke faruwa a cikin zuciyarsa.
Amma M-ARROW bai motsa ba.
Fuskarsa ba ta sauya ba.
Bai yi wata magana ba.
Matar ta sake yin shiru na ɗan lokaci.
Sannan cikin muryar da ta bayyana tsananin gajiya, nadama da hawaye...
Ta ce,
"...Na dawo."
...
A hankali...
M-ARROW ya sake lumshe idanunsa.
Ba tare da ya furta ko kalma ɗaya ba.
A waje...
Private Jet ɗinsa na ci gaba da shawagi cikin sararin samaniya.
Amma a cikin zuciyarsa...
Wata ƙofa da ya kulle da hannunsa tsawon shekaru uku...
Ta fara buɗewa sannu a hankali.
Kuma wata ɓangaren zuciyarsa da ya yi zaton ta mutu har abada...
Ta sake harbawa.
A hankali.......!
Mommyn Twins ce