BABI NA UKU
Bauchi
Cikin sand'a yake taku yana waige-waige cike da rashin gaskiya, har ya isa bakin ƙofar ɗakin da ya nufa.
Ya ja wandonsa da ke ƙoƙarin suɓucewa ƙasa, ya riƙe shi da hannu guda. Sannan ya matsa sosai jikin ƙofar, ya manna idanunsa a jikin ramin maɓallin ƙofar ya leka.
Ihun jin daɗi ya kusan kubuce masa, sai ya yi saurin kai hannu ya toshe bakinsa, tare da waigawa baya don tabbatar da babu wanda yake ganinsa.
Ya sake mayar da idanunsa kan ƙofar, yana damƙe gaban wandonsa, yana fidda harshe tare da lashe baki kamar tsohon maye.
A dai-dai lokacin da ta kai hannu za ta zare wandon uniform ɗin jikinta, bayan ta riga ta cire rigar uniform ɗin, duk da ta bai wa ƙofar baya, sai kawai ta ji a jikinta kamar ana kallonta.
Da sauri ta janyo hijabinta ta zura. tana kwaɓe fuska gami da turo lips ɗin ta gaba, yadda take yi ɗin zai tabbatar maka da yanayin bai yi mata daɗi ba.
fuska ta kuma shagwaɓewa tana luro baki gaba kamar wacce take tare da wani, ko take yi wa wani shagwaɓar.
sai kuma ta juya kwayar idanunta ta wani irin kaɗa ball eyes ɗin ta, tare da mara baki tana gyara zaman hejabin data mayar jikinta....
Kamar an ce ta ɗago, tana daga cikin ɗan madaidaicin kitchen ɗin da ke tsakiyar gidan, tana ta faman hura wutar itace wadda ke ta balbala hayaƙi.
"Kai Habu! Da kata nan!"
Cak ya tsaya da ƙoƙarin tura kansa cikin ɗakin.
Da sauri ya saki labulen, ya soma sosa kai yana ɗan waige-waige kamar mai neman wani abu.
Mama ta miƙe daga kan kujerar yar tsugunon da take zaune, ta fito tana sharce gumi da mussuke idanun da hayaƙi ya cika.
Ta tsaya daga bakin ƙofar kitchen tana dubansa.
"Wa kake nema cikin ɗakin? Su Zaliha ba sa nan."
Habu ya shiga kame-kame yana cewa,
"Dama wanki na ba wa Halima ɗazu, zan karɓa idan ta gama."
Mama ta girgiza kai.
"Shine za ka tsaya kana leƙe? Ba za ka yi kira daga bakin ƙofa ba ko ka yi sallama?
Sam bai kamata, da girman ka, kana aikata irin wannan abu ba, Habu. Dukansu yaran sun yi girman da bai dace ka riƙa faɗawa ɗakinsu kai tsaye ba."
Ta nuna shi da yatsa.
"Ba ma wannan ba, karo na biyu kenan na gan ka kana leƙen cikin ɗakinsu. Kai da ya kamata ka hana wani aikata irin wannan abu, kai ne kuma kake yi."
Ta sauke numfashi.
"Ka kiyaye. Ba shi da kyau, ba shi da amfani. Dukansu ƙannenka ne. Yanzu yarinyar nan ta dawo daga makaranta tana canza kaya, su Zaliha kuma ba su ma shigo gida ba. Gaskiya ka daina."
Salati Hansatu, da ta fito daga ɗaki, ta saki tana tafa hannaye tare da riƙe haɓa.
"Tirkashi! Abin mamaki baya karewa a gidan nan. Me zan gani ni Hansatu? Sharri kike son ƙulla masa ko me? Ko iyaka kika so ki yi masa da shiga wani sashe na gidan ubansa?
To wallahi, Maryamu, baki isa ki sa wa ɗana kashin zuka ba. Shi da gidan ubansa, ba a isa a hana shi shiga duk inda yake so ba. Saboda 'yar gol tana cikin ɗaki sai a hana shi shiga?
Ni kam na san ɗakin ƙannensa ne. Dole ya shiga duk lokacin da yake so. Shine za ki ce yana leƙe?
Me zai leka a jikin 'yar taki? Yarinyar da yanzu ma ta fara ƙirgen dangi, ko ƙosawa ba ta yi ba!
Na rantse da Allah, Maryamu, ki fita daga idona kafin na yi abin da za ki yi nadama. Ke da 'yarki, lokacin da Malam ya auro ki, ya ba ku ɗaki ke da ita ne saboda ku mallake gidan har ku hana 'ya'yan gida shiga?
In ba tsabar ƙwarewa a iya sharri ba, ta yaya za ki ce Habu yana leƙen ɗaki saboda 'yarki tana ciki?"
Da sauri ta buɗe labulen ta fito, bayan ta mayar da rigar uniform ɗinta.
Ta bi Habu da Hansatu da kallon sama da ƙasa, sannan ta ce,
"Sai Mama ta rasa wanda za ta yi wa sharri sai Habu?
Ai ni da kaina na ji a jikina ana leƙe na. Da na juya ma, sai na ga idon mutum a jikin ƙofar. Da Mama ta yi magana kuma, na ga labulen ya motsa.
Kuma babu kowa a wajen sai shi.
Don haka, Mama ba ta yi masa sharri ba."
Ta ƙarasa maganar cike da tsiwa, tana hararar Habu da Hansatu lokaci guda.
"Ke Rubaah! Wa ya saka ki cikin maganar nan? Wuce ki je ki yi min wanke-wanke. Kar na sake jin bakinki a nan! Hansatu sa'arki ce har za ki tsaya kina mayar mata da magana?"
cewar Mama cikin tsawa.
Tun kafin a gama maganar, Habu ya zame jiki ya sulale waje ba tare da kowa ya ankara ba.
Hansatu kuwa ta ƙara hargitsewa.
"Ke! Ina da 'yan iska irinki, wallahi. Zan sa su ci uban ki, su farfasa wannan ɗan iskan bakin naki na tsiwa da rashin kunya!
Fitsararriyar banza!
Dan uwarki Maryamu gata nan. Ni ba sa'arki ba ce!"
Rubaah ta wurga mata wani kallo ta gefen ido, tana cizon gefen lips ɗinta.
Mama ta yi mata alama da hannu da ta bar gurin.
Ta juya tana ta ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.
Sanin halinta ya sa Mama ci gaba da bin ta da ido har sai da ta isa wajen wanke-wanke.
Tana zama kuwa, ta saci kallon Mama, ta bankawa Hansatu wata muguwar harara tare da jan ƙwafa a hankali.
Mama ta girgiza kai.
Ta san halin Rubaah sosai. Duk inda aka rina, can za a sake yin wani sabon zane.
Duk wanda ya san halinta, ya san cewa...
Shiru nata ba yana nufin ta manta ba ne...
Yana nufin kawai ta ajiye lissafin zuwa lokacin da ya dace ne...
Har yanzu Hansatu ba ta daina surutun bala'i da masifa ba. Tana ta jera wa Rubaah zage-zage tana cewa,
"In ba don tsabar iya ƙwarewa a murafurci ba, da rana a tsaka a riƙa yi wa yaro ƙage.
Agola ba ta isa ta miƙe ƙafa a gidan nan har a riƙa yi wa 'ya'yan gida sharri a kanta ba.
Kuma ɗakin nan na uban Habu ne. Duk inda yake so ya shiga a cikin gidan nan, zai shiga. Babu uban da ya isa ya hana shi!
'Yar banza, mara kunyar yarinya! Kin sani ina da fitsararru irinki, wallahi."
Mama ta dubi Hansatu cikin sanyin murya, ta rage murya sosai ta yadda Rubaah ba za ta ji abin da take faɗa ba, sannan ta ce,
"Ki ja girman ki, Hansatu. In ba don ina takawa Rubaah birki ba, kin san da ke da 'ya'yanki ba ku ishe ta komai ba.
Sai dai ni ba na goyon bayan ƙarya. Ba zan zuba ido ina kallon yaro yana aikata abin da bai dace ba, sannan na yi shiru.
Amma idan babba bai ji kunyar hawa dokin ƙarya ba, wata rana dole zai sha kunya."
Da haka Mama ta juya ta koma kitchen ta ci gaba da aikinta, ba tare da ta sake kula da hayaniyar Hansatu ba.
Rubaah kuwa sai jan ƙwafa take, tana cizon gefen lips ɗinta a hankali.
Hansatu ma, da ta ga ba wanda ya sake bi ta kanta, daga ƙarshe ta gaji. Ta yi tsaki, ta juya ta koma ɗakinta tana jifan habaici.
Bayan Rubaah ta gama wanke-wanken, ta ɗauki kwanukan ta kai wa Mama.
Daga nan ta yi alwala, sannan ta shiga ɗaki.
Bayan ta idar da sallah, ta fito cikin shirin tafiya Islamiyya.
Mama ta dube ta, ganin ta shirya fita, ta ce,
"Ke Rubaah, ba za ki ci abinci ba? Ga abincinki can. Ki je ki ci kafin ki tafi."
Da sauri ta nufi kitchen, domin ta lura kaɗan ya rage ta makara.
Ta ɗan ci abincin cikin gaggawa, sannan ta fito.
"Mama, na tafi."
Mama ta yi murmushi tare da ɗaga hannu.
"Allah Ya tsare. Allah Ya ba ki sa'a. Allah Ya dawo da ke lafiya."
"Ameen."
Rubaah ta amsa da sauri, sannan ta fice ta nufi makarantar Islamiyya.
Daidai ƙarfe biyar da rabi na yamma, ɗaliban Islamiyyar suka fara fita.
Wasu na tsaye cikin ƙungiyoyi suna tattauna darasin da Malam ya koya musu.
Wasu kuma tuni sun sanya takalmansu suka kama hanyar gida.
Rubaah kuwa, kasancewarta ba ta son shiga harkar da ba ta shafe ta ba, littattafanta kawai ta rungume a ƙirji ta kama hanyarta ita kaɗai, ba tare da ta tsaya jiran kowa ba.
"Rubaah! Rubaah! Haba, don Allah ki tsaya mana!"
Wata murya ta kwala mata kira daga baya.
Rubaah ta ja ta tsaya, sannan ta juya tana kallon Deejat ta gefen ido.
Deejat ta ƙaraso gare ta tana ɗan haki sakamakon gudun da ta yi.
"Shine babu jira ko, Ruby?" ta faɗa tana murmushi.
Rubaah ta ci gaba da tafiya tana cewa,
"Sai na yi ta jiranki kina ta zagaya kan 'yan aji? Irin ga ƴarkin nan ma."
Deejat ta marairaice.
"Allah ba ki haƙuri. Dama haddan nan ne da Malam ya ba da. Don Allah ki ɗan biya min."
Rubaah ta girgiza kai.
"Sabo da ga gantalallu ai marasa lissafi. Dole mu tsaya bita a kan titi, Sai kuma gaki nan ai baki san hanyar gidanmu ba. Da ake karatun ma, ina kika kai kunnuwanki?"
Ta yi maganar cike da tsiwa, tana kaɗa ƙwayar idanunta masu tsananin haske, girma da sheƙin da ke tattare da wani sirri na musamman.
Deejat, wadda ta saba da halin tsiwar Rubaah, ta marairaice fuska ta ce,
"Ayya Ruby... to shikenan. Zan zo gidanku anjima bayan na koma gida na cire uniform. Don Allah ki ɗan koya mini."
Rubaah ba ta sake cewa komai ba. Ta kaɗa kai kawai, ta ci gaba da tafiya.
Deejat ma ba ta damu ba. Ta san halin ƙawarta sarai. Duk yadda za ta yi mata tsiwa, ba ta ɗaukar zafi a kanta.
Da sauri ta ƙarasa ta kama ta, suka ci gaba da tafiya tare suna hira a kan darasin da Malam ya koya musu a ranar.
Bayan sun shiga layinsu, gidan su Deejat ne farko. Ta tsaya a bakin ƙofar gidansu, ta juya tana kallon Rubaah.
"Ruby, kar fa ki manta. Wallahi zan zo."
Rubaah ta ɗaga hannu kawai ba tare da ta juyo ba.
"Ki zo mana."
Da murmushi Deejat ta shige gida.
Rubaah kuma ta ci gaba da tafiya ita kaɗai, tana rungume littattafanta a ƙirji. Iskar yammacin Bauchi na kaɗa gefen hijabinta, yayin da take takawa cikin sauri saboda ta san idan ta makara, Mama za ta fara jiranta.
Tana isa ƙofar gidan, ta shigo gidan da sallama.
Kai tsaye ta nufi kitchen, inda ta tarar da Mama tana tuƙa tuwon dare cikin natsuwa.
Hansatu kuwa na zaune a bakin ƙofar ɗakinta, tana kulla gyada soyayya, tana tauna cingam tare da rera waƙa. Duk wanda ya ji waƙar zai fahimci cewa habaici ne tsantsa, domin gaba ɗaya kalamanta cike suke da tsokana.
Rubaah ta ƙarasa ta gaida Mama cikin ladabi.
Da ta lura Mama ta tsare ta da ido, nan take ta fahimci abin da take nufi. Sai ta juya ta gaida Hansatu.
Ba tare da ta jira amsar gaisuwar ba, ta wuce abinta.
Hansatu ma ba ta amsa ba. Sai ma ƙara ɗaga sautin waƙarta da ta yi, tana ci gaba da rerawa kamar ba ta san da gaisuwar da aka yi mata ba.
Rubaah ta shige ɗakin Mama, ta cire uniform ɗinta, ta sauya wasu kaya masu sauƙi, sannan ta fito.
Kai tsaye ta nufi wurin wanke-wanken da Mama ta tara na yamma. Ta zauna ta fara wanke kwanukan cikin sauri da ƙwarewa, har sai da ta gama tas.
Tana shirin tattara kwanukan da ta wanke ta kai wa Mama, sai ga Zaliha ta fito daga ɗakinsu, riƙe da wasu kwanuka.
Cike da gadara, ta zo ta ajiye su a gaban Rubaah, tana watsa mata wani mugun kallo.
Rubaah ta taɓe baki.
Tun kafin Zaliha ta yi magana, ta riga ta fahimci cewa tabbas Hansatu ta zuga su kan abin da ya faru da safe tsakanin Habu da Mama.
Cikin isa da gadara, Zaliha ta ce,
"Ai kin san kwanukan ba su haɗu ba, amma kika yi saurin gama wanke-wanke. To ga wasu nan, sai ki wanke."
Idan akwai abin da Rubaah ta tsana a duniya, to shi ne ta gama wanke-wanke sannan a sake kawo mata wasu.
Ko da kuwa kwanukan sun kai na iyali goma, muddin an haɗa su gaba ɗaya kafin ta fara, za ta zauna ta wanke su cikin natsuwa. Amma idan ta gama sannan a sake kawo wasu, wannan ba ƙaramin ɓata mata rai yake yi ba.
Ta miƙe tsaye, ta ɗauki kwandon kwanukan tana faɗin,
"Da dai kin kwashe kin mayar da su ɗaki, gobe sai ki fito da su a wanke. Ko kuma ki bar su a gurin aljanu su sami wurin kwana. Ni kam na gama wanke-wanke. Sai kuma gobe, in Allah Ya kaimu.......!
Mommyn Twins ce