BABI NA HUƊU
Ta juya za ta tafi.
Da sauri Zaliha ta damƙo wuyan rigarta.
"Dan uwarki, dawo ki wanke! Ko kuma na ci ubanki a nan. Wallahi sai kin wanke yau. Zan ga ƙarshen rashin kunyarki."
Rubaah ta yi saurin dire kwandon kwanukan ƙasa.
Ta fisge hannun Zaliha daga rigarta, tana kallonta ido cikin ido.
"Ba dai uwa ta da ubana ba. Kin san wanda kika zaga. Idan kika sake zagi na, wallahi sai kin yi nadama."
"Dan uwarki! Me za ki yi?"
Zaliha ta sake cafke ta.
Rubaah ma, ba tare da ɗigon tsoro a idanunta ba, ta damƙe ta, duk da cewa Zaliha ta fi ta girman jiki da shekaru.
Hayaniyar tasu ta sa Mama ta fito da sauri daga kitchen.
Hansatu kuwa tana nan zaune, ko motsi ba ta yi ba. Sai ma ƙara sautin waƙar habaicinta da ta yi, tana girgiza kai cikin jin daɗin ganin Zaliha ta samu damar koyawa Rubaah hankali.
Mama ta ƙaraso cikin gaggawa tana cewa,
"Ke Rubaah! Sake ta! Kina hauka ne?"
Rubaah ta sake Zaliha, tana jan ƙwafa tare da cizon gefen lips ɗinta.
Ta juya za ta bar wurin.
Amma kafin ta yi taku biyu...
Zaliha ta sake cafke ta daga baya.
"Ina faɗa da ni za ki yi? Ba ni sa'arki ba ce! Zo mu gwada, dan ubanki!"
Da ƙarfin da ta janyo Rubaah, kaɗan ya rage samtsin wurin wanke-wanken ya kife da ita.
Cikin sauri Rubaah ta juyo, ta hankaɗa Zaliha da ƙarfi.
Timm...Zaliha ta faɗa ƙasa.
Da ƙyar ta miƙe tana riƙe da ƙugunta, fuskarta cike da zafin faɗuwar da ta yi.
Ba ta tsaya ba, ta sake rugawa kan Rubaah ta damƙe ta da kokawa.
Mama ta yi saurin matsowa tsakaninsu tana cewa,
"Ke, Zaliha! Sake ta! Ba na son wannan fitinar."
Ko kallon inda Mama take Zaliha ba ta yi ba. Sai ƙara damƙe wuyan rigar Rubaah da ta yi, tana son sake janyota.
A daidai wannan lokacin ne...
Malam Musa ya shigo gidan.
Tun daga bakin ƙofa ya hangi abin da ke faruwa.
Nan take ya ɗaga murya cikin tsawa.
"Ke, Zaliha! Me zan gani haka? Ban hana ku faɗa da ita ba?"
Ya ƙaraso cikin hanzari yana nuna ta da yatsa.
"Maza! Sake ta! Ko na ci mutuncinki. Ba da ke nake magana ba?"
Tsawar da ya buga mata ta sanya jikinta rawa.
Nan take ta saki Rubaah, tana ci gaba da harararta da idanu masu cike da ƙiyayya.
Ta yi ball da kwanukan wanke-wanken, ta juya zuwa ɗakinsu tana tura baki tare da gunaguni.
"Sai na ci uwarki, wallahi... za mu gamu."
Malam Musa ya bi bayanta da kallo, sannan ya juyo wajen Rubaah.
Fuskarsa ta sauya zuwa fara'a.
Ya washe baki cikin sanyin murya.
"Yi haƙuri, kin ji? Tafi ki ci gaba da abin da kike yi."
Rubaah ta yi ƙwafa.
Ta kaɗa ƙwayan idanunta, kana ta shanye su suka kankance, sannan ta sake buɗe su cikin wani salonta na musamman.
Ba ta ce komai ba.
Ta ɗauki kwandon kwanukan ta kai wa Mama, sannan ta juya ta nufi ɗakin Mama.
Malam Musa ya tsaya yana kallonta har ta ɓace ma ganin sa.
A ransa ya kasa daina mamakin yarinyar.
Wace irin halittar idanu Allah Ya yi mata?
Idanunta manya ne, masu sheƙi na ban mamaki, kuma suna ɗauke da wani irin sirri da ke jan hankalin duk mai kallonsu.
Wani lokaci idan ta motsa su, sai su zama tamkar ana sarrafa su ne daga ciki.
Ya girgiza kai a hankali, sannan ya wuce cikin gidan.
Da yake Mama ce da girki a ranar, bayan ta idar da sallar Isha'i, Rubaah ta yi mata sai da safe.
Mama ta amsa da murmushi.
Har Rubaah ta kai bakin ƙofa...
Sai Mama ta kira sunanta.
"Rubaah!"
Ta tsaya, ta juyo.
"Na'am, Mama."
Mama ta kalle ta da ido mai cike da nasiha.
"Kar na ji kin sake neman faɗa da Zaliha ko Halimatu. Lokacin kwanciya ne yanzu. Ki je ki kwanta, kuma kar na ji bakinki a wurin."
Fuskar Rubaah ta marairaice.
"Mama... ni fa ba ni nake neman su da faɗa ba. Su suke fara tsokana ta."
Mama ta girgiza kai.
"To, saboda sun neme ki da faɗa, ke ma sai ki rama? Ba za ki iya haƙuri ki tura musu aniyarsu ba?"
Ta ɗan dakata kafin ta ci gaba.
"Wallahi, idan na sake jin wata magana a kan hakan, ranki zai ɓaci. Na gaya miki."
Rubaah ta sauke kai.
"To, Mama."
Ta juya ta nufi ɗakin 'yan matan gidan.
A nan take kwana duk ranar da Mama ce da girki.
Dalilin haka kuwa shi ne, Malam Musa ba shi da takamaiman ɗaki; duk ɗakin matar da take da girki a ranar, a nan yake kwana.
Rubaah na shiga ɗakin...
Ta tarar da Zaliha da Halimatu kwance, kowacce riƙe da ƙaramin wayarta ta Itel keypad, waɗanda samarinsu suka saya musu.
Ko da yake wayoyin ƙanana ne, amma yadda suke nuna alfahari da su, sai ka rantse iPhone ta zamani ce a hannunsu.
Rubaah ta isa gefen katifarta ƙarama, ta kwanta ba tare da ta kula da su ba.
Tana shiga ɗakin kuwa...
Suka fara jifarta da habaici da zage-zage.
Sai dai wannan karon...
Ba ta bi ta kansu ba.
Ta tuna gargaɗin Mama.
Sai dai tana ta cizon lips ɗinta tare da girgiza kai a hankali.
A zuciyarta kuwa ta ce,
"Ku yi ta yau... In Allah Ya kaimu gobe a hanyar makaranta, za mu haɗu."
Ta toshe kunnuwanta, ta karanta addu'o'in kwanciya, sannan ta lumshe idanunta.
Ba a daɗe ba...
Barci ya yi gaba da ita.
Washegari da asuba...
Kasancewar Rubaah ta kwana a ɗakin 'yan matan gidan, kamar yadda aka saba, Mama ce ta buga musu ƙofa da sassafe.
Tun bugun farko, Rubaah ta farka. Ba ta da nauyin barci ko kaɗan.
Ta miƙe da sauri, ta buɗe ƙofar, sannan ta nufi wurin alwala.
Ta dawo ta idar da sallar Asuba cikin natsuwa, yayin da Zaliha da Halimatu har lokacin suke sharar barci, ko motsi ba su yi ba.
Bayan ta gama addu'o'inta, ta ɗauki Alƙur'aninta ta nufi makarantar Asuba.
Karfe shida da rabi na safe ta dawo gida.
Har lokacin kuwa Zaliha da Halimatu suna nan kwance; barci ya yi musu nauyi.
Tana tura ƙofar ɗakin...
Zaliha ta buɗe ido cikin muryar da bacci yake wa daɗi ta ce,
"Ke! Dalla rufe mana ƙofa. Kin wani wangale mana ƙofa."
Rubaah ta girgiza kai cikin takaici.
"Lallai ma har yanzu ba ku tashi kun yi sallah ba? Kuma ba ku je makarantar Asuba ba. Wallahi, Malam ma sai da ya tambaye ni ina kuke. Ya ce in gaya muku gobe ku zo da shirinku."
Halimatu ta yi ɗan tsaki.
"Dalla rufe mana baki, kar ki ishe mu. Ina ruwanki idan ba mu je makarantar ba? Idan mun je gobe, ya kashe mu."
Rubaah ta murguɗa baki.
"Dama ni ina ruwana. In kun so ma, kada ku sake zuwa."
Ta ajiye Alƙur'aninta a gefe, sannan ta fita da sauri, ganin gari ya fara haske. Ba ta son ta makara zuwa makarantar boko.
...
Tana fita, Mama ta ce,
"Rubaah, ga ruwan wankanki can. Na juye miki a bokiti, je ki yi wanka yanzu ki zo ga abin karyawa."
"To Mama."
Ta amsa cikin ladabi, ta ɗauki bokitin ta nufi bayi.
Ba ta daɗe ba ta fito, sabo da gudun kada tayi latti.
Da ta lura babu takalmin Malam Musa a bakin ƙofar ɗakin Mama, ta fahimci ya fita.
Sai ta shiga ɗakin da sauri, ta shirya cikin uniform ɗinta na makaranta boko.
Mama ta shigo riƙe da kofin koko da kuma leda mai ɗauke da kosai da ta saya mata domin ta karya.
"Zo ki karya kafin ki tafi."
Rubaah ba ta musa ba.
Ta zauna cikin sauri ta ci kaɗan, ta sha kokon, sannan ta miƙe ta ɗauki jakarta.
Mama ta gyara mata hijabi da hannunta, sannan ta shafa kanta cikin tausayi irin ta uwa.
"Allah Ya tsare ki, Ya ba ki sa'a, Ya buɗe miki ƙofofin alheri."
"Amin, Mama."
Rubaah ta amsa da murmushi.
Ta juya ta fice daga gidan cikin sauri, tana takawa da ƙwazo zuwa makaranta, yayin da Mama ta bita da kallo har sai da ta ɓace daga ganin ta, sannan ta furta a hankali,
"Allah Ka kiyaye mini ita..."
Ranar ta kasan ce ranar Alhamis ce, don haka babu Islamiyya.
ko da ta dawo daga makarantar boko, Rubaah ta yi wanka, ta ci abincinta kaɗan, sannan ta kwanta domin ta ɗan huta.
A wannan rana kuwa, Hansatu ce da ke girki.
Mama tana zaune a tsakar gidan tana wanki, yayin da Hansatu ke ta kai-komo tsakanin kitchen da ɗakinta, tana gudanar da girkin rana.
Kamar yadda ta saba, Hansatu na rera waƙoƙin habaici cikin ɗaga murya,
da alama tana nufin wani ne kai tsaye...
"A hayye ni Hansatu nazama ciwon ido karyar makiya ganin bayanmu...
da d'an bori da matsafi sai dai mu buga mu gogi juna,
idan mutum na harka da aljanun bishiyan kuka ne, mu da na bishiyan tsamiya muke harka."
Mama ba ta ko ɗago kai ta kalle in da take ba.
Ta ci gaba da wankinta cikin nutsuwa, tamkar ba ta ji komai ba.
Ta saba da irin waɗannan habaice-habaicen na Hansatu, don haka ba ta ba su muhimmanci ba.
Da ta gama wankin, ta tattara kayan ta shiga ɗakinta..
Motsin Mama a cikin ɗakin ne ya sanya Rubaah buɗe idanunta daga barcin da take yi.
Ita ba ta da nauyin bacci sam; ƙaramin motsi kaɗai ya isa ya tashe ta.
Mama ta dube ta, ta yi murmushi kaɗan sannan ta ce,
"Tashi ki je ki yi alwala. Lokacin sallar la'asar ya yi."
Rubaah ta gyaɗa kai a hankali. Ta sauke ƙafafunta daga kan doguwar kujerar da ta saba kwana a kai idan tana ɗakin Mama..
Ta miƙe tana gyara ɗaurin ɗankwalinta da ya zame zuwa kafaɗarta.
Kitson da Mama ta yi mata reras a kanta, da gashinta mai laushi baƙi da ke kwance bisa kafaɗarta, sun ƙara fito da kyawun fuskarta a lokacin da babu ɗankwali a kanta.
Ta ɗauki butarta, ta nufi bayin da ke tsakiyar gidan domin yin alwala.
Ko da ta fito daga bayin, sai ta tsaya cak.
Idanunta suka sauka kan Habu.
Yana fitowa daga kitchen, kinkime da tukunya mai ɗauke da abincin da Hansatu take girkawa, sai tururi yake tashi daga cikinta.
Habu ya leka dama, ya leka hagu, kamar ɓarawon da ke tabbatar da babu mai ganinsa.
Da ya tabbatar babu kowa a tsakar gidan, ya yi saurin ficewa.
Bai ma lura cewa Rubaah na tsaye a gefe tana kallonsa ba.
Rubaah ta ɗan kyabe baki.
A zuciyarta ta ce,
"Ai, ko ka ji jiki..."
Ta tsugunna cikin nutsuwa ta fara ɗaura alwalarta, tamkar abin da idanunta suka gani bai dame ta ba.
Amma a zahiri...
Rubaah ba ta manta da abin da ta gani ba.
Duk wanda ya san halinta, ya san cewa tana iya yin shiru...
Amma ba ta taɓa mantuwa.
Da ta gama alwala, ta koma ɗaki ta tada sallar la'asar cikin nutsuwa.
Ko bayan ta idar da sallar, ba ta gaya wa Mama abin da ta gani ba.
Ta zaɓi ta yi shiru........!
Mommyn Twins ce