BABAN KAWATA

Chapter 11

by @smauta

Airport 



Halin ce tsaye a gefen babanta tana rizga wani irin kuka mai tsuma zuciya,gefe guda kuma manar tana share nata kwallan bana komai bane sai zata nisanta da abincin ruhi,shafa kan yar kwain tashi yake yana mata kalaman lallashi masu ratsa zuciya kiddo banace zanzo ba,nida kaina zan rakaki school din ma idan kinaso sorry kiddo u have to go karkisa damuwa a ranki ryt?gyada kanta tayi sannan ta koma wurin manar suka rungume juna sosai sai lokacin itama manar ta saki kukan bakin cikin ta sosai harda ihu,har abin yafara ba halim mamaki saboda zata tafi ne manar take wannan kukan????????




Takowa yayi a hankali ya sauke hannun shi a tsakiyar su idon shi cikin na manar ya fara magana da ita kamar haka,kukan na menene bazaku koma school ba?ya kuna abu kamar baku girma ba sorry pls sai lokacin ya juya wurin diyar tasa yayi mata nuni data wuce ita kuma manar ya nuna mata mota jiki a sabule kowannensu ya wuce bin bayan halim yayi yanata lallashi har ta karbi boarding pass ya mata sallama haka ya rabu da diyar tasa badan rai yaso ba saidan gujewa fadawar shi a halaka………….





Sunyi tafiya mai dan tsawo kadan kafin Allah yasa ta fara ganinsu sun shigo suleja sai a lokacin yaji wani farin ciki yana mamaye ta gefe guda kuma tana kewar kawarta da babanta sun shigo cikin suleja tsullum sannan ta farama driver daya kawo ta kwatance har kofar gida ya direta koda aka bude boot jakun kuna tagani ana saukowa tace malam lafiya wannan ba nawa bane Yes mah oga ne yace ayi maki tsaraba 😂😂😂 hmmmm kawai ta iya furtawa niki niki ake shigowa da kayan tsakar gidansu kaka na kwance kan tabarma yayarta dede larai na gefe jakar hannunta manar ta saki da sauri dede kece😳😳😳😳😳😳






Yar albarka karaso sannu malam sannu fa wannan kaya daga ina dede nawa ne saida ya shigo da akwatinta last yayi mata sallama ta kalleshi da kyau idan ka koma kace mashi nagode godiyar ma tagode kaikuma Allah ya kiyaye hanya ya huta gajiya,gefen kaka ta zauna wai hajia kaka yayadai bakida lafiya naganki wani sukuku,dede larai ce tace yaya fa ba lafiya tun tafiyar ki amma taki bari a gayamaki nima zirga zirga naga bazataman inzo in koma nace bari dai in dawo wurinta ciwo irin haka saida mutum kusa,kakace tayima dede gyaran murya alamar ta mata shuru,kefa yaya haka kike har sai yaushe zaki bari yarinya nan tasan bakida lafiya ne ehhhh……………




Kaka ta kuskura dakyar ta mike dede surutun ki na tsiya ke hadani dake da wannan zaman surutun naki tunda manara ta tadawo ki koma gida kawai a'a wlh duk duniya bakida kamata kina cikin hali na tafi nabarki kedai yaya Allah baki lafiya,marayan kuka manar ta saki kaka kun sani a duhu meke damunki kinji yadda muryar ki take fita da kyar duk inna kiraki saikiceman a kwance kike kwancen ashe ta rashin lafiya ce,kaka idan wani abu ya sameki wlh bazan taba yafema kaina ba,dede anje asibiti kafin dede ta bada amsa kaka ta anshe da eh munje jiya sai Litinin sukace in koma…………..





To wai meke damunki kaka?basu gayaman ba sai Litinin idan nakoma dede tayi karaf tace a'a kinsani nibanga amfanin ɓoye mata ba yaya shekara biyu kina fama da ciwon nan amma kinki bari a sani dangin mahaifinmu ma idan da ban maki jan wuya ai bazasu sani ba,meye amfanin shelar ciwo inakai karar Allah wurinsu ne?a'a yaya amma sannu nada dadi koda bazata warke ciwo ba to ki kwanta aita maki sannun ni baniso,manar ta fada jikin dede tace wayyo Allah na nashiga ukku kunsani a duhu dede dan girman Allah kiman bayani meke samun kaka shekara biyu tana ciwo tun bayan tafiya ta amma ba wanda ya taba fadaman banida wani gata sai Allah saike kaka dan soyayyar ku da Muhammadu Rasulullah ku sanar dani mike faruwa ko zuciya ta ta samu sauki cikin salama, innalillahi wainna ilaihir rajiun dede ta sharce zufa data tsatsufo mata a goshi………





Dede ce ta kalli kaka data saddar da kanta kasa ta juyo akalar ta akan manar ta fara cewa yaya kiyi hakuri amma manar tana ɗaya daga cikin wanda yakamata susan meke damunki,dede kibarni zan mata bayani da kaina manar zonan sarrafawa tayi ta koma gefen kaka ta zauna hannunta ta kama ta riketa tace kisani duk tsanani yana tareda sauƙi,haka duk wani ciwo yanada magani muddin ba ciwon mutuwa bane,kuma inada yakinin ba zan mutu in barki cikin maraici ba,kinjini ko,ko da raina ko babu raina ki tsare mutuncin ki manar ki rike Allah da addu'a bazaki taba tabewa ba duk wani abun da kikasan ya sabama sharia kiyi kokarin kauce mashi……..




Tun bayan tafiyar ki makaranta da wata shidda manar na kamu da wata rashin lafiya mai tsanani tun muna zuwa chemist muna dawowa har abun dai yaci tura muka tafi babbar asibitin mu koda aka kaini bansan ina nake ba saboda tsananin ciwo danake fama dashi dede ce akaina sai kawu labaran mutanen nan biyu akansu na yarda da maganar hausawa da suke cewa ranar naka sai naka dadin zama sai bare,tsaye suke akaina awo kala kala har wani awo aka bamu mukaje kano wannan awo da muka dawo dashi ne fa ya idasa kwantar dani……………..





Duk wani abu dana mallaka nawa ya ƙare kan wannan jinya tawa a asibiti har takai ga ba muda komai sai mutanen unguwa suka hada mana kudi anata man magani har sauki ya fara samuwa ta akaimana sallama tun daga lokacin nan ban karajin ciwo ba sai gaf zaki dawo shima nayi ciwo kamar ba zan tashi ba amma Allah da ikon sa yasa na tashi,sai kuma yanzu da kikazo kika sameni kwance,kaka har yanzu kinki gayaman menene ciwon naki,manar zuciya ce😭………….




Innalillahi wainna ilaihir rajiun heart kaka nabani ya Allah kabarni cikin natsuwa ta karkasa na bijirewa umarnin ka ko nayi sabo Allah ka tausaya mana ya Allah ka kawomana mafita innalillahi wainna ilaihir rajiun dede larai itama kukan take kamar zata ciro kwayar idonta tace yanzu ma munje asibitin saidai dawowa mukayi manar ba kudi sunce nan da wata shidda za'ayi mata aiki kuma baayin shi nan kasar sai kasar waje daga yanzu kuma kafin ayi aikin zaayi mata allurar tsawon wata shidda duk wata so biyu duk allura daya dubu dari takwassssssssssss…………