Chapter 12
by @smauta
Manar ta kalli dede dake wani irin kuka itama tace dede dubu dari takwas so biyu a wata kuma tsawon wata shidda innalillahi wainna ilaihir rajiun, yanzu haka ga magunguna nan an rubuta munje chemist sunce wasu maganin ma sai abuja za'a samu gaba daya kudin maganin na wata biyu ne dubu dari da hamsin ne da tana shan maganin ma zata samu sauki a rage kwanciyar nan nidai Allah yasani banida su wlh amma da inada su dawani labarin ake ba wannan ba kawu labaran ma bayada su,masu hali basu taimakon mu………
Dede Ina Shaa Allah zan sai mata magani ga wata nan nasan nasaida ta zatayi kudi kamar dubu dari ukku sai a siyo maganin dashi sauran kuma a riƙe koda wani abu yakan taso mana na bakatatan bamu sani ba,tsulum ta mike ta cigaba da daukar jakunkunan ta tana shiga dasu daki kamar mahaukaciya ta fara bude jikar kaya ne ya sawo mata da agogo da takalma tsaki taja ta maidasu cikin jikkar su ta fito da jikkunan hannunta dede tace ke lafiya?ki zauna da kaka dede zan koma Abuja wannan kayan baban kawata ne yabani su tsaraba sunada tsada sosai akwai wani boutique dana sani suna ansar kaya su baka kudi indai sabbi zanje can na siyar dasu saimu hada mugani nawa zamu samu…………
Dede tace a'a manar zonan abuja yanzu?baki jima da dawowa ba zauna ki huta ko zan barki ki fita daga gidan nan to sai kuma gobe,dede nayi zaune ina kallon kaka cikin wannan ciwon bayan inada abinda zan saida ya kawoman kudi?ace sai gobe kakace tayi karaf daga kwance tace eh kidawo sai gobe kije bance kije yau din ba da yau da goben duk ta mai duka ce,da yardar Allah ba abinda zai faru dani kuma nace maki banison ina ganin ki cikin wannan yanayin naki na damuwa,ki fawwalama Allah lamuranki da sannu zakiga cigaba na wanzuwa tare dake………………
Har dare yayi manar ta rasa meke mata dadi duk motsin ta baya wuce tunanin kaka da yadda zasu samu kudin yimata allura ta saka wannan ta kwance wannan tayi yayi so ba adadi dede ce tayi masu waina da miyar taushe abincin dare,lashe ta kasa cin komai duk da waina tana cikin abinda takeso saida dede taimata dagaske sannan ta samu ta sa waina biyu a bakin salatin ta,ba abinda kunnuwan ta a yanzu suke muradin ji ila baya ga da kiran assalatu……….
Da sanyin sassafiya manar ta tashi ta kwala wanka kota kan dede daketa mata surutu bata bi ba,uwar dakar su ta kurda kanta taga kaka zaune kan sallaya ta idar da sallah kaka barka da asuba barka har kinyi wankan eh nayi kaya zan canza sai in tafi ki tsaya kisha kokon mana saboda ke fa nasa dede ta damashi,ai yaya gashinan na biyota dashi haba ina dalili kace bakicin komi zaki wuce har Abuja duk saurin unguwar zoma nace ai ta bari a haihu ko,ko kinje dai idan masu shagunan basuzo ba kin jirasu har su iso ko,ungo sha kokon saiki saka kaya kuma kin bari gari yayi haske sannan ki fice……………
Kaka ina prescription din,wai ina takardar maganin naki?tana wurin dede,dede bani insha kokon nan ki kyaleni ki bani takardar maganin da ita zan wuce idan Allah yasa na saida kayan nan da wayar sai in tsaya in sawo mata maganin kafin in dawo gida ko,to manar Allah yaimaki albarka yakai ladar kabarin iyayenki Amin,kaka tace manar na'am kaka karki saida wayarki iya kayan ma sun isa idan kudin basu isa ba ki sawo na iya kudin,kaka inada zaune da kayan kudi a hannuna kice kar in saida in zauna ina kallon ki da ciwo??????
Dan Allah kibar ma maganar nan waya gatacan na saida kedai kiman addu'a ayi mata sayen kirki, makaranta idan aka nemeki kuma fa dame za'a sameki In Shaa Allah wannan bazai gagara ba,da wasa da wasa dai sukai mata ta manya itace bata bar gidan nan ba sai karfe 7 har bakin titi dede ta rakota tahau keke napep yakaita tasha sannan dede ta dawo gida wurin kaka,abuja mutum daya abuja mutum zuruf ta fada mota aka tada sai Abuja babban birnin tarayya…………….
Baayi wata doguwar tafiya da ita ba suka iso Abuja rokon driver mota ta dingayi kan ya taimaka karya ajiye ta a bakin titi zata kara mashi kudi ya kaita kasuwar ƴan waya,kefa hajia bansan kalar wannan game din ya tun can baki fadaman ba kiyi bolt mana ni bawata kasuwar ƴan waya da zan kaiki idan zaki dire anan nan dalla ware uwar iyayi,jikinta na kyarma ta fito mashi a mota tace toooo shikuma wannan ba taimako haka ta fito ta rasa ina zata kama batada wani sarki sai Allah kudin hannunta bazasu isa tayi bolt ba tasan tsadar bolt na Abuja koda ba a garin take ba tanajin lbrn garin sosai wurin halim…………
Sai lokacin halim ta fado mata a rai , Allah sarki mutum inda yake nan ake ganinshi iya abinda ta iya furtawa kenan ta miki titi tafiya take ita kanta batasan inda zataje ba bin titi take sambar har aka kusa kiran azahar sannan ta hango wata plaza Amma nesa da ita kara sauri tayi tafiya take kamar batayi ga yunwa na cinta cikin ciki tun wannan koko da kaka ta tsarets tasha shine a cikin ta,koda ta isa bakin plaza samun wuri tayi ta zauna tana haki gaba daya kudin dake cikin jakar ta basufi dubu shidda ba ta dauki kusan minti talatin zaune taji kafar ta ta saki sannan ta yunkura zata kara gaba daga saman benen ta hango shago kamar na saida kaya hamdala tayi……
Koda tashiga shagon ba abinda basu sayarwa kayan gayu sannu da zuwa hajia yawwa duk kafar ta suka kalla hurtutu dan Allah kayan nan nakawo kuyi masu kudi ku siya buƙatar kuɗin ce ta tasoman dukka staffs din kallon kallo sukayi wani can daga baya yace hajia kiyi hakuri bama ansar kaya anan saidai in dayawa ne kamar dealer amma pieces bama karba saboda tsaro,daga inda take ta sauko dan Allah ku taimaka wlh kakata ce ba lafiya aka rubuta mana magani bamuda kudin siya shine akaiman kyautar kayan nan kan gaba nace bari na siyar…………..
Hajiya kinsan tsadar kayan hannunki kice akai maki kyautar su kuma wanda ya baki ya kasa siya maku magani dalla malama tashi ki fita kafin mu tara maki mutane barayin banza barayin wofi a turoku aikatau gidaje ku addabamasu da sata ku kawo mana nan mu siya a kamaku Ku sakamu harkalla ki tashi kibar shop din nan kafin in tattakaki anan🙄🙄🙄