Chapter 13
by @smauta
Haka tabaro shagon gwuiwa sage bayan cin mutunci da aka bita dashi,bataga laifin su ba mata dayawa sukan ja ma masu shaguna asara irin wannan wata zuciyar tace amma sunga nayi kama da barauniya,sata batada kama kowa yinta yakeyi,gaba ta karayi ta hadu da wani mai saida cincin ta tsayar dashi na 1k ta siya tacigaba da hadar cincin din nan ko ruwa babu mai cin cin dinne yaga yadda take halam halam yace idan tanason ruwa ta bada ya siyo mata dubu daya ta kara fiddawa ya kawo mata ruwan roba guda biyu saida taji tayi kat hankalinta ya dawo jikinta wayarta ta fiddo hudu saura kwata gabanta ya tsinke ba azahar bare laasar……………..
Gaban wani uncomplicated building ta tsaya jakarta ta ajiye gefe ta ta farayin alwala kallin kanta na atamfar ne ta shimfida kasa ta fara sallah koda ta idar ji tayi kafar ta na mata wani vibration kamar ba tata ba kuka ta fashe dashi a wurin ta rasa tudun dafawa ga kaya tanata fama dasu a hannu wurin biyar da rabi ta yanke shawarar komawa gida suleja kawai taji daga bayanta ana mata magana ya yanmata how far nawww,jikinta ne ya dauki ciri ganin wani wanda bata sani ba daga shi sai gajeren wando da singlet ga wata sarka a wuyan shi…………..
Tsoron dayaga tashiga ya tabbatar mashi da bakuwa ce a Abujar yanmata kin bata hanya ne ko kina neman wani wurin hamdala ta sauke a ranta da sauri tace eh kasuwar waya nake tun safe bangane wurin ba,AHH dakinyi mgn da wuri naganki kin dade anan ne nace bari na tambaye ki ko lafiya kuma yanzu ma suna gaf da tashi saidai ba lallai ki samu Mota daga nan ba akwai nisa sosai fa idan zaki bada 3k inada babur saina saitaki a hanya,aikuwa da ka taimakaman dan Allah zan bada…………
Wani ragargajajjan babur ya dauko yanata fitar da hayaki ya dauko ya karkata mata ta hawo da kyar ta zauna ya lula da ita,tafiya ake shuru ba alamun zuwan su malam har yanzu bamuzo ba, yanmata shiyasa nace maki 3k ne hajar ki fa da nisa sosai, Allah yasa ma dai mu isa basu tashi ba me zakiyi a wurin ne wayata ce zan siyar ahhh jungle din kudin harda ku kenan ciki hajia,daga nesa ta fara hango wasu dandazon mutane tsaitsaye da hannu yayi mata nuni hajia munzo nan ne yan waya ,yawwa aiko nagode kudin shi ta ciro ta bashi ya karba ita kuma taci gaba da takawa cikin mutanen……….
Kamar nama akaita kawo mata hari hajia nan ne nan ne wani yazo ya tareta hajia cover waya charger earpiece me kikeso tace waya ta na kawo zan siyar wace kala ce hajia iPhone 13normal,muganta muje daga can gaban shagon su ya kawota ta fiddo wayar sannan tace ga kwalin harda charger ansa yayi ya dudduba nawa zan bada wannan hajia?ka fada inji zan bada dari ukku,zaro ido dayi wace irin dari ukku dubu dari ukku nake nufi a'a gaskiya albarka wayata fa malam sabuwa ce ga komai nata…………
Nagani fa to ka kara gskia bazan saidata a dubu dari ukku ba wani ne daga gefen su yace hajia nina kara tamanin a sama last price ba gardama tace a bata sim card dinta ta cire aka goge komai na kan wayar, transfer ne zaayi maki ko kinason cash a'a idan akwai cash din a bani wani daki yashiga ya fito mata da damman kudinta ya bata cikin jikkar kayan ta daga ta zuba kudin kamar sun bata kyauta tashiga masu godiya ba abinda yake ranta sai ta samu abun hawa taje babban chemist siyan magani yau komai dare suleja zata kwana………..
Gefen su kaka hankalin su idan yayi dubu ya tashi tanata tari dede na kwantar mata da hankali dede naam yaya shiga gidan habi kice idan Ibrahim yadawo yazo yanzu yanzu ina nemansa to yaya,abayar ta dede ta saka a kofar gida tayi karo da Ibrahim na fitowa daga gidan su kazo malam iro yaya na kiran ka, lafiya dai ko dede ko jikin natane a'a jiki da sauki tadai ce na kirawo ka,dede na gaba Ibrahim na biye da ita a baya har cikin dakin kaka,ya gaisheta ta ansa ungo wayata laluboman number manara ta tun 7 na safe nan da abuja shuru shushushu…………..
Wallahi kau yaya ai shuru nayi dai kar in tada maki hankali wannan diya bata ba labarinta kaka harar dede tayi sbd dede irin mutanen nan ce masu surutu wanda ko luguden wuta akeyi sai tayi magana 😂😜 Ibrahim ya karbo wayar number manar ya nemo bugu na farko ance wayar kashe saida ya gwada so ukku sannan ya kalli kaka yace inda take ba service kilama tana mota ne shiyasa ba'a samunta,dede tace kai Ibrahim ba'a samunta bata samu ma ta saida wayar ba kenan to mudai mu bita da addu'a Allah de ya kawo mana ita gida lafiya da sauri Ibrahim yace amin gaba daya ya lura da kaka ba'a natsuwar ta take ba muddin yace mata wayar a kashe take baisan wane hali zata shiga ba,kuma tana jinya da wane zataji a ranshi ya tayasu da addu'ar Allah dai yasa lafiya………