BARA A KUFAI

Page 4.

by @zeeykumurya

*BARA A KUFAI*

*Zeey Kumurya*


4.


BRIGHT PENS 2026

YOTA ID 003


Bismillahir rahmanir rahim 



Babban parkour ne da ya ji komai na kayan alatu da yake ta tashin sassanyan ƙamshi wanda ya haɗu da sanyin AC. Fuskar mutumin da ke zaune a cikinsa a washe ya ɗauki ɗaga daga cikin wayoyinsa uku da ke zube akan Centre table ɗin gabansa, ya latsa ta na sakanni sannan ya kara a kunnensa.

"Komai ya tafi successful kamar yadda muka tsara." Ya faɗa yana jinjina kai tare da sakin gajiyar dariya sannan ya ci gaba da faɗin. 

"I will try my best na ganin ragowar ayyukan ma sun tafi yadda muke so, abin da nake so da ke kawai ki ci gaba da zaƙulo mana duk wani wanda kika ga alamun zai ba mu cikas, mu kuma za mu kawar da shi ba tare da ɓata lokaci ba, don ba zai yiwu mu shafe sama da shekaru ashirin muna faman haƙa ƙorama sai da lokacin shan ruwan cikinta ya yi kuma wasu ƙananun ƙwari su ce za su hana mu rawar gaban hantsi ko su zame mana barazana ba." 

Ya yi shiru na sakanni sannan ya ce. "That's very good, ni aikina na wannan shekarar saura yarinya ɗaya na gama shi gabaɗaya, ita ma cikin satin nan za a yi komai a gama, sai kuma na fitilun matasa 41 da aka ba ni na samo, shi ma na gama saita komai nan da wasu awanni komai zai kammala...." Shigowa parkourn da aka yi ya saka shi faɗin. "I will call you later, ko kuma ma ƙarasa magana idan mun haɗu a wajen taro." Daga haka ya kashe wayar ya dubi mai shigowar yana gyara zaman babbar rigar jikinsa da ta sha ɗinki na alfarma.

"Barka da hutawa Yallaɓai." 

"Yawwa barka Sita, bismillah zauna." 

Bayan Sita ya zauna ya dube shi a tsanake ya ce. "Ina muka kwana akan wannan batun ne, ka san na faɗa maka gobe ne dateline ɗina ko?" Cikin girmamawa Sita ya ce. "Ranka ya daɗe an gama komai, kamar yadda na faɗa maka mahaifin yaran bashina ya ci, kuma da ma da biyu na ba shi don na ɗana masa tarko, a yanzu da na matsa masa lamba ya ce ba shi da kuɗin shi ne na ce masa da ma kuɗin aure zan kai, amma tunda haka ne na samu labarin yana da 'ya'ya mata ya ba ni ɗaya a cikinsu na aura, ba musu ya amince da gaggawa saboda na ce ko kayan ɗaki kar ya yi, to yau in sha Allah zan je na gano yaran sai na zaɓo wadda za ta dace."
Numfashi Mutumin ya sauke ya ce. "Good Sita! Na ji daɗin wannan bayanin naka, abin da nake so da kai ka tabbatar ka zaɓo irin wadda na fasalta maka, ka kiyaye da kyau kar a samu matsala, kuma kar ka baro gidan ba tare da an ɗaura muku aure ba, amma sunana ne zai kasance na ango, kai kawai za ka kasance angon zahiri ne." 

"Ba ka da matsala Yallaɓai, ai tunda ka ba ni aikin tun kafin na je gare shi sai da na sauya suna, kuma na gama tsara komai har iyayen bogin da za su karɓa mini auren, anjiman ma tare da su za mu tafi."

Cikin gargaɗi mutumin ya ce. "Ina ƙara jan kunnenka Sita, kar a samu matsala, kar sunana da duniya ta sani ya fito, ka da ko wasa kar ka bar wata alama da za a gano ka ko a bibiye ka." 

"Yallaɓai na kiyaye komai kamar yadda ka ce mini, kuma sai da na duba na lalubo gidan da na tabbatar ba su da wayewa ko ƙarfin da za su bi ba'asin ƴarsu, ba mu da matsala da wannan ko kaɗan."

"Good! Za ka ji alert kana fita, ka je sai na ji ka." 

Risinawa Sita ya yi yana zuba godiya sannan ya bar parlon. Da wani irin kallo mutumin ya raka shi tare da sakin wani guntun murmushi haɗe da dunƙule hannu ya yi wa kansa jinjina, wayar hannunsa ya latsa ya kara a kunne a karo na biyu, cikin bayar da umarni ya fara magana da faɗin. "Akwai wani yaro da zai kawo mini saƙo daga daren yau zuwa gobe da safe a guest house ɗina, yana kawowa bayan ya fita ku ɓatar da shi, ko gawarsa bana son a sake gani." Daga haka ya katse wayar ya miƙe ya nufi steps ɗin da ke parlon yana baza babbar rigar jikinsa cikin takun ƙasaita.

***** *****

Zeenat ce a tsaye tana duban Ɗahiru a shagonsa fuska a cukule. 

"Dubu uku na gani fa Ɗahiru, gaskiya ka ƙara mini wani abu." 

"To ina laifi Zeenat? Amma idan kin raina ba ni abuna." 

Wani kallo ta wurga masa ta ce. "Tunda ga ni ƴar iska ba, na zo shagon naka tun goma saura har kusan shabiyu amma na mayar maka da abin da ka ba ni." 

'To da me ce in ba yar iskar ba?' 

Ya faɗa a ransa, a fili kuma sai ya ce. "To na ba ki kin raina, ya kike so na yi miki? Ita kenan a ajikina amma na dunƙule na ba ki duk da hakan kuma sai kin yi mini gunaguni." Baki ta cuna gaba ta ninke kuɗin ta saka a jakar makarantarta, sannan ta ɗauki hijab ɗin uniform ɗinta ta zura, ta juya za ta fice daga shagon Ɗahiru ya yi saurin tashi tsaye ya lalubi rigarsa ya zira yana faɗin. "Kya jira na duba layin ai kafin ki fita ko? in kuma so kike ki tona mana asiri to sai ki je." Tsaki ta ja cike da haushin dubu ukun da ya ba ta ta fasa fitar, raɓawa ya yi ta gefenta ya buɗe ƙofar shagon kaɗan ya leƙa waje, ganin babu kowa saboda rana ta take kuma layin ba ya ɓullewa shi ya sa ba a fiya wucewa ba ya sa ya ya juyo a gaggauce ya dube ta.

"Zo ki tafi!" 

Da sauri ta fice tana waige, ya mayar da ƙofar ya rufe bayan ya yi mata alama da hannu alamar sai ta zo gobe.

Sai da ta koma ta kai wa Umma Lantana dubu biyu ta ce iya shi aka ba ta rancen a gidansu Furera bayan ta yi mata ƙaryar break aka fito ta dawo ta kawo mata don ta samu ta je gurin malamin akan kari sannan ta ƙara bazawa wani yawon.

**** **** *****

SAUBAN


Da mugun gudu ya karyo da motar ya shiga layinsu har ya kusa kaɗe wasu ƙananun yara da suke tafiya, yana kallon yadda wasu mutane da suke zaune suka miƙe a hanzarce suka janye yaran amma ko alamar tsayawa bai yi ba, sai ma dogon tsaki da ya ja ya bi su da ƙasƙantaccen kallo a wulaƙance. 
Kamar zai tashi sama haka ya fara danna horn a bakin ƙofar makeken gate ɗin gidansu, da sauri Maigadi ya zo ya buɗe masa, a fusace ya shigar da motar kamar zai bi ta kansa ya wuce ya yi parking. 

Ƴanmata biyar ne zaune a parkour suna hira cikin raha, a haka ya shigo ya same su ba tare da ya yi sallama ba.

"Autan Mom ɗinsa." 
Babbar cikinsu ta faɗa tana yi masa murmushi, bai amsa mata ba sai ƙara tamke fuska da ya yi yana bin su da kallo, hakan bai saka sun yi yunƙurin suturce jikinsu ba, saboda kaf cikinsu babu mai shigar arziƙi. 

"Yaron nan ka shiga uku da faɗin rai, ba ka da aiki sai ƙunci da harare-hararen mutane." 

Bai tanka musu ba ya nufi part ɗinsa yana sakin siririn tsaki, yadda ya fita ya bar shi haka ya dawo ya tarar da shi, a fusace ya cilla wayar hannunsa kan gado ya dawo main parkour yana ƙwala kiran sunan Mom. 

Cike da ƙasaita wata hamshaƙiyar mace take saukowa daga steps ɗin da ke parlon, ta ci kwalliya cikin wani tsadadden lace sai tashin ƙamshi take, tana duban shi da fara'a a fuskarta ta ce. "Welcome my Son!" Bai amsa ba sai baki da ya tura gaba, da mamaki ta ce. "What's happening Son? Me aka yi maka?" Kyaɓe fuska ya yi a sakalce ya ce. "Mom yau ma still a cikin dirty zan kwana?" Da sauri ta rufe bakinta ta ce. "Oh God! Ka san yau ma na manta da batun mai aikinka, I'm so sorry Sweetheart, abubuwa ne suka sha mini kai, za mu fara exam a school ga tafiya wani taro da ya taso mini, to ina son na kammala shi ya sa na manta, ka yi haƙuri ka ji? In sha Allah yanzun nan zan kira na bayar da cikiya a samo maka." Sakin fuska ya yi kaɗan ya gyaɗa mata kai. Tana murmushi ta shafi kansa ta ce. "Mu je part ɗin Dad ka yi wanka, kafin ka gama na saka Laure ta gyara maka ko'ina." Yamutsa fuska ya yi kamar ya ga kashi ya ce. "No Mom, bana son na wannan tsofaffin, ko ƙofar part ɗina suka taɓa ƙyanƙyaminsa zan ta ji bare su taɓa mini bedsheet." Ya ƙarashe maganar kamar zai yi amai. Cikin lallaɓawa matar ta ce. "Mu je ka yi wankan, kafin ka gama ka ci abinci na gyara maka da kaina." Hangame baki ƴanmatan suka yi, cikin waro ido Shukura ta ce. "Mommy da kanki? Sauban ɗin za ki gyarawa ɗaki." 

"Ya ranku?" Ya faɗa yana kama hannun Mom.
Side hug ta yi masa ta ce. "Mu je Autana, rabu da su, ka kwaso gajiya su suna zaune a gida tun safe ba za su ƙara maka ciwon kai ba." 

Kamar ƙaramin yaro haka ta ja hannunsa suka haura sama ƴanmatan na tsokanar shi.


***** ****** *****

Haseena tana kwance a ɗakinta tana kallon status ɗin Salma ƙanwar Saudat na Mother's event ɗin da ta saka, yadda suka yi kyau da su da ƴan gidansu matar Zubairu ba ƙaramin tafiya da imaninta ya yi ba, ta dinga kallon Mama da surukanta yadda suka yi kyau sosai kamar ba su ne iyayen angwaye da amare ba. A fili ta furta. "Gayu da kuɗi sun yi a rayuwa, yanzu su Saudat kansu tsaye za su yi ta yaɗa hotunan nan ba wani ɗar saboda iyayensu a waye suke, sun kankaro musu mutunci a bikin gidansu, sun je sun yi rawa da liƙi ƙawayensu ƴan gayu suna taya su. 
Wani video da ya ja hankalinta take ta son ta buɗe tun ɗazu amma ya ƙi buɗuwa, hakan ya sa ta gane datarta ce ta ƙare. Tsaki ta ja a fili ta tashi ta ajiye wayar ta fito tsakar gida, da Amma ta fara tozali zaune a cikin rana tana tatar waken awarar yamma, tana sanye da ɗaurin ƙirji, gumi yana ta yanko mata ta ko'ina a jikinta, gajiyar aiki tun safe da rana ya saka ta cakuɗe ta ƙara baƙi, wani abu mai zafi ne ya zo ya yi tsaye a zuciyar Haseena, ta ji wani yanayi mai kama da haushi da ƙyama yana zagaye zuciyarta a game da Amman, yanzu ta gama ganin iyayen wasu fesfes da su abin sha'awa, amma ita ga tata uwar da ta manta rabon da ta gan ta ta yi wanka ta saka kaya masu kyau ta yi......

"Haseena bacci kike ne nake ta kiran ki ba ki amsa ba?" Umma ta katse mata tunanin da take da faɗin haka. 
Maimakon ta ba ta amsa sai ta keɓe fuska ta ce. "Amma don Allah ki nemi kayanki ki saka full ki daina zama da wannan ɗaurin ƙirjin zani daban ɗankwali daban, ga gida na mutane yara suna shigowa duk suna ganin ki a haka." Murmushi Amma ta yi ta ce. "Haseena kenan sarkin son gayu da gwalli, da ina da yadda zan yi da na koma yadda kike so, amma ina son ki sani duk yadda kika ga mutum yana rayuwa haka Allah ya tsara masa, ba shi ya tsara wa kansa ba, duk wani jin daɗi da rayuwar hutu babu wanda ba ya son samun su a duniyar nan, amma idan Allah bai ba ka ba haka za ka karɓi ƙaddararka, to mu ma wannan ita ce tamu Haseena, dole sai na yi wannan ficiccikewar sana'ar sannan za mu samu abinci da buƙatun yau da kullum, to ina ta sana'ata ina na ga lokacin yin kwalliya da saka kaya masu kyau?" Shiru Haseena ta yi don maganganun Amma ba su wani gamsar ita ba, inuwa ta nema ta zauna tana tunanin idan bikinta ya tashi za a yi event haka Amma za ta je a saka mata taken  uwar amarya ƙawayenta da familyn mijinta su gan ta? Ita tunda take ma ba ta taɓa ganin Amma da mayafi ba sai dai hijabi, ba ma ta iya yafa shi ba, to da hijabin za ta je kenan? Girgiza kai ta yi da sauri kamar wadda take magana da wani, ta fara hasaso matan danginsu ko za ta hango mai ɗan dama-dama da za ta yi replacing ɗin Amma a ranar, don gaskiya ba za ta iya nuna ta a yadda take ɗin nan a gaban kowa a matsayin mahaifiyarta ranar bikinta ba, ita da take burin bikinta ya kasance gagarumi da ko maƙiyinta sai ya yaba.

"Ba zama za ki yi ba, girki za ki tashi ki ɗora mana."

Tana turo baki ta miƙe ta ce. "Idan ban gama ba la'asar ta yi sai dai ki ƙarasa, don zan je kamun bikin Salma ƙanwar Saudat, kuma da wuri nake son zuwa don na zauna a gaba yadda zan fi ganin komai da kyau." 

Amma ta ce. "Au har an fara bikin? Shi ya sa kwana biyu na ji Saudat shiru ba ta leƙo mu ba, Allah Sarki, ita ma Allah ya kawo mata miji na gari, Maman nasu ba ta gayyace mu ba da na leƙa ko ranar yini ne na yi musu Allah ya sanya alkhairi." Da sauri Haseena ta ɗago daga gyara kwarfet ɗin da take ta kama haɓa ta ce. "Taɓ! Amma ya za a yi ta gayyace ku da ma? Ke kin ga mayan matan da suka je bikin kuwa? Ƴan gayu masu kuɗi, kin san gidansu matar Yaya Zubair ɗin suna da abin hannu sosai, ga shi sun iya ɗaukar wanka, idan ta gayyace irinku ai ɓata mata bikin za ku yi, wallahi ban ga laifinta ba da ta ƙi kawo muku kati." Da wani irin kallo kawai Amma ta bi ta, a ranta tana addu'ar Ubangiji ya shirya mata ita, tunda ta gane halin ƴar tata da inda ta saka gaba a rayuwarta take yi mata addu'a ba dare ba rana, amma kamar wadda ake ƙara turawa, kullum burikan nata ƙara hauhawa suke.



***** ******


Tun wainar masar da Ahayan ta siyo suka karya da ita da safe har yamma ba ta kuma saka komai a cikinta ba, ga aiki da Inno da Umma Lantana suke ta saka ta, yaran gidan duk sun tafi Islamiyya amma ban da ita saboda ba ta da mai biya mata kuɗin wata, ta yi nacin zuwa a baya ana koro ta, ƙarshe da Malaman suka yi mata wani cin mutunci da tozarci ya sa dole ta haƙura. 
Tana kwance a kan tabarma cikin galabaita ta ji ƙamshin mutumin da ta rasa me take ji a kansa a duk lokacin da ta gan shi, saurin tashi zaune ta yi gabanta na faɗuwa ta ɗukar da kanta ƙasa.
Umma Lantana da ke aikin tuwon dare tana yada wa Umma waƙe-waƙen habaici ma tsit ta yi da ta gan shi, lokaci ɗaya kuma ta washe baki tare da faɗin. "Abban yara sannu da zuwa." Ba tare da ya daina tafiya cikin takunsa na ƙasaita ba ya ɗaga mata hannu, cikin rashin nutsuwa Ahayan ta ce. "Sannu da zuwa Abba Adam." 

"Me ya hana ki zuwa Islamiyya?" 

Waige-waige ta fara don ba ta yi zaton da ita yake ba, a hakimce Inno ta fito daga ɗakinta ta ce. "Adam wannan yarinyar nan kake tambaya abin da ya hana ta zuwa Islamiyya? Sai ka ce ba ka san neman kuɗi kawai suka zo yi duniya ita da uwarta ba? Ina ta ga lokacin zuwa makaranta ban da abinka Kai ma?" Bai kula ta ba sai ido da ya zuba wa Ahayan, fuska a tsuke ya ce. "I'm asking you!" Yadda ya ƙarashe maganar ya sa ta dibibice ta ce. "Kuɗin... kuɗin wata ne na daɗe ban biya ba shi ne aka ce kar na ƙara zuwa." Kamar ba shi ta ba wa amsa ba haka ya basar da ita ya nufi inda Inno take wadda take ta aikin hararar Ahayan cikin tsana, wayarsa ya lallatsa ya ce. "Na tura miki kuɗi, a ba ta ta kai kuɗin watan." Daga haka ya juya ya bar gidan, tsabar baƙinciki daskarewa Umma Lantana ta yi, Inno kuwa wani yawu ta haɗiye mai ɗaci, don ko bare a waje ba ta son ta ga ya yi wa Ahayan alkhairi bare kuma jininta, ga shi Allah ya zuba wa Abba Adam wani irin kwarjini, duk da yana ƙaninta amma ba za ta iya musa masa ba, ba ita ba ma har Baba da yake babbansu ba ya iya jayayya da shi, ƙwafa ta ja cikin takaici ba ta ce komai ba ta koma ɗakinta. Kamar mahaukaciya haka Umma Lantana ta miƙe ta ce. "To Karima Sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha, aikinki ya ci, a je a ƙara wa Malam kuɗi, don na san idan ba aikin asiri ba babu yadda za a yi Adam ya ma bi ta kan ƴarki har ya biya mata kuɗin makaranta, mutumin da ƴaƴan ƴan'uwansa ma ba bi ta kansu yake ba." Numfashi Ahayan da mamaki ya ƙamar da ita ta sauke, tsabar al'ajabi ko godiya kasa yi masa ta yi, gani take kamar a mafarki, cike da zumuɗi ta tashi ta shiga ɗakinsu ta samu Umma a kwance kamar ruwa, don ko tsakar gida ba ta iya fita idan ba dole ba saboda azabar tsoron Inno da Umma Lantana.

"Umma ashe ina da rabon komawa Islamiyya, wallahi da har na cire rai, saboda Ko na yunƙura na ce zan tara kuɗin ba sa taruwa." Tashi zaune Umma ta yi ta ce. "Allah ya sa masu kauri ya bayar, don idan kaɗan ne haƙura za ki yi mu ci abinci da su, don muna fama da yunwa ba za a kwashe kuɗi akai wa wasu ba." Cikin rashin jin daɗi Ahayan ta ce. "Amma Umma idan ya kuma zuwa ya gan ni ban je ba fa?"

"A ina zai gan kin? Shi da sai ya yi kwanaki ba ya gidan ma!"

Za ta kuma magana Umma ta ce ta tashi ta ba ta guri, jiki a saɓule ta miƙe ta koma tsakar gidan. 


Da tsatsar takaici Inno take duban Husna da ke kwance tana danna waya ta ce. "Dubu goma ya tura fa, abin da ya fi baƙanta mini rai ko gaishe ni Adam bai yi ba amma ya tsaya kula wannan tsainanniyar yarinyar da ko buɗe ido na gan ta bana ƙaunar yi." 

"Halin Abba Adam ne ba ki sani ba Inno ko me? Kin san shi fa abin da ya yi niyya kawai yake yi." 

Ƙwafa Inno ta yi mai ƙarfi ta ce. "Aiko dubu biyar zan ba ta wallahi, shi ma don kar ya gane ne da ko biyar ba zan ba ta ba don makirar uwarta, kin san shi da ƙwaƙwa kamar mai gani har hanji tsaf zai gane idan na hana ta, shegiyar yarinya mai siffar aljanu, ba tana murna da rawar ɗuwawun zuwa ta sanar da uwarta ba? To wallahi Sai na gana mata azabar da za ta yi jinyar da sai ta ci fiye da kuɗin a magani."



Da yamma Baba ya dawo gidan fuska a haɗe yana muzurai, lokacin yaran gidan duk sun dawo daga Islamiyya, duk suka yi masa sannu da zuwa amma da Uhm kawai ya amsa musu, Ahayan na durƙushe a bakin murhu tana rura wa Umma Lantana wutar ice, ita kuma tana zaune a kusa da ita akan kujerar ƴar tsugunno tana yi mata faɗan babu gaira babu dalili. A sakalce Zeenat ta fito daga ɗaki tana hamma ta dubi mahaifiyarta ta ce. "Wai har yanzu tuwon nan bai sauka ba? Ni fa gaskiya yunwa nake ji." A ƙufule Umma Lantana ta ce. "To ta saka baƙin hali ta ƙi yin abu da jiki, sai wani salalo-salalo take yi." Daidai lokacin Umma ta fito daga ɗakinta ta nufi na Baba, Umma Lantana ta raka ta da harara tare da jan tsaki.

Sai da Umma ta ƙara kallon inda Ummi, Rauda da Sabira suke kwance male-male saboda yunwa sannan ta kama labulen ɗakin Baba ta buɗe cikin ƙwarin gwiwa, yana zaune ya baza tsire da yawa a cikin takarda yana ci, kunnensa kare da waya suna tattaunawa akan masu karɓar masa kuɗin hayar gidajensa, da sauri ya katse wayar ya lalubo babbar rigarsa da ya cire ya kifa a kan tsiren, yana muzurai cikin ɗaga murya ya ce. "Amma dai Karima an yi mahaukaciyar mata kuma dabba wallahi, ya za ki shigo mini ɗaki ba neman izni ba komai?" Tsugunnawa ta yi cikin laluma ta ce. "Allah ya ba ka haƙuri Malam ya huci zuciyarka, na yi ta sallama har sau uku ba ka ji ba n..."

"To tunda ban amsa ba ba sai ki kama gabanki ba? Ko dole ne sai kin zo kin nuna mini wannan taɓinanniyar fuskar taki?"

"Ka yi haƙuri Malam, wallahi dole ce ta saka ka ga na zo, yunwa muke ji tun safe ba mu ci komai ba, shi ne na zo ko za mu samu ko ɗari biyar ce mu sarrafa mu yi wani abun?"

Cikin hargowa kamar zai kai mata duka ya ce. "To ban da ita ban samo ba, wannan wacce irin jaraba ce? Daga dawowata ko hutawa ban yi ba za ki zo ki ishe ni da wani batun abinci, ku ga ku kaji iyayen ci da babu abin da kuka sani sai shi, daga ina kike abinci daga ina kika dawo yunwa." Za ta kuma magana ya buga mata tsawa da faɗin. "Tashi ki ba ni guri!" Sum-sum Umma ta miƙe tana jin kamar iska za ta iya kwasar ta ta watsar tsabar yunwa, tun kafin ta fita daga ɗakin ta jiyo dariyar da Umma Lantana take ƙyalƙyala mata. Tana rarraba ido ta wuce kanta a ƙasa tsabar kunya da baƙinciki. A fusace Baba ya biyo bayanta yana ci gaba da mita, Inno na ƙara zuga shi, sai da ya gaji don kansa sannan ya yi ƙwafa ya ce. "Ku tattara mini yaran nan bayan Magriba wanda ya ce yana son haɗa iri da ni zai zo ya zaɓi wadda ta yi masa, sai ku shirya, don har ɗaurin auren a yau za a yi ya tafi da matarsa." Daga haka ya juya ya koma ɗaki ya ci gaba da cin tsirensa hankali kwance.



*Zeey Kumurya*
*****