BABI NA BIYAR
Bayan ta kammala addu'o'i bayan sallah ta miƙe ta naɗe sallayar, ta ajiye shi a inda ya dace.
Sannan ta dubi Mama ta ce,
"Mama, zan je na amso littafina a wurin Deejat. Jiya ta tafi da shi."
Mama ta ɗaga kai tana kallonta.
"To, ki je ki dawo da wuri. Kar ki ɓata lokaci."
"To Mama."
Ta amsa sannan ta fice daga ɗakin.
A duk faɗin garin Bauchi, Deejat ce kaɗai ƙawar Rubaah ta kut-da-kut. Girmansu kusan ɗaya ne, domin ita ma Deejat ba ta ƙarasa shekara goma sha biyar ba.
A cikin dukkan ƙawayenta, Deejat ce kaɗai ta fahimci halin Rubaah. Ta san cewa zuciyarta tana da kirki, sai dai ba ta jure wulaƙanci ko raini.
Idan Rubaah ta fusata tsiwarta ya tashi tayi masifa, Deejat ba ta gardama da ita; sai ta yi shiru ta bari har zuciyarta ta huce.
Idan kuma miskilancin Rubaah ya tashi ta ƙi magana da kowa, a makaranta, Deejat ce za ta bi ta a hankali tana lallashinta har sai ta saki jiki.
Tana isa gidan su Deejat, ba ta tsaya hira ba. Littafinta kawai ta karɓa, ta yi wa mahaifiyar Deejat sallama, sannan ta fito.
Deejat kuwa ta biyo bayanta domin ta yi mata rakiya kamar yadda ta saba.
Deejat ta karɓi littafin ta riƙe mata har suka fito ƙofar gida.
Suna fita Rubaah ta karɓi littafin tana cewa,
"Deejat, ba ni na tafi gida. Mama ta ce kar na jima."
Bayan ta karɓi littafinta a hannun Deejat, Rubaah ta juya da nufin komawa gida.
"Ruby, ki tsaya mana ko da minti biyu ne. Daga zuwan ki kenan za ki tafi."
Rubaah ta dakata ba tare da ta juya gaba ɗaya ba, ta waiwayo ta kalle ta da gefen ido.
"Lafiya?"
Deejat ta matso kusa da ita tana murmushi.
"Wallahi baki da kirki. Da ƙyar ake samun ki ki tsaya hira. Idan kin zo gidanmu, ko zama ki ɗan daɗe ba kya yi. Ni fa nakan wuni a gidanku."
Rubaah ta taɓe baki.
"To me zan tsaya yi? Ai kin ba ni littafin da na zo karɓa, kuma na gaya miki Mama ta ce kar na jima."
Deejat ta ɗan yi dariya.
"Ke dai haka kike. kullum bakya canzawa."
Rubaah ta girgiza kai.
"Ni ba gyara nake buƙata da surutunki ba. Karatu nake buƙata, kuma yanzu zan je na yi."
Dukansu suka yi ɗan murmushi.
Deejat ta ɗan rage murya.
"Ruby... Allah ki kula da kanki. Bana son yadda kike yawan faɗa da mutanen gidanku. Kin ga ba kirki suke da shi ba."
Rubaah ta ja numfashi.
"Ni ba na neman faɗa, Deejat. Amma duk wanda ya taka ni, ba zan zuba masa ido ba."
"Na sani... amma wani lokaci haƙuri ya fi anfani."
Rubaah ta yi kwafa.
"Haƙuri ma yana da iyaka."
Deejat ta san halinta, saboda haka ba ta ƙara matsa mata ba. Sai ta ce,
"To Allah Ya kai ki gida lafiya."
"Amin."
Rubaah ta ɗaga mata hannu kaɗan, sannan ta juya ta kama hanyar gida.
Deejat ta ci gaba da ɗan taka mata suna ɗan hirarsu a hankali.
Suna isowa wani ɗan lungu da ke gefen layin.
Nan idanun Rubaah suka sauka kan Habu da wasu samari huɗu. Sun saka tukunyar abinci da ya ɗauko ta Hansatu a tsakiya, kowa na ta zuba manyan loma cikin baki kamar waɗanda suka shekara ba su ci ba.
Tururin abincin har yanzu na tashi daga tukunyar.
Deejat ta tsaya cak tana ware idanu.
"Ruby... wancan fa kamar Habun gidanku ne ko?"
Rubaah ta bi inda take nuna wa da kallo, sannan ta yi kwafa.
"Shi ne."
Deejat ta ƙara matsowa gaba tana kallon tukunyar.
"Amma... wannan tukunyar fa kamar ta girki ce. A ina suka samo ta?"
Rubaah ta kyaɓe baki.
"Ba su ka samo ba dai... ya sato musu daga gidansu dai. Tukunyar abincin mamansa ya sato musu."
Deejat ta buɗe baki da mamaki.
"Subhanallah! Da gaske?"
Rubaah ta gyada kai.
"Wlh kuwa na uwar shi ya ɗauko musu. Hmm wata kila ina sun gama tukunyar ma ya kaita wa masu alalumo."
Deejat ta dafe ƙirji.
"Jiya ma fa na gan su a bayan layin nan. Sun sace wata kaza suna gasawa."
Rubaah ta yi kwafa.
"Ki ƙyale su. Wata rana aikinsu zai bayyana. Duk wanda ya saba da abin wani, wata rana sai ya faɗa tarkonsa."
Ta ƙara matse littafin da ke hannunta, sannan ta ci gaba da tafiya ba tare da ta sake waiwayen lungun ba.
***
***
Tun daga bakin ƙofar gida, Rubaah ta fara jin hayaniyar Hansatu tana kaɗa murya kamar wacce za ta yi aron baki.
"Huhuhu! Jama'a ku zo ku gani! Wallahi yau na ga satar da ban taɓa ganin irinta ba! Kai ni Hansatu, wai har wannan abin zai faru a gidana?"
Muryarta ta cika tsakar gidan har ta sa maƙota suka fara leƙowa domin jin abin da ya faru.
Rubaah ta tsaya na ɗan lokaci a bakin ƙofar gidan, ta yi murmushin gefen baki.
A zuciyarta ta ce,
*"Au sai yanzu kika gano abin da ɗan naki ya aikata."*
Ba tare da ta ƙara cewa komai ba, ta shiga cikin gidan a nutse.
Hansatu kuwa kamar jira take yi ta hango Mama da ke zaune cikin ɗaki tana naɗe kaya.
Da sauri ta banko labulen ɗakin da ƙarfi tana huci.
"Fito nan Maryamu! Eh lallai yau kin nuna min cewa ko babu miji mace tana iya haihuwa da sata. Ashe har tukunyar abincin da ke kan murhu za a ɗauke mini ita!"
Mama ta ajiye kayan da take naɗewa cikin mamaki, sannan ta fito tana kallonta.
"Hansatu... lafiya? Wace tukunya kike magana a kai?"
Hansatu ta kama kugunta tana jijjiga.
"Wacce kuma? Tukunyar girkina mana! Na shiga ɗaki mintuna kaɗan, da na fito sai na tarar da murhu wayam babu komai. Sai itace kawai ke ci, amma tukunyar babu ita babu labarinta."
Mama ta girgiza kai cikin mamaki.
"Subhanallah! Amma me ya sa kika fara zargina? Ni fa ba na son irin wannan fitinar."
Hansatu ta ɗaga murya fiye da da.
"To wa kuma zai ɗauke ta a gidan nan? Daga ni sai ke! Ko aljanu ne suka zo suka ɗauka?"
Mama ta ɗan fusata.
"Hansatu, ki kiyaye zancenki. Zargi ba hujja ba ce. Kuma ni ban taɓa ɗaukar abin wani ba."
"Wallahi idan ba a fito min da tukunyar nan ba, sai na tayar da hankalin kowa a gidan nan!"
Mama ta buɗe baki za ta sake magana...
A dai-dai lokacin Rubaah ta iso tsakiyar gidan.
Ta dubi Hansatu na ɗan lokaci, sannan ta ce cikin kwantar da murya amma cike da kaifin magana,
"Ki daina zargin Mama. Barawon tukunyar ba ya cikin wannan ɗakin."
Hansatu ta juya da sauri.
"To uwar iya tsara zance, ai sai ki nuna min ɓarawon, bayan wanda na tabbatar da shi a gabanna."
Rubaah ta nuna hanyar waje da yatsarta.
"Ki yi sauri ki je bayan layi. Habu da abokansa suna can suna cin abincin da ke cikin tukunyar. Idan kika makara, ko alamar manja ba za ki tarar ba."
Ta kaɗa kwayar idanunta gami da shanye su kana ta kara girmansu a kan Hansatu, sannan ta ce
"Kuma daga yau... kada ki sake kiran Mama 'ɓarauniya'. Domin idan akwai ɓarawo a wannan lamarin, kin fi kowa sanin wanda kika haifa."
Hansatu ta tuma tsalle kamar wacce aka tsikara.
Ta mulmulo wani uban ashar ta jefawa Rubaah.
"Makira! Tacacciya! Shafaffiya! Rasai rasa kunya! Ɓeran tanka! Kin ga ɗana ya miki kama da mayunwaci ne? Ga ku nan mayunwata masu cin alfarma, shegiyar agola. Ana ciyar da ke, har kina da bakin yi wa ɗan gida sharri?"
Rubaah ta yi wata yar siririyar dariyar raini, sannan ta kaɗa ƙwayar idanunta cikin tsiwa.
"Kin manta ke ce mai ba mu numfashi ai. To daga yau ki riƙe iskar da muke shaka, kada ki sake bari ta iso gare mu."
Hansatu ta buɗe baki za ta sake ɗaura wata masifar...
A dai-dai lokacin ne aka turo ƙofar gidan.
Malam Musa ne ya shigo.
Tun daga bakin ƙofa ya ji ƙarshen maganar Hansatu da kuma amsar da Rubaah ta ba ta.
Ya tsaya cak, ya dubi kowa kafin ya ce da murya mai cike da tsawa,
"Kai! Ya isa haka!"
Tsakar gidan ya yi tsit.
Ya ƙaraso yana muzurai gami da kallon Hansatu.
"Akwai wanda yake ciyar da kansa a gidan nan bayan ni da nake ciyar da shi? Duk wanda yake ci a gidan nan, ni ne nake ɗaukar nauyinsa."
Hansatu ta karkace gefe tana taɓe baki.
"Ai dama duk wani iskancin da yarinyar nan take ji da shi daga gare ka yake. Ta ci mutuncin 'yan gida, kai kuma ka tsaya kana kare ta. To wallahi idan ba a fito min da tukunyar abincina ba, sai na ɗaga wa kowa hankali a gidan nan."
Malam Musa ya ɗan kwantar da murya.
"Lafiya, fara gaya min me ya faru."
Hansatu ta kwashe komai ta faɗa masa tun daga lokacin da ta ɗora tukunyar a murhu har zuwa lokacin da ta dawo ta tarar babu ita.
Mama ta ƙara masa bayani cikin natsuwa.
Kafin ta gama magana, Rubaah ta ce,
"Ni kuma na ga Habu da idona."
Duk suka juya suka kalle ta.
"Ɗazu, lokacin da na fito daga banɗaki, shi na gani yana fito da tukunyar daga kitchen. Yanzu kuma kafin na shigo gida na gansu shi da abokansa a bayan layi, sun saka tukunyar a tsakiya suna cin abincin."
Malam Musa ya waro ido.
Ya san Rubaah tana da tsiwa, amma abu ɗaya ya sani game da ita...
Ba ta cika ƙirƙirar ƙarya domin ta cuce wani ba.
Nan take ya naɗe babban rigarsa yana faɗin,
"Ku tsaya nan."
Sai ya fice da sauri ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Mama ta fahimci Hansatu ba za ta yi shiru ba.
Ta taɓa kafaɗar Rubaah a hankali.
"Shigo mu koma ciki."
Rubaah ta yi kwafa, ta ciza gefen lips ɗinta, sannan ta bi bayan Mama zuwa ɗaki.
Suna shiga ɗaki Mama ta ce,
"Ke Rubaah, me yasa baki faɗa ba tun da kika gan shi yana fita da tukunyar? Ai da ba za a bar shi ya fita da ita ba."
"Hmm Mama, bar su kawai. So nake na kure ƙaryar maƙaryaci."
Mama ta bi ƴar tata da ido cike da mamakin maganar da ke cikin bakinta, sannan ta girgiza kai ba tare da ta ƙara cewa komai ba........!
Mommyn Twins ce