BABI NA SHIDA
Hansatu kuwa...
Har yanzu bala'i take zazzagawa, tana ta jifar Mama da habaici, tana rantse-rantsen cewa sai ta gano wanda ya saci tukunyar abincinta.
Babu wani barikin da za a gwada mata.
Malam Musa bai tsaya ko'ina ba. Kai tsaye ya nufi lungun da Rubaah ta sanar masa da su Habu suke.
Tun daga nesa ya hangi Habu da samari huɗu. Su biyar ke nan gaba ɗaya. Sun zauna zagaye da tukunyar abincin, kowannensu na sakin loma.
Rabinsu ma har manja ya shafe musu baki da hannaye, amma ko ɗaya cikinsu bai damu ba.
Malam Musa ya tsaya cak na ɗan lokaci yana kallonsu.
Ya girgiza kai cikin takaici.
"Amma an yi ƴan iskan yara..."
Sai kuma ya ɗaga murya da ƙarfin gaske.
"HABU...!"
Muryarsa ta kaɗa lungun.
Habu ya firgita matuƙa. Da sauri ya ɗago kai, idanunsa suka haɗu da na mahaifinsa.
Gabansa ya faɗi.
Cikin ruɗani ya zare hannunsa daga cikin tukunyar, ya miƙe tsaye yana rarraba ido.
Abokan nasa kuwa, sai a lokacin suka fara ɗagowa ɗaya bayan ɗaya. Wasu ma har yanzu loma ce a bakinsu.
Malam Musa ya ƙaraso da sauri.
Bai tsaya sauraron kowa ba.
Tass...!
Ya kai wa ɗaya daga cikin yaran mari.
Sai ya juya ya fizgi kunnen wani.
"Kun ci ubanenku, shegun yara marasa mutunci! Barayin banza! Yanzu kai Habu, ɗan sabar rashin mutunci, ka shige madafa ka ɗauko tukunyar abincin da uwarka take dafawa, ka fito muku da ita kai da shashashshun abokanka, ku saka tukunya a gaba kuna loma dan rashin sanin ciwon kai.
To duk za ku ci ubanku! Gurin 'yan kwamitin unguwa zan kaiku su yi muku ɗan banzan duka. Baku da aiki sai satan kaji da agwagin mutane. Ni da kai na zan kaiku su yi muku pata-pata!"
Duk suka fara ja da baya cikin tsoro.
Ya sake ɗaga murya.
"Kun samu shinkafa kun saka gaba kuna aikawa cikinku kamar da kuɗinku aka saya? Ashe wannan shi ne abin da kuke yi kullum?"
Duk suka sunkuyar da kai.
Malam Musa ya nuna Habu da yatsa.
"Shashasha mara mutunci! Za ka gamu da ni."
Habu ya buɗe baki zai yi magana...
Amma tsawar da Malam Musa ya sake bugawa ta maida shi shiru.
Ya kai masa bugu a baki.
"Rufe mini baki! Yau ba ƙarya za ka yi ba. Za ka ci ubanka ne, mara hankali kawai."
Cikin fushi yaci gaba da faɗin
"Yanzu na fara yarda da ƙararrakin da ake ta kawo mini a kanku. Kullum sai an ce kun sace kaza, kun sace agwagwa, kun sace wani abu a unguwa. Ashe duk gaskiya ne."
Ya nuna sauran yaran.
"Ku kuwa ku tsaya a nan zanje na dawo, duk sai nayi maganin ku."
Ya juya ya dubi Habu.
"Ɗauki tukunyar, mu je."
Habu ya sunkuyar da kai ya ɗaga tukunyar, wadda tuni suka cinye rabin abincin cikinta.
Malam Musa ya tasa keyarsa.
suka nufi gida.
Habu ya bi bayansa a hankali, kansa a ƙasa, yayin da sauran samarin suka tsaya suna kallon juna cikin tsoro, ba su san ko su gudu ko su jira dawowarsa ba.
***
Hansatu na tsaye tana ta zazzaga bala'i.
Ba ta rufe baki ba sai ga Habu ya shigo cikin gidan, kansa a ƙasa, yana kinkime da tukunyar girkin da hannu biyu.
A bayansa kuwa Malam Musa ne, fuskarsa a ɗaure tamau.
Da ganin Habu da tukunyar, tsakar gidan ya yi tsit na ɗan lokaci.
Mama ta fito daga ɗaki tare da Rubaah, dukansu suka tsaya suna kallon abin da ke faruwa.
Malam Musa ya nuna Habu da yatsa.
"Ga ɗanki nan! Shi ya ɗauki tukunyar. Ai tun da Rubaah ta faɗa mini abin da ta gani, na san ba za ta yi mini ƙarya a kan irin wannan abu ba."
Mama ta riƙe haɓa ta yi kicin-kicin da fuska.
Habu bai iya ɗaga kai ya kalli kowa ba. Kunya ta cika shi, sai faman murza yatsunsa yake yi.
Hansatu kuwa, duk da ta ga ɗanta da idonta, sai ta ture fuska tana jan tsaki.
"Eh mana! Ai dole ka ce Rubaah ba ta ƙarya, tunda ita ce abar so a gidan nan. Ita da uwarta ai duk abin da suka ce shi ne gaskiya."
Ta fizge tukunyar daga hannun Habu da ƙarfi.
"Dalla matsa daga gabana! Kai ma ka biye wa waɗancan 'yan iskan abokan naka. Wallahi su suka lalata ka. Na sha gaya maka ka daina bin banza, amma ka ƙi ji."
Ta juya da sauri ta nufi kitchen, tana tafiya tana ƙunƙuni saboda kunyar da ta lullube ta.
Rubaah ta bi bayanta da kallo, sannan ta yi wata ƙaramar kwafa.
Ta ciza gefen lips ɗinta, ta girgiza kai a hankali, sannan ta juya ta koma ɗakin Mama ba tare da ta ƙara cewa komai ba.
Malam Musa kuwa bai bar Habu ya huta ba.
Ya damƙi wuyan rigarsa.
"Zo mu tafi!"
Habu ya ɗago kai a razane.
"Ina kuma za mu je, Baba?"
"Za ka sani idan mun isa."
Ya tasa keyarsa zuwa bakin ƙofa.
Sai da suka fita daga gidan sannan ya ce,
"Yau sai na kai ka gaban 'yan kwamitin unguwa. Sun daɗe suna kawo mini ƙararka, amma ina ganin kamar ƙage ne. Ashe duk gaskiya suke faɗa."
Jikin Habu ya yi sanyi ƙwarai.
"Baba, don Allah ka yi haƙuri. Wallahi ba zan sake ba."
Malam Musa bai ko waiwayo ya kalle shi ba.
"Yau haƙurin ya ƙare."
Suka ci gaba da tafiya, Habu na binsa a baya kamar wanda aka yankewa hukunci.
Hansatu kuwa, saboda takaicin abin da ya faru, ranar ba ta ba Mama da Rubaah abincin da ta dafa ba.
Tamkar su ne suka saci tukunyar.
Mama dai ba ta ce komai ba. Ta shiga ɗaki, ta tattara ɗan abin da Allah Ya hore mata, ta haɗa musu abin da za su ci, sannan ita da Rubaah suka ci cikin godiya ga Allah.
Bayan kwana biyu.....
Karfe uku na yamma, Rubaah ta yi shirin tafiya makarantar Islamiyya.
Ta sanya hijabinta cikin tsari, ta ɗauki littattafanta, sannan ta fito daga ɗaki.
Mama na zaune tana gyaran kayan miya.
Ta ɗago kai ta kalli Rubaah.
"Kin shirya?"
Kai ta gyada.
"Eh Mama."
Mama ta yi murmushi kaɗan.
"To Allah Ya tsare. Ki tafi a hankali, kuma ki dawo kan lokaci. Kar ki tsaya yawo."
"In shaa Allah."
Ta amsa cikin biyayya, sannan ta juya ta fita.....
★★★★★★
"Abban Mashkur, kar ka yi min haka. Ka taimake ni, ka ba ni haƙƙina."
Wani uban tsawa ya daka mata.
"Ke! Dalla dakata, Malama! Bana son fitsara da rashin kamun kai. Wani sabon salon makirci kika ƙirƙiro yanzu? Saboda yanzu na yi aure shi ya sa kika fito da wannan sabon salon ko?
To wallahi, ki saurara. Duk yadda kika kai ga iya makirci, haka za ki gan ni. Ki bar ni da amaryata, domin ina sonta.
Wannan sabon salon da kika fito da shi ba zai kai ki ko'ina ba.
Ai kin banza ne kawai. Saboda yau ina ɗakin amarya ne shine zane zaki fito da wannan sabon makirci.
Amma Ramlat, kin ba ni mamaki, wallahi."
Cikin ɗimbin mamaki take kallonsa.
Anya wannan Mustapha ne kuwa? Ko kuwa an sauya shi ne?
Kai ta dafe da hannayenta biyu, tana jin zafin kalamansa tare da tsananin haushin kanta.
Ta kuma tsani yanayin buƙatar da ta bijiro mata.
Tsawon wata guda kenan tana fama da wannan ƙaddarar.
Ta yi ta daurewa tana ɓoye abin da ke damunta.
Sai dai ina...
Yanzu lamarin ya fi ƙarfinta. Dole ta bayyana abin da ke damunta. Domin idan ta ci gaba da ɓoyewa, tabbas za ta jefa kanta cikin mummunar cutuwa.
Wallahi, da akwai hanyar da za ta cire wa kanta wannan abin da yake damunta, da tun tuni ta yi hakan. Kafin wutar fitinar ta ruru har ta jefa ta cikin wannan hali.
Duk da ta san cewa yau ba kwananta ba ne, amma babu yadda ta iya.
Ita kanta ba ta san daga ina wannan masifar sha'awa take tasowa tana addabarta ba.
Kai ta sake dafe wa, tare da riƙe cikinta da ya fara tsufa, wanda ya dunƙule ya cure wuri guda.
Tana jin tamkar ƙara rura mata wannan buƙata ake yi.
Ya sake jefa mata wani mugun kallo.
"Wannan hanyar da kika ɗauko dai ba mai bullewa ba ce. Gara ki dawo Ramlat ɗin da na sani, domin ni Mustapha na girmi irin wannan makircin."
Ya juya zai bar wurin.
Da sauri ta miƙa hannu ta riƙo bayan rigarsa.
Cikin zubar hawaye, da rasa mafita, tare da cushewar kwakwalwa, ta ce,
"Abban Mashkur... ka fi kowa sanin halina. Kai ne za ka ba da shaida cewa duk tsawon zamana da kai, matsayin da kake da shi na mijina bai taɓa sa na zo gabanka kai tsaye ina neman ka a shimfiɗa ba.
Duk da kuwa ba haramun ba ne.
Yau kam babu yadda na iya. Na kai matuƙa, ba zan iya jurewa ba.
Ni mace ce mai rauni. Don Allah kar ka zama sanadin jefa ni cikin halaka.
Wallahi, tun da ka yi wannan aure ban taɓa sa a raina zan yi zaman makirci da matarka ba.
Na san yau ba kwanana ba ne. Amma ka sani, ba ni da wani miji da zan je wajensa in ba kai ba.
Ita ma mace ce kamar ni. Wata rana hakan na iya faruwa da ita. Wallahi, har cikin raina na yafe mata wannan kwanan.
Don Allah, Abban Mashkur... ka nemi izininta ka zo gare ni, kar na shiga wani hali."
Da ƙarfi ya bige hannunta da ke riƙe da bayan rigarsa, ya kwace kansa. Ya sake jefa mata wani mugun kallo, ya ja dogon tsaki, sannan ya nufi ƙofar fita.
Ta riƙe cikinta da ya dunƙule ya cure tamkar dutse.
"Mustapha... don Allah!"
Ta furta cikin kid'ima, ganin ya buɗe ƙofar ya fice ba tare da ya waiwayo ta ba.
Nan ta zube a ƙasa tana murƙususu, yayin da hawaye ke ta kwaranya suna wanke mata fuska.
Wani irin ɗaci da baƙin ciki ne suka haɗu suka tokare mata zuciya.
Ta yi matuƙar nadamar nemansa da ta yi, musamman yadda ya wulaƙanta ta.
Sai dai duk da haka, ta san ba ta da wata mafita face ta neme shi, domin halin da take ciki ya fi ƙarfin juriya.
Tun bayan da cikinta ya fara tsufa ne ta fara fuskantar wannan matsananciyar sha'awa.
Sai dai ta yau ta zarce duk waɗanda suka gabata.
Ta kasa jurewa har ta kai ga nemansa da kanta, amma duk da haka ya ƙi taimaka mata, ya juya ya bar ta cikin wannan hali.
Ta fashe da kuka, tana ta ambaton sunan Allah, tana roƙonsa Ya yaye mata abin da take ji.
Ta daɗe tana fama da wannan azabar kafin daga bisani ta samu ɗan sassauci.
Da ƙyar ta miƙe, ta je ta ɗauro alwala.
Sannan ta shafe ragowar daren cikin sallah da addu'a, tana roƙon Allah Ya yaye mata wannan sabon ƙalubalen da ya shigo rayuwarta.
Kafin daga bisani barci mai daɗi ya yi nasarar ɗaukarta........!
Mommyn Twins ce