Hs 29
by @legendspen
_Page 29_
2Ɗagowa Bhatool ta yi ta kalli Yaya karima, Yaya karima ta ɗaga ma ta kai sanan ta ce. "Bhatool ita ta siya, namiji da kike ganinsa Sha-sha-sha ne, duk wani fushinsa da fiffigarshi ba abakim komai ba ne, duk ta yadda kika raini shi ta haka zai ta shi, a yanzu Senate kamar ƙaramin yaro jariri ne a wajenki, yadda kika raini shi haka zai ta shi, idan kin sa ba masa da mutuntawa da girmamawa da soyayyaa da fahimtar juna to haka zai ta shi, idan akasin haka to haka zai ta shi, mussaman ke mijinki dake shiru-shiru ki riƙe shi da mutunci da karramawa, ki nuna hallarci ga mahaifiyarsa da ta zage ta tsaya tsayin daka a kanki." Kuka Bhatool ta ci gaba da yi, Anty Abu ta ce. "Ya kamata kema kiyi mata nasiha, domin duk abinda zaki faɗa mata babu shida muhimmancin da ya kai wanan lokaci." Kallon Bhatool Umma ta yi sanan ta ce. "Duk wanda ya ci riba a rayuwar duniya, to ya haɗa da hakuri, Bhatool ki je Allah yabada sa'a, Allah ya albarkaci rayuwar aurenki da zuri'a ta gari." Ummah ta faɗa tana mikewa zuwa sif ɗinta. "Ga wanan alkur'ani ne da azkhar, a kowannw yanayi kidinga tunawa da Allah, a yanayin farin ciki ko na akasin sa, ki tuna shime ya jarabce ki da wanan, kuma zai iya canja shi a ko yaushe." Kuka mai ƙarfi ne ya ƙwacewa Bhatool, ta shiga yinsa babu ƙaƙƙautawa, babu mai rarrashin ta ko hanata, domin Yaya karima ma nata kukan take, haka Umma ma ta shiga matse na ta hawayen, ta shiga Anty abu ta yi ta basu wajen.
Sai da suka dau kusan mintu goma a haka sanan Umma ta ce. "Ya isa haka, Allah ya yi muku albarka." Tasowa Bhatool ta yi ta rungume Ummah, Yaya karima ma ta taso suka haɗe abunsu suna kuka, can sai ga Abdul nan da ta shi ƙwalal, sai da suka dau mintuna suna kukan sanan aka fara shirin tafiya da Bhatool.
Tun Bhatool na kuka ƙasa-ƙasa, har ta fara da ƙarfi. "Wayyo Umma, wayyo Allah na, Ummah ni bazan tafi ba." Irin ihu da take yi kenan, kowa sai da ya tausayawa Bhatool amma a haka aka fice da ita xuwa gidan Mom, sai da suka kusa isa sanan ta samu ta yi shiru, sai dai tana ta sauke ajiya zuciya da shasheƙar kuka. A haka suka ƙarasa gidan bakin ta shiru, babu abinda take sai faman tunanin Ummanta.
Wata sabuwar hidimar suka tarar gidan Mom, tarba ta mutunci a ka yi musu, sanan daga baya ƙawayen Mom suka zo suna ta yi Bhatool kyauta, kowace da abinda take bayarwa. Sai wajen ƙarfe takwas da rabi aka huce da Bhatool gidan mijinta da ke G.R.A.
Gida iya ganinka ya tsaru matuƙa, duk da bai cika wani girma ba, amma kana ganin kasan namasu hannu da shuni ne. Bhatool bata ta shi kuka ba sai lokacin da ta ga kowa zai tafo yabarta har da Yaya Karima, kuka sosai take kamar wacce ke tsoron azo a sace ta ko yankata, daƙyar da sinɗin goshi aka tafi aka barta.
Tana zaune tana fama shasheƙar kuka Senate ya shigo, shi kaɗai babu abokansa dan duk sun koma daga gate, wani irin bugu yaji zuciyarsa na yi kamar ranar farko da ya fara ganin Bhatool, sai ya ji ya zama asalin Senate ɗin sa mai rauni da tausayi akan al'amuran Bhatool, wata sabuwar soyayyarsa tana shigarsa a haka ya shigo cikin ɗakin, Bhatool tsoro ya gama cika ta, mussaman da ta ji ana shigowa a hankali kuma tasan ango dai ba zai taɓa shigowa shi kaɗai ba sai da gayya. Da gudu ta saklo daga kan gadon ta rungumeshi tana kuka, a hankali ya kai hannu shima ya rungumota. Sai dai ya bari ra ɗauki lokaci tana kukan sanan ya fara rarrashinta, da ƙyar ya samu ta yi shiru..................................................................................................... toopa, Allah ya kyauta.
~~~~~Washe gari.
Ƙarar ƙararrawar bakin ƙofar bangaren da suke ce ta tashi Senate, a hankali ya buɗe idonsa ya sauke su kan Bhatool da ta cukwikwiyeshi, ya kusa minti biyar yana kallon kyakyawar fuskarta, kafin ya xare jikinsa a hankali ya miƙe. "Ina zaka?." Ta faɗa cikin muryar bacci, juyowa ya yi ya kalleta idanunta a rufe. "Naji ana knocking." Ba ta ce komai ba shima ya fice, mai gadinsu ne riƙe da ƙatoton kwandon abinci. "Ranka ya daɗe gashi."
"Musa ya zaga dinga mana bugu da sassafe haka?."
"Ranka ya daɗe, bana so abinci ya yi sanyi ne, naga an kusa awa biyar da kawo shi ne."
"Ƙarfe nawa yanzu." Senate ya tambayeshi, wayarsa ya danna sanan ya ce. "Sha biyu da kwata."
"You're not serious." Senate ya faɗa tare da shigewa ciki, a ran shi ya na cewa. "Garin da ko tara ba ta yi ba zaka ce wani 12:15." dawowa ya yi ya kalli sama yaga yadda rana ta fito tas, ba shiri ya koma ciki bayan ya ajiye kwandon ya shiga cikin ɗaki. "Wifey, ta shi rana ya yi." Buɗe idonta ta yi sanan ta ce. "Ƙarfe nawa ne?." "12:30." Ya amsa mata.
~~~~~~~Nyan'ya.
Tun daren jiya da yan kai amarya suka dawo ake ta kuzaza gidan Amarya, kowa yana faɗin albarkacin bakinsa yana yaba gidan. Haka har gari ya waye ana ta maimaita zancen, ita dai Umma addu'a take kowa ya gama shiri a rabu lafiya ba tare da wani sabon tashin hnakalin ba, Su Amrah da Jannah sake kwana sukayi gidansu Na'ima, sai yau da safe suka shigo su ka yi wa Umma Sallama bayan sun yi breakfast, sosai Umma ta yi mus godiya tare da fatan sauka lafiya. A hankali baki kowa ya gama shiri suka fara tafiya gidajensu, kafin karfe biyu na rana gida ya zama daga Umma sai Yaya karima, sai Abdul dake shigowa yana fita.
Umma da Yaya karima na zaune suna hira, bayan sun kammala duk wani aikace-aikacensu an mayarwa sa makwafta yan kwanuka da su ka shigo cikin hidimar biki. "Ummah shikenan yanzu sai ke ka ɗai, ni dai aganina Abdul kawai ya ƙara gyara gidannan, ya yi part ɗin shi daban ya zauna." Yaya karima ta faɗa. "Wallahi kam Karima, ni kaina duk naji wani iri da zarar kin tai shikenan." Umma bata ƙarashe maganar ba kira ya shigo wayarta, ganin lamba babu suna ya sa ta ɗaga tana faɗin. "Kowa na samu?."
"Hello Ummah." Muryar Bhatool ta ƙaraɗe kunnenta. "Na'am wake magana?." Umma ta faɗa a sigar zolaya. "Haba Umma, daga kaini jiya har kin manta dani, to 'yar da kika fi so ce." Dariya Umma ta yi sanan ta ce. "Ƴar da nafi so ai gata a kusa dani." Kuka Bhatool ta fara tana cewa. "Ai daman na san Umma mantawa zakiyi dani."
"Ke ni bana son shirme, ina mai gidan naki."
"Gashinan Umma, nabaki shi?."
"Na shiga uku, ke wai bazakiyi hankali ba ne?." Umma ta faɗa tana mamakin hali irin na Bhatool. "Umma to me na yi?."
"Bakomai ya aka yi ne?." Umma ta tambayeta. "Na kirane na gaishe ki, sanan naje yaushe zaki zo?."
"Ina hanya yanzu xan zo." Umma ta faɗa tana jan tsaki. "Dan Allah fa, me zan dafa miki?."
"Kai ni nagamu sa sha-sha-sha." Umma ta faɗa tana miƙawa Yaya Karima wayar, amsa ta yi sanan ta ce. "Amarya Amarya."
"Na'am Hajiya Yaya ya gida, ta cikin naki?."
"Wai ni auren nan shirme ya samiki ko me?." Shiru Bhatool ta yi, ita ba ta ga abuj faɗa ba amma sai faɗa suke, a yadda ta kwana da kewarnan tasu amma su kamar ma ba su fuskanci ba ta gidan ba. "Yaya ke yaushe zaki zo?." Ta faɗa a hankali. "Yau dai zan koma gida, bari mu gani zuwa satin sama."
"Kai! Yaya sai satin sama?, za fa muje Dubai a satin sama."
"Kafin ku tafi zan zo in sha Allah."
"To Allah yayarda, ina Abdul fa?."
"Yanzu ya fita raka su Anty Hanya."
"Allah sarki bara na kira shi." Bhatool ta faɗa, daga haka suka ɗan ƙara gaiswa ta kashe wayarta, Umma ce ta ce da Yaya Karima. "Haka fa, kowacce macw rayuwarta gajeriya ce a cikin gidansu, yanzu daga haka har za'asaba."
"Wallahi fa Umma, muma duk a haka mu ka saba." yaya Karima ta bawa Umma amsa. "Allah dai ya dauwamarmuku da zaman lafiya a cikin gidajenku."
"Amin ya Allah Umma."
~~~~ Bhatool kam suna kashe kiran Umma, Mom suka kira itama lokacin duk bakinta sun fara ta fiya, saura su Anty shuwa sa wayansu ƙawayenta na jiki. Bayan sun gaisa da ita suka fara kiran ƙawaye. Amrah kam tun cikin biki Maman Anas ta amshi lambarta, har wani daɗi Amrah ke ji dan tasan ƙila aure zata haɗa ta da Ɗanta ko ba Anas ba, domin ta fahimci Faruq ba saurayin aure bane, saurayin kashe kuɗi ne kuma ya ce da ita gobe zai koma ƙasar da ya fito, duk ta matso maman Anas ɗin ta kirata dan itace ta amshi lamvarta, amma da ita ma ta amshi tata tuni ta kirata ko bangajiya ne ta yi ma ta. Tana faman tunanin ne kiran Bhatool ya shigo, da fara'a ta ɗauka tana faɗin. "Amarya! amarya."
"Amrah, ya gida ya gajiyarku?." Bhatool ta faɗa. "Uhm, aike za a tambaya gajiya dan mu mun warware." Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. "Kuma ai akwai taku gajiyan, yaushe xaku shigo?."
"Ahaba dai Amarya, ai akwana biyu ko?." Amrah ta faɗa. "A'a gaskiyya kuzo dan Allah, zamuyi tafiya ne fa."
"Ina zaku?." Amrah ta tambaya. "Dubai." Bhatool ta ba ta amsa. "Aha lallai ne Amara, zamu zo kowa."
"Yawwa to sai kun zo, bara na kira Jannah, da Suhaima."
"Okay to shi ke nan." Daga haka Bhatool ta kashe wayar, ta kira Jannah daga nan ta kira Suhaima, ranta a ɓace da Jannah, wai dan ta ce mata zasu tafI Dubai shine zata ce wai ta dinga riƙw sirrinta, to me takw nufi da ita?.
Legendspen
***