Chapter 20
Zaune suke gaba ɗaya a kan babban dining table ɗin da ke tsakiyar wajen. Duk da kasancewar sun kammala cin abincin dare, babu wanda ya tashi, hatta Daddy, saboda tattaunawar da suke yi a kan maganar auren Fahad da za a yi a watan goma. Dukkansu sun yi shiru suna sauraron A’isha da ke bayanin yadda komai zai kasance.
Duk da tana jin abin da ake fada amma bata fahimtar su, saboda gaba daya hankalinta ba a kansu yake ba. Ta yi shiru tana binsu da idanu. Ya yinda zuciyarta da hankalinta suka yi nisa sosai cikin tunanin abin da ya faru ɗazu, maganar da Abdul ya faɗa ne ke ta mata yawo a kunne har yanzu.
Ta yaya ma zai ce haka? Menene dalilinsa na faɗin hakan kuma,?
Wannan tambayar ne ke ta ɗawainiya da zuciyarta da tunaninta tun ɗazu. Duk da ko kaɗan ba ta yadda da abin da ya faɗa ɗin ba. Abin da take son sani kawai shi ne dalilin da ya sa ya faɗi hakan.
Sosai ta kurawa fuskar Daddy da ke zaune a kujerar kusa da ita ido, a ƙoƙarinta na son gano ko abin da Abdul ya faɗa ɗin gaskiya ne ko kuma kawai ya faɗa ne saboda wata manufarsa. Duk da dai a karan kanta ta san ƙarya ne, amma haka dai zuciyarta ke ta ƙoƙarin tabbatar mata da hakan.
Sai dai duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana kallonsa, babu abin da ta iya ganewa. Fuskarsa na nan kamar yadda ta saba ganinsa. A koyaushe a haɗe ba za ka taɓa shaida yana cikin farin ciki ne ko ba...
Daddy, ganin Mammyn nasa ta takura masa ido tana kallonsa, ya sa ya yi ɗan murmushi tare da faɗin:
''Lafiya dai, Mammy na? Me ya faru? Kina son wani abu ne...?"
A hankali ta girgiza kai tana shagwaɓe fuska tare da turo baki gaba, kamar ƙaramar yarinyar da ke shirin yin kuka.
Ta ce,
''No, Daddy, babu komai. Just, ina son in san a ina kuka fara haɗuwa da Ammi and who fell in love first. You know, I want to be a writer and ina so na fara da labarin soyayyarku. Please, Daddy, don’t say no. Please, please.''
Ta ƙarashe maganar tana jijjiga hannunsa da ke cikin hannunta, yayinda idanunta ke kansa, a ƙoƙarinta na son fahimtar reaction ɗin da ke fuskarsa.
Yes, ta ga sanji ɗin. Amma ba abin da Abdul ya faɗa take gani ba. Duk da ita kanta ba ta san menene take gani ɗin ba. Wani irin Sadness ne da ya fi ƙarfin fahimtar ta. Hakan yasa ta kasa karantar komai daga kan fuskarsa.
Ta juya a hankali tana kallon Ammi da Daddyn ke kallo shima. Sai dai ga mamakinta bbu komai a kan fuskar Ammin sai murmushin da kallon daya zaka masa ka fahimci na yake ne, Amma ita ta kasa gane hakan.
“Please, Daddy, I just…”
Sautin faɗuwar cokali a kan plate da tsananin tari irin na wanda abu mai yaji ya ƙware masa, da suka fara tashi lokaci ɗaya daga bangaren Ummi, ne ya sa Mammy da ke magana yin tsit.
Gaba ɗayan jama’ar da ke falon suka tattara hankalinsu, suka mayar da kallonsu zuwa ga Ummi, wacce ke ta faman tari tamkar ranta zai yi sallama da gangar cikinta. Tari take yi sosai tana shafe maƙogwaronta, alamar yana mata zafi.
“Sorry, Ummi. Ga ruwa sha, sannu.”
Mammy da ke zaune kusa da ita ta miƙa mata ruwan sanyi da ke cikin glass cup ɗinta, ta faɗa mata a raunane, kamar za ta yi kuka saboda tausayin Ummin.
Gaba ɗaya hankulan jama’ar da ke falon ya tashi. Suka shiga jera mata sannu-sannu kamar sannun ne zai sa ta daina.
Duk cikin masu jera wa Ummi sannu-sannu, ban da Daddy, yana zaune yana kallonsu. Daga ƙarshe ma ya tattara hankalinsa gaba ɗaya kan wayarsa, tamkar ba ya wajen, bai ga abin da ke faruwa ba.
Babu wanda ya yi mamakin hakan a cikinsu saboda sun riga da sun san halinsa tun ba yau ba. Sai dai Mammy ba ta ji daɗin hakan ba. A ganinta, ya kamata ko sannu ne ya faɗa.
Ta juyo tana kallonsa a shagwaɓe, sai dai ganin hankalinsa na kan wayarsa yana latsawa tare da taɓe baki kamar yadda takan yi a duk lokacin da ta ji wani abu bai shafe ta ba, ya lumshe idonta.
Cikin rashin jin daɗin hakan, ta mayar da kallonta ga Ammi, wacce ta fi kowa ɗaga hankalinta.
Kallo ɗaya za ka mata ka gane tana cikin tashin hankali da ruɗewa. Sai faman jerawa ummin sannu take yi, yayinda Aunty A’isha ke shafe mata baya, har aka samu nasarar tarin ya tsaya.
Ganin tarin ya tsaya ya sa dukkansu suka sauke ajiyar zuciya tare da yin hamdala.
Mammy kam, miƙewa ta yi a hankali saboda tana da bukatar keɓewa ita kaɗai ta yi tunani sosai a kan abubuwa, musamman a kan maganar Abdul da ta sa a ranta sai ta hukunta shi a kanta. Duk da har yanzu son jin labarin na ranta, sai dai haka nan ta haƙura zuwa wani lokaci.
''I’m going Bye Daddy Bye Ammi and Ummi.''
Ta faɗa cikin muryar shagwaɓa da ta saba magana da shi irin ta sangartattun yaran masu kuɗi.
Umar da ke zaune kusa da matarsa ya kalleta ya ce:
''Har za ki yi bacci? It’s 11:00 p.m. fa, ke da ke bacci wajen 2.''
Sake shagwaɓe fuska ta yi kamar wacce ke shirin sakin kuka, tana mita cewa yau ta gaji sosai a Company.
Da sauri Fahad, da ke chatting da masoyiyarsa ya dago jin abin da ta ce, ya kalleta.
Cike da son ya kunnata ya ce
''Kai Mammy, ƙarya haram! Ke ne kika yi aiki? To wannan kam aikin me kika yi? Ke da ko zaman minti goma mai kyau ba ki yi a cikin Company ba, kika fita ganin gari…''
Ya ƙarashe maganar yana dariya.
Bubbuga ƙafa ta fara tana turo baki gaba.
''Yah Fahad mana…''
Ta kira sunansa cikin shagwaɓa, ya yinda shi da su Ummi da ta samu kanta yanzu ke mata dariya.
Ta sake shagwaɓe fuska zata yi magana. Sai dai kafin ta samu damar cewa wani abu, Daddy da ke zaune yana sauraron maganarsu ya dago kai da sauri, kamar wanda ya ji an yi saɓo.
Ya kalli Fahad da babbar muryarsa ya ce
''Come again, Fahad ban ji da kyau ba You said Mammy ba a Company ta zauna ba?”
Duk jama'ar falon dake dariya su ka tsaya cak.
Fahad ya kalli mahaifinsa, sannan ya ɗan kalli Mammy. A wannan karon, murmushin da ke fuskarsa ya fara bacewa saboda maganar daddyn.
Nan take fuskan Daddyn ya canza gaba ɗaya. Zuwa na tsananin bacin rai sosai.
Ya dawo da kallonsa gare ta, ta na tsaye ta yi fiki-fiki da ido tamkar wacce tawa sarki sharri.
''Ba a Company kika zauna ba? Ina kika je?.."
Cikin rashin ɗaukar maganarsa seriously, ta juyar da kanta zuwa ga Fahad.
Suna haɗa ido, ta gwabe fuska kamar za ta yi kuka, tare da karkatar da kai alamar, Ka ga abin da ka jawo ko?
Shima babu wani alamar damuwa ko tashin hankali a fuskarsa kamar yadda yake a fuskar Daddy. Ya kifkifta mata manyan idanunsa da ya gado su a wajen Ammi, alamar kada ta damu, zai ji da komai.
Cike da ƙwarin gwiwar yin bayani, ya fara magana a hankali, tamkar mai shirin lallashin ƙaramin yaro.
''Nothing big to worry about, Daddy. Ba wani waje mai…''
Cikin tsananin ɓacin rai, Daddy ya miƙe a zafafe ya katseshi da faɗin:
''Yi min shiru! Stupid kawai! A Najeriyar kake faɗa min nothing big to worry about? Kana hauka ne? Ko ka rasa tunanin ka ne da za ka barta ita kaɗai ta fita iyee?''
Muryarsa ya cika falon.
Fahad ya yi shiru a kan kujerar da yake zaune a kai kamar baya nan. Bai sake ɗaga kai ba.
Ammi ta ɗan motsa bakinta kamar za ta yi magana, sai kuma ta shi shuru tana kallonsu duk da tana da abun fadan amma tasan shurun tana shine mafi alheri a gare ta.
Ummi ma dai yi shiru ta yi bata yi magana ba, Haidar da Umar ne kawai masu ƙarfin halin fadin daddy kayi hakuri.
Ganin Fahad ɗin ya yi shiru hakan ya sake tunzura Daddy. Ya dinga bala’i ta inda yake shiga ba ta nan, ya ke fita ba kamar wanda ake yi wa wani babban laifin da yake ji a ransa, har duniya ya tashi ba zai yafe ba.
Su dai jama’ar da ke falon duk shiru suka yi saboda sanin hali. Aka ce hali ya fi sanin kama.
Fahad kuwa ya sunkuyar da kansa ƙasa, yana mamakin mahaifinsa. Duk da ya san ma'anar hakan, amma ganin yake kamar bai kai Daddy ya dinga daga murya har haka ba.
Ganin yadda Daddy ya ɗauki zafi sosai, kuma Ammi da Ummi babu wacce ta yi yunƙurin masa magana, yasa ta ƙara kusantarsa.
Ta san abin da Daddy nata ya fi tsana a duniya shi ne ganin hawaye a idanunta.
Hakan ya sa ta shagwaɓe fuska.
''Daddy…''
Ta kira shi a hankali.
Ya juyo yana kalleta.
Sai ga hawayen sharr.
Kamar an kunna famfo.
A take, fuskar Daddy ya ɗan sanja yana yi.
Duk da ba kukan gaskiya ta shirya yi a ranta ba, amma nan take idanunta suka yi ja. Muryarta na rawa ta shiga faɗin:
“Daddy please, Daddy stop shouting at him. Ba laifin shi ba ne he doesn’t know anything about it. Daddy I’m sorry, and I won’t do it again. Sannan Daddy, supermarket kawai na je na yi shopping. If you want to see kayan, suna cikin mota har yanzu. I will show you.”
Ta ƙarasa maganar tana tuttura baki tare da mummurje idonta, ita a dole tana kuka.
A hankali Daddy, da ke tsaye, duk da shekaru da suka ja, bai bari hakan ya hana shi russunawa ba. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yana kallon fuskarta cike da tsananin ƙaunar da iyaye ke yi wa ƴaƴansu. Ya kama hannunta, sannan cikin taushin murya ya ce.
''Okay my sweetheart but please don’t do it again, kin ji? Idan you want to go out, call me first or go with your bodyguard kin ji Mamana? Take care of yourself. Kar ki yarda da kowa Never trust anybody okay? Kin san bana son ganin hawaye a idanunki ko? To maza share ki je ki kwanta saboda ki tashi da wuri.”
Cikin tsananin ƙaunar mahaifinta, ta ce
''Okay, Daddy. Thank you''
Ta ɗan rungume shi tare da sumbatar hannunsa, sannan ta juya. Nan take suka haɗa ido da Fahad. Ta sakar masa murmushin rashin damuwa, kamar ba ita ne ta gama share hawaye ba.
Sai dai yadda ta ga yanayin Fahad ɗin ya sa ta ji wani iri a ranta. Jikinta a sanyaye, ta ɗaga wa sauran jama’ar da suke zazzune a falon shuru tamkar ba su nan
hannu alamar bye, sannan ta nufi ɗakinta.
A hankali Fahad, wanda a yanzu yake jin ba daɗi a ransa, ya ɗago kai yana kallon Daddy. Cikin murya raunana ya ce.
''My bad, Daddy. I’m sorry. Allah ya huce zuciyarka. In Sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba.''
Ko kallonsa Daddy bai yi ba. Ya juya fuu ya fita daga falon a fusace.
Haka nan su ma duk suka watse, kowa ya tafi ransa babu daɗi saboda ganin yadda Daddy yake a fusace. Duk da sun san shi mutum ne wanda kusan kullum ransa yake a ɓace, ba za ka taɓa iya gane ranar da yake cikin farin ciki ko aka sin hakan ba.
Yawanci idan ka samu ka ga murmushinsa, to albarkacin Mamm ka ci.
Tana shiga cikin katafaren ɗakinta, ta yi wurgi da wayarta kan teburin dake gefen gado sannan ta shige toilet. Ba ta daɗe ba ta fito, tsaf cikin fararen wando da rigar bacci masu tsananin kyau da ɗaukar ido.
Kwanciya ta yi tare da kashe fitilar ɗakin, ta barshi da hasken da ya dace da lokacin bacci. Ta miƙa hannunta kan teburin da ke gefen gadon, za ta ɗauki wayarta, sai kuma ta tsaya cak sakamakon tunawa da ta yi da wayarsa da ta fizge ɗazun daga hannun Ummul.